Kwalliyar Matan Garin Gusau (1)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

    Kwalliyar Matan Garin Gusau (1)

    NA

    ÆŠAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

    Kwalliya

    SADAUKARWA

    Na sadaukar da wannan aiki nawa ga mahaifiyata Hajiya Maimunatu Aliyu, Allah ya jiƙanta da rahama, sai kuma mahaifina Alhaji Mustapha Ibrahim, da kuma yayata Hajiya Hadiza Mustapha Ibrahim waɗanda da taimakonsu ne cikin yardar ubangiji aka fara wannan karatu lafiya kuma aka gama lafiya. Allah ya saka da mafificin alheri.

    TSAKURE

    Wannan kundi yana Æ™unshe da bayanai akan Kwalliyar Mata a Garin Gusau, da ire-irenta da nau’o’inta da amfaninta, da kuma yanda mata Æ™anana ke yin kwalliya da ‘yan mata da zawarawa, da kuma matan aure.  Daga Æ™arshe, an bayar da shawarwari a kan yadda za a bunÆ™asa Kwalliya. Akwai kammalawa da kuma manazarta.

     

    GODIYA

    Ina fara jaddada godiyata ga Allah (S.W.T) mai rahama mai jinÆ™ai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (S.A.W) da sahabbansa da zuri’arsa da dukkan wanda ya bi tafarkinsa har zuwa ranar sakamako.

    Bayan haka, ina miÆ™a godiya da jinjina zuwa ga mahaifiyata Hajiya Maimunatu da Mahaifina Alhaji Almustapha Ibrahim a bisa jajircewarta domin ta ga na kammala wannan karatu, kuma na gode da irin addu’o’in da take yi mini ba dare ba rana. Allah ya saka mata da mafificin alkhairi, ya sanya Al-Janna Firdausi ta kasance makoma a gareta.

    Bayan haka, sai godiya da jinjina zuwa ga yayyena da kuma Æ™annena a bisa gudunmawarsu ta fuskoki daban-daban, tun daga addu’o’i, shawarwari da kuma kayan aiki daga cikinsu akwai; Aunty Hadiza, Aunty Hannatu, Yaya Babawo, Aunty A’isha, Aunty Halima da kuma kanene Attahir, da kuma Maimunatu da Fatima, da Sani, Rabiatu da kuma Hafsatu, duk Allah ya saka masu da mafificin alkhairi.

    Godiya ta musamman ga malamai na musamman na sashenmu, dangane da gudummawar da suka bani da kuma shawarwari. Haka kuma ina miÆ™a godiyata ta musamman ga Malamai kamar su; Prof. Aliyu Muhammad Bunza, Prof. M.T Yakawada, Prof. Balarabe, Malam Rabi’u A. ÆŠangulbi da malam Isah S. Fada da malam Musa Abdullahi da Dr. Nazir Abbas da Dr. Tahir da Dr. Fadama da Dr. S. Gulbi da sauransu. Allah ya saka da mafificin alheri.

    Bayan haka, ina miƙa godiya da jinjina ga malamina kuma wanda ya duba wannan aiki Malam Musa Abdullahi bisa ɗorani a kan hanya da kuma haƙuri da ya yi da ni lokacin gudanar da wannan aiki. Allah ya saka da alheri.

    Bayan haka ina miƙa godiya ta ga mutanen da aka yi hira da su a lokacin gudanar da wannan aiki, musamman yadda suke ba da lokacinsu sannan kuma suna da karamci, daga cikinsu akwai; Malama Halimatu, Malama Hurriya Mai Kwalliya da dai sauransu.

     

    Haka kuma, ina miÆ™a godiyata zuwa ga abokan karatuna dangane da taimakon da su yi mini ta fuskoki daban-daban, nagode da kulawarku, Aunty Amina, Abubakar Hassan, Abdulrashid S. Fawa, Ahmad M. Kabir, Abdulrahman Bala (ABG), Aliyu S. Ibrahim, Bashir Isiyaku, Mustapha Sa’idu, Hassan Galadima, Nura S. Kwatarkwashi, Hizbullahi ÆŠanlami.

    Haka kuma akwai godiya zuwa ga abokaina na musmaman waÉ—anda ba zan manta da su ba, kamar irin su; Safiyya Ahmad, Wasila Sani, Rahila Aliyu da Zainab Sani

    A Æ™arshe ina miÆ™a godiya ta musamman ga Faisal Musa bisa ga addu’arshi da kuma jajircewa wurin hakar karatuna na gode, Allah ya saka da mafificin alheri.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.