Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Auren Gargajiya A
Garin Kwatarkwashi (3)
NA
NURA SANI KOTORKOSHI
BABI NA BIYU
2.0 GABATARWA
Masana da
manazarta sun yi ayyuka masu É—imbin yawa a lokutta daban-daban masu
alaƙa da wannan aiki nawa. Saboda haka, a wannan
babi za a duba ayyukan da suka gabat masu alaƙa da wannan
aiki. Daga cikin ayyukan da za’a duba a kwai kundayen bincike, bugaggun
littattafai da kuma mujallu da muƙalu.
2.1 KUNDAYEN
BINCIKE
Akwai
kundayen bincike da dama masu alaƙa da wannan
aiki nawa. Akwai kundayen bincike kamar haka:
Al-hassan da
wasu (1982). A cikin littafinsu waÉ—annan marubuta sun tsara nasu littafi
ne a kan al’adun Hausawa, inda suka sanya littafin a cikin tsarin kanun
batutuwa kamar haka:
Duniyar
Hausawa da aure da haihuwa da Tarbiyya da sana’o’i da sarautu da muÆ™ami
da kuma ana Bukin duniya. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa
aikin ta fuskar aure. Bambancin dake tsakanin nawa aiki da nasu shi ne, nasu
aikin yana magana a kan ƙasar Hausa
baki É—aya, ya yin
da nawa aikin mai taken; Auren Gargajiya a Garin Kwatarkwashi.
Rabi’atu da
wasu (2009). Manazartan sun gudanar da aikinsu ne a kan ma’anar kayan adon É—akin Hausawa
na gargajiya da tarihin samuwarsu da hanyoyin samar da su da nau’o’insu da
muhimamncinsu ga rayuwar Hausawa, wannan aiki yana da alaƙa da nawa
aikin ta fuskar auren gargajiya.
Bambancin
dake akwai tsakanin nawa aikin da nasu shi ne, nasu aikin yana bayani game da
nazari a kan kayan adon É—akin Hausawa na Gargajiya. In da ni
kuma nawa aikin yake magana a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.
Abdullahi da
Wani (2011) a cikin littafinsu sun yi bayani a kan ƙasar
Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsu da wannan bincike shi ne wannan bincike anyi
shi ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi
Dashi (2009).
Ya yi bayani a kan “Kan gida da ire-irensa a Æ™asar
Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsa da wannan bincike shi ne wannan bincike ana
yinsa ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.
Bala (2012).
Ya yi bayani a kan tasirin zamani a auren Maguzawan Kwatarkwashi. Dangantakar
aikinsa da wannan ana bayani ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi. A
nan shi kuwa ya yi bayani ne a kan tasirin zamani a auren Maguzuwan
Kwatarkwashi.
Abdullahi
(2008). Ya yi bayani a kan tsafe-tsafe a Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi. A
wannan bincike kuma ana magana ne a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.
Shi kuwa
Balarabe (2019) a Laccarsa ta aji. Masanin ya yi bayani a kan yadda Hausawa
suke gudanar da auratayya a tsakaninsu da kuma al’adodi da kasha-kashen
al’adodin da kuma hanyoyin samar da kayayyakin Bahaushe na gargajiya da
muhallin Hausawa da tufafin Hausawa da kayan sufurin Hausawa da yadda suke
aiwatar da sana’o’insu da kuma ire-iren addinansu na gargajya. Dangantakar
aikinsa da nawa aikin shi ne nawa yana bayani ne a kan auren gargajiya.
Aliyu,
(2010). Manazarcin ya yi ƙoƙari
wajen bayyana ma’anar zumunci, zumunci a jiya, zumunci a yau, da ire-iren
zumunci, sai dai bai taÉ“o É“angaren al’adun aure a Æ™asar
Kwatarkwashi ba. Wannan aiki yana da alaƙa da wannan
aiki ta fuskar al’adu; Bambancin dake tsakanin wannan aiki shi ne, na shi aiki
na magana ne a kan zumunci a jiya da yau, ya yin da wannan aiki ke magana a kan
aure.
Sulaiman da
wasu (2010). Marubutan sun yi ƙoƙri
wajen bayyana ma’anar zamantakewa a birni da Æ™uaye,
zamantakewa a jiya da zamantakewa a yau da sauransu, sai dai ba su yi magana a
kan al’adun aure ba. Wannan aikin nasu yana da alaÆ™a da wannan
aiki ta fuskar al’adu.
Bambancin
dake tsakanin nasu aiki da wannan shi ne, nasu aiki yana magana ne a kan
zamantakewa a ƙasar Hausa gaba ɗaya, yayin da
wannan aiki ya keɓanta ne a kan
al’adun aure a garin Kwatarkwashi.
2.2 BUGAGGUN
LITTATTAFAI
Akwai
bugaggun littattafai da dama masu alaƙa da wannan
aikin nawa. Daga ciki akwai littafin Alhassan da Wasu (1981) a cikin littafin.
Marubutan sun yi ƙoƙarin kawo
bayani game da aure da kashe-kashensa. Aikin yana da alaƙa da nawa
aikin domin ya shafi aure a ƙasar Hausa.
Bambanci da ke tsakanin nasu aikin da nawa aikin shi ne, nawa yana magana ne
kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi.
Yakasai
(2002) a littafinsa. Marubucin ya yi ƙoƙari
wajen bayyana aure a da da kuma yanayin zaman aure a yanzu, tare da ire-irensa,
sai dai bai taɓo wasu ɓangarori na
al’adu ba. Wannan aiki yana da alaÆ™a da nawa
aikin ta fuskar aure da kuma yanayin zaman aure. Bambancin da ke tsakanin
wannan aiki da nawa aiki shi ne, nawa aiki yana magana ne a kan auren gargajiya
a garin Kwatarkwashi, yayin da nasa aikin ke magana a kan aure da kuma yanayin
zaman aure.
NTI (2013) a
wani littafi da ta rubuta, ta taɓo zaman Hausawa kamar iyali da tsarin
sarautu, sai dai ba tayi magana a kan auren gargajiya ba. Wannan aikin yana da
alaÆ™a da nawa aikin ta fuskar al’adun. Bambancin
dake tsakaninsu shi ne, nawa aikin na magana ne a kan auren gargajiya, ya yin
da nata aikin ke magana a kan tsarin zaman Hausawa na iyali da sarautu baki É—aya.
Gusau (2012)
a littafinsa. Marubcuin ya yi ƙoƙari
ƙwarai da gaske, don haka kuma ya taɓo wasu
Bukukuwa da al’adun Hausawa, sai dai bai taÉ“o auren Gargajiya
ba. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa
aikin ta fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakanin nawa aikin da nasa aikin kuwa
shi ne; nasa aikin na magana ne a kan Bukukuwan Hausawa baki É—aya. Yayin da
nawa aikin kuwa ya keɓanta ne a kan auren gargajiya.
B.U.K (1981),
a littafinsa. Ya yi ƙoƙarin
bayayna ma’anar aure da muhimmancinsa da shugabanci a gida. Wannan aiki yana da
alaƙa da wannan aikin ta fuskar aure. Bambancin
dake tsakaninsa da nawa aikin shi ne; Nawa aikin bai tsaya kan aure da
muhimmancinsa kaɗai ba, ya taɓo ire-iren
aure da al’adun aure kamin gudanar da shi, ya yin da nata aikin ya tsaya ne a
kan rayuwar Hausawa ne kawai:
C.N.H.N
(1981), a wannan littafinta ta yi ƙoƙarin
bayyana ma’anar aure da muhimmancinsa da shugabanci a gida, wannan aikin yana
da alaÆ™a da nawa aikin ta fuskar al’ada. Bambancin
da ke tsakaninsa da wannan aiki shi ne; su sun yi magana ne a kan rayuwar,
HAUSAWA jimlace, a wannan kuwa ana nazari ne a kan auren gargajiya a garin
Kwatarkwashi.
Yahaya da
wasu (2001) a littafinsu, marubutan sun yi ƙoƙari
ƙwarai da gaske wajen kawo zamantakewa
tsakanin maƙwabta da shugabanni. Wannan aiki yana da alaƙa
da wannan aiki ta fuskar al’adu. Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, wannan aiki
yana magana ne a kan al’adun aure a garin Kwatarkwashi, ya yin da nasu aiki
yake magana a kan zamantakewa al’umma.
2.3 MUJALLU
DA MAƘALU
Akwai mujallu
da maƙalu da dama masu alaƙa da wannan
aiki kamar haka.
Dalijan
(2016), a maƙalarsa. Marubucin ya yi ƙoƙari
ƙwarai da gaske wajen bayani a kan zamantakewar
Hausawa ta fuskar iyali da tasirin iyali ga Hausawa da zamantakewar Hausawa a
zaman gandu. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa
aikin ta fuskar aure. Bambancin dake tsakaninsu shi ne. wannan aikin yana
magana ne a kan zamantakewar Hausawa gaba É—aya yayin da
wannan aikin ke magana a kan auren gargajiya.
Sadiya
(2018), a maƙalarta marubuciyar tayi bayani a kan Bukin
auren Hausawa a yau, wannan aiki yana da alaƙa da nawa
aikin ta fuskar Bukin auren Hausawa a yau. Bambancin dake tsakaninsu shi ne
wannan aikin yana magana ne a kan bukin auren Hausawa a yau, yayin da nawa
aikin ke bayani a kan auren gargajiya.
JoÉ—i (2010) a
wata maƙala ya yi bayani a kan bukin aure tsakanin
Kwatarkwasawa ya kawo yadda suke aiwatar da Bukin aurensu.
2.4 KAMMALAWA
An kammala wannan ba
bi ne, domin fito da abubuwan da aka tattauna a kai a cikin wannan babi kamar
haka; an yi bayani a kan bitar ayyukan da suka gabata, sannan kuma aka duba
kundayen bincike. Haka kuma an duba bugaggun littattafai. Bayan nan daga ƙarshe an duba mujallu
da maƙalu, duk a cikin wannan babi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.