Ticker

Tasirin Waƙoƙin Shata Da Kiɗan Kalangu A Wasu Fadojin Ƙasar Hausa

Kiɗan kalangu kiɗa ne da aka fi saninsa ga mawaƙan jama’a da wasu daga cikin mawaƙan sana’o’i. wannan takarda za ta yi duba ne kan tasirin da kiɗan kalangu na mamman Shata Katsina ya yi a wasu daga cikin fadojinn ƙasar Hausa. Haka kuma takardar za ta duba irin alaƙar da ke a kwai tsakanin wasu fadojin da Shata ya yi wa waƙa da kuma shi kansa Shatan. Daga ƙarshe takardar zata yi bayanin irin yadda ƙiɗan kalangu ya yi tasiri a wasu fadojin ƙasar Hausa har ya zuwa yau ɗin nan, da yadda kidan ya zama mabuɗi a wasu mawaƙan Hausa na wannan lokaci.

Tasirin Waƙoƙin Shata Da Kiɗan Kalangu A Wasu Fadojin Ƙasar Hausa

Daga
Abdulrahman Aliyu
08036954354
ksarauta@gmail.com

Da
Yazid Abdulaziz
08060767379
yazidnasudan@gmil.com

Kalangu

1.0 Gabatarwa

Al’ummar Hausawa, al’umma ce wadda ta ginu bi sa fasahar harshe. Ta haka ne adabin baka ya ɗamfani ainun a rayuwar Hausawa tun ma ba a farko ba in da ayyukan adabin baka kamar kirari da Karin Magana da salon Magana da waƙe-waƙe da sauran hanyoyin sakayawa da gajarce zance cikin hikima da balaga suka zama ruwan dare. (Gusau, 2013:16)

Masana da Manazarta adabin Hausa sun rarraba waƙoƙi da Mawaƙan Hausa gida-gida dangane da irin yanayi da kuma mutanen da ke yin waƙar ko ake yi wa waƙar, ko wace waƙa ko mawaƙi ya na da irin rukunin jama’ar da ya ke yi wa waƙa. Akan ce makaɗan jama’a ko na  fada ko na sana’a ko na maza, ko waƙoƙin yara mata ko kuma waƙoƙin aiki na manyan mata da sauransu. Wannan bincike an gabatar da shi ta hanyar yin nazarin tasirin da kiɗan Kalangu na Dr Mamman Shata Katsina ya yi ga wasu fadojin ƙasar Hausa duk da cewa a da ba a san kalangu ba a kiɗan Sarakai a ƙasar Hausa, kuma ana ganin cewa Shata ne ya fi zuzuta kiɗan kalangu a fadojin ƙasar Hausa, har wasu suka ɗauka suka ci gaba da amfani da shi a matsayin kayan kiɗa a fadojin ƙasar Hausa.

 

1.1    Wa ye Dr Mamman Shata?

Duk da cewa wannan takarda bata ta’allaƙa ba ga kawo tarihin Shata, amma za a waiwaya baya kaɗan domin sanin ko wa ne ne Dr Mamman Shata, domin a fahimci irin rawar da ya taka wajen amfani da Kalangu a kiɗan sarauta a ƙasar Hausa.

An haifi Mamman Shata a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.  Sunan Mahaifin shi Ibrahim Yaro wanda Bahillata ni ne mai arziki sosai, wanda daga bisani ya baro dajin da yake zaune, ya yi ƙaura zuwa Musawa. (Gusau, 2005:192) Ba za a iya tantace haƙiƙanin shekarar da aka haife shi ba. A ƙiyasce ana kyautata zaton cewa an haife shi a cikin shekarar 1925. Cikakken sunan Shata, Muhammadu, Mamman laƙani ne irin wanda kakanni kan raɗa wa jikokinsu tun suna yara. Ita kuwa Kalmar “Shata” laƙani ne wanda ake kiransa da shi lokacin da ya ke cinikin goro. A ya yin da yake sayar da goro shi ba ruwansa da ya dinga ɗiba hamsin-hamsin ko kwarya-kwarya sai dai ko wa ya bashi kuɗi zai duntso goro ne ba tare da ƙirgawa ba ya miƙo masa. Saboda rashin ƙirgawa ɗin nan sai ya shato (ɗebo) ya ba mai saye aka laƙaba masa wannan kalma ta “Shata” mai yin nuni da halinsa wajen saida goro. (Gusau, 2005:92)

Wasu kuma masana sun tafi kan cewa, Baba Magaji Salamu Musawa, wanda a lokacin shi ne ubangidan Alhaji Mamman Shata, shi ya raɗa masa sunan “Shata” har yana ce masa “Shata mijin mai ɗaki”, Mai ɗaki kakar Shata ce, ita ta haifi Mahaifin sa Ibrahim Yaro Raruma.

Alhaji, Dakta, Mamman Shata ya soma waƙa a Musawa inda aka haife shi, kuma duk inda ya je yawo da waƙarsa suka ganshi. Shata shahararren Mawaƙin Hausa ne, wanda babu kamarsa a zamaninsa, yana da waƙoƙi da dama waɗanda suka haɗa da:

* Waƙoƙin Yabo da zuga na Jama’a

* Waƙoƙin Sa kai na gargaɗi da faɗakarwa

* Waƙoƙin Siyasa

* Waƙoƙin Wayar da kai bisa wasu Batutuwa

* waƙoƙin Sha’awa

* Waƙoƙin  Sauran Fannoni na rayuwa (Gusau, 2005:196)

Fitattaun kayan kiɗan da yake amfani da su a ya yin gudanar da waƙarsa sun haɗa da Kalangu da sauransu, ya yi waƙoƙin wanda har yanzu bincike bai san yawan su ba. Kuma kusan dukkan Masana da manazarta irin su Ɗangambo da Yahaya (1986) da Gusau (2005) da Yakubu (2002) da sauransu da dama duk sun tafi a kan  cewa Shata mawaƙin Jama’a ne. A sakamakon waƙoƙin da ya yi domin amfanin al’umma, ya samu yabo da lambobin girmamawa da dama, a lokacin mulkin Janar Gowon an ba shi lambar girma. Har ila yau, Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ta karrama shi da Digirin girmamawa na Dakta, (1988) wanda sakamakon haka yasa ake kiransa Dakta. Mamman Shata Katsina. Ya rasu ranar 18/6/1999 an binne shi a ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina, kamar yadda ya bar wasiyya. Ya bar  mata da ‘ya’ya da jikoki da dama. Allah ya jiƙansa ya gafarta masa kurakuransa.

1.2    Kalangu a Matsayin Kayan Kiɗa

Bahaushe na amfani da abubuwa da dama domin su samar da kiɗa , kuma daga cikin waɗannan abubuwa na samar da kiɗa akwai waɗanda bugasu ake yi wasu kuma busa su ake, yayin da wasu jijigasu ake. Kalangu na ɗaya daga cikin irin waɗannan abubuwa da ake amfani da su domin fitar da sauti na kiɗi a ƙasar Hausa.  Shi kansa kalangun ya rabu zuwa gida uku kamar haka.

Ire-iren Kalangu

1.     Babba

2.     Matsakaici

3.     Ɗan karami

* Babban kalangu shi ne wanda ake iya ajewa ƙasa ba dole sai an rataya shi a wuya ba saboda girmansa, wannan nau’in kalangun an fi kaɗawa Mahauta shi da ‘yan dambe.

* Matsakaici: wannan nau’in Kalangun bai kai babba ba. Amma ya fi ɗan ƙarami, shi wannan kalangun a na rataya shi a kafaɗa, wannan kalangun kuma shi ne ake kaɗawa manoma.

* Ɗan ƙarami: wannan nau’in Kalangun shi ne mafi ƙanƙanta a cikin kalangun da ake da su a ƙasar Hausa, shi wannan nau’in kalangu ana kaɗa shi ne ga mafarauta, da dandali, kuma da shi ne Alhaji Mamman Shata ya ke amfani a kaɗe-kaɗen da ya yi na fada.

Ana sassaƙa kalangu ne daga itace masu kyau da ƙwari na ƙirya ko gawo ko madobiya sai a fafare cikinsa amma za a matse tsakiyarsa sai a yi masa ɗan faɗi daga samansa, daga ƙasa kuma sai a ɗan matse, ana amfani da farar fatar akuya ne ta hanyar rufe bakunan guda biyu, sai a samu zaren tsarkiysa wajen tamke gangar jikin kalangu tun daga kangu na sama har ya zuwa na ƙasa amma tsarkiyar bata taɓa jikinsa. Kangu shi ne gammon da ake yiwa kalangu a sama da ƙasansa, kuma wannan gammon falsafar yin sa shi ne a samu damar ɗinke kalangu. Sai a sanya maɗauki wanda shi ne ake ratayawa a wuya. Sai kuma urya wato abin da ke sassaƙawa domin buga kalangu.

Sautin da kalangu ke fitarwa ya kasu gida biyu kamar haka:

1.     Sauti mai tashi

2.     Sauti mi yin ƙasa

Sauti mai tashi, kalangu na bada shi ne ya yin da makaɗi ya yi amfani da hamatarsa ya matse tsarkiya sai sauti ya yi sama, domin kuwa lokacin da ya matse tsarkiyar fatar ke yin tsauri,  hakan kuma ke sa sauti ya yi sama.

Sauti mai yin ƙasa; idan makaɗi na buƙatar kalangu ta ba da sautin da ke yin ƙasa sai ya bar tsarkiya a sake ba tare da ya matse ta ba.

An dai yi ittifaƙi cewa kalangu kayan kiɗan Hausawa na gargajiya ne ba aro su aka yi daga wata ƙabila ba, domin tun tale-tale Bahaushe na amfani da kalangu a yayin kiɗa da waƙarsa.

1.3 Matsayin Kalangu  a Ƙasar Hausa Kamin Ɓulluwar Waƙoƙin Shata

Kusan dukkan al’ummar Hausawa sun yarda da cewa, kalangu ba kayan kiɗan da ake amfani da shi ba ne a yi wa sarakuna, ko wani mai jibantar sarautar Gargajiya waƙa. Idan har akwai wani mai sarautar gargajiya  a ƙasar Hausa da ake amfani da kalangu domin yi masa waƙa to bai wuce Sarkin Fawa ko Sarkin Noma ko Sarkin Dambe ba, amma kacokam an fi sanin shi ga mahauta ko wurin Dambe, ko kokowa, ko sharu ko kuma a dandali inda ake kiɗawa ‘yan mata shi su yi rawa.

Kamin ɓulluwar waƙoƙin Shata kusan duk mawaƙan da ke kiɗa a fada babu mai kiɗan kalangu, duk da cewa an samu wasu mawaƙan waɗanda da farko sun yi kiɗan kalangu, amma da zasu koma kiɗan fada sai suka ajiye kalangu suka ɗauki wani kayan kiɗan daban. Misalan irin waɗannan makaɗa sun haɗa da:

1.     Makaɗa Ummaru mai Sa’a; ya yi kiɗan kalangu a lokacin da ya ke kiɗan dambe da noma da fawa da kuma kokowa, amma lokacin da zai tafi kiɗan fada sai ya ajiye kalangu ya koma kotso, kuma tunda ya koma kiɗan fada bai ƙara amfani da kalangu ba a matsayin kayan kiɗansa.

2.     Muhammadu Mai Damma Sarkin Taushi: wannan shi ma kiɗan kalangu ya gada a wajen mahaifinshi, kuma da shi ya fara kiɗan noma da dambe da fawa, da bukukuwa da sauransu, amma da zai koma kiɗan fada sai ya ajiye kalangu ya koma taushi, kuma shi ma bai ƙara bi takan kalangu ba.

3.     Muhammadu Mai Taushi: Asalin waƙarsa kiɗan kalangu ya ke yiwa ‘yan mata a dandali suna rawa, sai kuma kiɗan noma, amma daga baya da ya koma ya na bin ɗan uwansa wanda shi makaɗin fada ne, bayan rasuwarsa sai ya zama halifansa ya cigaba da kiɗan fada, inda ya bar amfani da kalangu a matsayin kayan kiɗansa

4.     Salihu Jankiɗi Rawayya: shi ma Salihu Jankiɗi Shaharren mawaƙin Fada ne tun daga fadar sarkin Kwantagora zuwa fadar Sarkin Katsinan Gusau, har ya zama sarkin taushin Sarkin Musulmi  Abubakar na uku. Amma asalinsa kiɗan kalangun ya ke, kuma kiɗan kalangun shi ne abin da ya gada wajen mahaifinsa, amma da ya koma kiɗan fada sai ya ajiye kalangu ya rungumi taushi.

Yahaya da Ɗangambo (1986) sun kawo ire-iren kayan kiɗan da masu Waɗannan misalan da aka kawo sun nu na cewa kiɗan kalangu a fada wani baƙon abu ne kafin Shata ya mayar da shi ruwan dare a fada. Kamar yadda aka riga dai aka sani su makaɗan fada, su ne waɗanda ba su yiwa kowa kiɗa, sai jinin  sarauta ko wanda ya ke riƙe da wata sarauta, musamman muƙamin da ya shafi gargajiya, misali Sarki, Hakimi, Dagaci ko manyan fadawa. To amma yanzu saboda canjin lokaci irin waɗannan makaɗa, sukan yi wa manyan masu kuɗi, ko ma’aikatan gwamanati waƙa, Shahararrun kaɗe-kaɗen fada su  ne irin su algaita , Jauje, kiɗan taushi da sauransu. A ƙasar Hausa kowane Sarki da Hakimi ya na da makaɗansa. Irin waɗannan makaɗa ba sa yi wa kowa kiɗa sai uban gidansu. To amma wani lokaci sukan nemi izini su yi wa wasu sarakunan waƙa.

 Kayan kiɗan da makaɗan fada ke amfani da su:

* Kiɗan Taushi

* Kotso

* Dundufa

* Algaita da sauransu

* Kakaki,

* Ƙuge

Shi ma Gusau. (2005) ya kawo kayan kiɗan da makaɗan fada ke amfani da su, waɗanda suka haɗa da:

* Tambari

* Taushi

* Jauje

* Bango

* Kotso

* Algaita

* Kakaki da sauransu

Gaba ki ɗaya Masana da hannunmu ya kai kan ayyuakan su ba su sanya kalangu, a matsayin kayan kiɗan da ake amfani da su a yi kiɗi a faɗa, ko ayi wa Sarakuna waƙa ba, duk sun tafi a kan cewa kalangu kayan kiɗi ne da ake amfani da shi a yi kiɗi da waƙoƙin Noma da maharba da mahauta  da ‘Yan Dambe  da sauransu.

1.3    Ko a Kwai Waɗanda Suka yi Amafani da Kalangu a Fada Kafin Shata?

Wannan bincike ya gano cewa ba za a ce akwai wani da ya riga Shata amfani da kalangu domin yin waƙoƙin fada ba, sai dai akwai waɗanda suka yi zamani ɗaya da shatan a cen shekarun baya da suka yi amfani da kalangu suka yi ma Sarakai ko masu rike da wata sarautar gargajiya waƙa, amma in aka lura sai aga cewa ba su yi irin waɗannan waƙoƙin da suka wuce biyu ba ko uku daga cikin su akwai;
 Dan’anace: Wanda ya fi shahara a kiɗan dambe da noma, wanda farko shi ma da ganga ya fara kiɗa, daga nan kuma sai ya yi kiɗan Duma sai kuma daga baya ya fara kiɗan kalangu duk da Gusau (2005:218) ya ambaci Ɗan’anace a matsayin mai kiɗan Sarauta, to amma bincike ya tabbatar da cewa sadda ya yi kiɗan  sarautar ba da Kalangu ya yi amfani ba, an fi tsammanin ya yi amfani da kalangu ne lokacin da ya yi wa Sarki Abubakar III waƙa, ana ganin waƙar da ya yiwa sarkin Daura Muhammadu Bashar da wadda ya yi wa Sarkin Sudan na Wurno Alhaji Shehu Malami da sauran waƙoƙin daya yi wa sarakai duk ya yi su ne bayan da Shata ya kai Kalangu fada, kuma tasirin waƙoƙin Shata ɗin ne suka sanya shi amfani da kalangun domin yi wa wasu sarakan waƙa.

Muhammadu Ganga-Ganga; Wannan mawaƙin ya rayu tsakanin 1925-1980 shi ma makaɗin jama’a ne sai dai ya yi amfani da Kalangu wajen yiwa Hakimin Wudil waƙa, amma dai binciken wannna nazarin ya tabbatar da cewa Shata ya riga shi amfani da kalangu domin yin waƙar fada.

Alhaji Muhammadu Dankura: Ya rayu a tsakanin 1915-1957 shima ya yi amfani da kalangu ya yiwa Sarkin Daura Abdurrahaman Waƙa, shi wanna mawaƙin ana ganin cewa, za su iya yin tangal da Shata wajen fito da Kalangu a fada, duk da cewa shi bai yi fice ba, amma a binciken da aka yi an tabbatar da cewa da Kalangu ya yi amfani wajen waƙoƙin da ya yi wa sarkin Daura Abdurrahaman, kuma shi ne mawaƙin fadar Daura, kafin daga baya Shata ya fara.

Bayan waɗannan mawaƙan akwai wasu irin su Tauɗa Inugu da Audu Wazirin Ɗanduna waɗanda ake kallon suna daga cikin waɗanda suka fara amfani da Kalangu wajen yin kiɗan fada, sai dai basu maida hankali ba kamar yadda Dr Mamman Shata ya yi ba.

 

2.1  Tasirin Kiɗan Kalangu na Dr Mamman Shata Katsina a Wasu Fadojin Ƙasar Hausa

Fada kamar yadda  Isma’il (1996) ya ce “wani  waje ne na musamman da ake taruwa domin tattauna muhimman abubuwa a gaban Sarki dangane da harkokin yau da kullum tare da shawarar yadda za a ɓullowa wani abu da ya taso, tare da neman hanyar da za a magance shi.|”

Su kuwa waƙoƙin fada kamar yadda Kafin Hausa (2002:241) ya rawaito yace, “waƙoƙi ne da suke cike da hikimomi da fasaha da nuna zalaƙa irin ta al’ummar Hausawa. Sannan kuma suna ɗauke da salo iri-iri na sarrafa harshe kamar su kirari ko Karin magan da karangiya da dai sauran abubuwa masu nuna gwanintar harshe.

Mafi yawan lokutta waƙoƙin fada suna da muhallin da ake bi wajen rera su, daga ciki akwai;

* Fada

* Wajen rangadi

* Wajen taron daba

* Bukukuwan Sallah

* Bikin ‘ya’yan sarki

* Naɗin sarauta

* Lokacin kai gaisuwa a kofar gidan basarake, da sauransu

Dr Mamman Shata ya yi waƙoƙi da yawa na fada, kama tun daga waɗanda ya yiwa sarakuna har zuwa hakimai da ma wasu masu riƙe da sarautun gargajiya, zama guda ba za a iya cewa ga adadin waƙoƙin da Shata ya yi na fada ba, domin ko shi kansa bai san adadinsu ba. A wani ɗan nazari da aka yi na ƙoƙarin tattara waƙoƙin da shata ya yi na fada an samu fiye da Dubu ɗaya, wanda ana iya ikirarin cewa ko waɗada aka ware ɗin a matsayin makaɗan fada , ba wani mawaƙi ɗaya cikinsu da ke da tarin irin waɗannan waƙoƙin.

Wannan binciken zai iyakance ne kan fadoji guda huɗu kawai da Shata ya yi waƙa a cikinsu, waɗannan fadojin sun haɗa da Daura, da Katsina da Kano da Zazzau.

Masarautar Daura: A kwai kyawawar alaƙa tsakanin Shata da masarautar Daura, domin ana ganin alaƙar da ke akwai tsakanin sarkin Daura Muhammadu Bashir da Shata ta wuce ta makaɗi da mawaƙi kawai, ta kai tamkar ‘yan uwantaka, domin ko kafin Shata ya mutu ya bar wasiyar cewa in ya mutu a rufe shi a Daura, kuma haka aka yi da ya mutu can aka rufe shi. Akwai ra’ayoyi mabambanta da ke nuna dalilan haɗuwar Shata da Sarkin Daura, Muhammadu Bashir, duk da cewa Shata ya fara yi masa waƙa tun yana Wambai kafin ya zama sarkin Daura. Domin a wata hira da akayi da matar Shata  Yalwa a jaridar Aminiya ranar 4/12/2014 an tambayi Yalwa mi ke alaƙar Shata da Sarkin Daura? Sai ta ba da amsa da cewa “ A gaskiya tsakanin Sarkin Daura Muhammadu Bashar da Shata sai Allah Shata ya maida shi uba yana cewa dukiyar Sarkin Daura kamar tasa ce” har ma a wata waƙa ta “ Lafiya Zaki” ya kira sarkin Daura da cewa, “Sarari mai ƙare gudun Doki” ma’ana babu yadda za a iya kure sarkin Daura kan kyauta duk yadda ka kai da abinka sai dai ka barshi.

Shata ya yi waƙoƙi da ba wani mawaƙi da ya yi su a fadar Daura kama tun daga waɗanda ya yi wa Sarki har zuwa wasu masu riƙe da sarautu a fadar, bari mu bada misali da wasu daga ɗiyoyin waƙoƙin da Shata ya yiwa Sarkin Daura Muhammadu Bashar

Jagora:     Mai Daurawa na Habu Mamman Ɗan Musa,

Amshi: Lafiya Zaki Mammab baban Galadima Ɗan Musa

Jagora: Katsinawa ga Badauri baban Sa’i

Amshi

Jagora: Zage-zagi ga na Daura baban Sa’i

Amshi

Jagora: Faɗawa Kanawa ga Badaurin nan ya komo

Amshi

Jagora: Na Kazaure ku zo tariyar mamman Ɗan Musa

Amshi

Jagora: Daurawa baba na Daura ne yak komo,

Amshi

Jagora: wani mai kwana da shirin Mulkin Daurawa

Amshi

Jagora: Baba Badauri na Daura Baban Sa’i

Amshi

Jagora; Lura da Allah Na daura Baban Sa’i

Amshi

Jagora: Komi ka barshi wurin Allah Ɗan Musa

Amshi

Jagora: kai ko Alhamdullilahi Dan musa

( Shata: Lafiya Zaki)

 

Bashari bari Duba girmansu

Bari duba ƙanƙantarsu,

Binciki littafi

Ka shiga cikin ofis,

Ka shiga shirin mulkin Daurawa,

Ka shiga shirin Mulki ka yi gyara.

                                                               (Shata: Lafiya Zaki)           

A Daura akwai waƙoƙi da yawa waɗanda ya yiwa mutane da dama da suka jibanci fadar Daura kama tun daga maza har mata, Misali waƙar Kilishi Jikar Dikko matar Sarkin Daura Muhammadu Bashar da kuma matarshi mai Ɗakin Gabas ‘Yar Iro da irinsu Ɗanmasanin Daura Alhaji Sani Zangon Daurada Ɗanmadamin Daura Alhaji Abdurrahman Ɗanmalam  da sauransu da dama, don haka muna iya cewa babu wata waƙa wadda ta kai tasirin kiɗan kalangu a masarautar Daura, Don haka a Daura Shata makaɗin Fada ne, kamar yadda Gusau ya sanya shi a cikin littafin sa mai Suna Diwanin Waƙƙoƙkin baka.

Masarautar Kano: Alaƙar Shata da  masarautar Kano daɗɗiyar Alaka ce wadda ta samo asali tun kusan Shekarar 1948, sannan alaƙar ta kara ƙulluwa ne a shekara 1952 a lokacin da aka yi bikin ‘Yayan Sarki Kano wanda Sarkin Kano Ado Bayaro yana ciki lokacin bai zama Sarki ba tun a wannan lokacin Shata ya yi fice  a wajen wannan biki, domin shi kaɗai ake jin amon waƙarsa sai da ya zarce kowa a fadar, kuma kiɗan kalangu da ya yi amfani da shi, shi ya ƙara fito da shi fiye da waɗanda suka ma gaji kiɗan Fadar.

Shata ya yiwa fadar Kano kiɗa da waƙa da ba za a iya cewa ga adadinsu ba, kusan ba za a iya samun wani mawaƙi da ya yiwa fadar Kano waƙa kamar Shata ba, Shata na da matuƙar tasiri a fadar Kano, ga misalan wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin da ya yiwa Sarkin Kano Ado Bayaro;

Jagora: Jikan Shehu Baban Shehu,

Na Ɗan iya Ɗan Bello,

Baban Ɗan Iya Ɗan Abdu,

Amshi:

Jagora: Ubanmu Ado San Kano Ɗan Bello,

Amshi:

Jagora; Mai Birnin Kano Ɗan Abdu

Amshi:

Jagora: Adamu mai birnin Kano Ɗan Abdu,

Adamu mai birnin Kano Ɗan Abdu,

Amshi:

Jagora: Ga Alheri ga Sada Zumunci

Ado San Kano Ɗan Bello

Amshi:

Jagora: Ga Alheri ga Sada Zumunci

Ado San kano Ɗan Bello

Amshi:

Jagora: Dattawa suna San barka,

‘Yan yara suna sun gode,

 

Ita ma masarautar  Kano kamar dai ta Daura babu wani mawaƙi da ya shallake Shata a Masarauta, domi kusan duk wata hidima ko biki da za a yi a Masarautar Shata ne kan gaba wajen kiɗa da waƙa a Masarautar. Ya yiwa mutane waƙa da yawa da suka jibanci fadar Kano irin Sarki Sanusi da Sarki Ado Bayaro, da su Jarman Kano wanda shi ne ya kai shi Ingila wato Alhaji Muhammadu Adamu Ɗan Kabo da Wamban Kano da Ɗanmasanin Kano da sauran su da dama.

Fadar Zazzau: Shata ya fara yiwa Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu waƙa tun wajen 1957. Ba yan naɗa Sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris. An ce Wata rana ya sa wani mawaƙin fada ya yi masa waƙa, sai ya zagi ‘Yan uwansa da ci masu mutunci, shi ne sai bai ji daɗin waƙar ba sai yasa a nemo mashi mawaƙi wanda zai yi masa waƙa ba tare da ya zagi danginsa ba to wai daga nan sai a ka ce a nemo Shata, to da  Shata ya yi masa waƙa ba tare da ya zagi kowa ba sai Sarkin Zazzau ya riƙe shi amtsayin mawaƙi wanda ke yi masa waƙa a fadar sa, ga wasu daga cikin ɗiyan waƙoƙin da Shata ya yiwa Sarkin Zazzau Shehu Idris:

Jagora: Uban ƙasa  Usmanu na Shantali,

Na Garba Jikan Malam Sambo,

Amshi; Alhaji Sarkin Zazzau Shehu,

Jagora: Jikan Mujaddadi a wajen Matarsa,

Amshi:

Jagora: Shehu Jikan Mujaddadi a wajen Matarshi,

Amshi:

Jagora: Malam uban Gari baban Jekada,

Amshi:

Jagora: Gwaron giwa mai ban tsoro,

Na Garba jikan Malam Sambo

Amshi:

Jagora: Rimi Adon gari baban Jekada,

Amshi;
Jagora: Mani na Garba Jikan Malam Sambo,

******

Jagora: tsaya nifa abin nan nai mani ciwo,

Abinga uku da kai man  Shehu,

Amshi:

Jagora: Na farko fita ya yi rangadi,

Ina gida bai aika man ba,

A kai hawan salla ba na nan,

A kai biki baka aika man ba.

Amshi;

Jagora: Ina dalilin da kai biki baka aika man ba,

Amshi:

Jagora: Yau naji dalilin da kai biki baka aika man ba,

Amshi:

Jagora; Ahaf bari dariya sai naji dalilin da kai biki baka aika man ba

Amshi

Jagora: Mugun madanbaci baban Jekada

 

Shata ya yiwa masarautar zazzau waƙoƙi fitattu, sannan kuma duk waƙoƙiƙin da Shata ya ke wa masarauta sun cika sharuɗɗa na waƙoƙin Fada, ta sigar yabo da ziga da zambo da habaici da akan san mafi yawan waƙoƙin fada suna zowa da su. Daga cikin waɗanda Shata ya yiwa waƙa a masarautar Zazzau sun haɗa da Iyan Zazzau da Sarkin Marraba da Sauransu.

 

Fadar Katsina: Hausawa na cewa wai in ana dara to hidda uwa ake, fadar Katsina nan ne gidan Shata kuma nan ne ya buɗe ido da waƙa, domin masana da manazarta masu bibiyar Shata sun tabbatar da cewa Shata ya yi wa Sarki Dikko waƙa tun lokacin da yake saurayi yana waƙar Assawara, a 1943 ke nan Shata ma tun fil’azal waƙoƙin fada ya fara bayan ya bar waƙoƙin Dandali, daga baya ne ma ya rikiɗe ya koma mawaƙin Jama’a kamar yadda sauran na fadar su ma suka yi. Shata ya yiwa Sarakuna da masu riƙe da Sarautun gargajiya a fadar Katsina waƙa wanda shi kansa bai san adadinsu ba. Daga cikin su akwai:

* Hakima Musawa Durbi Usman Liman

* Sarki  Katsina Usman Nagogo

* Sarki Katsina Kabir Usman

* Ciroman Katsina Hasan Usman

* Tafidan Katsina Shehu Musa ‘Yar’adua

* Yariman Katsina Yarima Audu

* Sarki Bai, Alhaji Sani Sito

*  Makaman Katsina hakimin Bakori (makama Idi da Makama Tukur da Sule)

* Sarkin Maska Alhaji Sambo

* Sarkin Sulluɓawa Hakimin Kaita Alhaji Sule Usman Nagogo

* Mairo Jikar Korau

* Kilishi Jikar Dikko

* Hajiya Yakkawu Matar Bebejin Katsina

* Hajiya Kukkuda Ubanta bawan Sarki ne a cikin gidan Sarkin Katsina

* M.T Liman

* Magajin Musawa Abdullahi Inde da dai sauransu.

 

2.2  Tasirin Kiɗan Kalangu a fada Bayan Shata

Bayani ya tabbatar da cewa Shata ne mawaƙi na farko da ya inganta kiɗan Kalangu a fada, ko ma ace shi ne mawaƙi ɗaya tilo da ya fito da martabar kalangu daga kiɗan fawa da dambe da noma zuwa kiɗan sarauata, Bayan Alhaji Mamman shata Katsina, an cigaba da samun mawaƙa da suka ci gaba da amfani da kalangu suna yiwa Sarakai waƙa, kuma daga nan sai kofa ta buɗe ga masu amfani da kalangun, bayan haka ma ko da zamani ya riskemu inda aka samu sauyin kayan kiɗa daga na gargajiya zuwa na zamani nan ma sai kalangu suka cigaba da tasiri, domin a binciken da aka yi kashi bakwai na mawaƙan zamani da suka yi wa sarakai waƙa duk sun yi amfani da Fiyano mai sautin kalangu ne a wajen gudanar da waƙoƙinsu daga ciki akwai:

Naziru Ahmed: yi yawa Sarkin Kano Waƙoƙi

Muhammadu Opera : Waƙar Sarkin Katsina Abdulmumini da sauransu.

 

Kamallawa

Wannan aikin ya yi bitar da kuma bayanin Tasirin da Shata ya yi wajen ɗaukaka martabar kalangu daga kiɗan dandali da noma da dambe zuwa fada. Sannan kuma an yi bayanin irin rawar da kalangun ya taka a fadar da kuma kawo misalan wasu mawaƙa da suka yi zamani da Kalangu a kiɗan fadar a lokacin da Shatan ke tashe, kuma an kawo bayanin yadda wasu mawaƙa suka riƙa jefar da kiɗan kalangu idan za su koma kiɗan fada. An kuma kawo alaƙar da Shata ya ke da ita da wasu fitattun fadojin ƙasar Hausa guda huɗu. Sannan kuma an kawo tasirin kiɗan kalangu a bayan da Shata ya shuɗe. A taƙaice dai wannan bincike ya gano cewa kamata ya yi Shata ya zama makaɗin fada ba wai na jama’a ba duba da irin ɗinbin waƙoƙin da ya yi a fada wanda ba wani makaɗin fada da ake jin ya yi su.

Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments