Idan an yi tsai an lura za a ga hoton da ya bayyana da sunan littafin ta fuskar jigo-jimla a iya cewa saƙo ko jigon wasan na soyayya ne, bisa manufar da marubucin wasan ya tsara. Idan muka yi nazari ta jigo-tahaƙiƙi ma, za a ga hakan.
Sharhin Littafin Matar Mutum Kabarinsa
Ali Usman Umar
Translation Unit –
News and Current Affair Department
Kano State Radio
Corporation
alusumshariff@gmail.com
Marubuci: Bashir
Faruk Roukbah
Sunan Littafi: Matar Mutum Kabarinsa
Rukunin Adabi: Wasan Kwaikwayo
Harshe/Kari: Hausa/Daidataccen Karin Harshe
Maɗaba’a: Northern
Nigeria Publishing Company
Wurin Ɗab’i: Zaria, Nigeria
Shekarar Wallafa: 1974
Yawan Shafuka: 48
Marubucin
wannan littafi, Bashir Faruk Roukbah, tun daga hoton bangon littafin ya nuna
saurayi ɗaya da
’yanmata biyu. A inda ko mutum bai shiga cikin littafin ba, zai fahimci ruhin
soyayya da aure cikin wannan littafi. A gaba ɗaya
marubucin ya tafiyar da ruhin wasan ta hanyar nau’in wasan tir-madalla inda Nura ya ja zaren wasan tun daga farko har
zuwa ƙarshe a
matsayin jangwarzo. Da farko rayuwarsa ta ƙuntata
cikin wahalar soyayya da ya yi ta fama har ya haƙura,
amma sai ya kasance a ƙarshe ya sami farin ciki. Idan aka duba za a ga
marubucin ya tsara wasansa daki-daki ta kan lokaci-miƙe wato mai jeriya kamar cikin sarka—daga
farko sai tsakiya sannan ƙarshe. An
nuna cikin littafin cewa kafin a fara aure abu na farko tsakanin saurayi da
budurwa shi ne, fara jan hankalin juna ta hanayar kwarkwasa da jefa kalmomin
yabo da kuma so da ƙauna a tsakanin juna. Daga nan, sai a tsunduma cikin kogin soyayya
wanda zai kai ga yin aure. Wannan ita ce rayuwar da Bashir Faruok Roukbah ya
kalla, tare da nuna irin tankiyar da ke dabaibaye masoya a kan turbar soyayya.
Kuma wannan littafin wasan kwaikwayon ƙirƙirarsa mawallafin ya yi.
Jigo
Idan an
yi tsai an lura za a ga hoton da ya bayyana da sunan littafin ta fuskar
jigo-jimla a iya cewa saƙo ko
jigon wasan na soyayya ne, bisa manufar da marubucin wasan ya tsara. Idan muka
yi nazari ta jigo-tahaƙiƙi ma, za a ga hakan.
Warwarar jigo
A nan ne
za a fito da jigo-tahaƙiƙi, ta hanyar haƙiƙance
cewa jigon soyayya ne ko kuwa. Haka ma idan da wasu ƙananan jigogi za a yi ƙoƙarin tabbatar da
su. Idan aka duba waɗannan
wurare a cikin littafin za a ga yadda aka ayyana ƙwayar jigon soyayya cikin
wannan littafi. Misali:
NURA: Jimmai za ki karɓi
tawa gudummawar. Ko wannan ta ishe ku?
(shf. 6).
NURA: Haka kika faɗi
a fili, amma kuma ina matuƙar samun haka. (shf 8).
JIMMAI: Ai
babu komai idan ya ji ni da ma can ban damu da shi ba, don ba na son sa (shf
9).
NURA: Mai yiwuwa ne ki ji mamaki idan na faɗa miki irin soyayyar da na… (shf 10).
Daga abin da za a gani na ƙwayar jigon soyayya akwai
bayar da kyauta sai kuma a zo kan yaba kyauta da kalmomin soyayya. Kai a taƙaice duk fitowar da ta nuna Nura da Jimmai
akwai irin waɗannan
kalamai na soyayya. Haka ma, idan muka je ga kalaman Nura da Asabe. Misali:
NURA: Dalili shi ne soyayya wacce ba abin da ya gagara
ta sa mutum ya yi… (shf 30).
ASABE:…ina ganin shiga gidan masoyi ba wani abin
mamaki ba ne…(shf 31).
Kusan duk haɗuwar
Nura da Asabe, kamar irin haɗuwar Nura
da Jimmai ce.
Akwai wasu ƙananan
jigogi da suka fito cikin wannan wasa, kamar al’adun bikin aure da kuma
lalacewar tarbiyyar, musamman a tsakanin iyaye da ’ya’yansu. Misali, irin yadda
suke bijire wa ra’ayin iyayensu. Su kuma kafe a kan wanda suke so. Wannan a taƙaice kenan game da jigo da warwarar jigo.
Zubi da tsari
Marubucin
wasan ya tsara wasan cikin kashe-kashe guda takwas inda ya nuna matsayin Nura
da Jimmai da Asabe da kuma Sambo waɗanda
labarin ya fi karkata a kai. Sannan kowane kashi yana da fitowa-fitowa.
1) Kashi na farko na da fitowa uku. An nuna haɗuwar Nura da Jimmai a gidan Mudi da kuma
kan hanya. A cikin kashin an nuna matsalar munafurci da al’adun biki na zamani.
2) Kashi na biyu na da fitowa biyar, inda aka nuna
soyayyar Nura da Jimmai da kuma tankiyar/matsalar da ke tsakanin wannan
soyayya, wato Abdu wanda shi ya kasance a matsayin ma’aurinta tun na farko.
3) Kashi na uku na da fitowa huɗu, inda magabatan Jimmai ke yi mata faɗa kan kada ta sa su zama ƙananan mutane. A inda ita kuma ta matsanta
kan cewa Nura take so ba Abdu ba.
4) Kashi na huɗu
na da fitowa biyu. A ciki an nuna duk da irin matsananci halin da Nura da
Jimmai suka shiga, Allah bai ƙaddara za su yi aure ba. Amma sai ga Jimmai da
Abdu a matsayin ma’aurata.
5) Kashi na biyar na da fitowa biyar. A nan aka nuna
irin darajar da aure yake da ita. Kuma an nuna mana sabuwar alaƙar Nura da
Asabe, kuma an nuna yanayin soyayya irin ta baya ne, wato Nura da Jimmai
6) Kashi na shida na da fitowa uku. An nuna soyayyar
Nura da Asabe ta fara ƙarfi tare da cewa tana da ma’aurinta na fari, Sambo.
7) Kashi na bakwai na da fitowa uku – sha’anin Sambo
da Asabe na tasamma lalacewa. Amma ita Tabawa Mai Tuwo ta tsaya kai da fata kan
cewa Sambo take so Asabe ta aura. Nura kuwa, ya fara ƙosawa da halayyar Tabawa
Mai Tuwo.
8) Asabe ta ƙi sambo fafur, yayin da Nura ya fitar da
rai da Asabe, masu magana kan ce “matar mutum…” Dawowar Nura daga rangadi ya zo
ya ishe sabuwar amaryarsa a ɗaki.
Duba da irin yadda marubucin ya tsara tunaninsa, za a
ga zubin ya tafi daki-daki cikin tsarin lokaci mai jerangiya. Watau daga wannan
batu sai wancan: daga farko sai tsakiya sannan ƙarshe. Kuma idan an duba za a
ga hakan daga yadda kowanne kashi ke ƙulluwa da kashi mai zuwa, haka ma kowace
fitowa take nunawa – daga wannan batu sai mai biye masa. Sai dai, akwai buƙatar
a kawo jerin sunayen ’yan wasa da bayanin fage da sauransu. A don haka, za mu
ga cewa marubucin ya bayyana mana yanayin ala’adun soyayya da neman aure da
zamantakewa a ƙasar Hausa cikin wasan.
Salo da sarrafa harshe
Kamar yadda
za a gani marubucin ya yi amfani da salo mai ban sha’awa da jan hankali cikin
kalmomi da jumloli sauƙaƙa. A taƙaice dai,
solonsa ya yi armashi cikin sassauƙar zantarwa da ’yan wasa suka aiwatar – wato
babu kalmomin aro ko kalmomi masu tsauri. Haka ma zaɓen kalmominsa ya dace da yadda marubucin
ya ba wa kowane ɗan wasa. Misali, Nura da Jimmai da Asabe da Abdu da Sambo an
nuna cewa matasa ne kuma dukkan kalmomin zantarwarsu na matasa ne. Haka ma Mudi
da Kallamu da Mal. Hashimu sun zo a matsayin manya kuma kalmominsa sun dace da
matsayinsu cikin wasan.
Dangane da dabarun sarrafa harshe kuwa, an sami wurare
masu ɗan dama
da marubucin wasan ya ba wa, musamman ’yanmatan ko budurawoyin cikin wasan
damar yin karin magana da baƙar magana da habaici d.s. Misali tsakanin Jummai
da Abdu da kuma tsakanin Asabe da Sambo an sami irin waɗannan adon harshen ko
dabarun sarrafawa. Ga misalansu kamar haka:
Baƙar
magana:
JIMMAI:…ka faɗa mini nan gaba…(shf. 19).
JIMMAI :…idan ya zama fa? Sai kuma ƙaƙa?
(shf. 19).
ASABE:…Amma ai kai ne ka fara fito… ka san
kuwa idan kiɗa ya sauya rawa ma… (shf. 39).
ASABE:…Da haƙuri ta mutu sadakar me ka yi
mata? Kai malam ba na son tsotsogulon…(shf 39).
Karin magana:
JIMMAI:…A yi dai can matar kaɗaici ta jiyo guɗa a bayan gida… (shf 23).
NURA:…son maso wani ƙoshin wahala…(shf 27-28).
ABOKI NA UKU:…komai nisan dare gari zai
waye…duk sa’ada da ta yi tsami ma ji 929).
Adon magana:
ASABE:…labarin zuciya a tambayi fuska(shf 31).
SAMBO:…Da ma an ce dokin mai baki ya fi gudu (shf 30).
Siffantawa:
SAMBO: …kukan kurciya ma jawabi ne… (shf.45).
Habaici:
JIMMAI:…da ma an ce gwano baya jin warin jikinsa. Ko
an manta da zafin rana ne saboda yanzu ana cikin hunturu? Ba a san komai daɗewa,
bazara za ta sake dawowa ba? (shf. 22).
Kurman zance:
TABAWA MAI TUWO:…Ba shakka. Ai kamar mace ce mai ciki,
babu wanda ya san abin da za ta haifa sai ran da Allah ya sauke ta. Mu dai
fatanmu shi ne Allah ya tabbatar da abin da ya fi alheri. (shf. 34). d.s.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin adon harshe ko kwalliyar
magana da aka zaƙulo daga cikin littafin.
’Yan wasa
Wannan
wasa na ƙunshe da ’yan wasa da yawa amma biyar daga ciki, su wasan ya fi son nunawa.
Tun da an ce jigon soyayya ne, an tafiyar da shi ta kan ruhin wasan
tir-madalla.
Nura, Jimmai, Asabe, Abdu da Sambo su ne manyan ’yan
wasa. Amma za a iya cewa uku daga ciki su ne muhimman ’yan wasa wato: Nura da
Jimmai da Asabe.
Kowanne daga cikin ’yan wasan ya taka rawa muhimmiya.
Kuma ta kansu ne aka ga jigon wasan ya fito da kuma manufofin da ake son a nuna
wa mai karatu. Bisa la’akari da rawar kowanne daga cikin ukun nan, za a iya
fahimatar Nura a matsayin jangwarzo a wasan, wanda amonsa ya ja wasan tun daga
farko har ƙarshe – wato dai, shi ne ya yi dakon manufar da ta yi mamaya cikin
littafin.
Wasu dabaru cikin littafin Matar Mutum Kabarinsa
Baya ga
manyan tubalan nazarin da aka bayyana a sama, akwai wasu dabaru da wannan
littafin ya ƙunsa. Idan aka zurfafa wajen nazari wannan littafi na Matar Mutum Kabarinsa za a iya fitar da
abubuwa masu yawa da suka haɗa da yanayin zantarwa da tufafin wasa da yadda ake
tafiyar da wasa. Sai dai, a nan za a duba yadda aka tafiyar da wannan wasa
kamar haka:
Tankiya
Dole ne
wannan dabara ta bayyana a cikin kowane irin nau’in wasan kwaikwayo. A cikin
wannan wasan an sami tankiya a wurare biyu waɗanda kuma su ne suka ja hankalin
mai karatu.
Tankiyar farko ita ce tsakanin Nura da Abdu a kan
Jimmai. Masomin wannan tankiya ya faro tun daga shafi na (6) inda Mudi yake
cewa:
MUDI: … Da ba don tana makaranta ba, ai da tuni an yi
mata aure. Ka ga sa’o’inta duk suna ɗakunan mazarsu.
NURA: Cikin
hanzari: Ashe a halin yanzu ba ta da miji tukunna!
MUDI: Wa ya faɗa maka? Ai ba za ta kasa shekara biyar
da ɗaurarren aure ba. Ka tuna da yaron nan Abdu, malamin makaranta?
Daga ɓangaren Abdu, kuwa ya fara tun daga lokaci da
mutum na uku ya ishe shi har gida ya ba shi labarin abin da ke faruwa tsakanin
Nura da Jummai:
JIMMAI: Ai
babu komai idan ya ji ni da ma can ban damu da shi ba, don ba na son sa (shf
9).
MUTUM NA UKU: Abin da zan faɗa maka shi ne Nura, wan
matar surukinka…. suna ƙulle-ƙullen warware auranka da Jummai don Nura ya aure ta… kusan duk mutanen
unguwarmu sun sami cewa Jimmai tana zuwa gidan Nura. Idan kana shakka, to ka yi
bincike bisa wannan. (shf. 16-17).
ABDU:.. Yanzu Nuran da muka tashi tare gaba ɗaya ne
har yake yi mini wannan aiki? (shf. 17)
Wato duk da irin taurin kai da bijirewar Jimmai sai ga
Abdu a ƙarshe shi ne ya yi rinjaye kan Nura. Wannan tankiya ba ta zo wa Nura da
sa’a ko nasara ba, don kuwa bai yi rinjaye kan Abdu ba.
Tankiya ta biyu kuwa ta faru tsakanin Nura
da Sambo a kan Asabe. To, idan an duba littafin za a ga hakan.
Waraka
Duk inda
aka sami tankiya, to, akwai yiwuwar a sami waraka daga ƙarshe. Duk inda tankiya
ta mamayi zaren labari, lalle za ta zo ƙarshe.
Wato, idan an duba sha’ani Nura da Jimmai, bikin aurenta shi ne batun da ya
kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Nura da Abdu. To, amma masomin waraka a
nan ita ce tun daga lokacin da Mutum Na Uku ya ankarar da Abdu; sai kuma
matakin da Kallamu da Mal. Hashimu suka ɗauka na sanya ranar aure Jimmai da
Abdu. A tsakanin Nura da Asabe kuwa, sakamakon sawwaƙe wa Asabe da Sambo ya yi
ne, ta kawo ƙarshen tankiyarsa da Nura.
Zancen zuci
Marubucin
ya nuna wannan dabara a inda ya nuna Abdu a shafi na (16) da Jimmai a shafi na
(23). Abdu ya yi wannan lokacin da Mutum Na Uku ya zo masa da labarin matarsa
Jimmai. Ita kuma Jimmai ta yi wannan cikin tunani, yayin da ta dawo daga kiran
da Mal. Hashimu ya yi mata, wato lokacin da take dawowa gida ita kaɗai a kan
hanya.
Arashi
Wannan
dabara ta faru ga Nura a kashi na ƙarshe
fitowa ta II, game da abin da ya faru gare shi amma bai sani ba. Wato bayan ya
dawo daga rangadi sai ji ya yi ana yi masa guɗa ana kiransa ango. Nan ne fa ya
iske ɗakinsa ya tarar da amaryarsa ciki zaune.
Ba waɗannan kaɗai ne ba. Akwai sauran abubuwan da suka
shafi zantarwa (kamar taɗi da sambatu da muryar wasiƙa) da ba a faɗe su cikin
wannan ɗan ƙwarya-ƙwaryar nazari ba. Haka kuma, akwai buƙatar a duba lokaci ko
zamani da tufafin wasa da aukuwar lamura da isharori; tare da nazartar
tasirinsu a cikin wannan wasa. Amma idan an so, za a iya narzarta wannan
littafi na wasan kwaikwayo ta mabambanta fuskoki yayin da aka buƙaci yin
tarken-waje. Alal misali, za a iya kwatanta shi ta mahangar zahiriyya ko kuma
mararanci d.s.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.