Ticker

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Auren Gargajiya A Garin Kwatarkwashi (5)

NA

NURA SANI KOTORKOSHI

Dakin amarya 

BABI NA HUƊU

4.0 MA’ANAR AURE

“Aure kana ba manya kashi ‘yan yara na ganin damarka” Da harshen Hausa a kwai hanyoyin guda huɗu da muke iya kiran Kalmar aure da su kamar haka: Ko dai muce “Aure ko amre ko Anre ko kuma Arme. Amma daga cikinsu wadda ta fi shahara kuma aka fi amincewa da ita a daidaitacciyar Hausa ita ce “Aure”.

 

Ga ra’ayoyin masana game da ma’anar aure kamar haka:

Yahaya da Wani (1992) sun ce “Aure wata hanya ce ta ƙulla zaman tare tsakanin namiji da mace ba tare da iyakancewa ba sai in mutuwa ta raba.

 

Alhassan da Wasu (1992) sun ce “Aure alaƙa ce ta halaccin zaman tare tsakanin namiji da mace.

 

Kwantagora (2010) ya ce “aure hanya ce ta rayuwa mai ɗorewa tsakanin namiji da mace, wadda aka gina ta hanyar shinfiɗaɗɗun ƙa’idoji”.

 

Bashir (2002) ya na cewa “Aure hanya ce dake haifar da zama mai ɗorewa tsakanin mace da mijinta bisa ga amincewar al’adun al’ummar da ma’aurata su ka fito”.

 

Bunza (2016) laccar aji ya ba da ma’anar aure da cewa “Aure shine haɗa wani abu da wani abu da suke daidaituwa da juna”.

Ta la’akari da ra’ayoyin masana a kan ma’anar aure. A kan iya cewa “Aure shi ne haɗuwar mutane biyu mabambanta jinsi, wato mace da namiji.

 

4.1 IRE-IREN AURE

Kamar yadda muka sani cewa aure yana da ire-ire ko kuma kashe-kashe kamar haka:

1.      Auren soyayya

2.      Auren tilas

3.      Auren Zumunta

4.      Auren Sadaka

5.      Auren Dibar Wuta

6.      Auren Dangana sanda

7.      Auren Dibar Haushi

8.      Auren Jeka da Kwarinka

9.      Auren Buta.

 

1.      Auren Soyayya: Aure ne wanda yaro ke ganin yarinya ya ce yana son ta da aure, ita kuma ta amince. Ko kuma ace “Aure ne da ake gina shi a kan tafarkin soyayya tsakanin saurayi da budurwa, wato ma’aurata da iyayensu da ‘yan uwansu kowa na muradin ganin anyi wannan auren”.

 

2.      Auren Tilas: A nan, yaro yakan ga yarinya ne, yace yana sonta da aure, amma bata amince ba. Iyayenta kuma su zartar da hukunci, watau su na so, ko suna ƙi. Har ma a kan ba da yarinya da wanda yake sa’an mahaifinta ne, ko sa’an kakanta alhali kuma ba ta so.

 

Kuma a kan nema wa yaro yarinya ba tare da yana so ba, saboda wata alaƙa ko yarjejeniya tsakanin iyayensu. Wannan ma auren tilas ne.

 

3.      Auen Zumunta: Wannan aure ne wanda a kan nema wa yaro yarinya daga cikin dangin uwa ko na uba, ba tare da an shawarci yaron ko yarinyar ba. Irin wannan aure, ana yin sa ne don ƙara danƙon zumunta tsakanin ‘yan uwa.

 

4.      Auren Sadaka: Shi kuma aure ne da ake bayar da yarinya ga wani saboda neman tubaraki, kamar irin sadakar da ake ba Malamai, almajiransu, musamman idan yarinya ta girma ba ta sami manemi da wuri ba. Ana kuma yin auren sadaka don gudun ka da yarinya ta jawowa iyayenta abin kunya. Wani Lokaci kuma idan mutum bai sami haihuwa da wuri ba, yakan yi alƙawarin cewa, zai ba da ɗiyarsa sadaka in ya samu.

 

5.      Auren Diɓa Wuta: Bayan an saki mace, saki uku, alhali kuwa matar tana son mijinta, shi ma yana son ta, dole sai taje ta auri wani mutum, kafin ta sami dammar komawa ga mijinta na farko. To, auren nan da ta yi da ƙudurin cewa za ta dawo wurin mijinta na da, wannan shi ne auren ɗibar wuta.

 

6.      Auren Dangana Sanda: Mutum yakan auri matar da ke zaune a gidan kanta. Sai ya zama ba za ta iya tasowa tazo gidansa ta zauna ba, saboda waɗansu dalilai. Haka shi ma ba zai iya zuwa gidanta ya zauna ba, sai dai ya riƙa zuwa can gidanta yana kwana.

Irin wannan aure abin da ya sa ake kiransa auren dangana- sanda, wai saboda mai gida yana dangane sandarsa a bakin ƙofar ɗakinta ne, kana ya shiga ya kwana.

 

7.      Auren Diban Haushi: Ana kuma kiransa auren ɗiban takaice ko auren ɗiban tsiwa, ko na kece raini da kashin ƙwarnafi. Idan matar mutum ta dame shi da fitina, yakan tashi ta kanas yaje ya auri wata mace mai kyau ko dukiya ko asali ko addini, fiye da wadda ke gidansa ko wadda ya saki.

Ana yin wannan aure don kawai fashe haushi ko ɗebe takaici ko don a gusar da walakanci da raini da tsiwace-tsiwace na ba gaira ba dalili.

 

8.      Auren Buta: To shi ma irin wannan aure yara basa yinsa sam-sam sai dai tsofaffi waɗanda ƙarfinsu ya ƙare, kuma babu sauran amfani. Sannan ga ‘ya’ya da jikoki har ma wani zubin da tattaɓa kunne.

To amma don neman lada da fatan a mutum da igiyar aure sai tsoho ya auri tsohuwa. Sannan kuma idan ‘ya’yan tsohuwar ko jikokinta suka yi ƙoƙarin hana ta auren sai ta ce masu “Ni dai ku barni, ko rowan alwala na dinga zuba masa a buta na sami lada” to saboda haka ake kiransa auren buta.

 

9.        Auren Jeka da Kwarinka:  Shi ma wannan aure, galibi mata ne manya kuma masu abin hannunsu suka fi yinsa. Saboda haka, ba za su iya tarewa gidan sabon mijinsu ba. Don haka sai su yi yarjejeniya cewa, mijin ne zai dinga bin ta a gidanta a ranar kwananta, ko kuma ya kasance namiji ne mai gidan kansa inda iyalinsa suke, sai ya auri wata matar. Saboda wadata ko don gudun fitina ko kuma don nuna fifiko da ƙauna sai ya ware mata gidanta daban a wata unguwar yana zuwa wurin a duk ranar kwananta.

 

To irin wannan aure dai shi ake kira jeka-da-kwarinka wato dai mutum ya isa gidan cikin shirin faɗa ko kare kai, saboda ko zai tarar da wani yaje wajen matar. Alhassan da Wasu (1982).

 

4.2 AUREN GARGAJIYA A KWATARKWASHI

Aure abu ne da kan fara tun a lokacin samartaka ko budurci. Samartaka wani matsayi ne a rayuwar kowanne ɗan’adam da yake faruwa bayan ƙurciya. Wato tun daga shekara goma sha takwas zuwa ashirin da biyar (18-25 years) ga namiji kenan.

 

Ga mace kuwa Budurci ko ‘yanmatanci yakan fara ne daga shekara goma zuwa sha biyar (10- 15yrs). Wadda take ƙasa da haka kuwa, ita ake kira ƙwaila. Haka kuma da namijin da macen duk wanda ya haura waɗannan shekaru a kan kira shi da suna Tuzuru ko Tuzuruwa.

 

Idan yaro ko yarinya suka girma, babu abin da iyayensu ke son ji da gani irin su yi aure shi kuwa aure baya yiwuwa sai akwai ma’aurata wato mace da namiji. Saboda haka neman aure ya kan fara ne daga lokacin da saurayi ya ga budurwar da yake so da kansa, ko aka nuna masa ita, ko ya ji labarinta.

 

Saboda haka wurare da dama saurayi kan iya ganin yarinyar da yake so. Wuraren sun haɗa da; Gidansu Yarinyar da gidajen yan uwa da gidan buki da dandali da kasuwa da wurin kalankuwa da wurin tallace-tallace da makarantar allo.

 

Idan yaro ya gamsu da yarinyar da yake so ɗaya daga waɗannan wurare da aka lissafa a sama, zai yi ƙoƙarin nuna mata yana sonta, ko dai kai tsaye ya sanar da ita, ko ta hanyar ƙawarta ko kuma ta tura abokinsa. Kuma da zarar saƙon ya isa gareta, sai fara’a da murmushi idan sun haɗu kuma ta nuna tana so.

 

Daga nan sai ya yi mata wata ‘yar kyauta da bata taka kara ta karya ba. Sannan kuma sai sanar da iyayen juna domin su haɗa baki. Da zarar sun amince sai a baiwa saurayi damar fara zance ko hira da ita don ƙara danƙon soyayya. Ana yin hira ne a gidansu budurwa, sai dai kuma a kan yi a kan hanya ko a dandali in an haɗu. Daga nan sai ayi wa yarinya abubuwa kamar haka:

a.      Toshi: Toshi a Hausa shi ne, wata kyauta ce da namiji kan yi wa macen da yake so, kyautar kuma komai girmanta kuma ko mai ƙanƙantatta. Amma kyautar da namiji kan yi wa mace ita ce toshi. Haka kuma komai mace ta baiwa namiji ba a kiransa toshi. Haka kuma ga al’ada toshi ya kasu kashi-kashi. Akwai toshi na gani ina so da kayan jinkira da Barka da shan ruwa da toshin sallah da makamantansu.

b.     Baiko: Abin da ake nufi da baiko shi ne alƙawarin da iyayen yarinya kan yi wa ɗaya daga cikin manemanta cewa an ba shi ita da aure. Akwai dalili da dama da sukan sanya a yi wa yarinya baiko kamar haka

Nafarko dai idan aurenta ya matso kusa.

Na biyu: kuwa idan masoya sun yi wa yarinyar yawa don a tsayar da saura.

Na’uku: don tsoron kada wani wanda ake ji wa kunya ya shigo domin nema wa wani nasa. Kuma da zarar an yi baiko a kan buƙaci sauran manema da su janye.

 

Kafin ayi wa budurwa baiko da wani, a mafi yawan lokuta sai an tambaye ta wanda ta fi so a cikin manemanta. Iyayen budurawa kan sha matuƙar wuya kafin ta bayyana wanda take so. Sau da dama mata ne kan tambayeta, kuma za a riƙa faɗar sunayen samarinta ne ɗaya bayan ɗaya tana girgiza kai, har sai an kai ga sunan wanda take so, sai ta yi shiru, to, wannan shi zai nuna cewa shi take so. Bayan ta fitar da saurayinta, sai iyayenta da saurayin su sa rana da lokaci da za’a yi baiko. Dagan an sai a raba goron gayyata. Idan ranar ta zo jama’a za su taru a gidansu yarinyar sai dai bisa ga al’ada shi saurayin ba ya halartar wajen.

 

Idan jama’a da Malamai da dangi da abokan arziki da maroƙa sun taru, sai waliyin yarinya, wato mai bayar da ita ya miƙe tsaye ya bayyana da bakinsa a gaban jama’a cewa; “Na yi alƙawarin bayar da auren wance ga wane. Amma ba tare da ambaton sadaki ba. A wani lokaci a kan yi baiko ne tare da sa ranar buki ko ɗaurin aure. Bayan an yi baiko ne ake sa ranar aure da kai kayan lefe da tsarance. Ibrahim (1982).

 

4.3 ZAMAN LALLE

Zaman lalle wani zama ne da amarya kan yi a gidan uban wankanta daga lokacin da ta shiga lalle har zuwa tarewa gidan angonta. Wannan zama ana yinsa ne a gidan ɗaya daga cikin dangin uba ko abokansa.

 

Domin su ne al’adar ta yarda su yi wankan yarsu ko su ba da ita ga wanda suka aminta ya wanke ta. Dangin uwa ko mahaifiyar amarya ba su da hurumin da za su wanki ‘yar yayarsu ko ƙanwarsu. Ana yinsa ne domin amarya ta ɗan saba da zaman aure. Wato dai zaman lalle kamar wani share fage ne na zaman aure ga amarya. Zaman ya kan ɗauki mako ɗaya ko biyu a wasu wurare.

 

a.      Asalin Zaman Lalle:

Mawuyacin abu ne a bugi ƙirji a ce ga asalin zaman lalle. Amma bisa hasashe ana iya cewa ya samo asali ne daga gudu da amarya ke yi idan lokacin aurenta ya ƙarato.

Amare sukan gudu su shiga uwa duniya wasu ma sai ya zama sanadin shiga barikinsu. Wasu kuwa idan sun gudu sukan tafi wajen ‘yan uwansu na nesa ko na kusa. Ganin irin yadda ake rasa wasu ‘ya ‘yan sai aka ga ya dace a fito da wata hanya mai ɗaukar hankali da za ta riƙe amare ta hana su gudu, idan lokacin aurensu ya ƙarato. To daga nan ne sai aka ɓullo da wannan al’ada ta zaman lalle. Kuma aka ƙawata ta ta hanyar samar da ‘yammatan zaman lalle irin su abokai da ‘yan ƙannen amarya da kuma bayi wato ‘yanmatan da suka zo daga ɓangaren miji domin su kula da amaryarsu, sannan kuma aka tanadar masu nau’o’in abinci iri-iri da zai ɗauke su tsawon lokacin zaman lalle.

b.     Ire-Iren Zaman Lalle:

Zaman lalle a ƙasar Hausa ya kasu zuwa gida biyu kamar haka:

i.                    Na Amarya: Wannan zama ne da ake yi da ya shafi amarya da ‘yanmatanta.

ii.                 Na Ango: Wannan zaman lalle ne da ake yi wa Ango. Shi ma yakan zauna tare da abokansa da kuma wata yarinya da ya zaɓa a matsayin abokiyarsa. Ita ma ta kan zo da ƙawayenta. Wani abin sha’awa a nan shi ne duk yarinyar da ta yi wa ango abuta, to a kasari takan zamo matarsa ta biyu.

 

c.       Wuri da lokacin da ake Yinsa 

Dangane da wuri, a iya cewa ana yin zaman lalle ne a gidan yayan uban amarya ko ƙanensa ko abokinsa uba na kusa ko na nesa. Ta fuskar lokaci kuwa, ana yin zaman lalle ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da bukukuwan aure a ƙasar Hausa, mafi yawa da kaka lokacin hunturu ko ɗari. Ana yinsa ne na tsawon mako guda ko mako biyu.

 

Domin idan za a sawa amarya lalle takan ɓoye a gidajen ƙawayenta. Haka kuma taubasanta maza za suci gaba da cigiyarta da lallensu kwaɓaɓɓe a hannu. Da zarar sun ganta sai su yaɓa mata shi a jiki. Shi ke nan sai su taru su ci gaba da kuka ita da ƙawayenta.

d.     Masu yin Zaman Lalle: Masu yin zaman lalle su ake kira da suna ‘yanmatan amarya, wato ‘yan mata ne zalla, su suke yin zaman lalle. Kuma sanin kowa ne a duk inda gungun ‘yanmatan ya haɗu to sai an haɗa da haƙuri. Wannan ma shi ya sa ake yi masu Karin magana mai cewa “Yan matan amarya masu abin a tanka”. ‘Yan matan zaman lalle sun kasu gida uku kamar haka .

i.                    Bayi: Su ne ‘yan matan da suka fito daga ɓangaren ango, kuma su suke yi wa amarya hidima da kula da ita, amarya ba ta raga masu, tana basu wahala iri daban-daban kamar dukansu da kalaba a lokacin da suke ƙoƙarin yi mata cuɗa. Ta kan karɓe masu abin ci baki ɗaya da dai sauran ɗabi’u na musgunawa.

ii.                  Abokai: Waɗannan su ne abokan amarya na kusa waɗanda aka tashi tare. Abokai iri-iri ne, domin akwai babbar abokiya da matskaiciya da ƙaramar abokiya. Su ma suna yiwa amarya hidima su ba ta abinci, su yi mata cuɗa, sai dai hidimar da suke yi wa amarya ba ta kai ta bayi ba.

iii.                Ƙanne: ‘Yan ƙannen amarya, sun haɗa da ɓangaren dangin uwa da na uba. Amarya ce ke gyara masu abincinsu ta yi masu komai, wani lokaci ma har ta kan ƙara masu da abincin da ta karɓa ga bayi.

e.      Kayan Zaman Lalle: Kayan zaman lalle sun ƙunshi, kayan abinci irin su; Gero, Dawa, da mai da gishiri da tabarmi da dai duk wani abu da amarya da ‘yammata ke buƙata a lokacin zaman lalle.

 

A kan kai kayan ne gidan uban wanka tun kafin amarya ta je. Kuma ana kawo su ne daga gidan miji. Kai har ma duk da kayan wankan amarya ake kaiwa kamar irin su tukunya da tasoshi da sauransu.

f.       Al’adun Zaman Lalle: Al’adun zaman lalle sun ƙunshi duk wasu ɗabi’u da al’adu da ake aiwatarwa a lokacin zaman lalle. Waɗannan al’adu sun haɗa da kamu da kwantar kai da abinci da cuɗa da tuƙe da wankan amarya da sauransu.

i.                    Kamu: Da zarar an shafa wa amarya lalle takan zauna ne a gidan babbar abokiyarta, ita za ta kula da ita daga litinin zuwa laraba. Daga nan ranar larba da yamma sai a tura matan uban wanka su tafi su zo da ita gidansa. Wanan shi ake kira kamu. Idan sun kamo ta za su biyo hanya da ita tare da ‘yanmatanta suna tafe suna kuka. Don su sanar da al’umma cewa ansa wance lalle ko amaryar wane ta shiga lalle.

ii.                  Kwantar Kai: Bayan an zo da amarya gidan wanka, sai babbar abokiyarta ta kwance mata kai, wato a banye kitson da take da shi, a wanke kan. Haka za ta ci gaba da zama har zuwa asabar sai a yi mata kitson zuwa gidan ango.

iii.                Abinci: Abinci na nufin duk wani nau’in abinci da ‘yan matan amarya ke yi don su ci da amaryarsu. Abincin da akan yi ya haɗa da fura da tuwo da ɗanwake ko ɗan gabda.

iv.                Cuɗa: Wannan wata al’ada ce, inda ake kwaɓa lalle da man shanu da turare don a riƙa cuɗa jikin amarya da shi. A kan yi cuɗa ne sau uku a wuni da safe da rana da yamma. Sai dai akan yi ta ne da ƙarfi, domin sai an kada amarya sannan a yi mata cuɗa. Babbar abokiya ce ke fara kama ta da kokawa, ita kuwa amarya tana bugun ta da makami ko kalaba. Da an ga abokiyar ta riƙe amarya sai sauran yammata su taimaka mata su kada ta. Daga nan sai a riƙa ɗebo lallen ana cuɗe mata jiki da shi.

v.                  Tuƙe: Wani abinci ne na musamman da ake yi wa amarya. Ana yinsa ne da wasa-wasa ko shinkafa da man shanu da garin magani sai a tuke a riƙa bata tana ci. Sai dai kafin a bata ta ci sai an ɗora mata a kan wasu gaɓoɓi na jikinta, ta cinye ba tare da ta taɓa da hannu ba. Kamar a kafaɗunta da gwiwar hannu da sauransu. Ana yin haka ne domin a cire mata duk wani makaru ko fitsara da take da ita. Tsohuwa ita take yi mata wannan abinci. Kuma ana yinsa sau ɗaya a wuni

vi.                Wankan Amarya: Wankan amarya wanka ne na musamman da ake yiwa amarya da rowan magani. Ana yinsa ne da dare. Tare da kiɗa da waƙa daga ‘yan matan amarya. Ana yinsa ne sau biyu, na farko ranar alhamis, na byu ranar Assabar, sai dai akan zuba mata rowan jiƙon ta tafi tayi da kanta. Abubuwan da ake yin jiƙon da su sun ƙunshi sayyun lalle da na jema da magaryar kura da duman kada da sauransu. Zainab (2017).

 

4.4 DAURIN AURE

Daurin aure shi ne babban ginshiƙi a duk matakan aure. Sauran kuwa ‘yan rakiya ne, domin daga shi babu sauran mai wata magana game da nema. Kafin bayyanar addinin musulunci, Hausawa kan taru ranar ɗaura aure maza da mata kaɗe-kaɗe da tulunan giya da kuma abinci.

 

Bayan an ci an sha sai a kawo akuya a matsayin sadaki, tare da gishiri da za a raba wa dangi a matsayin shaida. To; daga nan sai a ci gaba da kiɗa, saurayi da budurwa su fito suna taka rawa.

 

Ana cikin haka sai kawun budurwar ya kama gefen rigar saurayin sai ya ƙulle a gaban idon jama’a. sai ya ce; “Daga yau na ɗaura auren wane da wance, sai na ga ɗan babbar kazar da zai kwance shi”. Shi kenan aure ya tabbata sai a cigaba da bukin. Galibi an fi ɗaura auren Bazawara da dare na Budurwar kuwa da sassafe. Umar (1980).

 

4.5 AL’ADUN AURE KAFIN GUDANAR DA BUKI

Kwatarkwasawa suna bin irin al’adunsu na aure domin gudanar da buki da kuma tabbatar da tsarkin yarinya wadda za’a aura, ana yin haka ne domin gane yarinya bata san namiji ba lokacin gudanar da budurcinta. Maguzawan Kwatarkwashi suna da abubuwan da suke bautawa watau mutanen ɓoye, kuma sun yi imanin cewa mutanen ɓoye sun fi karfinsu shi yasa suke bauta masu. Ga dai irin abubuwan da ake bautawa kamar haka:

1.      Magiro

2.      Ɗanƙunƙurutu

3.      Kyauka

4.      Ɗaukar Maiki

 

Malam Sule Turɗe (1984).

1.      Magiro: A lokacin da ake gudanar da bukin masu addinin Magiro, idan ranar da za a kai yarinya ta zo sai a sami baƙin ɗan akuya da jan zakara da goran giya (wadda aka yi da dawa) a kai wurin wani dutse mai suna kwamar wuliga inda magero yake zaune. Idan safiya ta waye sai a koma wurin a gani, idan an tarar da ɗan zakaran da ɗan akuyar sun mutu, kuma babu goran giyar, to sai a ɗauka wannan budurwa ta kai budurcinta, don magiro ya duk shanye giyar da jinin. (Ma’ana ba ta taɓa sanin wani namiji ba).

 

Idan kuwa har aka tarar da ɗan akuyan da zakaran da ransu, kuma da goran giyar ba a shanye ba, to an san wannan budurwa bata kai budurcinta ba. (Ma’ana wani namiji ya santa kamin tayi aure). Don haka a ƙarshe magiro zai zo ya shanye mata jinni ta mutu. Shi ke nan buki ya watse.

2.      Ɗanƙunƙurutu: Idan za a kai ‘yar masu bin addinin Ɗanƙunƙurutu su kan fito da amarya a fili a kuma a za ta a kan turmi ayi mata wanka. Da zarar an kamala wanka za a dauki amarya zuwa ɗakin mijinta.

 

Idan aka kai yarinya ɗakinta, ga al’adar masu bautar Ɗanƙunƙurutu idan dare ya yi, bayan kowa ya yi barci, sai Ɗanƙunƙurutu ya zo a bayan ɗakin da aka kai yarinyar ya dinga kewayar ɗakin amarya yana zagayawa yana ƙugi. Saboda haka a wannan dare babu wanda ke fitowa ko fitsari. Idan yarinyar ta san maza ko ta ƙofar gidan Ɗanƙunƙurutu ba zai bi ba, balanta na ma har ya kewaya ɗakinta.

 

3.       Kyauka: Al’adun masu bin addinin kyauka sun haɗa har da yanka bakin sa, haka kuma da zakara domin a ba Kyauka ya sha jinni. Alokacin aure su kan yi fiye da kwana goma sha huɗu, suna wasa da Kyauka.

Kyauka shi ne wankan amare ko guda nawa ne, kuma ba ana nufin a ɗebi ruwa ayi masu wanka ba. Sai dai kyauka ya zo ya rufe su da baza, wadda take zaman makwafin rigarsa ta tsafi.

4.      Daukar Maiki: Maiki sunan wani tsuntsu ne wanda ke zaune a kan Dukura, wato ƙaton dutsen nan na garin Kwatarkwashi. Shi wannan tsuntsu ana samun mai shekara ɗari biyar ko dubu ɗaya kai har ma fiye da dubu ɗaya.

Al’adun masu ɗaukar maiki dangane da gabatar da ɗaurin aurensu sun haɗa da dafa giya a zuba tulu-tulu tare da shimfiɗa inda za a zauna don ɗaurin aure. Da mutane sun hallara sai kawai a ci gaba da shan giya. Ana nan sai kaji uban ɗiya yace “na bada iri gidan wane” shi ke nan aure ya tabbata har abada. Ranar da za a kai amarya dole ne sai ango ya hau dutsen Kwatarwkashi ya ɗauko maiki, idan kuwa har bai ɗauko ba to babu aure a tsakaninsu. Malam Sule Turɗe (1984).

 

4.6 AL’ADUN AURE LOKACI DA BAYAN MUTUWARSA A TSAKANIN KWATARKWASAWA

Al’adun aure suna da yawa, kaɗan daga cikinsu, wannan babi za zo dasu.

i.                    Yaji: Kamar yadda muka sani cewa a tsakanin ma’aurata saɓani yakan shiga ko kuma rashin jittuwa. Idan kuwa har irin wannan ya auku, kuma ya zamana wannan saɓani ya bunƙasa a tsakanin mata da miji, to abin da ka iya faruwa shi ne, yaji.

Saboda haka a can zamanin da irin wannan rashin jittuwa ko kuma saɓani yakan auku a tsakanin mutanen Kwatarkwashi. Idan kuwa har irin wannan ta faru a tsakanin mata da miji kuma har ya zamana sun kasa sasanta wannan al’amari a tsakaninsu, sai kurum matar tayi fushi ta tafi gidansu. Wannan shi ake cewa yaji.

ii.                  Biko: Bayan da mata tayi yaji zuwa gidan iyayenta, kuma ya zamana an sami lokaci mai tsawo, iyayenta basu mayar da ita ba. Sai daga gidan miji a samu waɗansu tsofaffi su tafi gidansu yarinya domin a samu sasantawa a tsakanin ma’auratan.

Idan tsofaffin da aka tura daga gidan miji sun tafi sai su nemi iyayen ita yarinyar ko kuma waɗansu muƙarrabanta, su zauna ayi binciken dalilin yin wannan yajin nata, domin a fahimci ko laifin mijin ne ko kuma laifin matar ne.

A wannan lokaci idan har ya zama da cewa laifin mijin ne to, sai iyayensa suyi masa faɗa ya daina yi wa matarsa irin wannan laifi, idan kuwa laifin matar ne ita ma iyayenta za su yi mata faɗa ta daina irin wannan laifin.

 

Bayan wannan kuma sai waɗannan, tsofaffi da aka turo domin sasanta wannan rikici su ba yarinyar haƙuri; su kuma nemi yarda daga iyayenta domin ta koma a gidan mijinta. Wannan shi ake cewa biko.

iii.                Saki: Kamar yadda na bayyana a baya da cewa; mata takan yi yaji ko kuma fushi idan wani saɓani ya auku a tsakaninsu. Haka kuma na bayyana da cewa idan har irin wannan ya auku, to a kan tura waɗansu tsofaffi daga gidan miji zuwa gidan iyayen yarinya domin sasanta wannan matsala, wato a nemo biko domin yarinya ta dawo gidan mijinta.

 

Idan kuwa bokon da aka yi na yarinyar, bai sa sun daidaitaba, to, abin da zai iya aukuwa kuma shi ne saki. Ko da yake yanayin saki a tsakanin ma’aurata a ƙasar Kwatarkwashi a wancan lokaci ya bambanta da yadda ake gudanar da shi a yanzu.

A wancan lokaci namiji ya kan saki matarsa ko kuma ita matar ta saki miji. Wato a nan idan mata ta gudu ta bar mijinta, ta koma wurin wani to, ta sake shi ke nan. Idan kuwa mijin zai saki matarsa sai kurum ya koreta, haka kuma dole sai ta biya shi duk abin da ta san ta ci nasa.

iv.                Iddah: A wancan lokaci idan aure ya mutu, to babu ruwan Kwatarkwasawa da yin idda. Wato da zarar dai mata ta biya mijin da ta fito gareshi, duk abin da ta san ya kashe a lokacin aurenta to sai tayi wani aure. Ko da kuwa ranar da auren ya mutu ne, saboda haka yanayin aure a tsakanin Kwatarkwasawa a wancan lokaci babu ruwansu da yin idda.

v.                  Sake Wani Aure: A wancan lokaci kamar yadda na bayyana a baya cewa, idan aure ya mutu, a tsakanin Kwatarkwasawa to babu ruwansu da yin iddah. Da zarar aure ya mutu, idan matar bata samu wani miji ba da wuri sai ta shiga zawarci. Saboda haka, a wannan lokaci zawarawa za su yi ta kai mata ziyara. A wani lokaci har takan kwana a ɗakin wani bazawari ko kuma shi ya zo ya kwana a gidansu.

 

Idan ta fitar da wanda take so daga cikin zawarawan sai a yi shirin ɗaurin aure da buki. Domin na faɗa da cewa a wannan lokaci babu ruwansu da yin iddah. Idan bazawara ta yi aure duk lokacin da ta haihu a ɗakin mijin ta abin da ta Haifa nasa ne.

 

Ba za a yi tunanin ko, ta zo da cikin ba, domin a baiwa mijin da ta aura kafin wannan ɗan ba. Watau ko da sabon mijin ba shi ya yi cikin ba ya samu ribar aure kenan. Ɗan Azumi (1992).

 

4.7 KAMMALAWA

An kammala wannan aiki ne, wanda ya ƙunshi wannan babi, wanda ya fara da ma’anar aure, in da aka yi bayanin ma’anar aure daga bayanin magabata.

 

Bayan wannan kuma an tsunduma ka cukan wurin yin bayani, ɗaya bayan ɗaya a kan ire-iren aure. Daga nan kuma sai aka ci gaba da yin bayani a kan auren gargajiya a garin Kwatarkwashi. Haka kuma a ka ci gaba da bayani game da zaman lalle da kuma abin da zaman lalle ya ƙunsa.

 

Sai kuma aka yi bayanin yadda ake ɗaurin aure. Daga nan kuma sai a yi bayani a kan al’adun aure kafin gudanar da bukukuwa a tsakanin Kwatarkwasawa. Kuma an ci gaba da zayyana al’adun aure lokaci da bayan mutuwarsa a tsakanin Kwatarkwasawa.

Post a Comment

0 Comments