Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen
Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Shaye-Shaye A Garin
Gusau (2)
NA
BASHAR ISYAKA
BABI NA ƊAYA
1.0 GABATARWA
Dukkan yabo
da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin sarki, mahaliccin kowa da
komai. Tsira da amincin allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad
(SAW) da Sahabbansa da Alayensa da waɗanda suka bi shi da
kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bisa ga
binciken da nake son in gudanar a kan shaye-shaye a garin Gusau ya sa na ɗauki wannan
dama don in yi aikina a kan abin da ya shafi rayuwar matasa na wannan zamani
irin su, ‘yan wasan tsallake- tsallake da guje-guje da ‘yan aikin ƙwadago
da direbobi masu yin doguwar tafiya; kai har ma da makiyaya waɗanda ke
tafiye-tafiye zuwa wurare daban-daban da dai sauransu. Dukkan waɗannan rukunin
al’umma suna amfani da ƙwaya ko abubuwa masu
sa maye domin nishaɗi ko akasin haka.
Shaye-shaye
ba karamin tasiri ya yi ba wajen gurɓata taribiyar matasa a garin Gusau,
domin kuwa matasa masu shaye-shaye su ne ke aiwatar da abubuwa kamar irin su
bangar siyasa, da faɗace-gaɗace tsakaninsu da
sace-sace, da rashin ganin darajar mutane da rashin kyakkyawar manufa cikin
rayuwarsu ta yau da kullum.
Saboda haka ɗabi’ar
shaye-shaye ɗabi’a ce
wadda ta kawo matsaloli masu ɗinbin yawa, da kuma taɓarɓarewar
tarbiyar matasa ta kowane fanni; kamar yadda za’a gani a wannan bincike nawa.
1.1 MANUFAR
BINCIKE
Kundin
bincike na ɗaya daga
cikin abubuwa waɗanda ake buƙata
ga kowane ɗalibi kafin
ya kammala karatunsa a jami’i. Wannan shi ne zai bai wa ɗalibi damar
mallakar takardar shaidar kammala karatunsa. Wannan yana ɗaya daga
cikin manufar wannan bincike.
Haka zalika,
irin la’akarin da na yi da yadda rayuwar ɗabi’ar shaye-shaye ta
zama ruwan dare ga matasanmu ya sa na yi sha’awar gudanar da bincike a wannan
fanni na ilimi.
Saboda haka,
ganin yadda shaye-shaye ke ƙara ƙamari
ga rayuwar matasa ya ƙara mani ƙaimi
in yi bincike a kan wannan matsala, domin in ba da tawa gudummawa wajen magance
ko rage wannan mummunar halayyar ta shaye- shaye a zukatan matasa maza da mata.
Wannan mummunar ɗabi’a ta
taimaka wajen ruguza tarbiyar wasu daga cikin matasa, kasancewar yanzu halin da
ake ciki kashi sittin na matasa suna aiwatar da wannan mummunar ɗabi’a ta
shaye-shaye.
Har wa yau,
wannan bincike zai taimaka wajen jawo hankalin hukuma, musmaman wadda ke kula
da wannan ɓangaren na
Shari’ar Musulunci, da ta sa ido ga masu aiwatar da wannan ɗabi’a domin
ta ɗauki ƙwaƙƙwaran
matakin kawar da ita a cikin matasa.
A ƙarshe
wannan bincike zai taimaka ainun wajen magance wannan mummunar ɗabi’a mai
tarin illoli barkatai. Kuma zai nuna ma matasa ilolin da ke cikin wannan
mummunar aƙidar da suka ɗauka
gadan-gadan, wadda idan ba su bari ba, daga bisani za su yi da na sani. Ita
kuwa “da-na-sani ƙeyace, a baya ake barin ta”. Da fatan wannan
bincike zai yi tasiri ga rayuwar matasa da kuma al’umma baki ɗaya
1.2 DALILIN
BINCIKE
Kamar kowane
irin bincike da akan gudanar ana yin sa domin zaƙulo wasu
muhimman abubuwa da kila a da ba a san su ba, ko kuma an sani amma ba a kula da
su ba. Ko kuma ba a taskace su ba domin amfanin masu nazari. Hausawa na cewa
“kowa ya yi da kyau zai ga da kyau” . Wannan magana ta yi dai dai da dalilina
na yin wannan bincike. Dalili ke nan da ya sa na ja ɗamara na kuma
zage damtse domin in yi nazari a kan wannan matani mai taken “shaye-shaye a
garin Gusau”. Ga dukkan alamu wannan bincike shi ne irinsa na farko da aka
aiwatar a kan abin da ya shafi illolin shaye-shaye a tsakanin matasa a garin
Gusau. Don haka wannan shi ne babban dalilin da ya sa na zaɓi wannan batu
in yi nazari a kansa domin in zaƙulo illolin
da shaye-shaye ke haifarwa ga rayuwar matasa. Da fatar Allah ya ba ni ikon
aiwatar da wannan bincike cikin nasara.
1.3 MUHALLIN
BINCIKE
Wannan
bincike da zan gudanar a kan shaye-shaye a garin Gusau, bincike ne da ya shafi
rayuwa ta yau da kullum da matasa ke ciki. To da haka ne na ga ya kamata in yi
rubutu a wannan fanni, domin in ba da tawa gudummawa a wannan ɓangare, haka
kuma binciken zai taƙaita ne a garin Gusau
domin nan ne matattarar matasa masu irin wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye
ta yanke cibi.
1.4 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
Kowane
al’amari akwai hanyoyi da dabarun da ake bi domin gudanar da shi. Haka ne ya sa
wannan aikin zan bi wasu hanyoyi wurin aiwatar da shi, domin samun nasarar
kamala shi cikin sauƙi.
Hanya ta farko
da za ni yi amfani da ita, ita ce ta yin amfani da kundayen bincike da kuma
wasu littafai da aka wallafa masu alaƙa da wannan
bincike. Haka kuma zan ziyarci ɗakunan karatu daban-daban, domin duba
ayyuka musamman waɗanda suka jibinci tarbiya da ɗa’a a makaratu
domin samun ƙarin bayani a kan nawa aikin.
Wata hanya da
zan yi amfani da ita ta huɗu itace ta amfani da ƙasidu
da mujallu da jaridu masu bayani a kan ilolin shaye-shaye. Haka kuma wata hanya
da zan yi amfani da ita wurin tattara bayanai ta haɗa da tuntuɓar wasu
malaman addini domin jin ra’ayoyinsu dangane da wannan ɗabi’a ta
shaye-shaye. Bugu da ƙari zan tuntubi wasu
daga cikin waɗanda abin ya
shafa wato matasan da wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye ta zama masu alaƙaƙai
a zukatansu. Har wa yau bincike zai gana da jami’an hukumar yaki da safara da
shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta ƙasa
domin samun ƙarin bayani dangane da illolin wannan ɗabi’a a
tsakanin al’umma musamman matasa.
1.5 HUJJAR CI
GABA DA BINCKE
Akwai ayyuka
da dama da aka riga aka gudanar a wannan fage, waɗanda sun suka
rawar gani wajen faɗakarwa da tunatarwa ga al’umma, da kuma nuna
masu illar shaye-shaye.
Waɗannan
rubuce-rubuce sun nuna wa jama’a muhimmancin kyakkyawar tarbiyya ga matasa ta
yadda za su kasance ‘yan ƙasa na gari. A
sakamakon ayukkan da suka gabata an samu nasarar rage wannan mummunar ɗabi’a ta
shaye-shaye. Haka kuma an samu rage gurɓatar tarbiya. Amma
duk da haka za a iya cewa “akwai sauran rina a kaba”, watau akwai buƙatar
a sake mai da hankali a waɗannan fannoni domin ganin cewa an ci
nasara ɗari bisa ɗari, wajen
kawar da wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye a cikin al’umma.
Saboda haka
ne na ga ya kamata in cigaba da bayar da gudummawa, watau in yi iyakar abin da
nake iya yi na ci gaba da bincike a wannan fanni. Domin a samu nasarar kawar da
wannan mummunar ɗabi’a ta
shaye-shaye a garin Gusau.
1.6 BITAR
AYYUKAN DA SUKA GABATA
Masana da
manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce a wannan fanni na ilimi, saboda haka ya
zama dole in bayyana inda nawa binciken ya dosa. Sannan kuma in faɗi wasu daga
cikin rubuce-rubucen da aka aiwatar a wannan farfajiya ta fannin ilimi.
A cikin wani
sharhi da wani shehin malami ya yi watau (Narahatsi) watau mai nazari a kan ƙwayoyi,
wanda ya fito daga arewa maso yamma a wata babbar asibiti da ke chicago. Cewa
ya yi ‘nikotin’ yana haifar da yawan mutuwa kuma yana rage wa mai shakensa
karfin nazari a kwakwalwarsa. Sannan kuma ya ce “giya da Nikolin (koken) suna da tasiri ga mai amfani da su,
amma a lokacin da ya mai da hankalinsa gare su suna illata shi ainun.
Bisa ga
maganar kambri (1993) cewa ya yi ‘ƙwaya wadda
ita ce mataimakiyar rayuwa, amma yanzu ta koma shaye-shaye, ta kuma haifar da
ruɗani ga
jama’a. To ita wannan ƙwaya kamata ya yi a
yi hani daga shanta.
Idan muka
duba za mu ga dukkanin kundayen da aka yi bayani a sama sun kalli fuskoki
daban-daban da nawa binciken. Ni kuma nawa binciken zai mai da hankali ne
kacokan kan shaye-shaye a garin Gusau. To amma idan muka duba waɗannan ayukka
da suka gabata kusan abubuwa ne da suka danganci junansu sai dai kowane aiki
akwai inda ya dosa.
1.7 KAMMALAWA
Wannan babi
ya yi magana a kan abubuwan da suka shafi gabatarwa da manufar bincike, dalilin
bincike muhalin bincike, hanyoyin gudanar da bincike, hujjar cigaba da bincike
da kuma bitar ayukkan da suka gabata, daga ƙarshe sai
kammalawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.