Ticker

    Loading......

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Taubasantakar Bazamfare Da Badakkare (6)

NA

ABDULRAHMAN BALA

 

Taubasantaka

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 KAMMALAWA

Wannan babin kammalawa ce kuma shi ne babin ƙarshe a wannan aikin na bincike, sannan kuma wannan babi ya ƙunshi wasu muhimman abubuwa waɗanda za a tattauna game da su a cikin wannan babi. Babin ya ƙunshi abubuwa kamar haka; akwai sakamakon bincike, sai ra’ayin mai bincike/shawarwari, sai kuma naɗewa, sannan akwai manazarta. Waɗannan su ne abubuwan da babin ya ƙunsa, kuma su ne za tattauna a wannan babi.

 

5.1 SAKAMAKON BINCIKE

Sakamakon wannan bincike shi ne ya gano dalili ko in ce abubuwan da suka haifar da taubasantakar da ke tsakanin Bazamfare da Badakkare wato (Zamfarawa da Dakkarawa). Babban dalilin da za mu ce shi ne silar haifar da taubasantakar shi ne; Dakkarawa jikokin Zamfarawa ne, ma’ana Dabai shi ne ɗanɗan Dakka, sai ya yi hijira zuwa wani yanki daga cikin ƙasar Kebbi inda ya yadda zango a cikin wani daji, wanda yanzu haka dajin ya koma gari kuma an sa mashi suna “Dabai”. To a wannan wuri ne Dabai ya zauna tare da iyalansa, har zuri’arsa ta hayayyafa ko ta bunƙasa, sai shi Dabai ya sama zuri’arsa sunan Babanshi wato “Dakka” ya yi haka ne saboda riƙo da sunan mahaifinshi. Shi kuma Dakka yana zaune ne a ƙasar Zamfara tare da zuri’arsa, haka ya sa Zamfarawa suka ɗauki Dabai a matsayin ɗansu, su kuma ‘ya’yan Dabai, sai suka ɗauki Zamfarawa a matsayin kakaninsu. Don haka wannan taubasantakar da ke tsakanin waɗannan al’ummomi, taubasantaka ce irin ta jika da kaka.

 

Bayan haka kuma, wannan taubasantakar ta yi tasiri sosai, domin har ta haifar da wasu muhimman abubuwa a tsakanin waɗannan al’ummomi daga cikin abubuwan da taubasantakar ta haifar sun haɗa da:

1.      Ƙarfara zumunci

2.      Auratayya tsakaninsu

3.      Sun fahimci al’adun juna

4.      Taimakon juna a kan sha’anin rayuwa

5.      Haƙuri da girmama juna

A taƙaice dai waɗannan su ne abubuwan da taubasantakar ta haifar a tsakanin Zamfarawa da Dakkarawa. Daga ƙarshe dai waɗannan bayanai da suka gabata, su ne sakamakon wannan bincike.

 

5.2 RA’AYIN MAI BINCIKE/SHAWARWARI

Ra’ayi ko shawarwari su ne abubuwa da ake dubawa domin a cigaba da fagen ilimi gaba, dangane da wannan bincike, zan iya ba da shawara zuwa ga ma’abota bincike ko ma’abota nazarin harsuna da ma tarihi da su mai da hankali sosai wajen nazarin dangantakar da ke tsakanin al’ummomi abokan zaman juna, domin samun cikakken zaman lafiya mai ɗorewa a wannan ƙasa tamu. Da ma sauran wasu ƙasashe na duniya.

Sannan ina ba da shawara ga wanda zai gudnaar da wani bincike mai alaƙa ko kusanci da wannan bincike. To idan ya ci karo da wannan aiki, ka da ya ce zai kwashe aikin gaba ɗaya, ina ba shi shawara da ya yi ƙoari ya zurfafa bincike domin ya ƙara gano wasu muhimman abubuwan da ke tsakanin waɗannan al’ummomi da tunanena bai kai garesu ba, saboda yin hakan zai taimaka sosai wajen samar da ingantattun bayanai waɗanda za su taimaka wajen ƙara samar da cikakken zaman lafiya a tsakaninsu.

 

Haka kuma ina mai ba da shawara ga ‘yan uwana ɗalibai da su farka daga bacci; su tashi su yi aiki tuƙuru wajen binciko abubuwa masu muhimmanci, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa ko ciyar da harshen Hausa gaba.

 

Sannan kuma ina mai ba da shawara ga wanda zai duba ko wanda hannunshi ya kai ga wannan bincike idan an ga wani kuskure dangane da bayanan da ke cikin wannan kundi ko dangane da rubutu, za a iya gyarawa domin hakan ya kasance raunina ne saboda zamana ɗan ƙaramin ɗalibi mai nazarin Harshen Hausa.

 

Daga ƙarshe dai ina ba ‘yan uwana ɗalibai shawara cewa; bincike abu ne mai matuƙar muhimmanci, kuma yana taimakawa sosai wajen ciyar da fagen ilimi gaba. Sai dai kuma bincike abu ne mai son haƙuri da juriya gami da naci, dole ne sai mai bincike ya haɗa waɗannan abubuwa sannan haƙarsa za ta cimma ruwa. Duka, duka dai ina roƙon Allah da ya ba mu sa a da nasara a sha’anin rayuwarmu. Kuma ina roƙon Allah ya ɗaukaka harshen Hausa da kuma masu nazarin harshen, amin.

 

5.3 NAƊEWA

A taƙaice dai zan iya cewa wannan shi ne matakin ƙarshe na wannan bincike. Haka kuma wannan bincike ya yi tsokaci a kan abubuwa da dama waɗanda suke ƙunshe a cikin babuka-babuka, tun daga babi na ɗaya har zuwa na biyar kamar haka: babi na ɗaya ya ƙunshi manufar bincike, dalilin bincike, farfajiyar bicike da Hanyoyin gudanar da bincike, sai bitar ayyukan da suka gabata, sai muhimmancin bincike sai Naɗewa.

 

Babi na biyu; akwai Gabatarwa, ma’anar dangantaka, wane ne Bazamfare, Asalin Bazamfare, ƙasar Zamfara, sai kuma wane ne Badakkare, da Asalin Badakkare, sai ƙasar ko mazaunin Badakkare da kuma alaƙar Bazamfare da Badakkare, sai naɗewa.

 

A cikin babi na Uku; ya ƙunshi Gabatarwa, ma’anar Taubasantaka, asalin taubasantaka, su wane ne taubasai, sai taubasantakar Bazamfare da Badakkare, daga ƙarshe sai naɗewa.

 

Babi na Huɗu; akwai Gabatarwa, ƙarfafa zumunci, akwai auratayya tsakanin Bazamfare da Badakkare, akwai fahimtar al’adun juna, sai taimakon juna, da kuma haƙuri da girmama juna, sai naɗewa.

Babi na Biyar shi ne babi na ƙarshe wanda ya haɗa da Gabatarwa, sai sakamakon bincike, da ra’ayin mai bincike/ shawarwari, akwai Naɗewa sai kuma manazarta.

 

Waɗannan su ne abubuwan da wannan kundin bincike ya ƙunsa ga baki ɗaya, kuma a kan su ne wannan bincike ya yi bayani.

MANAZARTA

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments