Shaye-Shaye A Garin Gusau (1)

 Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Shaye-Shaye A Garin Gusau (1)

NA

BASHAR ISYAKA

Shaye-shaye


SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki nawa zuwa ga Mahaifiyata, Marigayiya Salamatu Isyaka Muhammad Birnin Magaji wadda Allah (SWA) ya yi wa rasuwa shekarun da suka gabata, domin ita ta bani ƙwarin gwiwa a wajen karatuna da kuma irin addu’o’in da ta yi mani a lokacin rayuwarta. Da fatar Allah ya jiƙanta da Rahama amin.

GODIYA

Ina matuƙar godiya ga Allah (SWA) mai kowa mai komai, mai iko a kan kowa, wanda ya ƙaddare ni da kammala wannan kundin dirigirina na farko. Ina salati Marar iyaka ga Jagoran wannan al’umma, Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da kuma waɗanda suka bi tafarkinsa har ya zuwa ranar ƙiyama.

Ina miƙa godiya ta musmaman ga Malam Aliyu Rabi’u Ɗangulbi, wanda ya kula da duba wannan aiki tare da ba da shawarwari haɗi da gyare-gyare, don tabbatar da wannan kundin bincike ya kammalu ta yadda zai zama mai amfani ga jama’a. Haka kuma ya taka gagarumar rawa wajen ganin binciken ya zama mai amfani ga al’umma ba tare da nuna gajiyawa ba, ina roƙon Allah ya cika masa burinsa, amin.

Haka kuma ina godiya ga Malamaina da suka shayar da ni ilimi kamar Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, da Farfesa Halliru Ahmad Amfani, da Farfesa Balarabe Abdullahi Ibrahim da Farfesa Magaji Tsoho Yakawada da Farfesa Muhammad Lawal Amin, Mal. Rabi’u Aliyu Ɗangulbi, Musa Abdullahi da Mal. Isah S/Fada da Sauran dukan Malaman da suka shayar da ni ilimi.

Haka kuma ina godiya ga mahaifina Alh. Isyaka Muhammad Birnin Magaji, wanda ya ba ni tarbiya tun ina ƙarami har Allah ya nuna man na kammala karatuna, bisa ga addu’o’i da shawarwari da taimakon da yake ba ni.

Haka ina miƙa godiyata ga matata Zainab Abuabakar da ‘ya’yana Abubakar, Aliyu da Hajaru (Khairat) da Yaya Amina, Yaya Ruƙayya, Yaya Luba, Yaya Jamila, Yaya Idris, Hajiya Balkisu, Hassan Isyaka, Ibrahim Isyaka, Aliyu Isyaka da dukkan suaran yanuwana maza da mata, Haka ba zan manta da abokan karatuna irin su Sani Adamu, Nasiru Hassan, Aliyu Salisu Ibrahim, Hizbullahi Ɗanlami, Ahmad M. Kabir Nura Sani Kwatarkwashi, Abdurrahman Bala, Abubakar Hassan, Mustapha Saidu, Amina Abubakar Moriki, Dayyaba Mustapha Ibrahim, Hassan Galadima, haka ina miƙa godiya ta musamman ga wanda yake taimakamun tun lokacin da muka fara wannan karatu har zuwa ƙarewa wato Alh. Hassan Ɗangaladima Birnin Magaji, haka ba zan manta da abokai na ba, wanda ya taimakamun sosai wurin wannan karatu wato Umar Dikko, da kuma Umar Liman Argungu, Nasiru Muhammad Lawal, Anas Abdulra’uf  da sauransu, dukkansu Allah ya saka masu da alkhairinsa, amin.

TSAKURE

Wannan bincike ya yi nazari a kan shaye-shaye da illolin shayaye, da masu yin shashaye, da wuraren da ake yin shaye-shaye da kayan da ke sa maye. Bugu da ƙari ya kawo mana yadda masu mu’amala da shaye shaye suke shiga wani hali na shiga bangar siyasa, sace sace, fyaɗe da sauransu. Haka kuma mun kawo hanyoyin da ya dace domin kawar da wannan matsala ta shaye-shaye a gaba ɗaya a garin Gusau.

Post a Comment

0 Comments