Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Zamfarci Da
Rabe-Rabensa (5)
NA
AHMAD MUHAMMAD KABIR
BABI NA HUƊU
ZAMFARA ƘASA
4.0 SHIMFIƊA
A babi na uku
an kawo muna ma’anar harshe da kare-karen harshen Hausa, sannan an yi magana
game da karin harshen gabas, haka kuma an yi magana game da karin harshen yamma
daga ƙarshe naɗewa.
A wannan babi
na huɗu, mai taken:
“Zamfara Ƙasa”, za a yi bayani a kan tarihin ƙasar
Zamfara, kuma za a yi magana game da karin harshen Zamfarci da rabe-rabensa.
Daga bisani za a kawo yadda suke a Daidaitacciyar Hausa. Bugu da ƙari
a kuma kawo kalmomin Zamfarci da kuma yadda suke da Daidaitacciyar Hausa, haka
zalika, daga ƙarshe naɗewa.
4.1 TARIHIN
ZAMFARA
Jihar Zamfara
na cikin jihohin Nijeriya masu amfani da harshen Hausa. Hausawa na cikin manyan
ƙabilu na ƙasar nan. A
sashe na tarihin (Dogo 1982:20:22) ya nuna daular Zamfara ta wanzu tun ƙarni
na goma sha biyar (15). Daular Zamfara ta mallaki faɗin ƙasa
wanda ya kama tun daga Kogin Rima a shiyar arewa zuwa Gulbin Zamfara ɓangaren kudu.
A ɓangaren gabas
kuma ta yi iyaka da dajin Rugu zuwa dutsin Disau a sashen yamma. Wannan
farfajiya ta Zamfara tana sashen yamma na ƙasar Hausa
kuma ta sami matsayi babba a jarumtaka kamar yadda sauran dauloli na wannan
lokaci suka samu waɗanda suka haɗa da Katsina
da Daura da Kano da Kebbi. Augi (Barkindo (ed) 1982:188) ya tabbatar da akwai
mutane a ƙasar Zamfara tun a ƙarni na (15).
Ƙasar Zamfara tana da muhimman garuruwa waɗanda suka haɗa da Dutsi da
Birnin Zamfara da Kiyawa da Tumfafi da sauransu.
Baya ga waɗannan
garuruwa akwai kuma tungaye da ƙauyuka da
unguwanni da suka yi tasiri a daular Zamfara.
Garin Dutsi
yana daga cikin wurare na farko da aka fara kafa daular Zamfara. Daga nan
saboda daɗa ɗaukar matakan
tsaro da samun dausayi da samun wurin noma ingantacce sai aka taso da mazaunin
sarauta da mulki daga Dutsi zuwa Birnin Zamfara.
A daular
Zamfara, sarkin Zamfara shi ne ja-gaba wanda yake da wuƙa da nama a
wajen zartar da harkokin al’ummar Zamfara. Shi yake da iko mai cin gashin kansa
a Zamfara yakan naɗa wasu mutane waɗanda suke
taimaka masa a sha’anin mulki da ake kira masu sarauta. Daga cikin masu sarauta
akwai Sarakunan karaga kamar haka.
Danau Sarkin Bazai
Magajin gari Sarkin Tudu
Uban dawaki Sarkin Ƙaya
Galadima Galadima
Baya ga
sarakunan karaga, Sarkin Zamfara yana da fadawa da baraden yaƙi
da ‘yan sulke da zagagai da sauransu. Bayan zuwan addinin musulunci kuma ƙasar
Zamfara ta samu malamai da limamai da alƙalai. Ga kuma
jami’ai mata masu sarauta. Harwayau akwai wasu muƙaman sarauta
da suka haɗa da Galadima
da Marafa da Sardauna da Bunu da Yarima da sauransu, kuma duka waɗannan sarautu
‘ya’yan Sarki ne, bisa wasu sarautu ta ƙauyuka a
matsayin na iyayen ƙasa.
“Ƙasar
Zamfara tana da shuwagabanni na sana’o’i waɗanda ake
gudanarwa na yau da gobe. Daga cikinsu akwai ajiya da Sarkin Noma da Sarkin maƙera
da Sarkin Fawa da Sarkin Aska da sauransu. Sarki shi yake naɗa waɗannan masu
sarauta sannan suna da nasu ƙananan fadodi
waɗanda suke
gudanar da ayukkansu na mulki”. (Dogo 1982, 69 – 72).
“Tarihi ya
nuna Zamfarawa, mutane ne ƙarfafa, masu
yaji, jarummai kuma zarata manoma. Manyan dakaru ne a fagen yaƙi,
sukan iya tunkarar kowace runduna ta mayaƙa batare da
fargaba ba ko razana ba. Mayaƙa ne waɗanda suka faɗaɗa kai hari
zuwa ƙasashen Zabarma da Katsina da Kano da Yawuri
da Kebbi da kuma Adar. Ta haka Zamfarawa suka sha gwabzawa da wasu dauloli da
ke kusa da su kamar Katsinawa da Kabawa da sauranasu” (Augi, 1984:113 – 135).
Ta fuskar
addinin musulunci kuwa, tun a ƙarni na 17,
musulunci ya barbazu a cikin daular Zamfara. Sarkin Zamfara Aliyu ya gina
babban masallaci a birnin Zamfara tare da wasu garuruwa na cikin Zamfara.
Sarakunan
Zamfara
Nalado (1999)
ya ƙididdige sunayen sarakunan Zamfara hamsin da
huɗu (54) tun
daga Baƙuruƙuru (1300)
zuwa Ahmadu Barno (1946 – 1967). Daganan kundayen tarihi na Zamfara suka
bayyana bayan mutuwar Sarkin Zamfara Maroƙi ɗan Malo (1754
– 1764) an sami shekaru arba’in ba a yi sarkin Zamfara ba saboda warwatsuwar da
Zamfara suka yi zuwa wasu wurare da ƙoƙarin
da suke ta yi na sake haɗuwa waje ɗaya domin su
tsayar da mulki.
Domin haka, a
duk lokacin da wani rukuni na Zamfara ya sake haɗuwa ya kafa
wani gari sai su samar da nasu jerin Sarakuna. Ta haka ne yau ake da jerin
Sarakuna na Zamfara a Kuryar Madaro da Anka da Talata Mafara da Gummi da
sauransu.
Akwai Jerin
sunayen Sarakunan Zamfara waɗanda tarihi ya bayyana, inda wasu an
samu tabbacin shekarar da suka hau mulki har suka sauka, amma wasu daga cikinsu
ba a samu shekarar da suka hau ba har suka sauka.
Ga sunayen
kamar haka:
1.
Baƙuruƙuru 1300
2.
Baƙara
3.
Gimshiƙi
4.
‘Yargoje
5.
Karafau
6.
Gatama
7.
Kuɗanɗan
8.
Bardau
9.
Gwabrau
10. Taskarin
Burun
11. Durƙushi
12. Kigaya
tabarau
13. Daudu Fanau
14. Burun – Burun
1536
15. Fati – Fati
16. Taritu 1550
17. Zartai
18. Daka
19. Tasau
20. Zaudai
21. Aliyu
22. Hamitu
23. Abdu na
Bawanka 1660
24. Sulaimanu 1674
25. Muhammadu Na
Makake
26. Abdu
27. Usman
28. Baba 1715
29. Yakubu Ɗan
Babba
30. Jirau ɗan Babba
31. Faskare ɗan Yakubu
32. Babba 1734
33. Yakubu ɗan Faskare 1734 – 1739
34. Gigama ɗan Yakubu 1739 – 1741
35. Malo ɗan Yakubu 1741 –
1748
36. Gado ɗan Gigama 1748 –
1754
37. Maroƙi
ɗan Malo 1754 –
1764
38. (Gibi)
Shekaru 40 1804
– 1805
39. Ɗanbawa
ɗan Gado 1805 – 1815
40. Abarshi ɗan Maroƙi
1815
41. Fari ɗan Maroƙi
42. Ɗanbaƙo
ɗan Abarshi 1815 – 1824
43. Ɗangado
ɗan Abarshi 1824
44. Abdu Tukuɗu ɗan Fari 1825
45. Abdu Fari Ɗan
Abarshi 1825
– 1829
46. Abubakar
Bawan Adam 1829
– 1853
47. Ɗan
Ɗanbaƙo
48. Muhammad Ɗan
Gigala 1853 –
1877
49. Hassan Ɗan
Muhammad Ɗan Cigama 1877
– 1896
50. Muhammadu
Farin Gani ɗan Abubakar 1896
– 1899
51. Gado ɗan Muhammad Ɗan
Gigala 1899 – 1904
52. Abubakar
Caccaɓi Ɗan
Muhammad Dan Gigala 1904 -1916
53. Muhammadu
Katar Ɗan Hassan 1916
– 1928
54. Muhammadu
Fari Ɗan Abubakar 1928
– 1946
55. Ahmad Barmo ɗan Muhammad
Katar 1946 – 1957
56. Muhammad Lawal
1957 – 1993
57. Attahiru
Muhammad Ahmad 1993
Kirƙiro
Jahar Zamfara
Ranar Alhamis
1 ga watan Oktoba, 1996 aka tabbatar da an yi jihar Zamfara tare da wasu jihohi
sababbi guda biyar waɗanda suka haɗa har da
Jihar Gombe a lokacin mulkin shugaban ƙasa Janar
Sani Abacha, Gwamnatin tarayya ta ayyana garin Gusau ya zama babban birnin
Jihar Zamfara. Sannan kuma an yi wa Zamfara ƙananan
hukumomi goma sha huɗu (14) da suka ƙunshi ƙaramar
hukumar Anka da Bakura da Bunguɗu da Birnin Magaji da Bukkuyum da Gummi
da Gusau da Ƙaura Namoda da Maradun da Maru da Tsafe da
Shinkafi da Talatar Mafara da Kuma Zurmi.
Farfajiyar
jihar Zamfara sabuwa an tsago ta ne daga tsohuwar jihar Sakkwato daga arewa.
Daga gabas kuma ta yi iyaka da jihar Katsina, sannan ta yi iyaka da jihar
Kaduna. Akwai manyan gulabe waɗanda suka ratsa ta cikin jihar Zamfara
da suka haɗa da gulbin
Bunsuru da gulbin Gagare da kuma gulbin Zamfara. Akwai kuma ƙoramu
manya waɗanda suke
tare ruwa ba tare da saurin ƙafewa ba
kamar Kakale a garin Ɗangulbi da Natu a
Bakura da Saru a Gummi.
Gwamnatin
tarayya ta Janar Sani Abacha ta naɗa kanal Jibril Bala Yakubu a matsayin
Kantoma na Jihar Zamfara kuma ya yi mulki daga 1996 zuwa 28/5/1999.
4.2 KARIN HARSHEN
ZAMFARCI
Zamfarci
karin harshe ne da mabambanta al’ummar da suke zaune a farfajiyar ƙasar
Zamfara ko gundumar daular masarautar Zamfara suke amfani da shi a matsayin
harshensu na sadarwa. Daular masarautar Zamfara tana ɗaya daga
cikin manyan dauloli masarautun ƙasar Hausa.
Karin harshen Zamfarci yana da wasu fitattun kalmomi da ake haɗawa a yi
furuci sai su bada ma’ana. Akwai karin harshen Zamfarci wanda ya shafi yanayi
sannan kuma akwai wanda ya shafi lafazi.
To a nan
wannan bincike ya ƙudurci yin magana
game da Zamfarci da rabe-rabensa ta hanyar da Zamfarawa suke amfani da shi
domin isar da saƙo. Bugu da ƙari, da wasu
kalmomi da Zamfarawa suke amfani da su a cikin maganganunsu na yau da kullum waɗanda
zamfarawa ne suke amfani da su.
Masana sun
karkasa Hausa wadda ake amfani da ita a arewacin Nijeriya zuwa manyan sassa guda
biyu, wato Hausar gabas da kuma Hausar yamma. Bargery (1934), Zarruƙ,
(1978) da sauransu. Hausar yamma ta ƙunshi shiyoyi
kamar su Sakkwatanci da Katsinanci da Adaranci da Kurfayanci da sauransu, yayin
da Hausar gabas ta ƙunshi shiyoyi kamar
su Kananci da Zazzaganci da Dauranci da Bausanci da Haɗejanci da
sauransu. Karin harshen Sakkwatanci kari ne da ake amfani da shi a jihohin
Sakkwato da Zamfara da Kebbi. Hausar Zamfara duk da kasancewarta Sakkwatanci
tana da bambance- bambance da Hausar Sakkwato da kuma ta Kebbi, ‘yan bambance-
bambance da ke akwai su suka haifar da samuwar karin harshen Zamfarci. Wato
ma’ana Hausar Zamfara wani ƙaramin kaso
ne daga cikin Hausar Sakkwatanci. Karin harshe na Zamfarci ana amfani da shi ne
a jihar Zamfara wacce take a gabas ko gabas maso kudu da Sakkwato. Zamfara wata
tsohuwar daula ce da aka ce tana cikin daulolin Hausa da ake kira Banza bakwai.
4.3 RABE-
RABEN KARIN HARSHEN ZAMFARCI
Zamfarci
karin harshe ne da mabambantan al’ummar da suke zaune a farfajiyar ƙasar
Zamfara ko gudumawar daular masarautar Zamfara suke amfani da shi a matsayin
harshensu na sadarwa.
Wannan
al’umma ta Zamfara ta kasu zuwa rukuni – rukuni, wanda kuma kowane rukuni yana
da suna ko take na musamman, kuma duk wanda ya fito ɗaya daga
cikin waɗannan rukunin
za a iya yi masa laƙabi da sunan wannan
yankin, daga cikin rabe-raben Zamfarci akwai:
1. Albawa
2. Ma’alleɗawa
3. Garewa
4. Ɓurmawa
5. Zamfarawa
6. Gobirawa
7. Fulani
Bugu da ƙari
wannan rabe-rabe Zamananci ya yi tasiri gare shi, muna iya kallon sa ta hanyar ƙananan
hukumomin da jihar Zamfara take da su yanzu muna iya duba manyan yankunan Jihar
Zamfara guda uku kamar haka:
1. Zamfara ta
Arewa: Alibawa
·
Ƙaura Namoda
·
Birnin Magaji
Gobirawa
·
Shinkafi
2. Zamfara ta
Yamma: Mu’alleɗawa
·
Maradun
Ɓurmawa
·
Bakura
Zamfarawa
·
Talatar Mafara
·
Gummi
·
Anka
·
Bukkuyum
·
Zurmi – wadda ta fito daga Zamfara ta Arewa
3. Zamfara ta
Tsakiya: Garewa
·
Tsafe
·
Maru ta Kudu
Fulani
·
Bungudu
·
Gusau
4. Maru ta Yamma
Wannan shi ne
ɗan taƙaitaccen
bayani game da rabe-raben karin harshen Zamfarci ta fuskar ambaton yankunan
masarautu da taken karin harshensu.
4.4
DAIDAITACCIYAR HAUSA
Kasancewar
ana samar da ire-iren sunaye da ake raɗawa harsuna da kuma
bambancin karorin harshe da ake samu a harshe guda ya sa ake tacewa don a samu
daidaito yadda kowa zai fahimta.
Idan aka duba
kusan kowane harshe mai cin gashin kansa, ana samun karɓaɓɓe da kuma
wanda ba ƙarɓaɓɓe ba. Amma ga
mai nazarin harshe, bai kamata ya ɗauka cewa akwai karɓaɓɓe da wanda ba
karɓaɓɓe ba, sai dai
kawai an samar da karɓaɓɓe ne domin samun sauƙin
fahimtar juna, shi ya sa ake samun karɓaɓɓen harshe.
Daidaitacciyar
Hausa samfuri ne na salon maganar da dukkan Hausawa suka yi tarayya a kansa.
Wannan samfuri kuwa, ƙari ne da aka zaɓa aka
daidaita masa ƙa’idojin rubutu da na nahawu, kuma aka adana
su cikin littafai da ƙamusoshi.
A nan
daidaita ƙa’idoji yana nufin tanadin hanyoyi na yadda
za a sarrafa harshe. Saboda haka, ma’anar daidaita ƙa’idojin
rubutu ita ce tanadin haruffa da za a rubuta harshe da su da sharaɗin haruffan
da za a rubuta harshe da su da sharuɗɗan harhaɗa su wajen
gina kalmomi da jumloli. Daidaita ƙa’idojin
nahawu kuwa, yana nufin tanadi a siffofin harshe da rukunnansa ta yadda za a
iya bayyana ma’anoni kowace iri da su, walau sababbi ne ko tsofaffi, na fasaha
ne ko na kimiya, da sauransu. Kuma daidaita ƙa’idojin
nahawu ya na nufin hallarar dukkan rukunnan nahawun da ke cikin sauran
kare-kare, ya kamata a same su a karin da aka daidaita. Misali, muddin akwai
karin harshen Hausa, inda ake bambanta kalmomi maza da mata, to Daidaitacciyar
Hausa ma ya kamata ta sami rukunin jinsi a nahawunta. Haka nan idan akwai karin
da ke da lokatai takwas, to Daidaitacciyar Hausa ma kada ta gaza hakan da dai
sauransu.
Bayan haka
duk mai magana da Hausa, ko daga wane kari yake kuwa, bai kamata wani abu ya
gagare shi ba cikin Daidaitacciyar Hausa, shi zai sa a ji daɗin karɓar ta a
ko’ina. Kuma wannan shi zai sauƙaƙa
koyar da harshen ga masu wasu harsuna daban. Saboda haka, sauƙaƙa
nahawu ma wani aji ne na daidaita harshe. Kuma ya kamata Daidaitacciyar Hausa
ta yi sauƙin kai, shi zai taimake ta tafiya tare da
zamani, wajen bayyana abubuwan da za su yi ta ɓullowa a
fagen kimiyya ko fasaha ko wanin waɗannan.
4.5 KALMOMIN
ZAMFARCI DA DAIDAITACCIYAR HAUSA
Karin harshe
wasu ‘yan bambance-bambance ne da ake samu tsakanin masu magana da harshe guda.
Karin harshen Zamfarci nau’in karin harshe ne wanda al’ummar da ke zaune a
farfajiyar ƙasar Zamfara suke amfani da shi. Ana samun
‘yan bambance- bambance tsakaninsa da Daidaitaciyar Hausa wadda sauran
kare-kare suka yi tarayya gare ta, abin ban sha’awa bambance- bambancen sukan samu
ta hanyoyi da dama daga cikinsu akwai:
a.
Jimloli
b.
Kalmomi
Gundarin
Kalmomi
“Kalma ita ce
ƙwayar lafazi ko furuci mai cikakkiyar ma’ana,
ko samun harhaduwar gaɓoɓin kalma wuri guda domin su ba da
kalma mai ma’ana (Mukhtar 2010)”. Wannan
wani fanni ne a karin harshe, inda ake samun kalmomi mabambanta furuci kuma
mabambanta rubutu, amma ma’ana ɗaya.
Wannan yana
samuwa a kowane karin harshe, to a nan karin harshen Zamfarci ya bambanta da
Daidaitacciyar Hausa har ta fuskar kalmomi kamar haka:
S/N |
Zamfarci |
Daidaitacciyar
Hausa |
1.
|
Tagguwa |
Riga |
2.
|
Jakki |
Jaki |
3.
|
Ƙoƙewa
|
Koɗewa |
4.
|
Ayya |
Kayya |
5.
|
Ɓota
|
Ƙota
|
6.
|
Kire |
Kira |
7.
|
Bagire |
Wur |
8.
|
Kore |
Kora |
9.
|
Bisnewa |
Rufewa |
10. |
Lumui |
Ƙalau |
11. |
Fantamawa |
Warwatsuwa |
12. |
Husuma |
Rigima |
13. |
Kara-kaina |
Kaiwa-da-komawa |
14. |
Sargafewa |
Ratayewa |
15. |
Suɓulewa |
Kuɓucewa |
16. |
Habɓasa/ wuɓɓasa |
Ƙoƙari
|
17. |
Yanda |
Yadda |
18. |
Haɓaka |
Ci-gaba |
19. |
Danga |
Darni |
20. |
Kumallo |
Amai |
21. |
Wargi |
Wasa |
22. |
Yauɗi/ guro |
Kuɓewa |
23. |
Kwana |
Bacci |
24. |
Yuƙa |
Wuƙa |
25. |
Masai |
Shadda |
26. |
Samrayi |
Saurayi |
27. |
Arme |
Aure |
28. |
Annoba |
Alloba |
29. |
Attanin |
Litanin |
30. |
Anguwa |
Unguwa |
31. |
Bahwade |
Bafade |
32. |
Burgu |
Gafiya |
33. |
Shigihwa |
Ɗaki
|
34. |
Biɗa |
Nema |
35. |
Ragaita |
Shiririta |
36. |
Alkwato |
Dodonkoɗi |
37. |
Anka |
Aka |
38. |
Ɗumi
|
Surutu |
39. |
Basilla /
masilla |
Allura |
40. |
Ciyo |
Ciwo |
41. |
Swaɓani |
Saɓani |
42. |
Shibka |
Shuka |
43. |
Mussai |
Mushe |
44. |
Ukku |
Uku |
45. |
Shidda |
Shida |
46. |
Agalemi |
Buzu |
47. |
Ƙabari |
Kushewa |
48. |
Halshe |
Harshe |
49. |
Canka |
Zaɓi |
50. |
Tiya |
Mudu |
51. |
Guntu |
Gajere |
52. |
Illi |
Mutunci |
53. |
Daffo |
Yawa |
54. |
Huriyarsu |
‘Yanci |
b. Jimloli
“Jimla ita
ce, harhaɗuwar kalmomi
daban-daban cikin ƙira karɓaɓiya domin
samar da zance ingantacce wanda za a iya rubutawa kamar yadda dokar harshe ta
tanada”. (Zaria 1981 – da Mukhtar da wasu 2004). A wannan fanni, ana samun
jimloli su bambanta wajen ƙira da
furuci, amma suna ɗauke da ma’ana guda, kamar haka:
S/N |
Zamfarci |
Daidaitacciyar
Hausa |
1.
|
A gaida waɗan gidan |
A gaida
mutanen gidan |
2.
|
Tahiya za
mui gobe |
Gobe za mu
yi tafiya |
3.
|
Audu ya
kire ni |
Audu ya
kira ni |
4.
|
Mun tashi
lahiya lumui |
Mun tashi
lafiya ƙalau |
5.
|
Ɓarayi
sun kore masu shanu |
Ɓarayi
sun kora masu shanu |
6.
|
Bari in yi ƙurari
|
Bari in yi
fitsari |
7.
|
Amina ta
murmuje daga ciyon da ka damunta |
Amina ta ji
sauƙi daga ciwon da ke damunta |
8.
|
Yanzu Audu
yat tahi gida |
Audu ya
tafi gida yanzu |
9.
|
Yaron ya
tcere da kuɗɗin |
Yaron ya
tsere da kuɗin |
10. |
Baba ya
tahi gona |
Baba ya
tafi gona |
11. |
Tanko ya
hwaɗi jarrabawa
|
Tanko ya faɗi jarabawa |
12. |
Ka tahi yak
ka |
Ka tafi
abin ka |
13. |
Audu mika
ka yi nan? |
Audu me ka
ke yi nan? |
14. |
Shi yas sa
ban son yadin ga |
Shi ya sa
ba na son wannan yadi |
15. |
Wanga
littahin nawa ne |
Wannan
littafin nawa ne |
16. |
Mu tahi
gida |
Mu tafi
gida |
17. |
Ki anso min
lambasshi |
Ki amso min
lambarsa |
18. |
Zo gaya nan
|
Zo gashi
nan |
19. |
Mu ukku ka
zuwa |
Mu uku ke
zuwa |
20. |
Tanko ya
sheƙa da gudu |
Tanko ya
ruga da gudu |
21. |
Lado ya ƙetara
Katanga |
Lado ya tsallake
gina |
22. |
Buda ya ce
wagga tagguwasshi ce |
Buda ya ce
wannan rigarsa ce |
23. |
Zan ci ma
illi |
Ina ci ma
mutunci |
4.6 NAƊEWA
Wannan babi
na huɗu, mai taken
“Zamfara ƙasa” tun farko ya fara da shimfiɗa sannan kuma
ya kawo muna tarihin Zamfara, kuma ya zo da rabe-raben karin harshen Zamfarci,
daɗin daɗawa ya yi
bayanin Daidiatacciyar Hausa. Bugu da ƙari, ya yi
bayanin kalmomin Zamfaraci da Daidaitacciyar Hausa inda bincike ya dube su ta
fuska biyu, na farko ta fuskar kalmomi, na biyu kuma an dube su ta fuskar
jimloli daga ƙarshe ya zo da naɗewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.