Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Tarihin Masarautar Kwatarkwashi (4)
Na
AMINU MURTALA
BABI NA UKU
1.0
Ma’anar
Sarauta
Sarauta kalma ce babba mai ƙima da kwarjini da kuma mu’ujiza ga dukkan
Jinsi na al’ummar duniya. Abin lura a nan shi ne, dama sarauta ce ake nema a
zama sarki. Haka kuma it ace ake nema domin in ba sarauta ba za’a samu
masarauta ba, balle Gidan sarauta, har a samu sarki da fadawa.
Jigon sarauta ya ƙunshi manya-manyan abubuwa da al’adun
Bahaushe ke kallon sarauta das u. daga cikin abubuwan da ke shika-shikan ƙarƙashin
sarauta akwai:-
i.
Samuwar Sarauta
ii.
Faɗuwar Sarauta
iii.
Yadda ake neman Sarauta
iv.
Waɗanda suka cancanci Sarauta
v.
Waɗanda basu cancanci Sarauta ba
vi.
Yadda Sarauta take
vii.
Kokuwar neman Sarauta
viii.
Naɗin Sarauta
ix.
Daɗin Sarauta
x.
Wuyar Sarauta
xi.
Shimfiɗar gadon Sarauta / Hawa gadon Sarauta
1.1
Su Wane ne Masarauta
Mutum ba zai yi sarauta ba sai ya gajeta, haka kuma ba
zai gajeta ba inn ba Gidan sarauta ya fito ba ga asalinsa. Don haka ashe
masarauta da Gidan sarauta sun fi sarki muhimmanci, domin da su sarki ke tinƙaho ba su ke
tinƙaho da sarki
ba. Kuma su suka yi sarki, ba sarki ya yi su ba, samun irin wannan tsari ya sa
makaɗan fada kan
keɓe jigo na
musamman domin fito da wannan bayani ga sarakai da jama’arsu.
Ba dole don mawaƙi na yiwa fada waƙa ba, ace ba
zai yiwa wata fada waƙar ba.
1.2
Tsarin Siyasar Ƙasar Kwatarkwashi
Ga al’ada ba bu abin day a kai naɗin sarauta didima da annashuwa da farin ciki
da buki da cashewa. Haka kuma nadin da za a yiwa sarki shi zai tabbatar da zaɓen da aka yimasa.
A ranar naɗin sarauta ne sarki zai yi bayani ga jama’a ya yi godiya
gare su da neman goyon bayansu. A ranar ne wani babban sarki na ƙasar zai
yiwa jama’a jawabi game da wanda aka zaɓa masu da kuma neman goyon bayansu ga sabon sarki.
Narambaɗa Ya Fito da Wannan Jigo
Fili a Waƙarsa Ta
Fadar Mai mar taba Sarkin Kwatarkwashi Yana Cewa:-
Yai halin mazan jiya ɗan sanda mai kwatarkwashi
Waɗan su sun sarauta sun sani ban tahoba
Da anka ce Alu assarkin gidanga gani na taho
Waɗan su sun shekara goma sarki basui abinda kayiba
Sarki kamin kyautar Doki gami da kwakwata, in kai hakanga
ka biya
1.3
Tsarin Shugabancin Ƙasar
Kwatarkwashi
Ga al’adun Maguzawa za muga cewa ana fara shugabanci tun
cikin gidajensu za’a samu wanda shi ke faɗa aji a Gidan, don shi ne babba. Idan wani abu ya faru
shi za a nufa don ya kashe wutar ko ya bada shawara akan a bun da ke faruwa ko
ake so ayi. Haka kuma wadda ke uwargida ita ke gudanar da komi don itace yaya a
Gidan kuma itace mai cewa ayi ko a bari, tana samun umurni da shawarwarin abun
daya shafi Gidan ne daga kakansu uwayen Gidan mazansu da matansu idan yafi kowa
shekaru a gidan.
Idan kuwa namiji shi ne yafi kowa shekaru a Gidan to shi
ne zai riƙa ba da umurni gaba ɗaya. Ga al’adarsu suna ba da shugabanci tun daga
gidajensu zuwa ga unguwanninsu da ƙauyukkansu zuwa garururwansu har ƙasar baki ɗayanta saboda nuna kwazonsu da jarumtarsu da
juriya tareda kwarjininsu da kula da dangantakar zumuncin jama a. Ana bada
shugabanci a sassan fannoni al’adun na sana’o’I da suka gada tun asali.
Ga tsarin shugabancin kamar haka:-
a.
Masarautar Kwatarkwashi na daTsarin Uwayen ƙasa Kamar
Haka:-
1-
Sarkin Yamman Kwatarkwashi
2-
Uban Ƙasar Sankalawa
3-
Uban Ƙasar Samawa
4-
Uban Ƙasar Tofa
5-
Uban Ƙasar Gulubba
b.
Tsarin Muƙaman
Sarautar Ƙasar Kwatarkwashi:-
1.
Wazirin Kwatarkwashi
2.
Magajin Kwatarkwashi
3.
Makaman Kwatarkwashi
4.
Garkuwan Kwatarkwashi
5.
Turakin Kwatarkwashi
6.
Wamban Kwatarkwashi
7.
Marafan Kwatarkwashi
8.
Ubandoman Kwatarkwashi
9.
Baraden Kwatarkwashi
10.
Tafidan Kwatarkwashi
11.
Walin Kwatarkwashi
12.
Yariman Kwatarkwashi
13.
Chiroman Kwatarkwashi
14.
Iyan Kwatarkwashi
15.
Ɗan Iyan Kwatarkwashi
16.
Talban Kwatarkwashi
17.
Sardaunan Kwatarkwashi
18.
Jarman Kwatarkwashi
19.
Tambarin Kwatarkwashi
20.
Katukan Kwatarkwashi
21.
Kogunan Kwatarkwashi
22.
Marafan Samawa
c.
Tsarin Shugabancin akan
sana’o’i:-
Ƙasar
Kwatarkwashi a matsayin ƙananan sarauta na al’ada ana bayar da su ne ga wanda ya
nuna jaruntakarsu da kwarjininsa ga sana’arsa a fili ga inda yafi shahara
kwarai a kan sana’arsa.
Ga kuma nasu tsarin kamar haka:-
1.
Sarkin Noma
2.
Sarkin Fada
3.
Sarkin Aski
4.
Sarkin Baushi
5.
Sarkin Ƙira
1.4
Sauye-Sauyen
Sarakunan Ƙasar Kwatarkwashi
Gabanin zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo Ƙasar Kwatarkwashi suna naɗa sarakunansu ne ta hanya kamar haka:-
Mutanen garin ko ƙasar Kwatarkwashi suna haɗuwa a wuri guda gaba ɗayansu su zauna su yi shawara a kan wanda ya
kamatasu zaɓa a mastayin
sarkinsu. Suna duba jaruntakar mutum mutuncinsa da irin yadda yake hulɗa da mutane wato suna zaɓen mutum mai nagarta mutumen kirki. Sai su zaɓe shi a matsayin sarki haka za’a naɗa shi a bashi sarauta.
Yanda kuma suke sauya shi, shi ne idan sarki ya yi masu
wani laifi ko ya yi wani abu marar kyau ko abun kunya to sai mutanen gari su
sake taruwa suje fada su fito da shi su fita ta ƙofar baya wadda a yau ake kira ƙofar bai
zasu raka shi har ƙarshen gari wato gaba da Gulubba. A kan hanyarsu ta dawo
wa duk wanda suka gamu da shi to shi ne Sarkin da zasu sake zaɓa a matsayin Sarkinsu.
Bayan zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo shi ne yanayin sarautar ya canza
domin a wannan lokacin su na la’akari da wanda yak e Musulmi kuma mai riƙon Addini
sannan kuma ana ba da sarauta ne idan mutum ya gaji sarautar wato idan mutum ɗan Gidan sarautar ne, ya gajeta ga mahaifinsa
ko kakansa. Ba’a kuma ba wanda ya gaji sarauta ga mahaifiyarsu wato wanda yak e
ɗan mace baya
gadon sarautar wannan garin. Dole sai ɗan namiji wanda ya gajeta ga mahaifinsa ko kakansa.
1.5
Naɗewa
Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi an yi Magana a
kan Ma’anar Sarauta in da mai bincike ya kawo ra’ayin wasu masan daban-daban
dangane da ma’anar sarauta, wannan ya nuna mana cewa, a taƙaice sarauta
kalma ce babba mai ƙima da kwarjini da kuma mu’ujiza ga dukkan jinsi na
al’ummar duniya.
A gaba kuma, mai bincike ya fayyace ko su wane ne
masarauta a cikin wannan babi wanda ya nuna mana cewa masarauta sune mutane da
suka gaji sarauta ga iyayensu kuma wanda bai gajeta ba, ba zai zama cikin
masarauta ba.
A gaba kuma, mai bincike ya yi bayani a kan Tsarin
siyasar sarautar Ƙasar Kwatarkwashi. A in da mai bincike ya nuna yadda
tsarin sarautar Ƙasar Kwatarkwashi ya ke, da kuma kawo yadda tsarin uwayen
ƙasar
kwatarkwashi yak e daga ƙarshe kuma a ka kawo yadda tsarin shugabanci a kan
sana’o’in ƙasar kwatarkwashi ya ke.
A ƙarshe, mai bincike ya tattauna a kan sauye-sauyen
sarakunan ƙasar kwatarkwashi tun gabanin zuwan Shehu Usman Ɗanfodiyo har
zuwansa.
Wato mai bincike ya yi bayani a cikin wannan babi na
yadda ake naɗa sarki da
kuma yadda ake sauya shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.