Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Zamfarci Da
Rabe-Rabensa (6)
NA
AHMAD MUHAMMAD KABIR
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 SHIMFIƊA
Da sunan
Allah mai rahama mai jinƙai. Dukkan
yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai ubangijin duKkan
halittu, wanda yakasance tun kafin kasancewa ta kasance.
Salati da ɗaukaka su ƙara
tabbata a kan shugabanmu Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da sahabbansa da
masu bin su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
A cikin
wannan babi na ƙarshe, wato babi na biyar za a gabatar da
jawabin taƙaitawa sannan kuma ya zo muna da shawarwari
zuwa ga ‘yan’uwa ɗalibai da
masu nazarin irin wannan aiki nan gaba. Haka zalika za a yi ta’arifin wasu
kalmomi da aka yi amfani da su a cikin wannan aiki daga ƙarshe sai naɗewa.
5.1 TAƘAITAWA
Kamar dai
yadda mai karatu ya gani a shimfiɗa cewa akwai abubuwa da dama da aka
ambata a cikin wannan bincike, hakan baya nuna cewa an ambaci dukan abin da ya
shafi karin harshen Zamfarci da kuma rabe-raben karin harshen Zamfarci ba, a a
an dai ambaci wasu ‘yan abubuwa muhimmai waɗanda ake
ganin ya kamata a ambace su.
Da farko a
cikin babi na ɗaya an gabatarwa
mai karatu ko mai nazari dalilan da suka sanya a gudanar da wannan aiki, haɗi da muhallin
da aka yi wannan binciken tare da hanyoyin da aka bi domin gudanar da binciken.
Bugu da ƙari an yi bayanin muhimmancin bincike da kuma
matsalolin da aka fuskanta ya yin gudanar da wannan aiki.
A babi na
biyu an yi bayanin ayukkan da aka duba waɗanda suka yi alaƙa
da wannan bincike, an yi bitar wasu daga cikin rubutattun littafai, muƙalu
da kuma kundayen bincike, haɗi da gudummuwar aiki ga ilimi. Daɗin daɗawa an yi
bayanin yadda tsarin gabatar da aikin ya kasance. Daga ƙarshe sai naɗewa.
Harwayau a
cikin babi na uku binciken ya kawo ma’anar harshe, da kuma kare-karen harshen
Hausa, wani abin burgewa an yi bayanin karin harshen gabas da kuma karin harshen
yamma sai kuma naɗewa.
Ba a nan
kawai aka tsaya ba a cikin babi na huɗu an kawo tarihin
Zamfara, inda a ciki har da taswirar ƙasar Zamfara
aka gabatar, sannan kuma karin harshen Zamfarci ya biyo baya da kuma
rabe-rabensa, sannan aka yi bayanin Daidaitacciyar Hausa. Haka zalika aka
gabatar da kalmomin Zamfarci da kuma na Daidaitacciyar Hausa daga ƙarshe
aka naɗe.
5.2
SHAWARWARI
Kasancewar
duk wani aiki da mutum ya gabatar ko ya gudanar akwai buƙatar shawara
daga gare shi domin cin gajiyar wannan shawarwarin ga al’umma. Saboda haka, ina
ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da
wannan kundin kuma in har binciken nasa yana da alaƙa da wannan,
da su yi ƙoƙarin ɗorawa daga
inda wannan bincike ya tsaya, kar su ce su kwashe kaɗai, wannan
baya taimakawa nazari. Kamar yadda aka zaƙulo wannan
taken na “Zamfarci da rabe-rabensa aka yi ƙoƙari
har aka tattaro bayanan da suka gina wannan kundin, ya zama abin karatu ko
nazari ga ‘yan uwa ɗalibai, to lallai su ma ya zama wajibi su
dage don su samar da wani abu mai amfani, ga al’umma ba wai su kwashe abin da
suka wani ya yi ba.
5.3 TA’ARIFIN
WASU KALMOMI
1. Alaye –
Iyalan gidan Annabi
2. Bagire – Wuri
3. Bincike –
Nazari
4. Bisnewa –
Rufewa
5. Fantamawa –
Warwatsuwa
6. Galaba – Nasara
7. Gudana –
Faruwa
8. Haɓaka – Ci-gaba
9. Habɓasa /Wuɓɓasa – Ƙoƙari
10. Husuma –
Rigima
11. Tagguwa –
Riga
12. Kire – Kira
13. Huriyarsu –
‘Yanci
14. Karakaina –
Kaiwa-da – Kamowa
15. Sargafewa –
Ratayewa
16. Suɓulewa – Kuɓucewa
17. Surmuƙewa
– Yamutsawa
18. Warwatsuwa –
Rarrabuwa
19. Zaƙulowa
– Samowa / Fitowa
20. Waɗan – Mutane
21. Canka – Zaɓi
22. Mussai –
Musshe/ Marar rai
23. Surutu –
Magana/ Batu
5.4 NAƊEWA
Wannan babi
na biyar kuma babi na ƙarshe ya fara da
gabatarwa da shimfiɗa, bayan nan ya yi bayanin kundin gaba ɗaya, amma a
taƙaice sannan ya kawo shawarwari kuma ya yi
ta’arifin wasu kalmomin da aka yi amfani da su a cikin kundin baki ɗaya, daga ƙarshe
ya zo da naɗewa.
MANAZARTA
Tuntuɓi masu gudanarwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.