Bayani A Kan Wasu Abubuwa Da Suke Faruwa Ga Dafi A Hausa

    Most of the works on the aspect of Hausa language are descriptive. Theoretical analysis is rare. For this reason, the article intended to look at some post syntactic operations during word formation in Hausa language with emphasis on affixes. These post syntactic operations include: Fusion, fission, impoverishment, morphological merger, linearization, ornamentation, syncretism, competition and blocking, allomorphy and productivity. The topics will be discussed from Distributed morphology point of view as explained in details Halle & Marantz (1993, 1994), Halle (1997), Marantz (1997), Embick (2010, 2015).

    Dafi

    Bayani A Kan Wasu Abubuwa Da Suke Faruwa Ga ÆŠafi A Hausa

    Daga

    Isah Abdullahi Muhammad (Ph.D)
    Department of Nigerian Languages,
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. Nigeria
    (+234) 07037484144

    &

    Muhammad Mustapha Umar (Ph.D)
    Department Of Nigerian Languages,
    Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. Nigeria
    (+234) 08065466400

     

    1.0       Gabatarwa

    A nazarin Æ™irar kalma babu abin da ya fi ban sha’awa da burgewa, kamar ‘ÆŠafi’. WataÆ™ila, wannan ya sa Spencer (1991:14) ya yi wannan furuci cewa “

    “Affixation is morphology par excellence’ ma’ana:

    ÆŠafi madara ce ta ilimin Æ™irar kalma mai ban sha’awa”.

    Duk wanda yake son nazarin ɗafi (a fahintar wannan takarda) akwai buƙatar ya lura da waɗannan abubuwa biyar, su ne:

    a)      Ma’anar É—afi a harshen da ake nazari

    b)     Nau’o’insa

    c)      Yadda ake samar da É—afin.

    d)     Abubuwan da suke faruwa ga É—afi.

    e)      AlaÆ™arsa da mai masaukinsa wato ‘saiwa’.

    Daga cikin abubuwan da suke faruwa wajen samar da É—afi (wanda shi ne taken takarda) akwai:

    a)      ÆŠayantawa (fusion)

    b)     Biyuntawa (fission)

    c)      Shafewar ma’ana (Impoverishment)

    d)     Ƙulli na Æ™irar kalma (Morphological merger) da Jerantawa (Linearization)

    e)      Ƙarin Æ™wayar ma’ana (ornamentation)

    f)       Sajewa (syncretism)

    g)     Gasa da shingewa(competition& blocking)

    h)     Jirwayen tsarin sauti (allomorphy)

    i)       Yalwa (productivity).

    Duk waÉ—annan abubuwa ne da suke faruwa bayan tsarin ginin jumla ya Æ™are aikinsa (postsyntactic operations). A taÆ™aice, a wannan takarda za a bisu É—aya bayan É—aya tare da kawo ma’anar kowannensu da kuma misalai. An raba takardar zuwa waÉ—annan sassa: (a) 1.0 gabatarwa da (b) 2.0 Bayani a kan abubuwan da suke faruwa ga É—afi a Hausa da (c) 3.0 kammalawa da (d) Manazarta.

    2.0       Abubuwan Da Suke Faruwa Ga ÆŠafi A Hausa[1]

    2.1       Ma’anar ÆŠafi A Hausa

                ÆŠafi asali ‘yantacciyar Æ™wayar ma’ana ce mai aiki irin na nahawu, wadda sai daga baya ne take bayyana a zahiri ko a baÉ—ini a matsayin turkakkiyar Æ™wayar kalma wadda ba saiwa ba, kuma wadda kuma da ake É—afawa a wani amintaccen muhalli na turken kalma (Saiwa ko kalma). Ana É—afa É—afi ne, domin ajinta saiwa ko sauya ajin ko kuma, don yin wani Æ™arin bayani irin na nahawu,sannan É—afi, yakan kasance jagora a cikin kalma.

    ÆŠafi a Hausa ya kasu gida biyu.

     

    a) ÆŠafi ajintau: ÆŠafi ajintau É—afi ne wanda yake nuna ajin saiwar kalma, ko kuma ya sauya ajin kalma. Misali:

     

    (1) i- kaamaawaa

     

    Kalmar ‘kaamaawaa’ tana Æ™unshe ne da sakakkiyar saiwa (Ö[2]Category-neutral) da kuma ajintai guda biyu na aikatau da na suna bayan aikatau (vp & np categorizers). Sannan su ne nau’in É—afiajintau mai sauÆ™i. Domin a nan bayan aikin ajintawar ba wani aiki da suke yi. Amma idan aka ce ‘gidaa’, tana Æ™unshe da saiwa É—aya ‘Ögid-‘ da É—afin ‘-aa’[3] wanda yake aikin nuna ajin suna da Æ™arin fayyace jinsin namiji da kuma nuna adadin tilo. Wannan shi ne ajintau mai sarÆ™aÆ™iya.

     

    b) Ɗafi ba-ajintau:Ya ƙunshi ɗafi mai nuna: mallaka da nasaba da nuna muhallin sifa da abin da ya gabata da lokaci da taƙi. Misali:

     

    (2) i- riigarsa

    ii- huular ƙarfee

    ii- farar huulaa

    iv- riigar

    v- yaa tafi

     

                Bayan haka, abubuwan da suke faruwa lokacin samar da É—afi da bayan samar da shi, su ne za a tattauna a sashe na gaba, wato 2.2

    2.2 ÆŠayantawa (Fusion)

                Asalin kalmar ‘É—ayantawa’ daga ‘É—aya’ ne, sai aka É—auko sakakkiyar saiwarta ‘É—ay-‘ aka É—afa É—ofanen ‘-anta’ da ‘-wa’, sai aka sami ‘É—ayantawa’ wato dai suna ne ‘É—an aikatau’. Da ingilishi É—ayantawa shi ne ‘fusion’.

    Halle& Marantz (1993:116) sun ba da ma’anarta kamar haka:

    “ Fusion takes two terminal nodes that are sisters under a single category nodes and fuses them into a single terminal node”

    Fassara:

    ÆŠayantawa yana É—aukar gundarin Æ™wayoyin ma’ana biyu waÉ—anda suke ‘yan uwa ne Æ™arÆ™ashin aji É—aya, sai a Æ™ulla su a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya kuma Æ™wayar kalma É—aya”. Muhammad (2016:5) ya bayyana ma’anarsa kamar haka:

    “ Fusion simply fuses features into single terminal node”.

    Fassara: “Cikin sauÆ™i, abin da ake kira É—ayantawa, Æ™ulli ne da ake yi na Æ™wayoyin ma’ana cikin Æ™wayar ma’ana É—aya”.

     Saboda haka,‘É—ayantawa’tana nufin inda harshe ya É—auko gundarin ma’anoni daban-daban waÉ—anda suke iya zama tare sai a Æ™ulla su a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya[4], sai kuma a cusa su cikin tubali É—aya a matsayin Æ™wayar kalma É—aya[5]. Misali

    (3)‘wàtàà’

    A misali na (3), kalma ce ‘suna’ ‘tilo’ ‘namiji’. An zaÉ“o suna daga É“angaren azuzuwan kalmomi, ‘tilo’ kuma daga ‘adadi’ sai kuma ‘namiji’ da aka zaÉ“o daga ‘jinsi’. Gaba É—ayansu aka Æ™ulla su wuri É—aya a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya kuma cikin Æ™wayar kalma a matsayin É—afi É—aya wato ‘-àà’. Wannan shi ne É—ayantawa. Sai kuma shi É—afin ya zaÉ“o saiwar ‘Öwat’ a matsayin mai yin Æ™arin bayani na É—afin. Wannan ya nuna Hausa tana zaÉ“o gundarin ma’ana na ajintau (suna ko sifa) ta haÉ—a da adadi (tilo ko jam’i) da kuma jinsi (namiji ko tamata) ta hanyar Æ™ulla su wuri É—aya[6] a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya wadda za ta bayyana a matsayin Æ™wayar kalma kuma É—afi É—aya. Misali:

     4 a) gidaa  gidaajee

      b) faraa  faraaree

    Kalmar gidaa da kalmar‘gidaajee’ duka suna da saiwa ‘gid-‘[7]. Idan aka cusa suna da adadin tilo da jinsin namiji waÉ—anda dukkansu suna cikin É—afin ‘-aa’, sai a samar da cikakkiyar kalma ‘gidaa’. Idan kuma aka É—afa É—afin ‘-aajee’ mai É—auke da suna da adadin jam’i ba takamaiman jinsi, to, sai a samar da cikakkiyar kalma ‘gidaajee’. Haka abin yake idan saiwar ‘far-‘ ake magana a kan ta. Idan aka Æ™ara mata É—afin ‘-aa’, sai a samar da sifa ‘faraa’wadda take da adadin tilo da jinsin tamata. Idan kuma É—afin ‘-aaree’ aka Æ™ara wa saiwar ‘far-‘, sai a samar da kalmar sifa ‘faraaree’ wadda take da adadi amma ba jinsi.

    2.3       Biyuntawa (Fission)

                Kalmar biyuntawa daga ‘biyu’ ne, an É—auki saiwarta ne wato ‘biy-‘ aka É—afa mata ‘unta’ da kuma ‘wa’, aka tayar da cikakken gininta na ‘biyuntawa’wato ‘fission’ da Ingilishi. Har wa yau, Halle & Marantz (1993:116) sun ba da ma’anarsa kamar haka:

    ’… a given node may be fissioned into two”.

    Fassara: ‘..Æ™wayar ma’ana É—aya tana iya rabuwa gida biyu’.

     Abin da take nufi shi ne bayan an samar da Æ™wayar ma’ana daga gundarin ma’anoni wajen bayyanarsu (Spell-out), a matsayin Æ™wayar kalma É—aya, sai a sami akasi ta zo a wurare biyu cikin kalma maimako wuri É—aya. A Hausa, bayan an zaÉ“o ajin suna da adadin jam’i, ana Æ™ulla su a wuri É—aya a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya. To maimakon ta zo a muhalli É—aya, sai ta rabu kuma ta zo muhalli biyu na saiwa. Dalilin cewa É—aya ce ta rabu, shi ne, da za ka yi amfani da É—aya ka bar É—aya, ba za a sami biyan buÆ™ata ba ta sadarwa. Misali idan aka É—auki saiwar ‘gulb-‘ aka cusa mata É—afin ‘-aa-‘ kawai, za a sami ‘gulaab-‘, Bahaushe ba zai gane abin da kake nufi ba, dole sai an Æ™ara É—ayan wato É—afin ‘-ee’, bayan ‘gulaab-‘, sai a sami ‘gulaabee’ wato suna kuma jam’i.

    5 a) turaamee

      b) kutaaree

    Abin da ya faru a nan misali na (5), shi ne, É—afin ajintau ne da adadin jam’i. Maimakon ya zo a Æ™arshen saiwa, sai ya zo a tsakiyar saiwa da Æ™arshenta. Asali sayyun kalmomin su ne da ‘turm’ da ‘kutur-‘. Sai suka koma, ‘turaamee’ da ‘kutaaree’, da aka É—afa musu É—afin ‘aa-ee’ wato ajintau-jam’i, a cikinsu da Æ™arshensu.

    2.4       Shafewar Ma’ana (Impoverishment)

                Shafewar ma’ana tana faruwa ne, inda aka shafe wata Æ™wayar ma’ana,ta Æ™wayar kalma wadda can asali akwai ta saboda wani dalili na tsarin nahawun harshe. Fabrigas (2005:27) ya ba da ma’anar sahafewar ma’ana kamar haka:

    “ ..Impoverishment, Grammar deletes features from the bundle of a syntactic terminal node”.

    Fassara: .. shafewar ma’ana, a cikin tsarin nahawu yake shafe wasu gundarin ma’anoni daga Æ™unshiyar ma’anoni na Æ™wayar ma’ana”.

    Misalin kalmar ‘jaakii’ da ‘jaakaa’ da ‘jaakunaa’. A É—afin ‘-ii’ yana nuna ajin suna da adadin tilo da kuma jinsin namiji. ÆŠafin ‘-aa’, yana nuna ajin suna adadin tilo da jinsin mace. Sai ‘-unaa’, shi ma yana nuni ne ga ajin suna da adadin jam’i. Ya kamata a ce akwai jinsin maza zalla da na mata zalla, kamar yadda yake a sauran harsuna (kamar larabci). Abin tambaya a nan, shi ne, me ya sa babu jinsin maza zalla ko mata zalla? Greenberg (1963:90) ya ansa wannan tambaya kamar haka:

                Universal 37: A Language never has more gender categories in non-singular numbers than in the singular. This latter statement may be illustrated from Hausa, which has a masculine and feminine gender distinction in the singular but not in the plural. The opposite phenomenon, to my knowledge, never occurs.

    Fassara:

    Ƙa’idar bai-É—aya ta 37: Harshe ba ya taÉ“a nuna ajin jinsi a wuraren da ba adadin tilo (wato jam’i) ba, fiye da yadda yake nunawa a tilo. Wannan furuci yana iya zama gaskiya a Hausa, saboda harshe ne wanda yake bambanta jinsin namiji da jinsin tamata a matakin tilo, ba a matakin jam’i ba. A iya sanina kishiyar haka, ba ta taÉ“a faruwa ba.

    Wannan ya isa ya zama hujja cewa Hausa ba ta nuna jinsi a matakin jam’i. Irin wannan al’amari ne ake kira shafewar ma’ana wato ‘Impoverishment’ da Ingilishi a ra’in Æ™ira-jumla-sak (Distributed Morphology).

    6a) huulaa da huulunaa

    b) riigaa da riigunaa

    c) jikkaa da jikkunaa

    A waÉ—annan misalai na (6), É—ofanan ‘-aa’ duk suna nuna ajin suna da adadin tilo da jinsin mace, amma da aka je jam’intawa babu jinsi sai kurum ajintau da adadi. Saboda Hausa ba ta nuna jinsi a matakin jam’i. An shafe gundarin Æ™wayar ma’anar jinsi (Gender feature) ne aka bar saura[8].

    2.5       Ƙulli Na Ƙirar Kalma Da Jerantawa(Morphological Merger& Linearization)[9]

                Ƙulli na Æ™irar kalma yana bayani ne, a kan abubuwan da suke faruwa lokacin Æ™ulla tubalan Æ™wayoyin kalma (wato É—ofanai) a harshe. Noyer & Harley (1999:5) sun ba da ma’anarsa kamar haka:

    Morphological merger proposed first in Marantz (1984)was originally a principle of well-formedness between levels of representation in Syntax.

     Fassara:

     Æ˜ulli na Æ™irar kalma wanda ya fara kawo shi a fagen nazari shi ne ‘Marantz (1984).Asali Æ™ullin doka ce ta samar da nau’in jumla mai ma’ana a dukkan matakan bayyana fasalin jumla waÉ—anda ake da su.

    Ƙulli ya kasu gida biyu akwai: (a) Ƙulli na ciki (Internal merge) da (b) Ƙulli na waje (External merge). Ƙulli na ciki, shi ne inda harshe yake ɗauko tubalin ɗafi da turken saiwa sai ya ƙulla su wuri ɗaya a matsayin kalma. Misali:

    7 a) gidaa

    b) faraa

    c) kaamaa

    WaÉ—annan kalmomi, an gina su ne ta amfani da tubali biyu. Wato tubalin saiwa da na É—afi. Kamar haka: ‘Ögid-‘ da ‘Öfar-‘ da ‘Ökaam-‘. Sai kuma, É—afin suna ‘-aa’ da É—afin sifa ‘-aa’ da kuma É—afin aikatau ‘-aa’. Babban abin da wannan yake nunawa shi ne, akwai jinsin É—ofanen da a kodayaushe a jikin turken[10] saiwa ake Æ™ulla su. Haka ma, Æ™ulli na waje, Æ™ulli ne da ake yi a tsakanin turken kalma da na É—afi. Misali:

    8a) tiilasta

    b) kaamaawaa

    A nan, É—afin ‘-ta’ an Æ™ulla ta ne ga turken kalmar suna ‘tiilas Ø’. Ita ko ‘-waa’an Æ™ulla ta ne ga jikin kalmar aikatau. Ta farko, ‘Ötiilas Ø’. Ma’ana kalma ce da aka gina da saiwa da kuma É“oyayyen É—afinsuna. Sai ‘kaamaa’ da aka gina saiwar ‘Ökaam-‘ da É—afin aikatau ‘-aa’. To sai aka Æ™ulla É—afin ‘-ta’ ga turkan ‘tiilas’, ita ko ‘-waa’ ga turken ‘kaamaa’. A nan wannan ya nuna ga urken kalma kawai ake Æ™ulla su, ba ga turken saiwa ba.

    Ita ko jerantawa, tana ba da bayani ne a kan wane tubali ne ake fara samarwa? Sannan inane, tabbataccen muhallinsa a cikin kalma? Wannan bincike ya gano cewa É“angare na farko da ake fara samarwa na kalma shi ne ‘É—afi’. Dalili kuwa, a nan neake samun ma’ana ta suna ko sifa ko aikatau ko kuma bayanau. Sannan É—afi ne yake da haƙƙen zaÉ“o saiwar da yake ganin ta dace, sai jerantawa ta kai saiwa muhallinta na dindindin wanda za ta yi aiki. Misali, Hausa tana zaÉ“o gundarin Æ™wayar ma’anar ‘suna’ da ‘adadin tilo’da ‘jinsin mace’ ta Æ™unsa su wuri É—aya a matsayin Æ™wayar ma’ana, sai a cusa su cikin ‘-aa’ a matsayin É—afi[11]. Daga nan É—afin ‘-aa’ sai ya shigo rumbun sayyun kalmomi, ya zaÉ“o saiwar ‘jaak-‘ a matsayin wadda za a Æ™ulla su tare, su ba da kalma. Ita ko daga nan, jerantawa ita take da haƙƙen kai saiwar É“angaren hauni na É—afin domin samar amintacciyar Æ™ira. Wato sai ta ba da kalmar ‘jaakaa’.

    2.6       Ƙarin Æ™wayar ma’ana cikin É—afi (Ornamentation)

                ÆŠafi a harshe yakan sami Æ™ari na ma’ana a dalilin samun kansa a wani muhalli. Har wa yau Noyer & Embick (2007:305) a kan wannan batu, sun ce

     “..certain morphemes are added at PF”.

    Fassara: “..akan Æ™ara wasu Æ™wayoyin ma’ana kafin a kai matakin Æ™arshe na furucinsu’.

    Kamar‘Jituwa’ (agreement feature) tana daga cikin ma’anar da ake samun Æ™arinta musamman a cikin fasali na jumla. Ƙarin ma’anar yana iya kasancewa ko na sharaÉ—in kwaikwayo (copying) ko kuma na dacewa a muhallin da ta zo (contextual). A Æ™ira-jumla-sak ana kiran waÉ—annan Æ™wayoyin ma’anar da Ingilishi ‘ Dissociated morphemes’, wato Æ™wayoyin ma’ana masu zuwa daga baya. Misali

    9a) jaakii ne

    b) kaama[12] zoomoo

    A misalan da suke sama, bayan aikin nuna ajin suna da adadi da kuma jinsi wanda É—afin ‘-ii’ yake yi har wa yau, shi ne madugun nuna jituwa ta kwaikawayo domin kalmar ‘nee’ ta zo ne a dalilin dacewarsu ta fuskar adadin tilo da jinsin namiji.Wannan ne sharaÉ—in kwaikwayo. Da za ka ce ‘*jaakiicee’ za a sami matsala domin babu daidaito na jinsi, sai dai a ce ‘jaakiinee’. Haka ma, bayan nuna aikatau da É—afin ‘-a’ yake yi, har wa yau, shi ne aka É—orawa masa alaÆ™alanci abin da zai biyo baya, wato ko wakilin suna ko maf’uli É“oyayye ko suna maf’uli ko kuma na sigar kauce (passive). A nan, sai ya kasance maf’uli suna ne, ya dace ya biyo baya ba wakilin suna ko wani na daban ba. Wannan ne, Æ™ari na cancanta. Ka ga a nan, É—ofanan biyu wato ‘-ii’ da ‘-a’ an Æ™ara musu wata Æ™wayar ma’ana ta ‘jituwa’[13]wadda can farko babu ita.

    2.7       Sajewa (Syncretism)

                Sajewa muhimmin batu ne a nazarin Æ™irar kalma, musamman a ra’in Æ™ira-jumla-sak (Distributed Morphology). Embick (2015:113) ya bayyana ma’anarsa kamar haka:

                 The term syncretism is used differently in different description and analytical traditions. In this book, it refers to situations in which distinct syntacticosemantic enviroments (i.e sets of synsem features bundled into a morpheme) show the same phonological exponent.

                Fassara: Kalmar ‘sajewa’ ana amfani da ita ta fuskoki daban-daban kamar yadda aka saba gani a nazarce-nazarce daban-daban. A cikin wannan littafi, abin da ake nufi shi ne yanayi ne wanda gundarin ma’ana na muhalli daban-daban (wato shi ne inda gundarin ma’ana na tsatson tsarin ginin jumla da ainihin ma’ana ake Æ™ulla su, a matsayin Æ™wayar ma’ana É—aya)kuma suke nuna tsarin furuci É—aya.

     Sajewa ta kasu gida biyu: Akwai mai cikakken tsari da ragaggen tsari. Mai cikakken tsari (Systematic syncretism) ita ce mai nuna gundarin furuci É—aya kuma ma’ana É—aya. Misali:

    10a) huulunaa

    b) riigunaa

    c) bargunaa

    A nan, É—ofanan da aka ja wa layi a misali na (10), siffarsu É—asa kuma ma’anarsa É—aya wato nuna cewa saiwar sun ace kuma jam’i. Sai kuma sajewa mai ragaggen tsari (non-systematic syncretism), wato inda aka sami, ma’ana É—aya furuci daban ko kuma furuci É—aya amma ma’ana daban. Misali:

    11a) bukkookii

    b) shugabannii

    c) sayaa

    d) faraa

    Misalan É—ofanan farko (a,b) wato ‘-ookii’ da ‘-annii’ duk ma’anar da suke nunawa É—aya ce wato bayan nuna ajin sayyun, sai kuma jam’i amma kuma furuci ya sha bamban. Amma, sai ga shi an sami É—afi furucinsu É—aya sai dai ma’anarsa ta bambanta domin na farko aikataune, mai bi masa kuma sifaa misalin (c) da na (d).

    2.8       Gasa Da Shingewa (Competition & Blocking)

                Gasa da Ingilishi shi ne ‘competition’.Ana samun gasa ne ga tubalai (kamar É—afi) masu aiki É—aya, sannan kowanne yana gasar ne da manufar a zaÉ“e shi a matsayin zakara, kuma a sanya shi a muhallin da zai yi aiki. Dalilan zaÉ“en É—aya, a bar É—aya, yana faruwa ne saboda fifikon cancantarsa ta fuskar nahawu (Competition for grammaticality). Misali:

    12a) gulaabee

    b) riigunaa

    A waÉ—annan misalai na (12), kowace saiwa an É—afa mata É—ofanen da ya dace da ita. Wannan ya sa aka sami amintacciyar Æ™ira mai ma’ana. Da za a sauya wannan tsari na Æ™irar waÉ—annan kalmomi, misali ‘*riiaagee da ‘*gulbunaa’. Ba sai an faÉ—a ba, É—ofanan da aka É—afa ya haifar da rusasshiyar Æ™ira. Haka ma, wani lokaci akan sami zaÉ“in son mai sadarwa (Competition for use) (Embick 2008:61-62). Misali

    13a) ƙasidooji

    b) ƙasiiduu

     A waÉ—annan misalai na (13), akwai É—afi biyu, wato ‘-ooji’ da ‘-uu’. Sannan kowanne ya ba da Æ™ira madaidaiciya. Haka kuma,duk lokacin da za a yi zaÉ“en zakara (Winner) ba a son wanda ya zarce (overspecified).ko kuma wanda ya kasa (underspecified) da kuma wanda ya saÉ“a gaba É—aya (conflict feature) (Siddiqi, 2006, 2009). Gasa ita take haifar da shingewa ‘Blocking’, domin duk tubalin É—afin da aka zaÉ“a aka saka a wani muhalli, wannan zai ba shi damar shingace masu adawa da shi. Shingewa a fahintar Aronoff (1976:43) “ the non occurrence of form due to simple existence of another”. Fassara: ‘ ..rashin zuwan wani tubali saboda kawai wani tubalin a wurin’. Misali:

    14a) jaakii   jaakaa      jaakunaa

    b) farii    faraa       faraaree

    c) gidaa  *gidanyagidaajee

    d) bargoo *barganyaa   bargunaa

    Abu na farko da za a fahinta daga waÉ—annan misalai na (14), shi ne, Hausa harshe ne wanda yake da sigogi daban-daban masu nuna adadi da jinsi.Wannan ya sa duk lokaci da za a samar da wata siga ta jinsi ko ta adadi to lalle za a fuskanci matuÆ™ar gasa a tsakaninsu. Sannan kuma, akwai shinge domin misalan (c) da (d) ba su da jinsin mace kamar yadda aka nuna a misalan (14a) da (14b). Wani Æ™arin bayani shi ne, jinsin namiji da aka jinginawa ‘gidaa’ da ‘bargoo’ ba na haÆ™iÆ™a ba ne Æ™agagge ne domin a zahiri babu gidaa namiji babu gidaa mace, haka ma ‘bargoo’ abubuwa ne sandararru marasa rai, saboda haka jingina musu jinsin namiji, jinsi ne kawai irin nahawu ‘ Grammatical Gender’ kamar yadda Kramer (2009,2014) ta bayyana.

    2.9       Jirwayen Tsarin Sautia Æ™irar kalma (Allomorphy)

                Jirwayen tsarin sauti wani al’amari ne muhimmi a fagen nazarin alaÆ™ar É“angarorin ilimin kimiyyar harshe (Linguistic interface). Ga abin da Embick (2015:170) ya ce game da shi:

     The term allomorphy is sometimesused to refer to any variations in phonological shape that morphemes undergo when they are combined. Allomorphy can be suppletive or phonological”

    Fassara:

     Kalmar jirwayen tsarin sauti a wasu lokuta ana amfani da shi domin nuna duk wani bambanci na fasalin gundarin tsarin sauti wanda ya shafi Æ™wayoyin kalma idan aka Æ™ulla su. Jirwayen tsarin sauti zai iya kasancewa na tsarin sauti da wanda ba na tsarin sauti.

    Ɗafi shi ne madugu uban tafiya da yake ƙulla alaƙa tsakanin ƙirar kalma da tsarin sauti (Sani 2011:5). Akasarin jirwayen tsarin sauti da ƙirar kalma yana da alaƙa da naso. Misali:

    15 a) gídààjéé

    b) bírìì

    Bayanin da za a yi a nan dangane da misali na (15), shi ne, asalin kalmar gídààjéé daga kalmar‘gídáá’ aka samo ta. Da aka zo samar da jam’i ya kamata ta kasance ‘gidaadee’, amma saboda dokar tsarin sauti wadda take nuna duk inda wasali /e/ ya gabaci baÆ™in /d/, yana nashe shi zuwa sautin /j/, wato dai, an sami inda wasali yake nashe baÆ™i. Sannan kada a manta, wannan wasali da baÆ™in sun zo ne a matsayin É—afi, a nan abin ya faru. Haka ma, asali kalmar tana da tsarin karin sauti sama-sama ‘gídáá’ amma da aka É—afa mata É—afi mai nuna jam’i sai tsarin ya sauya zuwa sama-Æ™asa-sama[14].  Kalmar ‘biriiÉ—afinta mai nuna ajinta da adadinta da jinsinta shi ne ‘-ii’, yana da kusanci sosai da wasalin saiwar wato ‘i’ ka ga ke nan, ya zama jituwar wasali ( Vowel harmony)[15].

    2.10     Yàlwáá (Productivity)

                Yalwa al’amari ne muhimmi a nazarin Æ™irar kalma, wanda duk akasarin littafai masu koyar da limin Æ™irar kalma suke ware babi guda domin yin bayaninsa. KaÉ—an daga cikin waÉ—annan ayyuka su ne: Aronoff (1976) da Bauer (1983,1988, 2001) Katamba (1993) da Haspelmath (2002, 2010) da Aronoff & Fudeman (2005, 2011) da McCarthy(2002) da Plag (2003)[16] da sauransu. Amma kash! A nazarin Æ™irar kalmomin Hausa yalwa babu shi, wato ba a kai can ba, musamman a akasarin littafan karatu (Kamar Fagge (2004,2013) da Newman (2000) da Abubakar (2001) da Jaggar (2001) da Sani (2002) da Amfani (2007)). Bauer (2001:211) dangane da ma’anar ‘yalwa’ ya ce

     “Productivity” deals with a number of new words that can be coined using a particular morphological process..”

    Fassara:

     “Yalwa” ta magana ne a kan É—imbin sababbin kalmomi da zaa iya Æ™irÆ™irowata yin amfani da wata keÉ“aÉ“É“iyar hanyar Æ™irar kalma..”

    Malamin ya bayyana wasu hanyoyi biyu na gane ‘yalwa a Æ™irar kalma su ne “ Availability” wato ‘yawa’ da “ Profitability” ‘farin jini wajen amfani(da shi ga masu harshe). Katamba (1993:67) ya ce “ Productivity is a matter of degree” Fassara “ Yalwa” al’amari ne mai hawa-hawa”. Lalle ‘ÆŠafi’ a fagen samar da kalmomi, hanyace mai matuÆ™ar yalwa a Hausa. A wani lokaci a kan sami wani É—afi yana da yalwa. Ga abin da Du & Zhang (2010: 60) suka ruwaito (an ciro batun ne, daga Bauer (2001;12)) :

    “..an affix to be used to coin new complex words is referred as productivity” Fassara

    ÆŠafi wanda za a iya amfani da shi don Æ™irÆ™arar kalmomi masu sarÆ™aÆ™iya shi ma, ana ce masa ‘yalwa’. Misali:

    Dubi waÉ—annan misalai:

    16a) san> sani>sananne>sananniya>sanannnu>masani>masaniya>masana

    b) riguna> wanduna> alluna> barguna> jakuna> tarkuna>bankuna>

    hukuna>jikkuna> É—unkuna .

    A waÉ—annan misalai na (16 a) an ga irin yadda saiwar ‘san’ ta nuna É—abi’ar yalwa wajen samar da kalmomi takwas. Sai kuma, misali (16b ) inda aka ga yadda É—afin ajintau mai Æ™unshe da jam’i wato ‘-una’ ya taimaka wajen samar da kalmomi goma.

    3.0       Kammalawa

                A taÆ™aice, al’amarin da ya shafi abubuwan da suke faruwa ga ‘ÆŠafi’ abu ne mai faÉ—i da ban sha’awa. Sannan waÉ—annan ‘yan misalai da aka goya a Æ™arÆ™ashin kowanne ya Æ™ara fitowa da abin da suke nufi. Sannan batutuwan da aka kawo za su zama jagora ga mai son zurfafa nazari a kan É—afi. Baya ga haka, daga cikin abubuwan da suke faruwa an gano cewa dai, akwai waÉ—anda suke faruwa kafin bayyanar É—afi, da kuma bayan samuwar É—afi. HaÆ™iÆ™a, Spencer (1991:14) ya yi gaskiya da ya kira ‘ÆŠafi’ cewa “ Affixation is morphology par excellence” ma’ana “ÆŠafi madarar ilmin Æ™irar kalma ce mai ban sha’awa”.

    Manazarta

    Tuntuɓi masu takarda.



    [1] Wannan nazari yana gudana ne, ta lura da manyan aÆ™idoji biyu: (a)AÆ™idar rarrabewa ko bambantawa a tsakanin gundarin ma’ana da gundarin furuci wato ‘separation hypothesis’ da Ingilishi..(b) Sannan da daidaitawa a tsakanin tsarin ginin kalma da tsarin ginin jumla.

    [2] Alama ce mai nuni ga ‘saiwa’ ta ginin kalmomi a harshe.

    [3] A zahiri babu gida namiji balle mace, Æ™agaggen al’amari na nahawu wato da Ingilishi shi ne ‘Grammatical Gender’ Kramer (2009, 2014) ta yi faffaÉ—an bayani a kan batun.

    [4] A fahintar ra’in wannan bincike, Æ™wayar ma’ana É—aya wato ‘morpheme’ tana Æ™unshe da wasu gundarin ma’anoni ‘features’. Kamar ‘suna’ da ‘adadi’ da ‘jinsi’.

    [5] Ba abin mamaki ba ne, a sami gundarin ma’ana É—aya a matsayin Æ™wayar ma’ana kuma Æ™wayar kalma É—aya.

    [6] Da Ingilshi ana kiran wannan al’amari ‘Bundling of features or features bundling’

    [7] Wannan saiwa ce, a ra’in wannan bincike ‘saiwa’ ba ta da ma’ana balle yin wani aiki na nahawu, sai an ajinta ta. (Embick, 2012,2015), Panagiotidis (2011,2014).

    [8] Ba harshen Hausa kaÉ—ai yake nuna wannan halayya ta shafe Æ™awara ma’anar jinsi a wurin jam’i ba, har a harshen Rasha kanwar ja ce kamar yadda Bobaljik (2015: 8-9) ya bayyana.

    [9] Ganin cewa suna da kusanci, ya sa aka haÉ—e su wuri É—aya.

    [10]Abin da wannan bincike yake kira ‘turke’ shi ne da Ingilishi ‘Base’ Bauer (1988:238), ya ba da ma’anar turke kamar haka: “Base: A base is any item to which affixes may be added. Roots and stems are special types of base. A base is sometimes termed operand“: Fassara: Turke: Turke shi ne duk wani tubali wanda ana iya Æ™ara masa É—afi. Da turke da tushe duk nau’o’i ne na turke na musamman. A wasu wurare ana kiran turke ‘ ginshiÆ™i’. Aronoff & Fudeman (2005:235), sun ce ‘Base: The root or or stem to which affix attaches’ Fassara: ‘Turke: Shi ne saiwa ko tushe inda zaa É—afa É—afi’.

    [11] ÆŠafin da yake nuna suna da tilo da mace, ba É—aya ba ne, suna da yawa, harshe yana zaÉ“o wanda ya fi cancanta . A nahawun samau (Generative Grammar) Æ™arÆ™ashin Minimalisanci (Minimalism) ana kiran al’amarin ‘Numeration’, wato ‘zaÉ“en gundarin ma’anoni’.

    [12] A ra’ayin wannan bincike cewa wannan É—afi ‘giredi’ kamar rage masa matsayin ne domin da shi ne saiwar take zama aikatau, saboda haka ajintau ne na aikatau ‘ verbalizer category’. Sannan a tsarin nazarin Æ™ira-jumla-sak, ana fara ginin jumla daga matakin sakakkiyar saiwa ‘neutral root’ da É—afin ajintau ‘categorizer affix’, ba daga matakin kalma ake somawa ba, kamar yadda saba a tsarin nazari na farko. Kuma shi ne ake kira ‘phase-based analysis’ wato tsarin nazari kula da Æ™ananan tubalai. Ba za ka ce dole, sai an biyo da wani abu ba, baya ga saiwar da É—afin ajintau ba.

    [13]Agreement feature’ da Ingilshi.

    [14] Wannan ne Newman (1986) ya kira ‘Tone-integrating affix’ wato É—afi mai sauya akalar tsarin karin sauti na farko.

    [15]Schane (1973:52) ya bayyana ma’anar jituwar wasali kamar haka: ‘Vowel harmony is a case in which vowels agree in certain features’. Fassara: Jituwar wasali al’amari ne, wanda ake samun wasula sun jitu ta wasu fuskoki.  

    [16] Littafin da aka wallafa kacokan a kan wannan É“angare na ilmin kimiyyar harshe guda É—ayane kawai, wato ‘Morphological Productivity’ na Laurie Bauer (2001).

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.