Shaye-Shaye A Garin Gusau (6)

     Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Shaye-Shaye A Garin Gusau (6)

    NA

    BASHAR ISYAKA

    Shaye-shaye 

    BABI NA BIYAR

    KAMMALAWA

    5.0 GABATARWA

    Babi na biyar kammalawa, wannan babi na biyar shi ne na ƙarshe wanda ya ƙunshi taƙaitawar aikin da aka gudanar, sakamakon bincike, shawarwarin marubuci, naɗewa sai manazarta.

    5.1 KAMMALAWA

    Dukkan godiya ta tabbata ga Allah (SWA) da ya ba ni ikon kammala wannan aiki, wanda yana É—aya daga cikin sharuÉ—É—an kammala karatun mallakar takardar shaidar Digiri na É—aya.

     

    Lura da irin mawuyacin halin da matasanmu suke ciki game da gurɓacewar rayuwa ta hanyar amfani da miyagun ƙwayoyi, shi ya ba ni ƙwarin gwiwa wajen gudanar da wannan bincike.

    HaÆ™iÆ™a a wannan binciken na gabatar da abubuwa daban-daban waÉ—anda suka haÉ—a da ma’anar shaye-shaye. A wannan kundin bincike na ji cewa shaye-shaye wani abu ne da ke haifar da maye, kuma an ji irin abubuwan da ke haifar da maye waÉ—anda suka haÉ—a da, giya, wiwi, shalinsho, da dai sauransu.

    Haka kuma an ji illolin da ke tattare a cikin wannan É—abi’ar ta shaye-shaye, da nau’o’in mutanen da ke shan abubuwa masu haifar da maye. Bugu da Æ™ari an bayyana tarbiyya da cewa reno ne na Æ™ananan yara ta hanyar nuna masu abin da ya kamata da nuna masu abin da bai kamata ba. Sannan a hore su da su guje shi domin su zamo masu kyakkyawar É—abia, abubuwan da ke kawo taÉ“arÉ“arewar tarbiyya tare da kawo hanyoyin da za a bi domin magance matsalar.

     

    Bayan haka a cikin wannan kundin bincike nawa an bayyana irin hanin da addinai suka yi dangane da mummunar É—abi’a ta shaye-shaye da kuma Æ™oÆ™arin da gwamnati ke yi da wasu Æ™ungiyoyin sa kai na ganin an kawar da wannan É—abi’ar ta shaye-shaye. Daga Æ™arshe an bayyana hanyoyin da za a bi a magance wannan matsala baki É—aya.

     

    5.2 SAKAMAKON BINCIKE

    Sakamakon bincike shi ne yake bayyana irin abubuwan da shaye-shaye ke haifarwa ga rayuwar masu yin sa da kuma al’umma da ke kewaye da su, kadan daga illolin da ya haifar da lalaci, jahilci da zaman kashe wando. Haka kuma yakan haifar da rashin lafiyoyi daban daban ga rayuwar mai yinsa. Haka kuma illolin shaye-shaye ga al’umma, masu shaye shaye sukan dami al’umma da sace-sace, fizgen wayoyi, fyaÉ—e, sare-sare, da sauransu.  Daga Æ™arshe, sakamakon binciken ya gano irin illolin da shaye-shaye ke haifar wa ga masu yin shi da kuma al’umma baki É—aya.

     

    Misali yawan mahaukata da masu ciwon faɗuwa a sanadiyar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauransu.

    5.3 SHAWARWARI

    Kasancewar wannan bincike nawa, bincike ne wanda ya shafi shaye-shaye da faÉ—akarwa ga al’umma. Tabbas wannan mumunar É—abi’a abar Æ™yama ce da ke ci gaba da gudana a cikin wannan al’umma tamu. Saboda haka, shawarwarin da za ni bayar a cikin wannan bincike nawa mai taken “Shaye-Shaye a Garin Gusau” su ne kamar haka:

     

    1.      Shawara ta farko da za ni bayar ita ce akwai buÆ™atar gwamnati ta sanya wannan fanni na tarbiyya a cikin manhajar karatun Æ™ananan makarantu. Domin inganta tarbiyar yara kafin su balaga har su san abinda ake nufi da shaye-shaye da ayyukan baÉ—ala cikin al’umma, domin yaro tun yana Æ™arami in ya Æ™yamaci abu ko da ya girma ba zai yi shi ba. Wannan zai taimaka ainun wajen kyautata tarbiyar yara kafin su kai manyan makarantu.

     

    2.      Bayan haka, ina mai ba da shawara ga É—alibbai ‘yanuwa na masu nazarin harshen Hausa su Æ™ara faÉ—aÉ—a bincike a wannan fanni domin Æ™ara fitowa da illolin shaye-shaye fili don masu wannan mummunar É—abi’ar su guje ta baki É—aya.

     

    3.      Haka zalika, akwai buÆ™atar marubuta littafai su tashi tsaye tuÆ™uru, su ci gaba da wallafa littafai waÉ—anda ke nuni a kan illolin wannan mummunar É—abi’a. Sannan ya kamata masu gudanar da wasan kwaikwayo su bayar da tasu gudunmuwa wajen shirya wasanni, waÉ—anda ke faÉ—akarwa dangane da rashin kyawon wannan É—abi’a ta shaye-shaye.

     

    4.      Daga Æ™arshe ina ba da shawara musamman ga malaman Firamare da na sakandare da su tsaya tsayin daka wajen bayar da tasu gudunmuwa a lokacin da suke koyar da yara domin tarbiya ba ta rataya ga iyaye ba kawai har da Malamai.

    WaÉ—annan su ne shawarwarin da na bayar a cikin wannan bincike da na gudanar. Da fatan za’a karÉ“i shawarwarin da na bayar domin cimma nasarar kawar da wannan dabi’ar baki É—aya.

     

    5.4 KAMMALAWA

    Wannan babi kammalawa ce ta aikin da aka gudanar akan shaye-shaye, babin ya yi bayani akan abubuwa kamar gabatarwa, taÆ™aitawa game da aikin da a ka gudanar, haka kuma an bayyana sakamakon bincike, da shawarwari/ ra’ayin marubuci, daga Æ™arshe sai manazarta.

    MANAZARTA

    Tuntuɓi masu gudanarwa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.