Kwalliyar Matan Garin Gusau (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Kwalliyar Matan Garin Gusau (4)

NA

ƊAYYABA MUSTAPHA IBRAHIM

Kwalliya


BABI NA UKU

3.0 GABATARWA

A wannan babi na uku za a duba taƙaitaccen tarihin garin Gusau ta fuskar al’adunsu, saboda fito da al’adunsu waɗanda suka shafi rayuwar su ta yau da kullum, sannan a duba samuwar kwalliya domin sanin daga ina kwalliya ta samo asali, sai kuma a duba ma’anar kwalliya da nau’o’inta da kuma amfaninta, daga ƙarshe sai a kammala wannan babi.

 

3.1 TAƘAITACCEN TARIHIN GARIN GUSAU

Tarihin garin Gusau ta fuskar al’adunsu.

Ma’anar Al’ada:

Ibrahim (1982) ya nuna al’ada tana da ma’anoni daban-daban. Amma al’adar da muke nufi a nan ita ce wadda ta shafi abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya.

 

Al’ada ta ƙunshi hanyoyin zamantakewa na al’umma kamar zaman aure da sana’o’i da tsirface-tsirface da sauran matakan tattalin arziki da dangogin abinci da sutura da nau’o’in wasanni na al’umma da halaye da ɗabi’u da makamantan waɗannan hanyoyi na rayuwar ɗan-adam da suka gudana tun daga goyon ciki da haihuwa da balaga da aure zuwa bayan mutuwa.

Wasu Halaye da Ɗabi’un Gusauwa

Mutanen Gusau, gungun jama’a ne waɗanda Allah mai girma da ɗaukaka, ya haɗa su waje ɗaya, suke zaune a matsayi na uwa ɗaya uba ɗaya, ta haka suka haɗu, suka zamanto masoyan juna, masu ƙaunar juna, masu yi wa juna jinƙai har suka zama turaku kuma dirkoki waɗanda suke tallafawa juna, a lokacin da kowace dirka ta sami wani zazzabi mutane ne masu son ziyartar juna masu yiwa juna tarbiyya waɗanda kuma suka mayar da hankali wajen neman ilimi da raya shi tun ma ba ilimin addinin musulunci ba.

 

Har wa yau kuma, mutanan Gusau, mutane ne masu girmama baƙi, masu taimakon kai da kai, da yawa mutum kan raba gidansa ya ba baƙo ya zauna don girmamawa gareshi da taimakonsa, kuma su zauna zaman lafiya da jin daɗi kamar ɗan’uwansa. Ta haka ne ya sa duk wanda ya zo Gusau ko da da kwana ɗaya ne ba zai so ya bar ta ba, idan ma ya barta to Gusau kan zama masa abar so har ko yaushe a duk inda ya tafi sai ya ji yana son ya dawo mata. Har ma sarakuna da ma’aikata da ake kawowa daga Sakkwato, idan sun zo ba su san tashi don jin daɗin zaman garin ba tare da fitina ko tashin hankali ba. Son baƙin da ke gare su ya samo asali ne daga magabata, da suka ce “Gusau baƙi za su cika ta fal har a rasa wurin da za a zauna” (Hira da ƙungiyar Mutane, 1978).

 

Don haka mutanen Gusau ba sa gudun baƙo a ko ina ya fito suna yi masa maraba, saboda haka Allah ya hore wa mutanen Gusau ƙwazo na neman ilimi da harkokin safara da saye da sayarwa daga wajen ayyukan gona. Mutane ne waɗanda ba su son lalaci da raggwanci da rashin sanin ciwon kai, sukan yi faɗa matuƙa a kan mutum wanda suka lura bai kula da tsiwirwiri ko yin tanadi ko rashin aikin yi da sauransu (Hira da M.M.W.N.A Gusau, 1987).

 

Bukukuwan Al’ada a Gusau

Daga cikin bukukuwan alada da ake aiwatarwa a garin Gusau akwai bikin zanen suna da bikin Sallah ƙarama da bikin Sallah babba da kuma bikin takutaha, da sauransu. Ga bayaninsu daki-daki kamar haka:

 

Bikin Aure: Kamar yadda al’ada ta nuna iyayen da suke bidarwa ɗansu mata ba lallai sai ya tafi gidansu yarinya da kansa ba, akwai wanda ke sanin yarinya da ake nema masa aure kamar a lokacin tsarince ko wasannin gargajiya, wani kuma baya saninta har a kawo masa ita.

 

Kafin a ɗaura aure wani wanda ake biɗarwa yarinya sai ya tafi gidan iyayenta ya gaishe su har kuma ya yi masu wani ɗan aiki kamar gyaran katsugga ko darni da sauransu, wani kuma gayyar samari zai yi a tafi a nome gonar iyayen budurwarsa idan lokacin damina ne, wani ko huɗar gyaɗa ko auduga zai yi masu a wata gona ya kuma gyara ta har zuwa lokacin ɗiba. Akan yi shekara guda ko biyu ko fiye ana haka kamin a tabbata an ba mai biɗar yarinya.

 

Bayan haka sai a kai wa iyayen yarinyar dukiyar aure wato kuɗin neman aure da na raba wa dangi. Sannan kuma za a sa yaron ya tafi ya gaida iyayen yarinyar maza da mata wasu ko ba a tura su. Da ya gama zuwa gaida iyayen sai a ɗaura masu aure, a nan ne ake biyan sadaki. Bayan ɗaura aure da ɗam lokaci sai iyayen yarinya su shiga shirye-shiryen kaita ɗakinta. Su kuma iyayen mijin za su tanadi lefe su kai gidan su yarinyar wadda aka tabbatar wa yaronsu.

 

Yayen amarya suke yi wa amarya kayan ɗaki, sannan kuma su shirya amarya su yi mata dilka, ƙunshi, kitso, sannan kuma kwalliya, idan an kai amarya kamar yau da dare sai da safe su shirya kayan ɗaki wasu har doki suke gamawa da shi, gwargwadon ƙarfin iyayen, sannan kuma za su kai gara kamar nakiya da alkaki gidan su ango Iyayen ango su ka sai su shirya wa baƙi abinci iri-iri, kuma su yanka kaji da yawa ko ɗan bunsuru kamar bakwai ko fiye da haka a ɗauka a kai gidan amarya.

 

Idan ‘yan biki suka watse sai abokan ango su kai shi ɗakinsa bayan sun sayi kayan sayen baki, sannan kuma su a za wani kuɗi saman kayan wato kuɗin sayen baki, shi ke nan biki ya ƙare- sai neman zaman lafiya na ango da amarya (Hira da aka yi da M.M.W.N. da H.N 1978, Gusau).

Bikin Zanen Suna: Akwai mu da al’adar aikewa da yarinya mai ciki na farko gidan iyayenta idan cikin ya yi wata bakwai don ta haihu gaban uwarta ko wakiliyarta. Da matar mutum ta haihu sai mijin ya yi sayayyar kayan barka da haihuwa ko ‘yan biki kamar: itace da kayan yaji da gishiri da buhun gero da na dawa har da na shinkafa da garwar kananzir da fitilar kalai da zannuwan goyo da kayan jariri da sauransu. Idan namiji ne aka Haifa bayan kwana uku ake shan magani ko shan kimba, idan ko mace ce sai an kwana huɗu. Ranar shan kimba angon ƙauri na sayen ƙauri wato kan sa da ƙafafuwansa, wani ko har rago yake saye ya aika wa matar mai haihuwa.

 

Bayan haihuwa ta kwana shida iyayen mata suna aiko wa miji da walima ko gara wato su masa ko waina da alkaki da ‘yan kuɗi, shi ko zai sayi rago dan raɗawa abin da aka Haifa suna, da goro don rabawa a wurin naɗin sunan. A ranar sunan wani zai yanka raguna biyu, wani ko rago ɗaya da sa. Ida kuma haihuwar ta biyu ce fiye da haka ana sayen rago ɗaya ne a yanka, wani ko har biyu yake saye ya yanka (wato gwargwadon ƙarfin kowa).

 

Jama’a sukan taru dan naɗawa jariri suna a rana ta bakwai da haihuwa, dangin uba da na uwa ke zaɓin sunan da za a sa wa yaron, wani lokaci ko dangin uba ne ke zaɓe kawai. Har wa yau ranar suna mai jego ana mata kwalliya da ƙunshi da kitso. A ranar suna dangi na taruwa a ci a sha, daga nan idan marece ya yi sai ‘yan biki su watse wato kowace mace ta nufi gidan mijinta. A salin wannan taruwa don a yi wa jariri aski a taru ana kaɗe-kaɗe ana ba maroƙa da wanzamai samu don kuwa a taya mahaifan jaririn ko jaririyar murna da farin ciki (Hira da M.M.W.N Gusau 1978).

 

Bukukuwan Sallah: A garin Gusau ana bukin sallah ƙarama da sallah babbah. Bikin Sallah ƙarama, ranar sallah ƙarama ita ce 1 ga watan Shawwal, bayan musulmai sun ƙare azumin watan Ramadan, wannan rana ranar farin ciki ce ga dukkan musulmi babba da yaro, namiji da mace. Kafin zuwan wannan rana da ‘yan kwanaki kaɗan mutane ke ta shirye-shiryen zuwanta kamar ɗinka sababbin tufafi na maza da na mata, wato na ƙawar sallah, ana sallah saura kwana biyu zaka ga kowace mace zatayi ƙunshi da kitso su kuma maza zasu yi aski da safiyar sallah kowane mutum zai sanya sababbin tufafinsa da turare da takalma manya mutane kuma za ka gansu da rawuna, dukkan suna tafiya zuwa Idi wasu suna tafiya ƙasa ne wasu bisa dawaki ko kekuna ko Babura ko motoci, Sarki da hadimansa duka suna hawan dokuna ne zuwa faƙon Idi, sannan bayan sarki ya sauka daga bisa dokinsa sai liman ya shiga gaba a masallacin Idi ya yi sallah.

 

Bayan an taso daga Idi, da marece sai makaɗa da samari wato ‘yan maza da mata da ‘yan dame da ‘yan sharu da gardawa masu wasa da ma’aji da sauransu su taru a Kanwuri wato farfajiyar gaban ƙofar gidan Sarki, a yi ta shagulgula da wasanni har zuwa kwana bakwai, sannan a bar zuwa, a kuma ci gaba da harkokin duniya sosai da sosai kamar yadda aka saba.

 

Bikin Sallah Babba: Lokacin sallah babba, lokaci ne na tazarar wata biyu da kwana goma daga sallah ƙarama. Abubuwan da ake yi a babbar sallah ba su canza ba da na ƙaramar Sallah dangane da shagulgula da wasanni da waƙe-waƙe da sauransu, sai dai a ranar babbar sallah bayan an dawo daga Idi mai ikon layya zai yanka ragonsa na layya, Liman shi zai fara yanka ragon layya da zarar an gama sallah a faƙon Idi. Ba a son mutum ya yanka dabbar da musulunci ya ƙayyadewa wanda Allah ya ba iko ya yi sadakar da ita.

 

A Gusau mafi yawa a kan yanka raguna ne, sannan a feɗe su a yi masu tareni- tareni, a kawace su, idan an gama sai kowa ya ɗauki nasa tarenin na rago ko ragunan da ya yanka ya kai gida ya adana. Da wanshekare kimanin da hantsi, sai a shiga rabawa ga jama’a kamar yadda Allah ya ce a yi sadaka. Wato ranar Sallah babba kayan ciki ne kawai ake soyawa sai kashegari a soya sauran naman bayan wanda aka yi sadaka da shi.

 

A ƙaramar sallah da babbar sallah yara maza da mata na zuwa yawo gidajen ‘yan uwansu da abokan arziki suna barka da sallah suna basu ‘yan kuɗi.

Wasannin Gargajiya a Guau: Akwai wasannin gargajiya nau’i-nau’i waɗanda ake yi a Gusau, sannan a cikinsu akwai waɗanda yara maza suke yi da waɗanda yan mata suke gabatarwa kamar haka:

 

Wasannin Yara Maza: Gusau kamar a kowane gari, yara maza sukan yi wasanni iri-iri a filin wasansu, yara maza suna wasa ne da dare idan sun ƙare cin abinci, musamman a ranakun da ba a karatun dare, su yi ta wasa har zuwa lokacin sallar Isha’i sannan kowa ya watse. A ranar Alhamis da Juma’a yara kan yi wasa har da safe saboda ba ranakun karatu ne ba.

Yawancin waannin yara maza suna yin su ne da waƙoƙi daga cikin wasannin yara waɗanda suke shahara akwai:

1.      Wasan Darjin da jinni

2.      Wasan ‘Yarbifillata

3.      Wasan Tashe

4.      Wasan Wawwo

Wasannin Yara Mata: Kamar yadda wasannin suka shahara a tsakanin yara maza haka ma ‘yan mata ba a barsu a baya ba. Daga cikin wasannin ‘yan mata akwai:

1.      Wasan ‘Yar tshohuwa

2.      Wasan Namailaye

3.      Wasan Dantaralle

4.      Wasan Gyallare

5.      Wasan Wawwo

6.      Wasan Tashe

Wannan yan maza da ‘yan mata, yawancinsu, duk sai an gama da waƙa da rawa da taɓi, musamman ma yara mata zaka ga dukkan wasanninsu raye-raye ne da waƙe-waƙe kuma suna yi suna taɓa hannuwa. Bayan haka ‘yan mata duk wani ɗan lokaci kaɗan sukan fito da wata waƙa sabuwa tare da kuma launin wasanta (Hira da S.I.G da M.Y.M Gusua, 1978).

 

Waɗannan wasu muhumman al’adu ne waɗanda ake aiwatarwa a garin Gusau. Abubuwan da aka tattauna sun haɗa da wasu halaye da ɗabi’un Gusawa da bayani kan bikin aure da bikin salla babba da ƙarama, sai kuma wasannin yara maza da mata.

 

3.2 SAMUWAR KWALLIYA

Kwalliya aba ce wadda ta jima Hausawa mata suna yin ta, kuma bisa dukkan hasashe babu wani ɗan Adam da zai iya bayyana takamaiman lokacin da mata Hausawa suka fara yin kwalliya. Tun fil’azal Hausawa sukan yi kwalliya domin neman lafiyar jiki da kuma ƙara masa kyau.

 

Haka kuma a littafin Babul ya yi magana a kai sai dai bai tattauna wannan batun dalla-dallah ba, amma bai haramta yin ado da kuma kwalliya da gwalla-gwallai ba. Duk da haka, littafin Bable ba mai da hankali ga yin ado kawai ba a maimakon haka, ya ce abin da ya fi muhimanci shi ne mutum ya zama mai ladabi mai lafiya (Bitrus 3:34).

Mata masu aminci da suka yi ado ada. Rifkatu wadda ta auri ɗan Ibrahim mai suna Ishaku, ta yi kwalliya da Azurfa da zinariya da kuma wasu kayan ado masu tsada da baban maigidanta ya bat a. Sannan Esther, ita ma an bata “Kayan gyaran jiki don ta gyara jikinta da shi ta zama sarauniyar Daular Fasiya, wataƙila waɗannan kayan gyaran jikin sun ƙunshi “Kayan kwalliya kala-kala”.

 

Littafin Babule ya yi amfani da kayan ado wajen kwatanta wasu abubuwa masu kyau. Allah da kansa ya kwatanta sha’anin da ya yi da Isra’ilawa da macen da ta yi ado da tagulla da ‘yan kunne da kuma sarƙa, wannan adon ya sa al’ummar Isra’illa ta zama “kyakkyawa kwarai da gaske”.

 

Haka kuma a wasu ƙissoshin Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) an nuna kwalliya ta zo tun a lokacin da wata rana, wata matar wani sahabin Manzon Allah (SAW) ta je wajen Annabi Muhammad (SAW) wajen karɓar karatu sai ya ga hannunta wajen bashi littafi sai ya ce ta je ta bambanta kanta da namiji sai ta koma gida ta faɗa ma mijinta abin da ya ce sai wannan sahabin mijin nata ya ce ta yi ƙunshi wato lalle sai taji ta koma ko da ta koma ta miƙa hannu ta bashi sai ya ce mata a koda yaushe mata su rinƙa bambanta kansu da maza.

 

3.3 MA’ANAR KWALLIYA   

Kwalliya ita ce gyaran jiki wadda take ƙara ina mutum kyau da armashi mace, ko namiji yaro ko babba. Ana yin kwalliya domin ƙawata jiki gashin kan hannu, domin ƙara ma jiki kyau, wanda masu iya magana kance ko kana da kyau ka ƙara da wanka wato (Ƙishiya NHN 2006).

 

Kwalliya ado ce da yawanci mata suke yinta saboda su ƙawata kansu, ta hanyar shafe-shafe da lalle da kitso da sauran abubuwan gyaran jiki domin gyaran jikinsu da kuma bayyana kyawansu.

 

Kwalliya na nufin ƙawata wani abu domin ya ƙara fitowa da kyau, mutum ne ko wani abu wanda ba mutum ba wanda ake yi ma ado domin ƙara kawata abun dan ya ƙara kyau da sheƙi, amma kuma kwalliyar mutun to mata sun fi yin kwalliya, amma kuma kwalliyar wani abu ana yima abubuwa da yawa kwalliya kamar gidaje, motoci, kayan amfanin gida na yau da kullum (Yola 2014).

 

3.4 NAU’O’IN KWALLIYA

Akwai nau’o’in kwalliya na mata da dama da suka haɗa da:

1.      Kwalliyar jiki

2.      Kwalliyar fuska

3.      Kwalliyar ƙafa da hannu

4.      Kwalliyar gashin kai

5.      Kwalliyar saka sutura

Kwalliyar jiki: Kwalliya ce da mata ke cema dilka mata suna gyara jikinsu idan sunyi dilka wanda dilkan nan ita ce a ke haɗawa da dilka da kurku da lalle, da kwai sai a haɗa su waje ɗaya a shafe jiki da shi. Wannan gyaran jiki da mata suke yi na dilka yana gyara masu jikinsu sosai, ya fi kyau da sheƙi.

Kwaliyar Fuska: Kwalliya da mata suke yi ma fuskokinsu tun daga ido, hanci, baki, kumatu wannan kwalliya ta fuska ana amfani da abubuwa da dama wajen yin ta kamar su hoda, kwalli, jan baki, gazal, da sauransu. Waɗannan abubuwa suna sa fuska ta yi kyau idan anyi amfani da su, wasu ba’a ma ganesu saboda fuskar tasha kwalliya ba na wasa ba, wannan ma wani nau’i ne na kwalliya da mata suke yi domin ƙara fitowa a mace.

Kwalliyar Ƙafa da hannu:  Wannan kwalliya, ce da mata suke yi ma hannayensu da ƙafafuwansu da lallen gargajiya ko kuma na zamani domin ya ƙara fito wa da kyau ya yi sha’awar kallo. Wannan kwalliya ana yinta da abubuwa kamar su lalle, gishirin lalle, sajan, rani, dayis, haidurojin da sauransu. Haka kuma wannan kwalliya ta hannu da ƙafa ana amfani da warwaro kuffa, agogo, zobba da sauransu wajen kawata hannu.

Kwalliyar Gashin Kai: Wannan kwalliya mata suna yin ta domin gyara gashin kansu don ya ƙara tsawo da sheƙi, wanda sanadiyar gyara gashin kai sai kaga kai baya wari saboda gyaran da yake sha. Wannan kwalliya ana amfnai da mayukkan wanke kai kamar su shamfo, kumfallus, da sauransu. Haka kuma kwalliyar gashin kai ana yin kitso kala-kala wajen yinta.

Kwalliyar Saka Sutura: Wannan kwalliya ita ce wadda mata su ka fi mai da hankali akai domin idan an yi ƙunshi an yi kitso an yi kwalliyar fuska duka idan har ba a iya saka sutura ba sai kaga duk kwalliyar bata yi kyau ba, saboda suturar bata hau wannan kwalliyar ba. Akwai ire-iren kwalliyar saka sutura da dama wanda ko wace mace da yadda take so ta yi ta shigar misali, akwai mai son kwalliyar hijab, akwai mai son ta gyale, akwai mai son zani, wani siket wasu ma doguwar riga to kowace sutura da kalar kwalliyar da ta dace da ita.

Kwallyar Kunne da Wuya: Su ma dai ba a barsu a baya ba, domin kuwa suma mata suna yi masu kwalliya saboda idan duk ka gama komi ka fito babu kwalliya a kunne ko wuya zaka koma kamar namiji shi ya sa shima kunne da wuya ake yi masu kwalliya da ‘yan kunne da sarƙa irin su zinari, azurfa, GL, Fashion da sauransu domin ƙara fito da wuya da kunne dan kwalliya ta ƙara fitowa da kyau.

 

3.5 AMFANIN KWALLIYA

A ko wane abu na duniya yana da amfani yana kuma da illa to haka ita ma kwalliya tana da nata amfanoni da take da su kamar su:

-          Kwalliya ta na da amfani sosai wajen gyaran jiki irin su dilka, kurkur da sauransu yana sa jiki ya sulɓi, ya yi haske ya yi ta sheƙi. 

-          Kwalliya ta na taimakawa wajen gyaran fuskar mace, saboda akwai kayan kwalliyar da ake amfani da su da suke ɓatar da duk wani tambo da ya ke a fuska wanda idan an yi kwalliyar ba zai fito ba.

-          Kwalliya ta na taimakawa wajen gyaran jiki wanda ya kansa jiki ya sulɓi da sheƙi da taushi, saboda kayan da ake amfani da su wajen gyaran jiki.

 

-          Haka kuma kwalliya na taimakawa masu bille, ko tsaga, ko kwale domin kuwa idan an zo wajen kwalliya ana amfani da kayan kwallyar da zasu ɓoye wannan bille da yake a fuskar.

 

-          Sannan kuma kwalliya tana da amfani matuƙa wajen gyaran hanci saboda akwai kayan kwalliya yar da ake amfani da su wajen jan hanci da ya yi tsawo ya ƙara fitowa da kyau, sannan kuma ana yi ma hanci huji asa ‘yan kunne dan ya ƙara kyau.

 

-          Kwalliya tana taimakawa wajen fito da gashin gira, saboda idan kina da yawan gashin gira idan anzo wajen kwalliya ana gyara shi a rage mashi yawa dan kwalliyar ta fito yadda ya kamata ko kuma idan kina da watsatstsen gashin gira idan an zo wajen kwalliya ana gyara shi ya yi dai-dai, idan kwalliyar ta ƙara fitowa da kyau.

 

-          Sannan kuma kwalliya tana da amfani ga mata waɗanda basu da gashin saman ido. Saboda suma ba a barsu a baya ba, saboda akwai gashin da ake sawa idan an zo kwalliya wanda zai fito sosai kamar gashin ido. Shi ma ya na da matuƙar amfani ga kwalliyar fuska ta mata.

-          Haka kuma kwalliya tana taimaka ma ƙafafu, saboda idan an yi ƙunshi gargajiya yana ɓoye duk wani faso da yake cikin ƙafafu. Sannan kuma idan an yi jan lalle ko sajan ko na fulawa yana ƙara ma ƙafa kyau da sheƙi.

-          Kwalliyar hannu tana da matuƙar tasiri ga kwalliya, saboda idan an yi ƙunshi ga hannu an ka zana fulawa mai ja da baƙi yana ƙara ma hannu kyau.

-          Kwalliyar kunne tana da matuƙar amfani ga kwalliyar mata, saboda duk yadda aka yi kwalliya muddin babu ‘yan kunnaye kwalliyar bata yin kyau, ana amfani da yan kunnen zinari, azurfa, GL da kuma fashon wajen kwalliya.

 

-          Har ila yau kwalliya ta na da amfani wajen ɗaura dan kwalli saboda ita kwalliya idan an yi ta an yi mata ɗauri mai kyau zaka ga kwalliyar ta ƙara haskawa. Irin wannan ɗauri ya haɗa da ture ka ga tsiya, A’isha Buhari, Mai sitef da sauransu, idan an yi ko wane da kwalli yar da ta dace da shi yana ƙar haskaka kwalliyar.

 

3.6 KAMMALAWA

A wannan babi na uku an yi magana a kan taƙaitaccen tarihin garin Gusau ta fuskar al’adunsu na rayuwar yau da kullum, sannan kuma ma’anar kwalliya da samuwar kwalliya da kuma nau’o’inta da kuma amfaninta ga mata.

Post a Comment

0 Comments