Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (3)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

    Ingausar Yarbawa Da Hausawa A Garin Gusau, Jihar Zamfara (3)

    NA

    ADAMU SANI

    Zamfara Gusau

    BABI NA BIYU

    WAIWAYE ADON TAFIYA

    2.0 SHIMFIÆŠA

    Ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jinƙai ga bayinsa, godiya ta tabbata gare ka mai mulki da iko na har abada. Salati maras iyaka ga fiyayyen halittu Annabi Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Wannan babi zai yi tsokaci ne dangane da bitar ayukkan da suka gabata waɗanda suka haɗa da rubutattun littattafai, da kuma maƙalu da aka gabatar a wurare daban-daban masu alaƙa da wannan aiki.

     

    2.1 BITAR AYUKAN DA SUKA GABATA

    Masu azancin magana kan ce “Waiwaye adon tafiya” haka yake domin masana da dama sun gudanar da bincike mabambanta dangane da ingausa, amma ba a taÉ“a wani bincike mai take irin wannan ba. Wannan ne ya tilasta a yi waiwayen aikace-aikacen da masana suka yi domin samun Æ™arin haske ga wannan bincike, daga cikin aikace-aikacen da aka gudanar waÉ—anda aka yi bitar su sun haÉ—a da: bugaggun littattafai da kuma maÆ™alu wanda za a É—auke su É—aya bayan É—aya.

     

    2.2 RUBUTATTUN LITTATTAFAI

    Masana da dama sun yi wallafe-wallafe ta fanin kimiyyar harshe, musmaman É“angaren da ya shafi walwalar harshe wanda yake kula da harshe da al’umma, wato yadda al’umma ke sarrafa harshe ta hanyoyi daban-daban, kamar ingausa, tashi da harshe, aron kalmomin harshe da sauransu, daga cikin malamai ko masanan da suka tofa albarkacin bakinsu a wannan fanni akwai:

     

    Yakasai S.A, (2012); ya yi magana kan tsakanin harshe da al’umma, inda wasu baÆ™in al’ummu kan zo cikin mazaunan asali, sai a samu kowace daga cikin al’ummun sukan tasirantu da harsunan juna har su sarrafa su ta hanyoyi daban-daban. Haka kuma ya kalli tasirin addini, zuwan addinai musamman musulunci da Kiristanci (addinin Masihya) sun kawo sauyi a harsunan mabiya addinan, da kuma tasirin al’adu, da tasirin zamantakewa, haka kuma ya kalli yanayin magana da kuma al’amurran jama’a duk waÉ—annan abubuwa da masanin ya kawo a cikin wannan littafi suna cikin abubuwan da aka kalla wajen gano dalilan da suka kawo ingausar da Yarbawan garin Gusau suke yi tsakaninsu.

     

    Mukhtar A.B, (2017), ya bayyana ma’anar harshe inda ya kawo ra’ayoyin masana game da ma’anar harshe, shi ma ya taimaka wajen ci gaban wannan bincike domin ya shafi harshe ne. Bugu da Æ™ari, masanin ya taÉ“o abin da ya shafi ingausa a Æ™arshen littafin, inda ya kira ta da gamin gambizar harshe, ya kalli abin ta hanya biyu, wato surki na ciki wanda ake gudanarwa cikin harshe guda wanda ake iya surka karin harshe biyu lokaci guda a yayin wani zance, sai kuma surki na waje wanda ake iya surka harsuna biyu masu zaman kansu lokaci guda a yayin wani zance. Wannan ma ya Æ™ara haske game samun nasarar wannan bincike.

     

    Holmes J., (2008). Masanin ya yi magana a kan ilimin walwalar harshe inda ya taÉ“o abubuwa da dama da suka haÉ—u suka samar da walwalar harshe, daga cikin ababen akwai; zaÉ“en kalmomi a cikin al’umma mai magana da harsuna fiye da É—aya, da kuma yadda ake rayar da harshe, da nau’o’in kimiyar harshe, da kuma harshen Æ™asa.

     

    Bayan wannan kuma masanin ya dubi ababe kamar yankuna da kare-karen harsuna da kuma jinsi da shekaru da kuma yadda harshe ke canjawa.

     

    Haka kuma masanin ya kalli kwalliyar magana, da kuma sadarwar al’ummu masu bambancin al’adu, da kuma yadda ake nazarin zantuka tare da duban halaye da É—abi’un yadda ake furta wasu kalmomi.

     

    Wannan aiki yana da alaÆ™a da aikin da ake gudanarwa domin ya taÉ“o abubuwa da dama waÉ—anda dole ne a kai hannu a kansu ko a yi la’akari da su domin samun nasarar wannan bincike kamar yadda masanin ya ambata zaÉ“en harshe a cikin al’umma mai magana da harshe fiye da É—aya, wanda kan haifar da abin da ake bincike a kansa wato ingausa. Iya harshen Hausa da Yarbawan Gusau suka yi shi ya sa suke surka kalmomin Hausa cikin maganganunsu.

    Pearson J.C da wasu, (2003). Masanan sun yi magana a kan yadda É—an-Adam yake sadarwa (magana), tare da duba sadarwa ta magana da kuma wadda ba ta magana ba. Haka kuma sun duba sadarwa tsakanin mutum biyu ko sassa biyu kamar ma’aurata, abokai, da kuma masu al’adu daban-daban. Bayan wannan kuma masanan sun kalli yadda maganar Æ™ananan harsuna ke canjawa domin tasirin mamayewar da aka yi musu, saboda ba sa iya tsayuwa da kansu a wuraren da suke zaune sai sun jingina ga mafi yawan al’ummar da ke wurin. Wannan kan sa harshe da al’adu su yi naso ga Æ™ananan harsuna, ko baÆ™i.

     

    Duk waÉ—annan abubuwa da masanan suka kalla suna cikin abubuwan da suka taimaka wajen samuwar ingausar Yarbanci da Hausa a garin Gusau.

     

    2.3 MUƘALU

    Maƙalu su ne takardu masu ɗauke da bincike na ilimi a wani fanni na musamman, mafi akasari waɗanda a kan gabatar a wajen taron ƙarawa juna sani. An gabatar da muƙalu game da ingausa ta fuskoki daban-daban, amma babu mai taken wannan aiki sai dai alaƙa, daga cikin muƙalun da aka yi bitar akwai:

     

    Chamo, (2012). Masanin ya bayyana harshe a matsayin katin shaida, inda a cikin takardar ya yi nazarin, tasirin zamananci ga Hausar matasan arewacin Nijeriya. Inda ya yi la’akari da ilimin boko da kuma tasirin mu’amula da baÆ™in al’ummu da matasan ke yi.

     

    Wannan takardar ta taimaka wajen mayar da hankali tare da kula da yadda matasan Yarbawan Gusau ke magana, inda nazari ya bayar da cewa suna ingausar Yarbanci da Hausa saboda tasirin zamantakewa.

     

    AlaÆ™ar wannan aiki da takardar ita ce, masanin ya kalli tasirin zamananci wurin hulÉ—ar matasa, inda wannan aiki ya kalli tasirin muhallin zama da ya kawo ingausar Yarbanci da Hausa a garin Gusau. 

     

    Haruna A. da wasu (2016). Masanan sun gabatar da takarda a kan muhimmiyar rawar da ingausa, ke takawa a cikin wasu zaɓaɓɓun littafan zube na Hausa, waɗanda marubutan zamani kan wallafa, littattafan da suka nazarta sun haɗa da:

    i.                    Ingausa a cikin littafin “Mai Æ™aunata”

    ii.                  Ingausa a cikin littafin “Rayuwar Gayya”

    iii.               Ingausa a cikin littafin “Matan zamani”

    Wannan takarda ta yi shige da wannan bincike amma ba taken su guda ba, sai dai an samu ƙarin haske game da yadda za a tsara aikin.

     

    Ehsan da Aziz, (2014). Muƙalar da suka gabatar a kan nazarin ingausa a cikin labaran Pakistani na rediyo inda sakamakon bincken su ya bayyana cewa masu labaran suna yin ingausar Ingilish da yaren Pakistani ne domin su isar da saƙonnin da suke so su isar cikin sauƙi musamman daga abubuwan da suka shafi kimiyya da ƙere-ƙere.

     

    Alaƙar aikin da wannan ita ce, tarayya a fagen nazarin ingusa inda masanan suka nazarci ingausa a harshen Pakistani, wannan aikin kuma ya kalli Ingausar Yarbanci da Hausa a garin Gusau.

     

    Muysken P. (2000). Masanin ya gabatar da muƙala game da abubuwan da kan haifar da ingausa, ya bayyana cewa matsakaitan mutanen Najeriya suna iya magana da wani harshe bayan harshen uwa. Wannan shi ya haifar da nazarin ingausa, musamman ta harshen Ingilishi da harshen uwa (Yoruba).

     

    Wannan takarda ta ƙara muna haske game da wannan bincike, domin masanin ya bayyana cewa fahimtar harshe fiye da ɗaya shi ya haifar da nazarin ingausa, hada Ingilishi da Yarbanci, wannan ya sa aka yi nazarin tuntuɓar Yarbawan Gusau masu jin harshen Hausa da kuma nasu domin samun bayanai da misalai.

     

    Ajibade A.C da wasu, (2017). A muÆ™alar masanan sun bayyana cewa fagen nazari na walwalar harshe ya shiga kowane irin fage na rayuwar al’umma kuma fage ne wanda ya É—auki hankalin mutane a yanzu. Masanan sun yi nazari ne a kan ingausar Yarbanci da Ingilish da ake yi a kudu maso yammacin Najeriya, domin waÉ—anda suka iya harsunan Yarbanci da Inglishi sukan yi amfani da bayun lokaci É—aya a cikin zantukansu. Wannan takarda ta Æ™ara share hanya game da yadda wannan bincike zai kasance, domin za a kalli ingausar Yarbanci da Hausa ne a garin Gusau.

     

    Yusuf, C.I (2012). Masanin ya nazarci ingausa ne a fina-finan Hausa na Kano (Kanny-Wood), ya kalli, ingausar Hausa da Inglishi, amma mafi akasari mai zuwa daga Æ™arshen zance, yadda ‘yan wasan fina-finan Hausa na Kano kan Æ™ulla zantukansu ta amfani da surka harshen Inglishi a Æ™arshen zantuka. Amma wannan binciken zai kalli ingausar Yarbanci da Hausa ne a garin Gusau, kuma ta kowace hanya ko farko ko tsakiya ko Æ™arshe.

     

    Ibhawaegbele, F.O. da Edokpayi J.N (2012). WaÉ—annan masanan sun yi nazarin ingausa a matsayin wani salo na musamman da marubutan Æ™agaggun labarai na Nijeriya ke amfani da ita domin fito da halaye da É—abi’un taurarin da ke cikin littattafan marubutan. WaÉ—annan masanan sun yi nazarin littattafai uku waÉ—anda wani shahararren masanin harshen Igbo ya rubuta, littattafan an rubuta su da harshen Ingilishi ne amma manazartan sun fitar da ingausa 38 daga cikin littattafan. Wannan ya nuna cewa ingausa tana taka muhimmiyar rawa ga marubuta Æ™agaggun labarai ‘yan Afrika.

     

    Waɗannan sun kalli ingausar Igbo da Ingilishi amma a littattafan ƙagaggun labarai, a wannan aikin za a kale ta a fannin zantawa ko fira tsakanin yarbawan garin Gusau.

     

    Sappapan (2013). Wannan masanin ya yi nazarin ingausa ne a cikin waƙar wani ɗan ƙasar Thailand mai suna POP, wadda ya yi da harshen Ingilishi da harshen Thailand, inda kalmomin Ingilishi suka rinjayi na harshen Thailand. Musamman ma sunaye, kalmomin sunaye na Ingilishi su ne masu babban kaso a cikin ingausar, sannan kalmomin aiki a cikin waƙar ta POP.

     

    Wannan takarda ta ba mu haske a kan kula da irin kalmomin Hausa da Yarbawa suka fi ambato ko amfani da su a wajen ingausar Yarbanci da Hausa da suke yi a garin Gusau.

     

    2.4 KUNDIN BINCIKE

    An gudanar da bincike- bincike da dama, domin samun shaidar kammala wani karatu ta fannonin nazarin harshe, amma ba a samu yawaitar masu binciken da ya shafi wannan ɓangare na walwalar harshe na Ingausa ba, sai dai an samu kai hannu a kundin digiri na uku na wani shahararren malami a fannin ilimin walwalar harshe, wanda ke da alaƙa da wannan bincike ta wani fanni, kamar haka:

     

    Yakasai, (1999); Ya yi nazari a kan Hausar Illela da ta Ƙonni a (Jamhuriyar Nijar). A wannan aiki ya nazarci yadda ɗaiɗaikun harsuna da kare-karen harshe ke haɗuwa a kan iyaka ta Illela da Ƙonni, su samar da wani Karin harshe na daban. A cikin nazarin ya yi maganar tasirin wasu harsuna kan wasu sanadiyar haɗuwar su wuri ɗaya da kuma abin da dangantakar tasu ta haifar na sauyi a cikin harsunan.

    Wannan aikin ya taɓo wani fanni na wannan aiki domin ya yi magana a kan tasirin wasu harsuna a kan wasu, inda ya haskaka game da duba tasirin harshen Hausa ga Yarbawan Gusau inda ya haifar da yanayin magana na ingausa, haɗa Yarbanci da Hausa lokacin magana.

     

    2.5 NAÆŠEWA

    Wannan babi ya fara ne da shimfiɗa tare da bayyana irin ayukkan da aka yi bita na binciken da ya gabata domin waiwaye kan ayukka masu ƙarin haske ko kuma shige da irin wannan aiki, an duba ayukka masu shige da irin wannan aiki da suka haɗa da bugaggun littattafai masu alaƙa da muƙalu da kundin bincike, dukan waɗannan ayukka babu mai take guda da wannan sai dai alaƙa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.