Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

    Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

    Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (2)

    Na

    AMINU MURTALA

    Kwatarkwashi 

    BABI NA BIYU

    1.0              Bitar Ayyukkan Da Suka Gabata

    A cikin wannan babi wato bitare ayyukkan da suka gabata hakika mai bincike ya ci karo da ra ayoyi daban-daban na masana da kuma manazarta, har ma da malamai da kuma dalibbai ba a barsu a baya ba domin sunyi ayyukka masu dangantaka da irin wannan aiki.

     Bunza (2009) a cikin littafinsa mai suna NarambaÉ—a ya yi bayani a kan sarauta da masarauta da yadda ake nadin sarauta da kuma yadda sarauta take. A wannan bincike kuma ana Magana ne a kan tarihin masarauta kwatar-kwashi.

    Sadi (1700-1995) a cikin littafinsa ya yi bayanin wasan Baura da yadda ake É—aukar maiki a kan dutse. Wannan aiki yana da alaÆ™a da binciken da za’a gudanar ta fuskar shi ya yi Magana a kan wasan Baura da yadda ake É—auko maiki a kan dutse shi kuma wannan bincike ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwatashi.

    Abdullahi da Muh’d (2011) a cikin littafinsu sun yi bayani a kan Æ™asar Kwatarkwashi dangantakar aikinsu da wannan bincike shi ne wannan bincike anyi shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Al-Hassan da Musa da Zaruk (1982) a cikin littafinsu sun yi bayanin ne a kan duniyar Hausawa da bayani a kan sarauta da kuma bayani a kan muƙamai waɗanda ke zagaye da masarauta. Dangantar wannan littafin da wannan aikin shi ne wannan bincike ana yinsa ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Dashi (2009) a kundinsa na Digirin Farko ya yi bayani a kan “Kan gida da ire-irensa a Æ™asar Kwatarkwashi dangantakar aikinsa da wannan bincike shi ne wannan bincike ana yinsa ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi, shi a nashi yana Magana ne a kan Kan gida da ire-irensa a Æ™asar Kwatarkwashi.

    Bala (2012) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan tasirin zamani a auren maguzawan Kwatarkwashi. Dangantakar aikinsa da wannan aikin binciken shi ne a wannan ana bayani ne a kan tarihin Masarautar Kwatarkwashi a na shi kuwa ya yi bayani ne akan tasirin zamani a auren maguzawan Kwatarkwashi.

    Sani Umar (2012) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Gwagwarmayar Musulunci da gudumuwarsa a ƙasar Kwatarkwashi Bungudu Local Goɓernment a wannan bincike kuma ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Abdullahi (2008) a kudin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Tsafe-tsafe a Bukukuwan maguzawan Kwatarkwashi. A wannan bincike kuma ana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Mainasara (2001) a kudin Digirin Farko ya yi bayani ne a kan Bautar Magiro a ƙasar Zamfara. Dangantarkar aikinsa da wannan aiki na bincike shi ne ya yi bayani a kan ƙasar Kwatarkwashi da Magana a kan Masarautar Kwatarkwashi, wannan bincikr kuwa ya na bayani ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Mashi (2001) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani ne a kan Maguzanci. A wannan aiki kuwa a na Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Na’inna (2011) a wata muÆ™ala ya yi bayani a kan taÆ™aitaccen tarihin Æ™asar Kwatarkwashi, wannan bincike kuwa an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Turaki (2011) a wata muƙala ya yi bayani a kan tarihin mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa yana Magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Birnin Magaji (2015) a wata muƙala ya yi bayanin taƙaitaccen Tarihin Kwatarkwashi. Dangantakar aikin sa da wannan bincike shi ne an gudanar da wannan binciken a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Joɗi (2011) a wata muƙala ya yi bayani a kan bukin mai Martaba Sarkin Kwatarkwashi ya kawo tarihin mai Martaba, wannan bincike kuwa anyi shi ne a kan Tarihin Masauratar Kwatarkwashi.

    Musa (2016) a kundin Digirinsa na Biyu ya yi bayani a kan gudummar Musulunci ga korar al’adu da Tsafe-tsafe a Æ™asar Kwatarkwashi, wannan bincike an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Millennium Target (2016) a littafinsu sun yi bayani a kan Kwatarkwashi a yau”, wannan bincike an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Hashimu (2015) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan Tarihin Liman Musa Kura, dangantarkar aikinsa da wannan bincike ya yi bayanin takaitaccen Tarihin Ƙasar Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa yana bayani ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Rikiji (2014) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan ƙungiyar Izalah a ƙasar Kwatarkwashi, wannan binciken yana Magana a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Safana (2001) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayani a kan “Maguzawa Lezumawa”. Dangantakar aikinsa da wannan bincike ya yi bayanin wuraren Bautar Maguzawa a Kotorkoshi a wannan binciken kuwa yana bayani ne game da Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Maikano (2002) a kundin Digirinsa na Farko ya yi bayanin a kan Maguzawan Yari-bori dangatakar aikinsa da wannan binciken ya yi Magana a kan ƙasar Kwatarkwashi wannan binciken kuwa yana magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Abdullmumini (2014) a kudin Digirinsa na Farko ya yi bayanin  a kan Canje-canjen da Musulunci ya kawo a bangaren Bukukuwa a Æ™asar Kwatarkwashi. Dangantakar aikin sa da wannan binciken shi ne ya yi tsokaci a kan Æ™asar Kwatarkwashi, wannan binciken kuwa an yi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Basarakiya (2011) ta yi bayani ne a kan taÆ™aitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Wannan binciken kuwa ya ta’allaÆ™a ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Basarakiya (2012) ta yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Wannan binciken kuwa ya na magana ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    Basarakiya (2013) ta yi bayani ne a kan taƙaitaccen tarihin Masarautar Kwatarkwashi. Dangantakar ta da wannan binciken kuwa an gudanar da shi ne a kan Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

     

    1.1              NAÆŠEWA

    Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi mai bincike ya yi Magana ne a kan bitar ayyukkan da suka gabata in da mai bincike ya kawo ra’ayoyin Malamai da ÆŠalibban daban-daban dangane da irin gudummuwar da suka bayar game da wannan bincike na Tarihin Masarautar Kwatarkwashi.

    A farko mai bincike ya yi amfani da littafai daban-daban da kundaye na wasu Ɗalibbai da kuma Muƙalu da Jaridu da aka gabatar a wurare daban-daban.

    A babi na gaba mai bincike zai yi Magana ko bayani ne a kan ma’anar sarauta da su waye masarauta da kuma tsarin siyasar sarautar Æ™asar Kwatarkwashi da kuma abun da ke sa a sauya sarki.

    A karshe sai mai bincike ya rufe babin da bayanin nadewa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.