Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

    Na

    AMINU MURTALA

     

    Kwatarkwashi

    BABI NA ÆŠAYA

    1.0              Gabatarwa

    Tarihi abu ne mai Muhimmanci da ke kawo abubuwan da suka gabata kuma ya fito da halin da ake ciki a yanzu da hasashen gaba. Tarihin masarautar kwatarkwashi mai bincike zai yi bayani ne kacukan a kan wannan masarautar tun daga yanayin ƙasar da yadda suke gudanar da harkokin sarautar su da abin daya shafi harkokin rayuwarsu na yau da kullun.

    Binciken zai yi bayanin yadda Æ™asar kwatarkwashi take tun gabanin jihadin Shehu Usman Danfodiyo da kawo tarihin mai martaba sarkin kwatarkwashi na yanzu, da kuma kawo sunayen sarakunan da suka riÆ™i Æ™asar kwatarkwashi tun daga sarki na farko har zuwa sarki na yanzu wanda yake akan mulki. Haka nan kuma mai bincike zai yi bayanin yadda ake É—auko maiki a kan dutse da wasar Baura da kuma yadda ake sauya sarakuna a Æ™asar kwatarkwashi.   

     

    1.1              Manufar Bincike

    Manufar bincike shi ne a fito da abubuwan da yasa mai bincike ke so ya nuna wa mutane wanda ba’a sani ba musamman tarihin masarautar kwatarkwashi, duk da za’a samu kundayen da suka yi tsokaci a kan Æ™asar kwatarkwashi ko wani abu daya shafi Æ™asar kwatarkwashi, sai dai za’a samu cikakken bayani ba kamar yadda mai wannan bincike ya gudanar da wannan aiki, saboda shi É“angare ne da yake Magana akan tarihin masarautar kwatarkwashi.

     

    1.2              Dabarun Bincike

    A wannan bincike, mai bincike ya bi hanyoyi da dama ta hanyar sa hikima da yin hira da mutane da ke da wani abin cewa game da wannan aiki na bincike.

    Ya kuma samu ƙarin bayani daga fadar ƙasar ko garin a tsakanin Wazirin kwatarkwashi da Magatakarda da Turakin kwatarkwashi da kuma Fadawan sarkin kwatarkwashi.

    Mai bincike ya bi Malamai don neman shawarwari a garesu da kuma samun ƙarin bayani a kan yadda mai bincike zai bi aikin tiryan-tiryan wato daki-daki a cikin tsari.

    Haka kuma anyi amfani da kundaye waÉ—anda suka yi kama ko suke da alaÆ™a da irin aikin don zaÆ™alo muhimman abubuwan da suka dace da waÉ—anda masarauta ke da shi.  

     

    1.3              Muhimmancin Bincike

    A duk inda ka ga ÆŠan Adam a doron Æ™asa yana yin wani abu to Gaskiya zaka tarar cewa abin yana da matukar amfani da muhimmancin Æ™warai. Haka kuma wannan bincike da aka gudanar yana da amfani ga jama’a musamman ma masu nazarin harshen Nijeriya da al’adu.

    A kan haka ne mai bincike ya zaÉ“i aiki a É“angaren Tarihin Masarautar kwatarkwashi, don sanin yadda masarautar take tun gabanin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo kamar yanayin zamantakewarsu da  sha’anin rayuwarsu da kuma abin da ya shafi aurensu, da yadda suke gudanar da bukukuwansu irin na É—auko Maiki ko hawan Dutse don É—auko Maiki da wasan Baura da yadda tsarin shugabancinsu yake da kuma sauye-sauyen da suke samu ga sarakunansu.

     

    1.4              Farfajiyar Bincike

    A wannan aiki na farfajiyar Bincike mai Bincike ya maida hankalinsa ne kacokan a kan tarihin masarautar kwatarkwashi, wato tun daga kafuwar ƙasar ko masarautar har zuwa yanzu.

    Mai Bincike zai yi tsokaci a kan yadda masarautar kwatarkwashi take da yadda ta samu tun kamin Jihadin Shehu Usman Danfodiyo da kawo yadda ake É—aukar Maiki akan dutse da yadda ake wasan Baura tare kuma da kawo sunayen sarakunan Æ™asar kwatarkwashi tun daga sarki na farko har zuwa ga sarki na yanzu wato wanda ke kan karagar mulki kuma tarihi ya nuna mana cewa su Ashirin da ta Kwas ne (28). 

    Ina fatar wannan aiki zai yi amfani ga manazarta a sashen harsunan Nijeriya, musamman masu karatun (B.A Hausa) a sashen harsunan da al’adu ga nazarin da suke yi mai kama da wannan na tarihin masarautar ko adabi ya Æ™arfafa ga idon duniya sosai. Allah ya sa ya kasance mai amfani ga na bayanmu a tsakanin Ƙannenmu da ÆŠiyanmu da ma Jikokinmu da su amfana da shi, amin.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.