Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (3)
NA
ABDURRAHMAN LAWALI
BABI NA BIYU
MAGUZAWAN KWATARKWASHI
2.0 GABATARWA
A babin da ya gabata na yi taƙaitaccen tsokaci dangane da bitar ayukkan da suka gabata,
da kuma hujjar ci gaba da bincike tare da muhallin bincike. Haka kuma na
bayyana dubarun da aka bi wajen binciken da kuma muhimmancinsa.
Saboda haka a wannan babin zan tsunduma ne kai tsaye
ga bayanin ma’anar Maguzanci. Sa'annan daga baya in yi magana a kan su wane ne Maguzawa? Da kuma
ya ya Maguzawa ke yin Maguzanci ta hanyar zamantakewarsu? Har wa yau kuma, zan yi taƙaitaccen bayani dangane da amfanin Maguzanci ga Maguzawa.
2.1 MA’ANAR MAGUZANCI
Maguzanci wata rayuwa ce wadda Bahaushe ya samu kansa a ciki gabanin karɓar kowane irin addini. lta wannan rayuwar ana iya cewa daɗaɗɗa ce tun daga iyaye da kakanni. Malamai sun tofa albarkacin bakinsu a kan
ma’anar Maguzanci kamar haka:
Kango A.U. (2008) ya ce “Maguzanci rayuwa ce wadda Bahaushe (Bamaguje) ya
samu kansa ko kuma ya tashi a cikinta ba tare da damuwa ko samun wata takura ko
hani dangane da irin abin da yake gudanarwa na rayuwarsa ba” wato kamar yadda
addini kan shimfiɗa dokoki ga mabiya.
Gambo, (2008) cewa ya yi “Maguzanci ’yantacciyar rayuwa ce ga Bahaushe
(Bamaguje) ta yin annashuwa kawai”. Don haka dai ko ya ya ne, Maguzanci yana
nufin rayuwar da Bahaushe (wato Bamaguje) yake gudanarwa bisa son rai, nishadi
da shugulgulan more rayuwa na zaman duniya.
A nawa ra’ayin, kalmar Maguzanci na nufin rashin addini. Maguzawa mutane ne
da ba su bautar Ubangiji. A ƙasar Hausa duk mutanen da basu karɓi addinin Musulunci ba ana kiransu da wannan suna na
Maguzawa, wato masu biyar addinin gargajiya.
A ƙasar Hausa, duk mutanen da ba su karɓi Musulunci ba ana kiransu da wannan suna kamar yadda ake gani a wasu sassa
na Kano, Jigawa, Katsina da Zamfara. Alal misali a Kano wajen Sumaila da
Gwarzo, Tudun wada, Jigawa a ƙasar Roni da Katsina a wajen ƙasar Bicci, a Zamfara kuma
Kwatarkwashi.
2.2 SU WANE NE MAGUZAWA?
Kamar dai yadda muka sani
kalmar Maguzawa kalma ce da ta ci karo da ra’ayoyin masana da manazarta da dama
dangane da ƙoƙarin gano asalinta. Kowane masani da manazarci da irin kallon da ya yi
mata.Duk da yake masana da dama sun yi tarayya kan ra’ayi ɗaya kamar haka:-
Kruisius (1915) cewa ya yi
“Wasu suna da ra’ayin cewa kalmar Bamaguje na nufin jinsin namiji na
Maguzawa.Ta samu ne a lokacin da fulɓe da laɓe suka karɓi sallah, wato suka zama Musulmai. Ɗan uwansu mai suna Bama ya ƙi yin sallar. Ya ɗauki ɗabi’ar rabuwa da su a duk lokacin da za su yi sallah. Tun daga lokacin Bama
ya guje wa masu sallah, ko ya guje sallar. Ta haka ne da tafiya ta yi tafiya
aka haɗe kalmomin guda biyu “Bama” da
“guje” (Bama + guje) aka sami Bamaguje. Daga nan aka ci gaba da kiran duk marar
sallah Bamaguje. Jam’in mutanen da suka ƙi yin sallah, ‘yan uwan Bama su ake kira Maguzawa.
Malamin ya ƙara da cewa, wannan ra’ayin mai rauni ne ƙwarai, domin ga dukkan alamu an
danganta kalmar Bamaguje ne da ɗabi’ar ta hanyar dabarar nan ta mutane ta ƙirƙiro labari ta yadda zai dace da
lafazi, a nuna dangantakarsu ko asalinsu.
Kruisius (1915) ya ƙara da cewa “A ra’ayoyin Robinson, a matsayin karɓaɓɓen ra’ayi da hankali zai iya ɗauka ya nuna cewa, akwai wata kalma a Larabci “Majusi” wadda ke nufin
“Masihirci” ko mai yin sihiri ko hatsabibi. Wannan kalma ta Larabci tsohuwar
kalma ce wadda ake amfani da ita wurin zagin mutum.Yana ganin daga kalmar “Majusi”
Hausawa suka mayar da ita “Maguzawa” (Majusi – Majuji – Maguji – Majusawa –
Majuzawa – Maguzawa).
Bargery (1934) yana da makusanciya da wannan ra’ayin da ke nuna an samo kalmar Maguzawa
daga kalmar “Majusi” ta harshen Larabci. Kamar yadda ya ce, kalmar na nufin
“Arne” daga nan ne aka sami Bamaguje (tilo namiji), Bamagujiya (tilo mace),
Maguzanci (hanyar rayuwar Maguzawa).
Mahdi Adamu (1980) shi ma ya yarda da wannan ra’ayi mai nuna kalmar ta
Maguzawa ta samu ne daga kalmar Larabci “Majusi”, mai nufin “Arne” ko “Azne”.
Ya ƙara da cewa “Wata ƙila Hausawa musumlmai sun fara amfani da kalmar ne bayan addinin Musulunci
ya fara yaɗuwa a ƙasar Hausa, a wajajen farkon ƙarni na sha tara (19).
Wato sunan da aka laƙaba wa Hausawa da basu karɓi Musulunci ba”.
Kamar yadda muka ambata da farko game da Maguzawa, inda muka ce su dai
Maguzawa ba wasu mutane ba ne daban illa Hausawa ne tantagarya, ba su da wani
harshe da ya wuce harshen Hausa tsinsta.
Don haka ke nan idan an yi maganar Maguzawa za a iya cewa su ne Hausawa
masu biyar addinin gargajiya. Kuma su Maguzawa su ne Hausawa na asali. Kuma waɗan da ba su yarda da munafunci, hasada, ƙarya, cin amana, zalunci
ko rudda ciki da dukiyar wani ba.
Su Maguzawa mutane ne waɗan da ba su da wani addini da su ke bi amma kuma ba su yarda da ɗaya daga cikin abin da aka lissafa a sama ba. Kuma ko da
a ce ɗan uwansu, ɗansu ko mahaifinsu ya aikata wani laifi a cikin al’umma
ba za su rufa laifinsa ba, sai sun faɗi laifin mai laifi.Sannan su ba wa mai gaskiya gaskiyarsa. Kuma ko da wani
zai zo ya yi wata magana da manufar ɓatawa wani suna, ko haddasa wani makirci!, to lallai za su binciki wannan
mutum da ya faɗi gakiya domin kuwa za su kira wanda
aka yi gulmar a tambaye shi game da waccan maganar da ya faɗi game da wannan mutum; wanda idan ba gakiya ba ne, wanda
ya yi gulmar zai samu kansa cikin masu Nadama a kan abin da ya faɗa. Kuma ba zai yi fatar ƙara irin wannan hali ba.
Don haka, su Maguzawa mutane ne da ba su bin kowane irin addini sai na
gargajiiya (tsafi). Amma kuma suna tsare gakiya da riƙon amana da kuma kula da haƙƙin kowane abokin zama.
Kuma su Maguzawa mutane ne waɗan da ba su da kowace irin sana’a bayan noma da kiyo, domin idan aka yi
maganar noma babu waɗan da ake ta’allaƙawa da shi face Maguzawa.Shi ya sa wasu ke tsokanar ‘yan uwansu da cewa
“Mutum ya kama noma ba ya gajiya kamar Bamaguje?”.
Kuma har bayan wucewar damana Maguzawa ba mutane ba ne masu son zaman
banza, domin da zarar rani ya yi maimakon su zauna haka nan, zaka ga sun fara
farauta don kama ƙananan namun daji, da manyan ma domin wadata kai da nama, domin ci da
sayarwa.
Kuma su Maguzawa mutane ne ma’abota son nishaɗi a kodayaushe, don haka da zarar damana ta wuce kafin su
fara farauta, zaka ga sun ci gaba da haɗuwa da ‘yan uwansu a kasuwanni a inda za su fara more rayuwarsu ta hanyar
shaye – shayen giya da burkutu. A nan ne za ka ga sun taru maza da mata da
iyaye tare da shahararrun makaɗansu waɗan da ke ƙara zuga su a lokacin da suke gudanar
da rayuwarsu ta Maguzanci.
A irin wannan lokacin ne makaɗansu ke zuga su da kuma nuna fifikon jaruntakarsu da
sauran Maguzawa ‘yan uwansu da ke wani gari. A lokacin kuma za ka ga wasu ma
suna kirari, kuma suna yi masu kyauta (watau su makaɗan), wanda ke nuna lallai sun gamsu da zugar da ake yi
masu.
Haka ma har a bukin shan giya, Maguzawa kan ziyarci wasu a garinsu domin
shirya liyafar shan giya, wanda a nan ne ake samun wanda zai zama zakara (wato
jarumi) a wajen shan giya, wanda ya fi kowa sha da yawa kuma bai faɗi ba. Kuma a nan ne wasu kan yi wa wasu ƙeta, ta hanyar sa masu
guba ko wata cuta a cikin giyar idan an ga mutum jarumi ne ta hanyar noma ko ta
hanyar shan giya. Kuma a cikin irin wannan mahaɗa ce waɗansu kan yi wa wasu kyautar ɗiyansu mata don su aura, a dalilin kyautar giya ko
jaruntaka da wani ko wasu suka nuna.
Kuma Maguzawa kan iya ɗaukar kwana da kwanaki suna yawo gari – gari domin shan giya ba tare da sun
koma gidajensu ba.
Haka kuma, su Maguzawa mutane ne masu son zumunci, domin Bamaguje kan iya
barin garinsa zuwa wani gari mai nisa domin ziyartar ɗan uwansa. Haka kuma yana iya ɗaukar lokaci mai tsawo tare da ɗan uwan nasa wanda
ya ziyarta. Kuma idan har ya tarar da wannan ɗan uwan nasa cikin wani aiki to ba zai yi wata – wata ba
sai ya tsunduma a ciki ko da kuwa wannan aiki yana da matuƙar wahala. Kuma ko da wannan aiki
zai ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da an ƙare shi ba.
Kuma Maguzawa mutane ne waɗan da abinsu ba ya rufe masu ido domin suna iya kyautar kome suka mallaka
ko da kuwa daga baya za su fuskanci matsalar abin da suka bayar. Misali,
Maguzawa kan iya samun kansu a cikin matsalar abinci da zasu ciyar da gidansu,
amma idan wani ya zo domin neman abin da zai ciyar da iyalansa, sukan ɗauka su bayar ga wanga ya nemi taimakon abinci, wato su
ciro su bashi domin ganin sun rufa masa asiri game da abin da yake buƙata garesu, don kada
yaga kasawarsu.
Bayan haka kuma, Maguzawa kan iya ɗaukar dawakinsu waɗan da suke hawa domin tafiye – tafiye su bayar da su kyauta ga wanda suka
ga dama, ya Allah maroƙi ne, ko makaɗi, ko sarkinsu, domin neman suna
kawai.
Kuma abu ne mafi sauƙi ga Maguzawa da su yi maka kyautar gona domin ka riƙa nomawa ba tare da sun
buƙaci ko sisin kwabo gare ka ba. Duk da tsawon lokacin da suka ɗauka suna faman saran dajin kafin su mayar da shi gona.
Maguzawa mutane ne masu ƙoƙari a wurin aikin gayya (taimako) wato sukan iya barin gonarsu zuwa gonar
wani, wanda ya buƙaci a taimaka masa idan ya gayyace su wajen huɗa, shuka, noma ko girbi da zarar lokacin ya zo. Misali a
gonar sarki ko wani marasa lafiya ko kuma wanda ɗansa zai auri ɗiyar wani. Akan taimakawa mahaifin yarinyar da ake nema aure wajen aikin
gayya, irin wannan taimakon shi ne wanda ya zama ruwan dare ga kowane daga
cikinsu da ya samu auren budurwa.
A cikin irin wannan lokaci na aikin gayya, Maguzawa ke haɗuwa a gidan wanda aka yi wa aikin gayya domin
gudanar da wasu shagulgula, wato bayan
an dawo daga noma. Irin waɗannan shagulgulan sun haɗa da wasan hoto, kai har ma da sihirce – sihirce da suka haɗa da yin dabon dawa, gyero, duman kwarya, jarirai, sarka,
nono, da sauransu. Kowa da irin nasa siddabarun. Haka kuma a nan ne wasu kan
cuta wa ‘yan uwansu ta hanyar cusa masu cimaka, ya Allah a cikin abinci, ko ta
hanyar haɗa su da aljannu domin naƙasa su, (wanda aka fi
sani da bayarwa). Don haka shi wannan shagali yana ƙara faɗakar da su (Maguzawa) domin a kodayaushe da su zama cikin
shiri, wato su zama masu tambaya kan asirin kare kai daga abokan adawa.
Kuma abin bai tsaya a nan ba, domin har ita kanta gonar noma ba ta tsira
ba, domin ana samun masu ƙoƙarin naƙasa ta da nufin ta zama marar amfani ga mai ita. A nan ma Maguzawa na da dabarun da suke yi da dama domin kare gonarsu daga
abokan gaba.
Maguzawa su ne tsintsar Hausawa
kafin shigarsu a cikin addinin Musulunci; kuma su ne suka mamaye ƙasar da aka sani ta
Hausawa, kuma waɗan da Allah ya yi wa kawaici da
gudun gori ko jin kunya.
2.3 YAYA MAGUZAWA KE YIN MAGUZANCI?
Kamar dai yadda muka ambata a baya cewa Maguzanci rayuwa ce da Hausawa suka
samu kansu a ciki gabanin shiga cikin kowane irin addini, wanda ya ƙunshi shagulgula na jin
daɗin rayuwa, ba tare da samun wata
doka ko tsari da kowane irin addini ya tanada ba.
Don haka, su Maguzawa suna gudanar da kowace irin rayuwa hankali kwance ba
tare da wata damuwa ba, misali:-
i.
Shan Giya
ii.
Cin Mushe
iii.
Tsafe – Tsafe
i. SHAN GIYA: Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da Maguzawa suka ba cikakken
muhimmanci wajen nuna jin daɗin rayuwarsu, kuma shi shan giya abu ne wanda Maguzawa kan yi amfani da shi
wajen ƙulla zumunta da ‘yan uwa da abokai da kuma duk wani muhimmin baƙo da Bamaguje ya samu.
Wannan buki na shan giya Maguzawa na gudanar da shi a cikin kowace irin hidima da ya samu kansa a ciki. Wato kamar bukin aure, zanen suna,
bukin sadaka, bukin cika shekara da kuma bukin rufe gawa da sauransu.
Ita giya a wurin Maguzawa abu ce da ba ta da laifi ko doka, har ma abu ce
da Maguzawa ke alfahari da ita domin
kuwa har gasa akan shirya domin gano wanda yafi ƙwarewa a shan giya tsakaninsu, wanda
daga ƙarshe akan yi masa kyauta. Kuma ana iya ɗaukar sa a matsayin sarkin shan giya ko mashaya. Shi
wannan sarki na mashaya yana da ikon shimfiɗa doka ga kowane mashayi, kuma dole ne ya tabbatar da ya
kiyaye wannan doka kuma idan har wani ya yi kuskure da ya keta wannan doka,
aikin sarki ne ya ladabtar da shi.Ya Allah ta hanyar yi masa tara ko ta hanyar
hana masa shan giya a mashaya idan har laifinsa ba ƙarami ba ne.
Maguzawa suna iya shan giya su bugu son ransu, su bi hanya suna tangaɗi ko ma idan har shan giya ya kai sha suna iya kwana a
mashaya ko a kasuwa ko a kan hanya ba tare da nuna damuwa ba.
Ita dai wannan giya ta Maguzawa ana
yinta da dawa ne da ƙwayar dabino. Ita kuma burkutu wadda muka ambata a farko ana yinta da dawa
ne, wadda suke tsimawa sai ta fara tsiri. Ita ake sarrafawa, kuma wasu ma suna
haɗa dawar da wani abu domin ta ƙara ƙarfi a sha a bugu sosai.
Bayan an gama dafuwar wannan burkutu ana zuba ta ne a cikin tuluna domin ɗauka zuwa mashaya. Ita kuma wannan giyar ta burkutu ko da
ta kwana ne za ka ga tana ta tafasa da bululuƙai a cikin tulu kamar wadda ke bisa
wuta ana dafawa. Kuma tana tafasa tamkar an sa tukunya saman wuta ana dafuwar
wani abu a ciki.
ii. CIN MUSHE: Yana ɗaya daga cikin halayen Maguzawa, wato shi dai cin mushe
yana nufin cin naman duk wata dabbar da ta mutu ba tare da an yanka ba.
Haka kuma, Maguzawa babu abin da ya dame su da kiran dabba mushe (Matatta)
domin a tasu manufa da a yanka, da ta mutu duk ɗaya ne domin dai ko yanka ta aka yi, ai sai an bari ta mutu.Wato rayuwarta ta fita, sannan a ci.
Kuma har suna wani iƙirari na cewa, su waye ‘yan riga?
Mahaukata ne, domin sun ce ba sa cin yankan Allah amma
suna cin na ƙato.
Ma’ana Musulmai wai su ne “‘yan riga”, domin ba sa cin yankan Allah.Wato
dabbar da Allah ya kashe ta mutu.Amma sai ga su suna cin yankan ƙato, wato wadda mutum ya
yanka da kansa. A ganinsu, mafificin yanka da
ya kamata a ci shi ne yankan Allah.Wato wanda ya mutu ke nan, ba wai
wanda mutum ya kashe ba.
Don haka suke ganin cewa, lallai “‘yan riga”, sun yi babban
kuskure a ganinsu, idan har da gaske suke yi. To kamar dai yadda aka riga aka
ambata a sama cewa su Maguzawa mutane ne da ba su karɓi kowane irin addini ba, don haka ba abin mamaki ba ne
idan an ce sun ci mushe. Saboda duk wasu dokoki na hani game da cin mushe an
same su ne daga addinin Musulunci, saboda akwai dabbobin da Musulunci ya hana
ci amma su suna cin su, kamar jaki, da kare da sauran
makamantansu.
Kuma ba su sami kansu a cikin kowane irin addini ba, don haka babu ruwansu
da wannan doka ko hani. Haka kuma game da sauran ƙananan namun daji da tsuntsaye duk
ba su tsira ba, domin babu abin da Maguzawa suka tsallake. Don haka ne ma har
akan yi masu kirari, ana cewa “Arna kunci kulɓa, kun ci maciji, amma har ma ƙadangare nama ne”.
iii. TSAFE – TSAFE: Tsafi yana ɗaya daga cikin babban abin da Maguzawa suka ba cikakken
muhimmanci. Don haka, kamar dai yadda aka riga aka ambata tun da farko cewa
Maguzawa ba su karɓi kowane addini ba in ba Maguzanci ba. Duk da haka wannan bai sa su zauna haka nan ba,
domin kuwa suna aiwatar da tasu hikima ko dabara ta ‘yan tsafe – tsafe. Kuma
suna yin su domin wasu muhimman dalilai da suka ba da gaskiya da aukuuwar su.
Misali kare kai daga maƙiyi, ko neman biyan kowace irin buƙata ta irin waɗannan hanyoyi da suka haɗa da:-
A. Sammu
B. Faskare
C. Kafin gida ko gona
A. SAMMU: Sammu shi ne wani abu wanda ya ƙunshi sihiri domin a raba mutum da
muhallinsa zuwa wani gari da nufin raba shi da iyalansa ko kuma gidansa, domin
a cimma wata biyan buƙata da ake nema.
Akwai kashe – kashen hanyoyin gudanar da sammu waɗanda suka kasu kashi huɗu (4). Ga su kamar haka:
a.
Turbuɗa
b.
Kiraye ko harbin kasko
c.
Aikin aljannu
d.
Cimaka (watau hanyar ci
ko sha)
a. TURBUƊA: Wannan hanya ce ta aiwatar da sammu wadda Maguzawa kan
yi ta hanyar shirya wani ƙulumboto ko shirka (shi ne gaskaka wani abu wanda ba
Allah ba). Misali, sanya hatsi
mararrabar hanya, ko kuma boka da za a kai shi a gidan wanda
aka yi don shi ko kuma gonarsa. Ana tona rami a tsakiyar gidan ko gonar a saka
wannan ƙulumboton, sannan a mayar da ƙasar a rufe.Wanda idan an yi nasara to wannan ka iya haifar da rasa rayuwar
wanda aka yi
wa wannan shirka (shi ne gaskaka wani abu wanda ba Allah
ba). Misali sanya hatsi a mararrabar hanya ko boka domin jefa shi a cikin wani
mawuyancin hali na lalura ko lalacewa.
Wato ko dai ya faɗa cikin matsalar juyewar ƙwaƙwalwa, watau hauka, ko ya kasance ba ya iya amfana wa
kansa komai a duniya.Ya kasance komai sai an ba shi wato kyauta ke nan. Kuma
ita wannan turbuɗa ana iya aika ta zuwa kowane gari
kuma ga kowane irin mutum.Wato ko da ba a yi amfani da hanya ta farko ba, watau
ta kai wannan turbuɗa a cikin gida ko gona ba.Wannan ya nuna Maguzawa tun farko suna da hanyar aika wa abokan gaba sammu daga gari
zuwa wani gari ko daga ƙasa zuwa wata ƙasa.
b. KIRAYE KO HARBIN KASKO: Wannan ita ma wata
hanya ce ta sammu da Maguzawa ke amfani da ita domin gudanar da sammu zuwa ga
abokan gaba. Wannan hanya kuwa suna amfani da kasko da za a zuba
wa ruwa da wasu sihirce – sihirce, daga nan sai a kira
sunan wanda ake son yi wa wannan sammu a cikin kasko kuma a ganshi a cikin
madubi.
To kafin haka dama dai wannan kiraye ko harbin kasko, ya riga ya tanadi
wani ɗan baka na shirka (shi ne gaskaka
wani abu wanda ba Allah ba) wanda sukan yi amfani da ƙashin awazar mutum don ɗaura wannan baka. Haka kuma za a samo ƙayar aduwa ko allura
wadda suke tsafawa domin yin amfani da ita wajen harbin wanda suka yi wa wannan
kiraye. Kamar dai yadda aka riga aka yi bayani cewa suna kiran sunan wanda ake
nufin yi wa wannan kiraye a cikin kasko, sai ka ga fuskar mutum a cikin kasko,
sai a soke shi. Kuma da zarar an yi nasara za ka ga wannan ruwan sun yi jawur kamar jini wanda ke nuna lallai an gama da wannan mutum.
Kuma da zarar haka ta kasance, to za ka ga shi wanda aka yi wa wannan
kiraye ko harbin kaskon, ya faɗa cikin wani mawuyacin hali na lalura ko kuma ya kasance sanadiyyar
mutuwarsa, matuƙar dai mutumin ba shiryayye ne ba.Amma idan shi ma ya shirya kansa, to ba
za a ga komai ba da an yi wannan aikin na kiraye ko harbin kasko, wanda shi zai
nuna cewa shi ma mutumin ya ci maganin faskara.
c. AIKIN ALJANNU: Aikin aljannu yana daga
cikin hanyoyin da Maguzawa ke bi wajen tafiyar da sammu zuwa ga ɗan uwansu ko abokan gaba.
Sukan tanadi jan zakara, baƙar kaza, mai wake – wake, baƙin bunsuru, jar akuya, goro, turare,
giya, madara da sauransu waɗan da sukan ɗauka zuwa wurin tsafe – tsafensu da
nufin bayarwa ga duk irin aljanin da suke ma’amala da shi ko wanda suke neman
wannan biyan buƙata daga gare shi.
Waɗannan wuraren kan iya kasancewa
wurin wata kuka, tsamiya, gidan tururuwa, mararrabar hanya da sauransu.
A nan ne, za ka ga suna wasu maganganu irin na nuna ban gaskiya da kuma
neman taimako ko biyan buƙata ga wannan aljani da suka zo wurinsa don ya taimaka
masu ga biyan buƙatunsu ko da kuwa na cutarwa ne ga wani. Bayan sun gama neman biyan buƙatunsu wasu za su saki
waɗannan abubuwan da suka tafi da su
wurin tsafin. Wasu kuwa sukan yanka waɗannan abubuwa ga waɗannan aljannun su sha jini. Suna kuma kai turare ko goro, su kuwa waɗannan ana ajiye wa a gindin wannan abu da aka tafi
wurinsa.
Wasu kuma suna zuba waɗannan abubuwa ne ga jikin wannan iccen da kuma kewayensa. Irin wannan tsafi
ne ake kira aikin Inna ko Doguwa ko Masharuwa da sauransu.
Bayan an aikata haka, shi wanda aka yi wa wannan aiki zai faɗa a cikin irin abin da aka buƙaci ya samu kansa a ciki, ko ma ya
kasance sanadiyyar rasa rayuwarsa ta hanyar kumburewa, ko shanyewar wani sashe
na jiki ko kuma juyewar ƙwaƙwalwa ko juyewar siffa da sauransu.
d. CIMAKA: Wannan ita ma daga cikin nau’in
sammu ne wanda Maguzawa kan yi. Cimaka ita ce mafi muni daga cikin sammu domin
ita tsabar rashin imani ce ko tausayi. Su kansu Maguzawa suna aikata ta ne
kawai ga abokan gabarsu ko waɗan da suke jiye wa (watau ƙyashi).
Ita cimaka tsiya ce da Maguzwa ke shiryawa domin bayar da ita ga wanda aka
yi wa, kuma cimaka ba ta samun nasarar bayarwa sai ta hanyar zamba cikin
aminci. Domin sai masoyinka ko ɗan uwanka ko abokinka kaɗai ake yin amfani da shi wajen haɗa kai da shi domin bayar da ita ga wanda aka yi ta domin shi.Ya Allah ta
abinci, ko ruwan sha, ko wanin wannan. Irin su goro, giya, nama da sauran
abubuwan da ake ci.
Idan ba a haɗa kai da wani mutum ba, to cimaka ba
za ta samu nasara ba ke nan a wajen bayarwa.
Har ila yau, idan an tuna an riga an faɗi cewa ana bayar da ita ne ta hanyar zamba cikin aminci. Wanda duk ba ka
shiri da shi, zai yi wuya ya ba ka wani abu ka ci domin kasancewar
komai na iya faruwa. Ka ga kenan ita cimaka tana samun nasara ta wurin da mutum
ya saki jiki, ya miƙe ƙafa, ganin babu wani makirci da za a haɗa kai da wani daga cikin abin da muka ambata.
Don haka, cimaka na faruwa ne ta hanyar zamba cikin aminci, kamar yadda
madawakin Ɗan Kande Takulawa (2002) ya ce
“Cimaka wata hanya ce ta cuta wa abokin gaba wadda aka jiyewa ta hanyar zamba
cikin aminci”. Don haka ita cimaka ba wata abu ba ce illa mugunta da nufin cuta
wa wani; ya Allah domin Allah ya fifita shi ne, ko wata baiwa ce da kuma ɗaukaka da ya samu, ko rashin jituwa. To ana yinta domin a
nakasa shi, ko dai da nufin kawar da shi ne ko kuma baiwar da ya samu ta gushe.
Saboda haka shi sammu wani ƙulle – ƙulle ne na makirci da ake gudanarwa ta hanyar shirka da
Maguzawa ke yi domin kawar da, ko jefa wani mutum cikin mawuyacin halin rayuwa.
Kuma Maguzawa suna alfahari ko iƙirari da nuna gagara, kuma har ma ya kasance mutane na
saunar wanda ya ƙware da shi (watau sammu ɗin). Kuma da wuya ka ga ana musanta wanda ya mallaki irin wannan mugun abu
don gudun faɗawa cikin ire – iren matsalolin da
aka ambata a sama.Saɓanin abin da addini ya zo da shi na mayar da komai ya same ka zuwa ga
Mahalicci.
B. FASKARA: Ita wannan wata hanya ce da
Maguzawa ke gudanar da tsafe – tsafensu na Maguzanci wanda suka bayar da
gaskiya a gare shi. Mai gida Gambo gidan cindo cewa ya yi “Faskara garkuwa ce
ga duk wani ƙulle – ƙullen da kan fito daga abokan gaba ko maƙiya”. Don haka ke nan, Maguzawa sun
yarda da cewa faskara tana kare su daga duk wani shiri da wani maƙiyi ko mai jiyewa kan yi
da nufin cuta masu; ya Allah ta hanyar sammu ko ta hanyar kafin gona ko gida.
Kuma Maguzawa na bugun gaba ko taƙama a kan faskara wadda har wasu ke ganin sun gagara a
kan kowace irin barazana da ta fito daga abokan gaba ganin cewa sun ci, sun
sha, ko sun yi wanka da faskara.
Kuma ita faskara ana samun ta kusan hanya ɗaya da yadda ake samun aikin aljannu. Domin ita ma ana
samunta ta hanyar ne, ko wurare tare da amfani da wasu kayayyaki da akan tanada
kamar dai irin na sammun aljannu. Kuma ana bin duk wata hanya da ake bi wajen
aiwatar da sihirce – sihirce, ko ana samun aikin aljannu a wurin ɗibar faskara.
Bambancinsu kaɗan ne, wanda shi ne irin furucin da akan yi wurin gudanar da sammu ya
bambanta da irin furucin da a kan yi wurin ɗibar faskara. Domin shi sammu, abin da ake buƙata ya kasance a kan
fade shi, shi kuma ɗibar faskara, kiraye ce ko garkuwa ko tsari ne akan ambata, ko kuma akan buƙata lokacin ɗibarsa. Wannan ya nuna cewa bambancinsu furuci kawai ke
nan, kuma kusan duk abin da akan tanada duk ɗaya ne.
C. KAFIN GIDA KO GONA: Ita ma wannan hanya ce
ta surƙulle ko sihirce – sihircen Maguzawa wanda shi ma ya kusanta da sammu ko
faskara. Yana iya zama ɗaya daga cikinsu, sai dai hanyar kowane daga cikinsu ta bambanta.Domin shi
dai kafin gida ko gona yana nufin wani turke ko ginshiƙi ko kare gida ko gona daga abokan
gaba, ko kuma nufin samun ingantattar albarka daga kowanensu.
Idan aka lura, kafin gida ko gona ya kusanta da sammu ko faskara ke nan ta
hanyar da ake bi wajen samun su ta zama ɗaya kenan.Kuma da hanyar gudanar da su. A nan shi kansa kafin gida ko gona
wani sihiri ne ko ƙulle – ƙullen Maguzawa da sukan shirya kuma su kafe a tsakiyar gidan ko gonar mutum
da nufin kare wannan gida ko gona daga sharrin duk wani abokin gaba ko masu
mugun nufi na sihiri domin ɗauke amfanin wata gona zuwa tasu gonar, misali:
- Hyune
- Kandun Baka (Kurkura)
a. HYUNE: Wannan wani shiri ne na Maguzawa da sukan yi wajen ɗauke amfanin gonar wani zuwa tasu. Wanda gwanin hyune
yakan iya ɗaura dame ɗari (100) a cikin ‘yar ƙaramar gonar da ba ta wuce a ɗaura dame hamsin (50) ba, ko arba’in (40). Wanda ke nuna
cewa sauran damman na gonar wani ne. Haka kuma shi mai gonar da aka yi wa
hyune, kan samu ɗaura dame arba’in (40) ne a cikin
gona ɗaya, wadda ya kamata ya ɗaura dame ɗari (100) ko fiye. Amma ta dalilin kariya ga irin wannan ke sa Maguzawa ƙara tashi tsaye domin
neman kafin gona.
b. KANDUN BAKA (KURKURA): Ita kuma wannan ba ta
da wani cikakken amfani ga mai yinta,
domin ita mai yinta ba ya ƙaruwa da komai daga abin da ya yi, illa mugunta da
cutarwa ga wani kawai. Saboda shi yakan ambaci wani abu mararsa amfani ko
alheri ga gona ko ga wani abu, kuma a sanadiyyar furucin nasa zai haifar da
nakasar wannan gona ko duk abin da ya yi wa wannan mugun ƙuduri ko furucin nasa.
Don haka ke nan, maimakon ya ƙulla wani abu wanda shi kansa zai amfana, ba zai yi haka
ba, sai dai ƙudurin lalata wani ko nakasa baiwar da wani ya samu. Don haka ke nan dole
ne Maguzawa su tashi tsaye domin kare kansu da muhallinsu da gonarsu daga maƙiya da duk wani mugun
nufi nasu. Kuma Maguzawa sun bayar da gaskiya a kan cewa kafin gida ko gona na
haifar da ingantacciyar kariya, domin kuwa a ganinsu gida ba ya zama lafiya ba
tare da an yi masa wata dabara ba (wato kafin gida).
Wannan dabara kuwa ita ce kafin gida. A imaninsu duk gidan da ka ga babu
cikakken haɗin kai, ko kuma aka cika yawan
rikici da yawan ƙaddarori, ana danganta haka da rashin kafin gida. Kuma ma ko da ɓarna ta mutane ta cika yawa cikin gida ta yara ko manya
ko kuma wata hasara ta cika samuwa a gida, to Maguzawa na danganta shi da
rashin kafin gida ko gona. Suna amfani da kafin gida wajen kare kansu daga ɓarawo da zai iya shiga gidansu ya yi masu sata.
Haka nan ma suna amfani da wannan sihiri domin kafe matansu, wanda ke hana
matansu fita su sake wani aure ko da kuwa suna cikin mawuyacin halin rayuwa
ne.Kuma ma ko da shi mijin nasu ya mutu, matuƙar dai ba karya wannan shiri na
kafin ba, to ba yadda za a yi su fita.
Shi ya sa yana da wuya matar Bamaguje ta fita daga gidan mijinta ko da kuwa
mijin nata sakarai ne. Wannan shi ya sa har ma yana iya tafiyarsa na wani
lokaci mai tsawo kuma idan ya dawo ya tarar da matarsa a gidansa. Kuma don
ganin wani, idan har wani ya yi kuskuren kawo wa wannan mata magana ta ɓatanci game da mijinta, to lallai za ta faɗa wa mijin nata. Kuma a nasu gani, duk wannan yana faruwa
ne domin irin kafin gida da suka tanada.
2.4 AMFANIN MAGUZANCI:
Kamar yadda aka sani cewa, komai mutum ke yi ba zai rasa amfani da kuma
rashin amfani gareshi ba. Haka shi ma Maguzanci yana da cikakken amfani da kuma
irin nasa rashin amfani ga Maguzawa. Wanda a cikinsa ne suke gudanar da al’amurransu
na yau da kullum hankali kwance ba tare da wata takura ba, ko bin doka irin ta
addinin Musulunci.
Don haka, Maguzanci hanya ce ta jin daɗin rayuwa wadda mutum kan iya yin abin da ya ga dama,
kuma yana iya ci ko sha na kowane irin abu da yake so, irinsu nama kowane iri,
ko shan giya don jin daɗin rayuwarsa.
Kuma maguzawa na iya taruwa mata da maza, yara da manya a wuri ɗaya domin raye – raye da kaɗe – kaɗe da waƙe – waƙe, saɓanin irin dokokin da ‘yan riga (wato
Musulunci) suka samu kansu a ciki.
Haka kuma maguzawa na amfani da tsafe – tsafe wajen kare kansu da
muhallinsu da gonakinsu daga sharrin abokan gaba da mahassada. Wato ta hanyar
faskara da kafin gona. Kuma suna iya kawar da duk wani abokin gabarsu ta hanyar
sammu, wanda ke sa har ya kasance ana jin tsoron wanda duk yake irin wannan
shirka (wato gaskaka wani abu wanda ba Allah ba).
2.5 NAƊEWA:
Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi, mun yi magana a kan ma’anar
Maguzanci, inda na kawo ra’ayoyin malamai daban – daban dangane da ma’anar
Maguzanci. Wannan ya nuna mana cewa a taƙaice, “Maguzanci wata rayuwa ce wadda Bahaushe ya samu
kansa a ciki gabanin karɓar kowane addini”.
A gaba kuma, na fayyace ko su wane ne Maguzawa a cikin wannan babi wanda ya
nuna mana cewa Maguzawa su ne Hausawa na asali. Kuma mun dubi yadda Maguzawa ke
yin Maguzanci, wato tun daga abin da ya shafi shan giya, cin mushe, tsafe –
tsafensu da kuma sauran al’amurra da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum.
A ƙarshe na tattauna akan amfanin Maguzanci da Maguzawa ta fuskar:-
i.
Sakewarsu cikin rayuwa
ii.
Rashin ƙuncin rayuwa
iii.
Kare kai daga sharrin
abokan gaba da mahassada.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.