Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.
Auren Gargajiya A
Garin Kwatarkwashi (4)
NA
NURA SANI KOTORKOSHI
BABI NA UKU
3.0 TAƘAITACCEN
TARIHIN MASARAUTAR KWATARWKASHI
Kwatkwarshi
gari ne mai daÉ—aÉ—É—en tarihin
asali da jaruntaka. An samu kafuwar kwatarkwashi a cikin ƙarni na goma
sha huÉ—u (14)
kimanin shekara É—ari shida da
goma sha É—aya (611) da
suka wuce (1,400 zuwa yau), sunan Kwatarkwashi dutse da ganuwa inda maiki ya
shahara, saboda yawan duwatsun da Allah ya albarkaci wurin da su. Garin
Kwatarkwashi ya yi iyaka ne da masarautar Mada daga gabas. A kudu maso gabas
kuma garin ya yi iyaka ne da masarautar Tsafe. Ta arewa kuwa garin ya yi iyaka
da masarautar Kaura Namoda. Har wayau garin ya yi iyaka da Gusau babban birnin
jahar Zamfara daga yamma.
Kasancewar
garin na kewaye da duwatsu masu ƙawatarwa,
wanda ya ba garin martaba da tsaro, haka kuma baƙi masu yawon
shaƙatawa sukan ziyarci garin domin ganarwa
idanunsu abubuwan sha’awa da mamaki.
Sunan
Kwatarkwashi ya samo asali ne daga wanda ya kafa Kwatarkwashi tun farko mai
suna (Mangul). Shi wannan bawan Allah ya yi ƙaura ne daga
Katsina a bisa ga sana’arsu ta harbi, lokacin sarkin Katsina kumiyo, da sunan
Mangul ya É“ata sanadiyar
kyautatawa da alherin da yakan kai wa Sarkin Katsina a cikin wani baho da ake
kira Kwatashi. Bisa haka ne, Sarkin Kwatarkwashi ya canza daga Kwatashi zuwa
Kwatarkwashi.
A cikin sana’arsu
ta harbi, sun fara zama ne ƙarƙashin
dutsin da ake cema kundun, cikin ƙasar Katsina,
wanda suka zauna har tsawon shekara huÉ—u daga nan suka yi
hijira zuwa Dungal ‘Dungal’ na nan gabas da Kwatarkwashi cikin yankin Gulubba
ta yanzu), sun yi zama na shekara uku daga nan sai suka isa wani wuri da ake
kira dukura (Dutsi mai daÉ—aÉ—É—en tarihi
wurin da Kwatarkwashi take a yanzu.
Kamar yadda
tarihi ya nuna zamansu a Dungai ya jawo jama’a suka yi ta karuwa har ya zamanto
wurin ya zama gari. A nan ne, jama’ar suka ga yadace su naÉ—a shugaba a
cikinsu. Duk da suke Maharba ne, an nuna Mungul (Kwatashi) yana sana’ar Koli,
sanin da aka yi mashi mai son zama lafiya ne da haba-haba da mutane da
jaruntaka, sai suka zaɓeshi ya zama shugabansu (Kuma Sarki).
Bayan sun
cimma matsaya ta ƙashin kansu a kan zaɓen Mangul a
matsayin Sarki sai suka yi tawaga zuwa Katsina domin gabatar da shi ga Sarkin
Katsina Kumayo tare da kyauta ta Kwatashi (Kwatashi wani abu ne da mata ke sa
kaya a ciki). Nan take Sarkin Katsina yaba Mangul Sarkin Kwatashi a Sanadiyar
wannan Kwatashi da aka zo mashi da shi.
Tun da aka
kafa Kwatarkwashi ba a taɓa cinta da yaƙi ba, saboda
Jaruntakar al’ummar mu da kuma kyakykyawan jagoranci da suka samu na
shugabanni. Duk da yawan kawo hari da Namoda da Banaga É—an Bature na
Morai suka kawo mata. Hasali ma dai lokacin mulkin mallaka, Kwatarkwashi ta yi
fice sosai inda har aka kai ga anajin tsoron auka mata ta hanyar hari,
tsangwama ko kwace, cikin wannan hari ne a cikin watan Juli na (1903) aka yi
arangama da wasu sojojin Turawan Mulkin Mallaka ƙarƙashin
(Captain Wallale Wright) inda suka sha kashi har daga baya aka ci Kwatarkwashi
tarar hwan talatin da biyar (35), a wannan faÉ—a da nasara
da Kwatarkwashi ta yi. Bayan rasuwar Kwatashi a shekara ta (1420) sai Gazara ya
zamo Sarkin Kwatarkwashi, wanda ya yi har na tsawon shekara 37 (1430 – 1469).
Bayan rasuwar
Kwatarkwashi Gazara (1469) sai sarautar ta koma ga Kwatarkwashi Mayaƙi
(Gemen Dodo), inda ya yi shekara talatin dai-dai yana sarauta (1470 – 1500).
Kwatarkwashi Mayaƙi ya samu wata matsala wadda tasa yabar
Sarauta ya koma gida Katsina.
Bayan
komawarsa Katsina ya taras da wani jarumi wanda ya fitini Katsina mai suna
Kuyafa, wannan magana ta kaiwa Sarkin Katsina, inda ya aika aka kira mayaƙi
Ɗanjaji daga bakinsa, kuma Mayaƙi
ya tabbatar mashi da wannan magana. Daga nan Sarki ya bashi abin da ya nema aka
fita fagen fama, Mayaƙi ya nuna
jaruntakarsa inda aka fafata kuma cikin yardar Allah ya zo da kan Kuyafa. Bayan
an samu nasara, Sarkin Katsina ya saka masa wato ya mayar da shi ga Sarautarshi
watau Kwatashi.
A nan ne Mayaƙi
ya nemi a kaishi Tsafe a matsayin Sarkin Tsafe na farko. Kuma wannan shi ne
dangantakar Tsafe da Kwatarkwashi. Babban abin sha’awa a nan shi ne tunanin faÉ—ar Sarkin
Katsina ya ta’allaÆ™a ne akan jaruntakar
mayaƙi ta kawo kan Kuyafa, da kuma tsoron karɓar Sarautar
Katsina daga hannunsu. Jin haka, suka ga ya dace a mayar da shi ga sarautarshi
ta Kwatarkwashi.
Samun nasarar
da Mayaƙi ya yi a Katsina da kuma kwazon Jaruntaka
daya nuna, da kuma dalilan da aka bayyana a sama, yasa mayaƙi
ya dawo gida, amma kasancewar ƙanensa ke
sarautar Kwatarkwashi a wancan lokaci watau Bita da ƙasari sai ya
wuce gaba inda wasu duwatsu suke inda ake kira tsafe a yau. Nan ya kafa nasa
jagoranci kuma shi ne ‘Yandoton Tsafe na farko, wannan shi ne dangantakar
Kwatarkwashi da Tsafe. Abdulkadir (2018) Tarihin Mai Martaba Sarkin
Kwatarkwashi, Alh. Ahmad Umar Mai Kwatarkwashi.
3.1 MA’ANAR
KALMAR KWATARKWASHI
Tarihi ya
nuna cewa daga cikin waÉ—annan mutane da aka faÉ—i a sama
akwai wani mutum mai girman jiki baƙi, ƙaƙƙarfa
wanda aka fi sani da suna “Kwatashi” to, wannan mutum kusan shi ne jagorancin
wannan ayari da suka taso. Bugu da ƙari ma daga
wannan sunan ne aka samu sunan da ake kiran wannan gari da shi a yanzu wato
Kwatarkwashi. Dantiye (2019).
3.2 KAFUWAR
GARIN KWATARKWASHI
Kamar yadda
aka sani cewa kowace ƙasa, haka kuma kowane
gari yana da tarihin kafuwarsa da irin ci gaban da ya samu, da irin mutanen da
suka fara zama a cikinsa. Haka ma garin Kwatarkwashi na da nasa tarihin, saboda
haka wannan shimfiÉ—a ce a kan tarihin garin Kwatarkwashi da
kafuwarsa.
Tun daga
farkon tarihin wannan gari an gano cewa mutanen da suka kafashi sun fito daga ƙasar
Katsina. A cewar wasu masana babban dalilin da ya rabo da waÉ—annan mutane
daga Katsina ya ƙunshi waɗansu muhimman
abubuwa da suka haɗa da ƙabilanci da
siyasa da bambancin addini da kuma rashin damuwa da ba’ayi da su a Æ™asar
da suka baro ba. Dantiye (2019).
3.3 ADDININ
GARGAJIYA
Tarihin
addinin waÉ—annan mutane
ya nuna cewa babban abun da suka mayar da hankali a kan bautawa su ne waÉ—ansu iskoki
guda uku watau Magiro da Kyauka da kuma Ɗanƙunƙurutu.
To amma duk
da haka shi wannan addinin nasu ya ƙunshi waɗansu abubuwa
da suka nuna yadda ake shigarsa da kuma hanyoyin bautarsu. Da farko dai shiga
wannan addini bai ƙunshi wani abu ba,
illa in mutum yana son shiga sai kurum ya raƙa bin sauran
mutane wato masu wannan addini zuwa wata kwama ta cikin dutsin Dukura wadda ake
cewa kwamar Wuliga. Ba a bin da suke yi sai shan giya da kuma yanke-yanke kamar
su kaji, awaki ko raguna musamman ma baƙaƙe
don baiwa Ɗanƙunƙurutu
jinni ya sha.
Bayan waÉ—annan abubuwa
da waÉ—annan addinai
suka ƙunsa, akwai kuma buki na shekara-shekara don
murnar kewayowar shekara dangane da kungiyar masu bautar kowane addini na
gargajiya da na faÉ—a a baya. Haka kuma shi wannan addini baya da
wani suna da aka laƙaba masa, amma masu
yinsa ana kiransu da Arna ko Maguzawan Kwatarkwashi. Dan Azumi (1992).
3.4 SANA’O’I
Kamar dai
yadda muka sani cewa duk inda al’umma ta taru, kuma har aka ce ta samu wurin
zama daram da gindinta to haƙiƙa
ita wannan al’umma ba za ta ji daÉ—in gudanar da sha’anin rayuwarta ba,
dole ne sai ta tanadi wata hanya domin neman abincinta
Saboda haka,
babbar sana’ar mutanen wannan gari ta kasance noma ga baki É—aya. Amma duk
da haka akwai waÉ—ansu dake yin
saƙa da jima da ire-iren kasuwanci baki ɗaya. Bala
Dawai Sankalawa (2019).
3.5 ZANEN
SUNA
Zanen sunan
waÉ—annan mutane
acan da ya bambanta da yadda muka san ana yinsa a yanzu. Dalili kuwa shi ne, a
yanzu ana bin Æ™a’idojin da addinin musulunci ya bayar, kafin
mutane su karɓi addinin
musulunci, suna bautar wasu iskoki ne guda uku wato Magiro da Kyauka da kuma Ɗanƙunƙurutu.
Don haka suna
bin Æ™a’idojin zanawa ‘ya’yansu suna ne dangane da
yadda suka tarar iyaye da kakanninsu suna yi game da É—abi’o’insu na
gargajiya. Kamar ga masu bautar Magiro da Kyauka zanen sunansu kusan ince duk É—aya ne; domin
su waÉ—annan mutane
ba suna yiwa ‘ya’yansu suna ba ne bayan kwana bakwai da haihuwa, wannan ko
alama ba haka bane. Ga tasu al’ada sukan tara fiye da yaro huÉ—u ko biyar a
raÉ—a masu suna
gaba É—aya.
Amma a nan ba
wai suna barin sai bayan kwana goma sha huÉ—u ba, sannan
a raÉ—a sunan ba,
ya danganta ne, yawan yaran da aka samu a wannan makon. Wato su waÉ—annan mutane
ba sukan raÉ—awa yaro É—aya suna ba,
kome tsawon lokaci, to, lallai sai sun kai huÉ—u ko biyar
har abin da ya wuce haka.
Idan kuwa
za’a raÉ—a wannan suna
akan ajiye ranar da za ayi, da lokaci ya Æ™aato duk ‘yan
uwansa maza da mata duk zasu haÉ—u ayi ta shaye-shaye na giya da kuma
yanke yanken kaji da awakai.
A wannan
lokaci ne bayan kakan yaron ya sha giya yayi tatil sai kurum a ji ya ce “Na
sanya wa yaron da wane ya Haifa suna Kaza” shi ke nan ta zauna babu mai ikon
canza masa wani suna.
Amma ga
al’adar masu É—aukar maiki
su nasu ba haka ba ne. Idan É—aya daga cikin matarsu ta haihu to
kafin a raÉ—a suna sai an
tabbatar cewa yaron baya da garwaye, wato sai an gane cewa ko wani namiji ya
takata bayan mijinta. Ko kuma wata hanya ta gane haka kuwa ita ce, sai a É—auki jinjirin
a buga shi a kan dutse, idan yaron ya liƙe a kan
dutsin kuwa a kwai garwaye to zai faÉ—o. Tun daga can wajen gwajin sai a
nufo uwar yaron a gaya mata jinjirin da ta Haifa É—an zuriyarsu
ne, idan kuwa ya faÉ—o sai a shaida mata ba cikin zuriyarsu yake
ba.
Daga nan ita
kanta matar mai haihuwar a saketa, ta fita daga gidan. Idan an tabbatar da yaro
ya zama nasu ne, sai bayan kwana goma sha huÉ—u, sannan a
shirya gagarumin shagali da shaye-shayen giya.
Su masu
wannan addinin yaro ne zai zanawa ɗansa suna, bayan ya sha giya ya ƙoshi,
sai kurum ya ce “sunan É—ana wane”. Bayan an gama shagali sai kowa ya
watse. Aminu (2008).
3.6 KACIYA
A zamanin da
Maguzawan wannan Æ™asa suna yiwa ‘ya ‘yansu maza kaciya a
lokacin da yaran suka shekara biyar ko bakwai. Su kan yi wannan kaciya a
lokacin huturu wato a lokacin É—ari.
Idan za ayi
wannan kaciya akan tara ‘yan unguwa É—aya ko gida É—aya ayi masu
gaba É—aya. Kamar
misali masu bin addinin Ɗanƙunƙurutu
da ÆŠaukar Maiki da Magiro kusan mataki É—aya suke bi,
idan za su yiwa ‘ya’yansu kaciya, su kan tara fiye da yara hamsin su yi masu
kaciya gaba É—aya.
Haka kuma
ranar da za a yi kaciya danginsu za su taru ashirya wani gagarumin buki, har da
makaÉ—a. Bayan
wannan kuma za a dafa giya da yanke-yanken kaji ayi ta sha, ana kuma rawa.
Dangi kuma za su dinga baiwa makaÉ—a da wanzamai kari da bacaka da kuÉ—i.
Bayan an yi
wa yara kaciya wanzame zai dinga zagayawa bayan ‘yan kwanaki kaÉ—an domin ya
duba yaran. In akwai wanda yake buƙatar wani
magani ya bashi. Haka zai tayi har yaran su warke. Idan sun warke sai wanzame
yasa musu ranar da zai zo ya yi masu wanka a sa musu bance ko kuma warki. To
wannan rana za a shirya wani buki, shi ne suke kira bukin fito.
Saboda haka,
a wannan buki za a yi tanadin abinci da giya wadda jama’a za su sha. Haka kuma
‘yan uwan yara za su yita tara wa yaran gudummawa kamar awaki da kaji, domin
ayi masu kiwo. A wannan rana ne za a salami shi wanzamen da ya yi wa yaran
kaciya.
Amma al’adar
masu bin addinin Kyauka ta bambanta da ta masu É—aukar maiki
da Magiro da kuma Ɗanƙunƙurutu,
domin su masu bin addinin Kyauka, Kyauka ne yake yiwa yaron kaciya, kuma sukan
tara kamar yara talatin a yi masu kaciya gaba É—aya.
Haka kuma
suma su kan dafa giya da kuma yanka kaji da awakai, domin baiwa jama’ar da suka
halarci wannan buki na kaciya. Wannan ita ce hanyar gargajiya ta yiwa yara
kaciya a ƙasar Kwatarkwashi. DAyyabu (2019).
3.7 KAMMALAWA
Kamar yadda
aka gani a cikin wannan babi an yi magana a kan, taƙaitaccen
tarihin masarautar Kwatarkwashi, inda mai bincike ya kawo ra’ayoyin wasu masana
daban- daban dangane da taƙaitaccen
tarihin masarautar Kwatarkwashi. Wannan ya nuna mana cewa sarauta kalma ce
babba mai Æ™ima da kuma mu’ujiza ga dukkan jinsi na
al’ummar duniya.
A gaba kuma
mai bincike ya yi bayanin ma’anar Kalmar kwatarkwashi. Mai bincike ya ci gaba
da yin bayani a kan yadda garin Kwatarkwashi ya samu kafuwa.
A gaba kuwa
mai bincike ya yi bayanin yadda Kwatarkwashi suke aiwatar da ire-iren addinansu
na gargajiya, domin gudanar da bautar su. A gaba kuma mai bincike ya yi bayani
a kan sana’o’in mutanen wannan gari na Kwatarkwashi iri daban-daban. A Æ™arshe
mai bincike ya yi bayanin irin yadda Kwatarkwasawa suke aiwatar da al’adunsu na
yiwa yara kaciya.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.