Ticker

Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (1)

NA

ADAMU SANI

Zamfara

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifina mal. Isah Sulaiman da fatar Allah ya jiƙansa da rahama, da maga’isana mal. Adamu Sulaiman, haka kuma da mahaifiyata Fatima Isah Sulaiman da Fatima Adamu Sulaiman, da kuma mai ɗakina Sadiya Abdulƙadir da Sauran ‘yanuwa da abokan arziki.

GODIYA

Ina mai farawa da godiya ga Allah (S.W.A) wanda ya ba mu damar gudanar da wannan bincike tun daga farko har zuwa ƙarshe, tare da yabo ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da Sahabbansa, da kuma mabiyansa har zuwa ranar ƙarshe.

 

Zan yi amfani da wannan dama in yi godiya tare da jinjina ga fitilar wannan bincike mal. Isah S. Fada Zugu wanda ya taimaka ainun wajen gudanar da wannan bincike ta hanyar shawarwari da kuma haƙuri tare da ba da gudummuwa ta ɓangoriri daban- daban, Allah ya saka masa da mafificin alkhairi amin.

 

Bayan wannan ina mai miƙa godiya ga shugaban sashe gogan koyarwa Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, da sauran malaman sashe kamar Farfesa Balarabe Abdullahi, da Farfesa Magaji Tsoho Yakawada, da Farfesa Muhammad Lawal Amin, Dr. Nazir Abbas Ibrahim, mal. Aliyu Rabi’u Ɗangulbi da malam Musa Abdullahi da sauransu da fatar Allah ya saka masu da alkhairi.

 

Haka kuma, ina miƙa godiyata ga mahaifina Isah Suleiman, Adamu Sulaiman, Salisu Sulaiman, da Fatima Isah, da Fatima Adamu. Ta sanadiyar taimako da addu’o’in da suka ta yi lokacin gudanar da wannan karatu, Allah ya saka musu da aljannah maɗaukakiya. Haka kuma ina miƙa godiya ga maiɗakina Sadiya Abdulƙadir domin nuna hali irin na haƙuri lokacin gudanar da wannan karatu. Hakazalika godiya ta musamman ga ‘yan’uwana Jamilu Salisu, Buhari Isah, Hauwa’u Adamu, Zainab Adamu (Nasara), Maryam Isah, da Halima Isah, Mubarak Adamu, Najib Adamu, Abdulƙadir Adamu. Bugu da ƙari, ba zan manta da mal. Nasiru Abubakar, Abdulhakim Ahmad, Auwal Muhammad (Onbitin), da AbdulFatah Alabi, da Sikiru Adisa, Mal. Aminu Mika’ilu da Mal. Abdulraheem Oladineji, da Rabi’u Shehu, da mal. Abdulrahman Muhammad Umar, domin ƙwarin gwiwa da suka ba ni ya yin gudanar da wannan aikin.

 

Daga ƙarshe ina miƙa godiya ga Dahiru Ahmad, da Yakubu Ahmad, Aminu Haruna Abba Jidda, haka kuma ba zan manta da abokan karatuna ba, kamar Nasiru Hassan, Ahmad Muhammad Kabir, Bashar Isyaka, Aliyu S Ibrahim, Mustapha Sa’idu, Abubakar Hassan, Nura Sani, Hisbullah Ɗanlami, Amina Abubakar, Ɗayyaba Mustapha, Hassan Galadima, Abdulrahman Bala, da Abdulrashid S/Pawa. Ina mai rufewa da aminina Alhaji Isah Ibrahim Mailemu dangane da irin gudummuwar da ya bayar domin cigaban wannan bincike. Da fatar Allah ya saka wa kowa da alhairi.

ƊUNGULMIN NAU’I (ABBREƁIATION)

 

YRB                            -           Yoruba

HAU                           -           Hausa

MAL.                          -           Mallam

M.                               -           Mallan

ALH.                          -           Alhaji

NYSC             -           National Youth Service Corp

TSAKURE

Najeriya ƙasa ce da Allah ya albarkata da harsuna mabambanta, mai kuma yawan mutane kimanin miliyan 180, Hausa da Yarbanci suna daga aikin su. Ƙaurace- ƙauracen sun taimaka inda ƙabilun suke yi wa junansu shigar hadarin giza-gizai, wanda ya samar da gamaɗe (ingausa). Wannan bincike ya waiwayi taƙaitaccen tarihin garin Gusau. Da kuma dalilan da suka haifar da ingausar Yarbanci da Hausa. Kamar haɗuwa wajen neman ilimi (Makarantu), kasuwanni wajen saye da sayarwa, da wuraren sana’o’i kamar kafintanci, da Kanikanci, haka kuma Yarbawan kan yi mu’amala da Hausawa a ma’aikatunnen Gwamnati; waɗannan mu’amulloli da makamantan su ne suka haifar da ingausar Yarbanci da Hausa a garin Gusau, waɗannan su ne fitattun ababen da za mu yi nazari domin su zama haske ga wanda ke cikin duhu.

Post a Comment

0 Comments