Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Zamfarci Da
Rabe-Rabensa (4)
NA
AHMAD MUHAMMAD KABIR
BABI NA UKU
KARE-KAREN
HARSHEN HAUSA
3.0 SHIMFIƊA
Babi na biyu
ya kawo bitar ayukkan da suka gabata, ya kuma duba rubutattun littafai da muƙalu
da kundayen bincike da gudummuwar aiki ga ilimi, daɗin-daɗawa ya kawo
tsarin gabatar da aiki.
Wannan babi
na uku kuwa zai yi bayanin harshe da kare-karen harshen Hausa. Bugu da ƙari,
zai yi bayanin karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma.
3.1 MA’ANAR
HARSHE
Masana da
dama sun bayyana ra’ayinsu a kan ma’anar harshe daga cikinsu akwai:
Sapir (1956),
ya bayyana ma’anar harshe da cewa “Wata hanya ce ta bayyana kai da kuma hulɗa tsakanin
mutum wadda dabbobi ba su da irin ta”.
Lado (1964)
ya ce “harshe ya zama shi ne rai ko zuciyar duk wani tunani da aiki na Ɗan-dam
musamman dangane da abin da mutum ke ji game da ƙabilarsa ko ƙasarsa
ko addininsa ko kuma yadda shi kansa ya ɗauki kansa”.
Yakasai
(2012) ya bayar da ma’anar harshe da cewa “Furuci ne mai ma’ana da mutane ke yi
ta hanyar magana domin su isar da saƙon da
zukatansu suka ƙudurta da irin mutanen da ke iya fahimtar
wannan nau’i na sarrafa harshe ba tare da ishara da hannu ba”.
Ɗantumbishi
(2004) ya ce “harshe shi ne magana ko furuci wanda ya bambanta mutum da dabba”.
Ta la’akari
da ma’anonin da masana suka bayar ana iya cewa, harshe wata muhimmiyar hanya ce
wadda Ɗan-adam yake amfani da ita wajen isar da saƙo
ta hanyar magana ko rubutu ko kuma ishara. Kuma ya nuna cewa harshe shi ne
tushen mu’amala tsakanin al’ummomi daban-daban na duniya.
3.2
KARE-KAREN HARSHEN HAUSA
Masana ilimin
harshe irin su Sani (2001) sun yi ƙoƙarin
kasa kare-karen harsuna zuwa gida biyu wato karin harshen gabas da kuma karin
harshen yamma. Karin harshen gabas karin harshe ne na mutanen gabacin ƙasar
Hausa. Kafin mu shiga ƙasar Hausa ya dace mu
san ina ne ƙasar Hausa? A ƙoƙarin
gano ina ne ƙasar Hausa abu ne da masana ilimin tarihi da
kuma masana nazarin ƙasa suka daɗe suna tafka
muhawara a kai. Sai dai kowane masani yakan yi ƙoƙarin
kafa hujja dangane da dalilin da za su kare ra’ayinsa.
Ƙasar
Hausa: Ainihin
ƙasar ta asali tana Afrika ta yamma ne, a
farfajiyar nan da ke tsakanin hamadar sahara da dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun
Atlantika daga kudu, kuma ana kiran ƙasar da sunan
sudan ta yamma, wato tsakanin tafkin Cadi da gwiwar kogin Kwara a can yamma. In
aka duba taswirar Afrika, za a sami ƙasar Hausa a
tsakanin layi na goma sha biyar (15N) zuwa na goma sha takwas (18N) na arewa da
Ikwaita. Kuma ƙasar tana tsakanin layi na takwas (8E) dana
goma sha biyu (12 E) a gabas da layin Greenwhich.
Taswirar ƙasar
Hausa
A bisa
bayanin Shaihi malami Mahdi Adamu, ƙasar Hausa ta
asali ta faro ne tun daga lalle da Asodu, can arewa maso gabas da Agades. Daga
nan ne Gobirawa suka taso, da kaɗan kaɗan har suka
zo inda suke a yau a Nijeriya.
A yanzu kuma,
Hausa tana yaɗuwa ne, tana ƙoƙarin
komawa har zuwa gidanta na Jiya, ƙasashen
iyakar ƙasar Hausa a kudu kuwa shi ne, Yawuri da
Zariya, da inda Bauci ta yi iyaka da Kano. (Mahadi 1998).
Gurun gabas
(wato Birom) ita ce iyakar ƙasar Hausa
daga gabas. A yamma kuwa bakinta Filingue. A bayanin Shaihi malam Mahadi Adamu
(1988), ƙasar Hausa ita ce inda ba a buƙatar
naɗa Sarkin
Hausawa. Wato wannan bayani ya ware duk wasu zango-zango, inda ake magana da
Hausa. Amma idan ana maganar inda harshen ya yaɗu ne, ya zama
harshe na ɗaya ko na
biyu abakin mutane, to wuraren da aka ambata a nan ba su fi rabin ƙasar
Hausa ba.
Ƙasar
Hausa galibinta shimfiɗaɗɗiya ce, mai yawan sarari. Akwai ta da
tsaunuka da tuddai jifa-jifa, kuma duk yawan wannan ƙasa, manyan
koguna biyu ne suka ratsa cikinta, da kogin Rima da kogin Haɗejiya. Haka
kuma kogin Kwara ya zama kamar iyaka ne daga yammacin ƙasar.
Kogin Rima
shi ne ya taso daga ƙasar Zamfara, ya
gangara ya yi arewa zuwa Nijar, sa’annan ya karkata kudu, ya bi ta yamma da
Sakkwato, ya je ya faɗa cikin kogin Kwara. Shi kuma kogin Haɗejiya,
masominsa, a ƙasar Kano ne. Daga nan ne ya gangara gabas,
ya bi ta Gashuwa ta Gaidam, ya je ya faɗa ta tafkin Cadi.
3.3 KARIN HARSHEN
GABAS
Kamar yadda
muka faɗa a baya cewa
masana ilimin harshe sun kasa kare-karen harsuna zuwa gida biyu wato karin
harshen gabas da kuma karin harshen yamma. A nan za a yi tsokaci ne a kan karin
harshen gabacin ƙasar Hausa. Kare-karen harshen gabacin ƙasar
Hausa su ne Kananci da Zazzaganci da Dauranci da Bausanci da Haɗejanci da
Guddaranci, waɗannan
kare-karen harsuna mutanen gabashin ƙasar Hausa su
ne ke amfani da su wajen mu’amalarsu ta yau da kullum.
3.4 KARIN
HARSHEN YAMMA
Bugu da ƙari,
akwai kare-karen harsunan yamma. Kare- Karen harshe na yammacin ƙasar
Hausa su ne:
Sani (2001),
Sakkwatanci da Gobiranci da Zamfarci da Katsinanci da Aranci. Bugu da ƙari,
akwai Kurhwayanci da Kabanci da Adiranci. A taƙaice waɗannan
kare-karen harsuna su ne masana suka kasa zuwa gida biyu wato karin harshen
gabas da karin harshen yamma.
3.5 NAƊEWA
A wannan babi
na uku kamar yadda bayani ya gabata ya kawo muna ma’anar harshe da ra’ayoyin
masana daban-daban bayan nan an kawo kare-karen harshen Hausa, an kuma kalli
karin harshen gabas da kuma karin harshen yamma, sai kuma daga ƙarshe
an zo da naɗewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.