Zamfarci Da Rabe-Rabensa (1)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Zamfarci Da Rabe-Rabensa (1)

NA

AHMAD MUHAMMAD KABIR

Zamfara

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki nawa zuwa ga mahaifiyata, marigayiya Bilkisu Muhammad Abubakar wadda Allah (SWA) ya yi wa rasuwa shekarun da suka gabata, domin ita ta ba ni ƙwarin gwiwa a wajen karatuna da kuma irin addu’o’in da take yi man a lokacin rayuwarta. Da fatar Allah ya jiƙanta da rahama amin.

GODIYA

Ina matuƙar godiya ga Allah (SWA) mai kowa mai komai, mai iko a kan kowa, wanda ya ƙaddare ni da kammala kundin dirigirina na farko. Ina salati marar iyaka ga jagoran wannan al’umma, Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa da kuma waɗanda suka bi tafarkinsa har ya zuwa ranar ƙiyama.

Ina miƙa godiya ta musmaman ga madugu uban tafiya wato malam Isah S/Fada Zugu, wanda ya kula da duba wannan bincike tare da ba da shawarwari haɗi da gyare-gyare, don tabbatar da wannan kundin bincike zai zama mai amfani ga jama’a. Haka kuma ya taka gagarumar rawa wajen ganin binciken ya zama mai amfani ga al’umma ba tare da nuna gajiyawa ba, ina roƙon Allah ya cika masa burinsa, amin.

Haka kuma ina godiya ga malamaina da suka shayar da ni ilimi kamar Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, da Farfesa Halliru Ahmad Amfani, da Farfesa Balarabe Abdullahi Ibrahim da Farfesa Magaji Tsoho Yakawada da Farfesa Muhammad Lawal Amin, Mal. Rabi’u Aliyu Ɗangulbi, Musa Abdullahi da Sauran dukan malaman da suka shayar da ni ilimi.

Ina miƙa godiya ta musamman ga malam Bashir Aliyu Tsafe, malami a FCET Gusau bisa ga gagarumar gudummuwar da ya ba ni da kuma irin shawarwarin da ya ba ni a cikin wannan bincike nawa. Allah ya saka da alhairi.

Godiya wadda babu adadi zuwa ga mahaifina Alhaji Muhammad Habib, bugu da ƙari ina godiya ga yayana alaramma Muhammad Kabir Muhammad Likita bisa ga yadda suka tafiyar da rayuwata da sauran ‘yan’uwa na maza da mata. Ba zan manta da abokina ba wato jamilu Mu’awuyya bisa ƙwarin gwiwar da yake ba ni, haka zalika ina godiya ga Mukhtar Umar wanda ta sanadiyar sa ne na samu shiga jami’a.

Daga ƙarshe ina miƙa godiyata ga matata Maryam Sulaiman da ‘ya’yana Bilkisu (Walida) da Aminatu Ahmad, dukkan su Allah ya saka masu da alhairin sa, amin.

Ina godiya ta musamman ga abokanin karatu na maza da mata, Allah ya biya wa kowa buƙatunsa na alhairi.

TSAKURE

Wannan bincike ya yi nazarin wasu kalmomin karin harshen Zamfarci da yadda suka saɓa ko suka sha bamban da Daidaitacciyar Hausa, inda aka zaƙulo bambance-bambance ta fuskokin ginin kalmomi da kuma ginin jimloli. Haka kuma wannan bincike za a zaƙulo rabe-raben karin harshen Zamfarci, inda aka raba su ta hanyar yankunan ƙasar Zamfara, kamar Zamfara ta arewa da ta yamma da kuma ta tsakiya.

Post a Comment

0 Comments