Ticker

Shaye-Shaye A Garin Gusau (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Shaye-Shaye A Garin Gusau (5)

NA

BASHAR ISYAKA

 

Magani

BABI NA HUƊU

4.0 GABATARWA

Wannan babi zai tattauna ne a kan hanyoyin kawadda shaye-shaye wuɗanda sunka haɗa da: Shigowar kungiyoyin addinai, ƙoƙarin al’umma ga kawadda shaye-shaye, ƙoƙarin kungiyoyin da ba na gwamnati ba, ƙoƙarin da hukuma ke yi ga kawar da ɗabi’ar shaye-shaye a cikin al’umma, da sauransu.

 

4.1 SHIGOWAR ƘUNGIYOYIN ADDINAI

Addinai da dama sun yi hani a kan wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye musamman ma addinin musulunci Allah (SWA) ya faɗa a cikin littafinsa mai girma “Ya ku masu imani ka da ku sha giya ko wani abu da ke sa maye…..” Sannan Manzon Allah (SAW) ya ce, “duk wanda ya sha giya sau ashirin Allah ba ya tare da shi”. Bayan haka, Annabi (SAW) ya ce, Allah ya la’anci mai shan giya da mai sayar da ita da mai aikinta da mai ɗaukar ta da wanda ya taimaka wajen daukar ta, da kuma wanda ya ci kuɗinta. Kuma Allah (SWA) ya ce; “Mutane uku ba su shiga al-jannah, daga cikinsu akwai mashayin giya”, bugu da ƙari Annabi (SAW) ya ce; “Wanda ya sha giya kamar mai bautar gunki ne”. Wannan shi ne hanin da addinin musulunci ya yi dangane da ɗabi’ar shaye-shayen abubuwa masu sa maye.

 

Haka kuma, addinin kiristanci shi ma ya yi hani a kan wannan mummunar ɗabi’ar, domin kuwa a cikin littafin Injila (Bible) wanda aka saukar ma Annabi Isah (AS), Allah ya ce “Na haramta maku cin mushe, da jini, da alade, da zina da sihiri da giba da duk abinda ke sa maye…..” (Bible babi na ɗaya aya ta goma).

 

Bayan addinin kiristanci, haka ma sauran addinai da dama su ma sun yi hani a kan  wannan shaye-shaye kamar yadda addinin musulunci da na kiristanci suka yi hani. Sun yi hani da wanda yake cikin halin maye ya yi wakilci ko jagoranci a cikin al’amuran yau da kullum. Haka kuma bayan hani da addinin musulunci da na kiristanci suka yi, shaye-shaye yana karya tattalin arzikin ƙasa sannan kuma yana illa ga lafiyar mai yin sa.

 

4.2 ƘOƘARIN AL’UMMA GA KAWAR DA SHAYE-SHAYE

Shaye-shaye ɗabi’a ce mai zubar da mutuncin mutum. Akasari mutane kan ɗauki wanda ke shaye-shaye a matsayin mutumin banza, kuma marar mutunci. A taƙaice dai duk mai wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye komi kuɗinsa ko iliminsa mutuncinsa da ƙimarsa kan zube a idon jama’a idan yana shaye-shaye.

 

Mutane kan kalli mutumin da ke shaye-shaye kamar dabba, domin dabba ita ce ba ta san abin da zai hallaka taba, sai in ta ji ya cimma ta. To haka nan mutumin da ke shaye-shaye yake. Saboda su waɗannan kaya na barasa da yake sha suna haifar masa da cututtuka daban-daban a cikin jikinsa. Amma saboda dabbanci (rashin kaifin hankali), ba zai gane abin da ke halaka shi ba.

 

Haka kuma wasu jama’a kan ɗauki masu wannan ɗabi’a tamkar mahaukata, domin idan mashayi yana cikin halin maye za ka ga wani lokaci har bugu yake yi. Kuma sukan yi abubuwa kamar mahaukata, saboda duk wani abu da mahaukaci ke yi shi ma a wannan lokaci zai iya yin sa, domin ba ya a cikin hankalinsa. Wannan ne ya sa mutane ba su ɗauki wanda ke shaye-shaye a matsayin cikakken mutum ba. Kuma za ka ga mutane suna kyamar shi da ya wakilcesu a al’amurran yau da kullum domin suna ganin ba ya da cikakken hankali.

 

A taƙaice dai al’umma kan ɗauki duk mutumin da ke shaye-shaye a matsayin mutumin banza.

 

4.3 ƘOƘARIN ƘUNGIYOYIN DA BA NA GWAMNATI BA

Kasancewar shaye-shaye mummunar ɗabi’a ce da ke zubar da mutuncin ɗan Adam da kimarsa, akwai ƙungiyoyi masu zaman kansu waɗanda suka tashi tukuru wajen yaƙi da wannan mummunar ɗabi’a ta kwankwaɗar barasa. Waɗannan ƙungiyoyin sun haɗa da Hukumar Hizba da ‘yan banga da ‘yan agaji da sauran ƙunyoyi na cikin unguwani. Haƙiƙa waɗannan ƙungiyoyi ba ƙaramar rawa suke takawa ba wajen magance wannan ɗabi’a. Sannan kungiyoyin malamai tun daga na gwamnatin tarayya har na jihohi musamman ma Malaman addini na cikin wannan jiha suna ƙoƙari ƙwarai wajen yin wa’azi tare da faɗakar da masu shaye-shaye, game da illolin da shaye-shaye ke haifarwa a al’adance da kuma a addinance.

 

Sannan kuma ƙungiyoyi irin su ƙungiyar ‘yan jarida watau (Ratawo) gidajen rediyo da talabijin da ƙasidu da mujallu suna taimakawa matuƙa wajen faɗakarwa ga illolin da ke tattare a cikin wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye.

 

Haƙiƙa wannan faɗakarwar da suke yi dare da rana tana taimakawa ainun wajen kawar da wannan mummunar ɗabi’ar ta shaye-shaye.

 

Bayan wannan akwai wata ƙungiya mai zaman kanta, ita wannan ƙungiya ta matasa ce wadda ke sa ido ƙwarai da gaske domin ganin an kawar da wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye a cikin wannan gari na Gusau.

 


 

4.4 ƘOƘARIN DA HUKUMOMI KE YI GA KAWADDA ƊABI’AR SHAYE-SHAYE A CIKIN AL’UMMA

A ƙoƙarin da hukumomi ke yi na ganin cewa ta kawar da wannan mummunar ɗabi’ar ta shaye-shaye, ta kafa ƙungiyoyi da dama. Irin waɗannan ƙungiyoyin sun haɗa da ƙungiyar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi (NDLEA). Ita wannan ƙungiya ta taimaka ainun wajen binciko masu shaye – shaye da kuma hukunta su.

 

A cikin shekarar (1983) shan miyagun ƙwayoyi a Najeriya ya zama ruwan dare. Saboda haka ne gwamnatin tarayya ta mulkin soji ƙarƙashin jagorancin janar Muhammad Buhari a cikin shekara ta (1984) ta yi ƙoƙarin magance wannan mummunar ɗabi’ar, inda ta ƙirƙiro wani shiri na musamman watau (laifukkan gobe). Shi wannan shiri an shirya shi ne domin faɗakar da masu wannan ɗabi’a. Sannan gwamnati ta samar da dokoki domin hukunta masu wannan ɗabi’a ta shaya-shaye.

 

Haka zalika, da aka samu canjin gwamnati a shekara 1985 a ƙarƙashin jagorancin janar Ibrahim Badamasi Babangida, Gwamnatinsa ta ba da ƙarfi ne wajen hana shan ƙwayoyi da barasa da kuma hana yawace yawacen banza a cikin ƙasa. Wannan gwamnati ta ɗauki alkawarin bincikowa da kuma hana amfani da kayan barasa a cikin Najeriya.

 

Sannan kuma a shekarar 2000 ma gwamnatin jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura ta ɗauki babban mataki ga dukkan masu wannan ɗabi’a ta shaye-shaye. Ta hanyar rufe duk wani wuri da ake shaye-shaye a cikinsa. Haka kuma da ɗaukar matakin hukunta duk wanda aka kama yana shan wani abu mai sa maye bayyane ko a ɓoye. Sanadiyar haka gwamnatin jihar Zamfara ta ɗauki aniyar magance matsalolin kwankwaɗar barasa musamman ma a cikin ƙaramar hukumar mulki ta Gusau. Wannan gwamnati ta lashi takobin ganin cewa ƙwanƙwaɗar miyagun ƙwayoyi zai zama tarihi a wannan jiha.

 

Bisa nazari da ƙiyastawa daga shekara ta (2000-2007) an samu sauƙi yadda ya kamata na kawar da ɗabi’ar shaye-shaye a cikin garin Gusau.

 

4.5 KAMMALAWA

Wannan babi na huɗu yana bayani ne a kan hanyoyin kawadda shaye-shaye waɗanda suka haɗa da shigowar ƙungiyoyin addini da ƙoƙarin al’umma ga kawar da shaye-shaye. Haka kuma da ƙoƙarin kungiyoyi da ba na gwamnati ba suke yi, da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi ga kawar da ɗabi’ar shaye-shaye a cikin al’umma.

Post a Comment

0 Comments