Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (1)

     Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (1)

    Na

    AMINU MURTALA

    kwatarkwashi

    SADAUKARWA

    Ni Aminu Murtala, na Sadaukar da wannan littafin kundin digirin farko da na yi a sashen Harsunan Nigeriya a jami’ar Tarayya Gusau.

    Na sadaukar da shi ga Ɗa na shi ne Al-Ameen Aminu Murtala da Babata da Mahaifina su ne Hajiya Habiba Muhammad Kwatarkwasi da Alhaji Murtala Salisu Kurah, Kwatarkwasi wanda shi ne ya ɗauki nauyin karatuna tun daga furamari zuwa sakandare har in da Allah ya kai ni a yanzu. Don haka ina mai roƙon Allah dare da rana da cewa Allah ya saka masu da mafificin Alkhairi ya kuma sa su gama lafiya da duniya ya sa su Aljannar Firdausi ce makomarsu, Amin.

    A kan haka ne na sadaukar da shi zuwa ga matata da yannena da Æ™anne na tare da ‘yan uwa da abokan arziki da na nesa da na kusa, da ma dattijai da samari da É—iyan yanne na da na Æ™anne na da waÉ—anda suka taimaka mani wurin nazarin da binciken a kan hirar da nayi da su daban-daban da wanda shi ne magatakardan masarautar kwatarkwashi ya taimaka mani wurin haÉ—a mani wasu kayan da suka taimaka mani don rubutu wannan kundin digirin farko a sashen Nazarin Harsunan Nijeriya (B.A Hausa) Jami’ar Tarayya Gusau.

    GODIYA

    Ina mai godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai kowa mai komi mai Rahama mai jinƙai zuwa ga bayinsa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (S.A.W) da sahabbansa da zuriyarsa da dukkan wanda ya bishi zuwa ranar sakamako, Amin.

    Bayan haka, ina mai nuna farin cikin godiya ta ga malamai na na sashen nazarin harsunan Nijeriya tare da irin gudummuwar da suka bani taimakawarsu har Allah ya kawoni wannan lokacin da nike haɗa kundin digirin farko a bisa ga haka ne nake ƙara yiwa Allah Maɗaukakin Sarki godiya a kan wannan baiwar da ya bani ALHAMDULILLAH godiya ta tabbata ga Allah.

    Ina mai nuna godiya ta musamman ga Shugaban sashen nazarin harsunan Najeriya wanda ya bani shawarwari a kan yadda za a wannan binciken cikin tsanaki tare da ban sha’awa Æ™warai shi ne Prof. Aliyu Muhammad Bunza, da sauran Malaman sashen nazarin da suka taimaka wurin aikin littafin ya gudana kamar su Malam Rabi’u ÆŠan gulbi da Malan Musa Fadama da Malan  Isah S. Fada da Malan S. Gulbi da Mallan Yakawada da Malan S. Gubir da Malan Balarabe da Mallan Imrana da dai sauran Malaman da ke sashen nazarin harsunan Nijeriya ina mai godiya a garesu bisa ga gaggarumin gudummawar sa suka bani Allah MaÉ—aukakin Sarki ya saka masu da alkhairinsa ya kaisu makomar Aljannar Firdausi.

    Godiya ta musamman ga Malamina wato Malan Musa Abdullahi wanda shi ne ya yi ta É—awainiyar duba wannan aiki tare da ba ni shawara ba bu gazawa dare da rana, kuma babu fushi ko nuna gajiya a duk lokacin da na sameshi, Allah MaÉ—aukakin Sarki ya saka masa da mafificin alkhairinsa ya kuma saka masa da Gidan Aljannar Firdausi, amin.

    Daga Æ™arshe, ina miÆ™a godiya ta ga abokaina waÉ—anda muke karatu tare kamar Jafar Usman da Mukhtar Abbakar da Sama’ila Aliyu da Bashar Haruna da Bilya Umar da Umar Yahaya Dogara da Abdulrahman Lawal da Sadiya Kabiru da kuma Shafa’atu Salihu Labbo da ma waÉ—anda suke abokai ne na gida, musamman Abubakar Muhammad da Nafi’u Ibrahim da Yusha’u Ibrahim da Murtala Lawal da Nafi’u Bello da Shafi’u Sulaiman da Aminu Totti da dai sauransu.

    Ba zan manta da manyan yanne kamar yaya Mukhtar da Anty Halima da yaya Surajo da Lukman da Marigayi Ibrahim Allah ya gafarta masa zunubbansa, Haka ƙanne kamar Ashiru da Mannir da Sakina da Nafisa da Haulatu da Aisha da Sumayya da Saifullahi da Abdulmuɗallib da Baihaƙi da Ummulkhairi da Usman da Maryam da Abdulmajid, da dai sauransu. Nagode Aminu Murtala.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.