Ticker

Aminu ALAn Waka a Fagen Rubutattun Kagaggun Labarai na Hausa

Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa), marubuci ne kuma mawaƙin Hausa na zamani ne wanda ya shahara sosai a fagen waƙoƙin fiyano. Sai dai kafin shaharar tasa a fagen waƙoƙi ya kasance marubucin littattafan labarin Hausa na Adabin Kasuwar Kano. Amma duk da irin wannan gudummawa da ya bayar a fagen rubutaccen labari, manazarta ba su mayar da hankali wajen nazartar littattafansa na labari kamar waƙoƙinsa ba. Shi ya sa wannan maƙala ta ɗinke wannan giɓi, ta nazarci gudummawar Aminu Alan Waƙa a fagen rubutaccen labarin Hausa. An tattauna matsayinsa na marubucin labari kafin mawaƙin zamani, sai kuma sharhin littattafansa da saƙonnin da suka ƙunsa. An yi nazarin ayyukansa da Tarihin rayuwarsa, an gano cewa saƙonnin da suke ɗamfare da littattafan da ya rubuta suna da kamanci da irin saƙonnin da yake tsarmawa a waƙoƙinsa na faɗakarwa da hannunka-mai-sanda da bayyana halin da ƙasa ke ciki da makamantansu. Sa’annan littattafansa suna ƙunshe da saƙonni na gyaran halaye da ɗabi’u kyawawa da kuma riƙo da addini bisa tafarki nagari.

Aminu Alan Waƙa a Fagen Rubutattun Ƙagaggun Labarai na Hausa

Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Na

Abdullahi Mujaheed

Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Jami’ar Jihar Kaduna

mujaheedabdullahi@gmail.com

+2348069299109, +2348156747550

1.0 Gabatarwa

Bahaushe kan ce a san mutum a kan cinikinsa. Da zarar an ce Aminu Ladan Abubakar (ALA), abin da galibi jama’a suka sani ALA ɗaya ne daga cikin mawaƙan zamani da suka shahara a wannan ƙarnin. Shi ya sa ma laƙabinsa Alan Waƙa. Nazarce-nazarce da dama (Dikko, 2010; Giɗaɗo, 2012; Rogo, 2013; Shehu, 2011; Yakasai, 2012 da sauransu) duk sun taɓo mabambantan batutuwa game da adabin ALA ta fuskar waƙa, sai dai ayyukansa na rubutaccen labari ba su sami tagomashi ta fuskar nazari da sharhi ba; ba su ma sanu sosai kamar waƙoƙinsa ba. Duk da cewa aikin Shehu, (2011), ya zayyano ayyukan ALA da suka shafi waƙa da wasan kwaikwayo da rubutaccen labari, sai dai bai yi sharhi ko nazarin ƙumshiyar littattafan nasa ba. Da yake Bahaushe kan ce sanin asali shi ke sa kare cin alli, wannan maƙala ta lalubo cewa ALA ya fara noma rubutaccen labari ne a gonar adabin Hausa, wato ya fara baje-kolin fasaharsa ne a fagen rubutaccen labarin Hausa na zamani, kafin ya sauya akala zuwa waƙa. Sai dai a fagen waƙar ne aka fi sanin sa, domin a nan ne ya shahara. Shi da kansa ya faɗa a waƙarsa cewa, shahararsa a rubutaccen labari ba ta kai ta waƙoƙi ba, shi ya sa ma ba a ji ɗuriyarsa ba a fagen rubutaccen labarin Hausa, ballantana rubuce-rubucen nasa:

Na tuno farkon ɗagawa,

Da ina ɗan ƙanƙanina.

 

Nai firamare garinmu,

Da sakandire sanina.

 

Na zamo alkatibin nan,

Marubucin so da ƙauna.

 

Ba domin ban iya ba,

Shahara ta hana sanina,

 

Babu wanda ya san da ALA,

To bare aikin wurina.

              (ALA: Waƙar Shahara ta 1)

 

Saboda haka, duk da cewa ALA bai shahara a fagen rubutaccen labarin Hausa ba, ba za a rasa abin tsinta ba ta fuskar nazari cikin littattafan da ya rubuta. Shi ya sa wannan maƙalar ta lalubo wasu daga cikin littattafan nasa ta nazarce su, musamman ƙunshiyar saƙonninsu.

 2.0 Marubuci Kafin Mawaƙi

Nazarce-nazarce da dama (Dikko, 2010; Giɗaɗo, 2012; Rogo, 2013; Yakasai, 2012 da sauransu) duk sun yi rubdugu kan tarihin rayuwar ALA da ayyukansa na waƙa. Saboda haka abin da za mu yi a nan ba batun haihuwarsa da ilimi da gwagwagwarmayar rayuwarsa ba ne, illa ƙyallaro abin da ya shafi kasancewarsa marubucin labarin Hausa kafin zama mawaƙi.

Batutuwan da suka shafi ilimi da tattalin arziƙi sun yi katutu a ƙasar Hausa a farkon shekarun 1980[1].Waɗannan batutuwa sun yi tasiri wajen samuwa da bunƙasar rubutaccen labarin Hausa na zamani, fasalin da ya haifar da Adabin Kasuwar Kano (AKK). ALA ya faɗo cikin rukunin marubuta irin wannan nau’in adabi na AKK. Kuma kamar yadda ya bayyana a wasu waƙoƙinsa, ALA ya yi karatun addini da na zamani, kuma ya sha fafutikar neman abin yi domin riƙe kansa da iyalansa amma abin ya faskara. Saboda haka sai ya jefa kansa cikin harkar rubuce-rubuce[2] daga bisani kuma ya koma waƙa. Domin jaddada wannan batu, ga abin da ALA ya ce:

Ba kurum nake wai na ƙi sanna’a ba,

Har karatun Arabic fa ban ƙi nai ba,

Har karatun boko fa ban ƙi nai ba,

Nashinal difiloma na yi duba.

 

Da takardu na zaga ofisoshi,

Bambaɗanci na yi shi har na ƙoshi,

Kamfanoni na bi su ofisoshi,

Babu aiki ba hanyarsa garan ba.

 

Ga iyalai ga matata da yara,

Babu natsuwa in koma in taƙara,

Cigaban boko ba tsimi dabara,

Mafakata ubangijinmu Rabba.

 

Babu aiki na dogaro na kaina,

A rubutu na fara jefa kaina,

Yau a waƙa kuma na tsinci kaina,

Faɗakarwa ba watsa tarbiya ba.

          (Aminu ALA: Waƙar Kurkuku)

Hada-hadar bugawa da sayarwa na littattafan ALA, duk sun kasance a kasuwa ne kamar duk wani adabin kasuwa. A cikin waƙoƙinsa, ALA ya jaddada rubuce-rubucensa suna cikin rukunin Adabin Kasuwar Kano (AKK) ne. Misali a waƙar Shahara ta 1, ya ce:

Da ina alkatibi na,

Marubucin so da ƙauna[3].

 

In na wallafa ɗab’ina,

Sai in sanya wayar kirana.

 

A jikin bangon kitabu,

Manufata ai kira na.

 

In da mai gyara ya ba ni,

Ko ko sukar ƙallamina.

 

In da mai ƙarin bayani,

Ko gani na ko yabo na.

 

Ko ko aiki ne a ba ni,

Ga wayar tarhon gidana.

        (ALA: Waƙar Shahara ta 2)

 

Abin ban sha’awa shi ne, marubucin yana maraba da suka ko gyara in an ga kura-kurai cikin rubutunsa, shi ya sa ma yake sanya lambar wayarsa. Sai dai ALA bai jima a harkar rubutaccen labari ba, ya watsar ya koma waƙoƙin fiyano, inda a nan ya fi shahara, a nan aka san shi, kuma a nan ya huda ya ga jini har ya samu gindin zama. Amma duk da haka, ai tushiya mafarin dawa; ALA marubuci ne kafin ya juya akalar fasaharsa zuwa waƙoƙin zamani a shekarar 2003, kamar yadda ya sha faɗin haka da bakinsa.

A hirar da aka yi da shi a Sashen Harsuna da Al’adun Afirka na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ranar 31/07/2018, ALA ya bayyana:

‘Na fara rubutu a shekarar 1992, amma ya fara bayyana a hannun mutane a shekarar 1999. Na fara rubuta littafi mai suna Jirgi Ɗaya Shi Ke Ɗauke Da Mu. Littafina na ƙarshe wanda hukumar A Daidaita Sahu ta yi ɗab’insa shi ne Ceto Ko Cuta? Na yi littattafai aƙalla guda tara, waɗanda ake kira Adabin Kasuwar Kano in ji wani Farfesa, masu karantawa kuma suka ce littattafan soyayya. Ni dai na ɗauke su a matsayin littattafan faɗakarwa.’ ALA.

Ke nan, ALA ya kasance marubucin labarin Hausa tun daga 1992 ko1999. Sai kuma ya zama mawaƙi daga shekarar 2003 zuwa yau, duk da ya cigaba da rubutun labari har 2005. Bugu da ƙari, har yanzu yana amsa sunansa a matsayin marubuci, kuma yana tutiya da kasancewarsa marubucin. Alal, misali, a waƙar Kyauta, ALA ya jaddada shi fa komai-da-ruwansa ne a harkar waƙa da rubutu da nazari:

   Idan aka ce ALA mawaƙi ni ne,

  In aka ce alkatibi ma ni ne,

  In manazarci anka ce muku ni ne,

  Fulani ki san wannan fa farilla ne.

                       (ALA: Waƙar Kyauta).

3.0 Rubutu a Tunanin ALA

Mallakar iya rubutu kowane iri ne, kafa ce ta mayar da tunani ko harshe a cikin takarda. Shi ya sa labarin da kowace al’umma ke badawa bayani ne game da rayuwa da yadda ta gudana ko take gudana ko za ta iya gudana, sa’annan yana tafe ne bisa matakai biyu na rayuwar, ko dai a shirya shi a ƙwaƙwalwa a wanzar da shi ta baki ko kuma a rubuta shi daidai da zamanin da ya samar da shi, (Malumfashi, 2018: Sh. 1-2). Aminu ALA ya bayyana cewa tsintar baiwar rubutu ya yi a tare da shi kawai, don haka ya zama wajibi ya yi rubutu. Sai kuma ya kawo wasu ƙananan dalilai da suka zama musabbabin yin rubutun gare shi, inda ya bayyana cewa fitar da abin da ke cikin zuciya da faɗakarwa da tallar harshe da kuma neman kuɗi su ne suka jefa shi cikin harkar rubutun zube, musammam na labarin Hausa, (Gidan Dabino, 2018)[4]. Abin lura a nan shi ne, ALA bai ɓoye batutuwan da suka shafi neman kuɗi a matsayin dalilinsa na shiga harkar rubutu ba, sai dai abin da ke da muhimmanci shi ne ya sanya tallata harshe da kuma faɗakarwa a gaba, shi ya sa ma ya ɗauka cewa tun da fa Allah (SWT) ya hore masa baiwar rubutun, to fa rubutun ya zama ‘wajibi’ a gare shi, ko ba komai ya sami kafa ta furzar da abin da ke cikin zuciyarsa. Bugu da ƙari, fasihin ya sake jaddada wannan batu a cikin waƙarsa ta Shahara, inda ya ce:

Yin rubutu gare ni,

Wajibi ne a wajena.

 

Ba batun samun muƙami,

Ko kuɗi daula sanina.

     (ALA: Waƙar Shahara ta 1)

 

Duk da a wannan misali da aka tsakuro daga waƙarsa, yana da’awar wajibi ne ya yi rubutu don ya isar da saƙon faɗakarwarsa ga al’umma, amma dai amfanin zunubi romo. Shi ma ALA kamar kowane ɗan’Adam yana buƙatar abin masarufi. Don haka ne ya bayyana cewa shi da sauran marubuta ‘yan’uwansa suna buƙatar goyon bayan hukuma da mazhabobin ilimi, (Gidan Dabino, 2018). Hakan shi zai sa a martaba ayyukansu har su sami karɓuwa cikin al’umma, karɓuwar nan kuwa ita za ta kai shi ga samun muƙami da kuɗi har ma da daular.

 

4.0 Rubutaccen Labarin ALA

 

ALA ya rubuta littattafai na ƙagaggen labarin Hausa guda takwas (8). Littattafan su ne Cin Zarafi 1da 2 da Jirgi Ɗaya waɗanda suka fito a shekarar 2001. Sai a shekarar 2002 ya fitar da Baƙar Aniya 1 da 2, sai Tarzoma a shekarar 2003 . Sai kuma Sawaba da Cin Fuska na 1 da 2 da kuma Jirwaye, duk a shekarar 2005. Sai kuma littafin Ceto Ko Cuta[5]. Duk littattafan da suka zo hannu sun dace da siffofi na Adabin Kasuwar Kano (AKK), domin kuwa littattafai ne na yayi, kuma har ma sun yi yayinsu sun ƙare. Sa’annan ba su da yawan shafuka, alal misali, littafin Sawaba yana da shafuka 64, yayin da Tarzoma ke ƙunshe da shafuka 48,  shi kuwa labarin Baƙar Aniya 1 an tsara shi ne cikin shafuka  40, sai Jirwaye…  mai shafuka 56, Cin Fuska kuwa, shafukansa 53 ne, da sauransu.

 

BAƘAR ANIYA 1 labari ne a kan rayuwar masoya biyu Hauwa da Auwalu, waɗanda suna gab da aure Auwalu ya yi haɗari a hanyarsa ta dawowa Kano daga Jigawa. Haɗarin ya yi sanadiyyar samun ciwo a ƙwaƙwalwarsa, wanda sai da aka fitar da shi ƙasar Indiya ya yi wata 6, bayan jinya ta tsawon wata 4 a Nijeriya. Gab da za a fitar da shi kuma sai ciki ya bayyana a jikin Hauwa’u duk da ba a ɗaura masu aure ba. Lamarin da mahaifinta ya danganta da Auwalu, amma ita ta yi musu ta kuma tabbatar da ba ta taɓa yin zina ba. Ƙullin labarin ya nuna za a iya ɗora lamarin ga Abbas abokin Auwal wanda Hawwa’u ta je gidansa gaishe da matarsa ta tarar ba ta nan, ya fita aikawa a kira ta, ya dawo ya tarar ta yi bacci ya haike mata.

Wannan ƙulli shi aka cigaba da warwarewa cikin labarin CIN FUSKA wanda ya kasance labari kan rayuwar Abbas ɗan da Hawwa’u ta haifa, wanda ya taso a matsayin malamin sunna kuma ya sha gwagwarmaya da malaman ɗariku wanda hakan ta yi sanadiyyar fallasa wani sirri game da rayuwarsa wanda bai sani ba, cewa an haife shi ne ba ta hanyar aure ba. Har ila yau, bambancin aƙida ta sanya mahaifin Abida ya warware alƙawarin aura wa Abbas ɗin ɗiyarsa har ya sa katangar ƙarfe tsakaninsu.

Labarin Abbas ya cigaba a littafin SAWABA inda aka nuna sakamakon takura da tsanani na ruɗanin al’umma, Abbas ya yi hijira da nufin ƙaro ilimin aƙida a ƙasashen Yemen da Sudan.  A kan hanyarsa, ya ya sda zango a ƙasar Nijar kuma ya sami karɓuwa wajen mutanen garin da ya sauka, saboda suna jin daɗin da’awarsa. Daidai lokacin da jama’ar garin suka tanadi fili da zummar gina masa makaranta da zai rinƙa koyar da su ilimin addini. Shi kuma Alhajin da Abbas ya sauka a gidansa ya ƙudiri aniyar aura masa ɗiyarsa Ramla, sai Abbas ɗin ya bijiro da uzurin ci gaba da tafiya don isa inda ya ɗauro niyya tun daga gida wato zuwa ƙasar Yemen ko Sudan. A nan ne Abbas ya ba Alhaji cikakken labarinsa, ya kuma yi alƙawarin in ya je zai dawo, daga baya a yi auren. Abbas da Ramla suka yi bankwana tare da ɗaukar alƙawarin riƙe amanar juna. Marubucin ya ƙare labarinsa da cewa sai a littafinsa na gaba mai suna MASLAHA za a ji ƙarshen wannan labari na Abbas.

Labarin TARZOMA an gina shi ne kan rayuwar Ayuba wanda ya kasance Bahaushe Musulmi ɗan asalin Sakkwato ta ƙasar Hausa, mazaunin Kudancin Nijeriya. Daga bisani, ya komo Kano da zama, ya ci gaba da fuskantar ƙalubale da tarzomar rayuwa, abin da ya kai shi ga rayuwa a garuruwa irin su Anambra da Ikko da Kaduna, har ya haura ƙasashen Libya da Spain. Ayuba mahauci ne wanda sana’ar fawa ita ta kai iyayensa har suka zauna a Anambra, bayan rikicin ƙabilanci ya yi sanadiyyar kashe iyayen nasa, ita kuma ƙanwarsa Asiya ta bi tawagar ‘yan gudun hijira zuwa ƙasar Libya. Ƙarshe dai sun haɗu da ƙanwar tasa a Libya suka dawo Kano inda a nan ne ta gamu da ajalinta, shi ma daga bisani ya mutu bayan taƙaitaccen lokaci na zamansa a Kano.

Shi kuwa labarin JIRWAYE an gina shi ne kan irin ta’annati da badaƙalar da ake aikatawa a bayan fage a masana’antar shirya fina-finai wadda ta shafi lalata da mata kafin shigar da su harkar da wasu ɓata-gari ke yi (kan-ta-waye).  A cikin labarin Nismatu ta kasance suna zaune da mijinta Assadiƙ a garin Yamai a ƙasar Nijar. Sai dai ba ta daraja shi duk da yana ƙoƙarin kyautata mata, ita a nata ɓangaren tana la’akari da irin rayuwar da take kallo a fina-finan Hausa. Hakan ya sanya ta gudu daga gidan mijinta ta tafi Kano domin shiga harkar fim. 

A karon farko ta faɗa hannu nagari, inda ta kai kanta wajen wasu furudusoshi biyu, suka ƙi amsar ta kai-tsaye. Suka ce sai ta zo da mahaifinta ko wakilinta da sauran wasu ƙa’idoji da suka gindaya mata. Daga bisani sai ta afka hannun wasu gurɓatattun furodusoshi, suka yi lalata da ita suka fara saka ta a fim.  Wannan ya buɗe mata ƙofar yin fice a harkar yadda ta fito a matsayin jaruma a fina-finai uku cikin watanni uku da kwana tara. Daga bisani dai bayan ta sami matsala da iyayen barikinta Dasal da Akwanga, sai ta yi fargar jaji, ta fara nadamar wulaƙanta kanta da ta yi, ta baro ɗakin aurenta, ta shigo harkar da ta mayar da ita gulbi makamfatar kowa. Sai dai lokaci ya ƙure mata, domin iyayenta sun cire rai da dawowarta, tun da ba-amo-ba-labari, sai suka aura wa Assadiƙ ƙanwarta Yasmin. Bayan auren ne, wata rana Yasmin da mijinta Assadiƙ da ƙaninta Nasir suna kallon wani fim mai suna BULAYI, sai suka yi kaciɓis da fuskar Nismatu cikin taurarin fim ɗin. A daidai nan marubucin ya gintse labarinsa inda  ya nuna sai a littafinsa na gaba mai suna ƘYANƘYASA zai cigaba da labarin domin kawo hannunka-mai-sanda kan gyare-gyaren da harkar fim ke buƙata, ko kuma nuna gyaran da aka samu in an samu.Ya kuma yi albishir zai baddalar da littafin zuwa fim. 

An lura cewa, yawancin littattafan ALA yakan gintse labari, ya cigaba a wani sabon littafin. Misali;

1.       Baƙar Aniya­à Cin Fuskaà Sawaba

2.       Jirwaye àƘyanƙyasa.

 

5.0 Abubuwan Da Aka Binciko

Abubuwan da aka binciko sun ta’allaƙa ne kan saƙonnin da suke ɗamfare cikin rubutattun littattafan ƙagaggun labarai na ALA. Saƙonnin da aka ci karo da su kamar a waƙoƙinsa ne, wato galibi faɗakarwa ce a ɓangarorin zamantakewar rayuwar yau da kullum. Saƙonnin sun haɗa da nuna muhimmancin haƙuri da riƙo da addini da taka-tsantsan a soyayya da sauran makamantansu. Saboda haka, abin da za mu yi a wannan gaɓar shi ne fasalta saƙo a cikin littattafan rubutattun ƙagaggun labarai na ALA.

5.1 Saƙo a Rubutaccen Labarin ALA

Rubutun ALA ya fara shiga hannun mutane daga shekarar 1999 kuma ya ci kasuwarsa ta rubutu har zuwa shekarun 2003-2005. Saboda haka, kafin nazarin saƙo a rubutaccen labarin ALA, yana da muhimmanci a yi bitar zangon da marubucin ya faɗo cikin tarihin adabin Hausa. Kenan idan aka yi la’akari da zangunan rayuwar Adabin Kasuwar Kano (AKK), littattafan ALA  sun faɗo cikin zanguna uku mabambanta, wato zangon ‘Balaga’(1990-1995) da kuma zangon ‘Tsufa da Hayayyafa’(1996-2001) sai kuma zangon ‘Ya’ya da Jikoki’(2002-2008). Galibi littattafan da aka samu a  waɗannan zanguna, sun zo da fasalin ni na rubuta, ni na gyara, ni na kai inda za a buga mini, ni kuma ke sayarwa da kaina (Sabe, 2011). Abin mamaki, galibi nazarce-nazarcen da aka gudanar kan AKK (in ma ba a ce duka ba) ba su taɓo littattafan Aminu Alan Waƙa ba[6].

Ta fuskar saƙo kuwa, marubutan AKK na farkon-farko yawanci, saƙonnin soyayya suka tanada a cikin littattafansu, sai kuma batutuwan da suka shafi zamantakewa da rayuwar aure da sauran saƙonnin da suka haɗa da rikici da kishi da sauransu (Sabe, 2011). Idan muka dawo kan littattafan ALA na rubutaccen labari muka yi masu fyaɗar kaɗanya, za mu tarar saƙonnin da suke karakaina cikin littattafan nasa galibi saƙonni ne na faɗakawa. Faɗakarwa ita ce nuna halin ɗa’a wanda zai kasance tsayayyiyar hanya ɗauke da ma’aunin halayyar ɗan’adam na zahiri da son rai kuma ya kasance a kawar da aiwatar da wata halayya mara kyau da mai kyau, (Encyclopaedia Britanica, 1943-1973:11). Kenan faɗakarwa na nufin gargaɗi wanda ya ƙunshi tunasarwa kan ‘yi’ ko ‘bari’ da yi wa mutum hannunka-mai-sanda cikin nusarwa da tsoratarwa da amfani da sauran hanyoyin gyaran zama ko kan gyaran rayuwa. Daga nazarin da aka gudanar, saƙonnin faɗakarwa cikin labaran ALA sun fito da fasalce-fasalce da dama da suka haɗa da:

5.1.1 Nuna Muhimmancin Haƙuri

Haƙuri na nufin juriya ga wani abu na ɓacin rai ko masifa, (CNHN, 2006:190). Haƙuri yana da matuƙar muhimmanci a rayuwa. Sanin haka ne ma ya sa Bahaushe yake da karin magana irin su ‘haƙuri maganin zaman duniya’; ‘mai haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romonsa’ da sauransu. A cikin labarin Sawaba, bayan an idar da sallah a masallacin da yake sallah a garin da ya sauka, Abbas ya yi nasiha tare da nuna muhimmancin haƙuri a rayuwa, inda ya ce:

 Mu ɗauki haƙuri, mu kau da dogon buri, mu zuba jari ga Allah, ta hanyar aiwatar da aiki nagari domin mu riski sakamako irin na masu haƙuri ranar tashin alƙiyama. (Sawaba, shafi na 26).

A nan, marubucin ya nuna muhimmancin haƙuri a rayuwar duniya, inda ya nuna shi haƙuri tamkar jari ne wanda ribarsa ba ma a duniya ba ne, har da ƙiyama.

5.1.2 Taka-tsantsan a Soyayya

 An lura cewa wajen gina rayuwar soyayya cikin labaransa, ALA yana aika saƙonni ga masu karatu cewa a kiyaye ƙa’idar al’ada da ta addini yayin da ake soyayya. Alal misali, a labarin Cin Fuska, marubucin ya nuna lokacin da Abida ta ziyarci Abbas a gidansu, mahaifiyar Abbas ɗin ta jawo hankalin Abida a kan ta kiyaye ƙa’ida a mu’amalarsu, inda ta ce:

Abbas na ɗaki yana karatu, ba na jin ya fita. Amma Abida kar ki sake kuskura ki ƙara yin haka daga yau, da zarar an tashe ku daga makaranta ki rinƙa zuwa gida iyayenki su gan ki tukun, kuma ma in dai ba gurina kika zo ba, to kada in ƙara jin cewa kin zo wurin Abbas, wannan ba mutuncinki ba ne kina ‘ya mace, duk da kuwa na san cewa haɗuwarku alkhairi ne tun da karatu yake koya miki, to in ba kin zo karatun ba ko kin zo gurina kar ki rinƙa zuwa gurinsa kai-tsaye. Kin ji ko Abida? (Cin Fuska, shafi na 5).

Wannan ya jaddada yadda Bahaushe yake taka-tsantsan a kan batun keɓancewar mace da namiji, ko da kuwa suna soyayya ne, domin gudun kauce wa ƙa’ida da aikata ɓarna. Har ila yau, a hirarsu da Ayuba cikin litttafin Tarzoma, Aminuddeen ya tambayi Ayuba cewa:

Ko da dai ka ce ba ka da ilimin addini amma dai duk da haka na san ba za ka fasa sanin illar zaman dadiro ba a addinance, don ko  addinin Kiristoci ya yarda da aure ko? (Tarzoma, shafi na 16).

Wannan ya tabbatar da cewa a al’adance, Bahaushe yana ƙyamar zaman dadiro da duk wani nau’i na fasiƙanci, tun kafin ya rungumi addinin Musulunci ko na Kiristanci. Shi ya sa marubucin ya saƙa wannan saƙo domin faɗakarwa ga al’umma. Bugu da ƙari, da yake an ce ‘abincin wani gubar wani’, abin da yake daidai a tsarin rayuwar wata al’ummar kan iya zama baibai ga wata al’ummar. Alal misali, a yayin da wata al’ummar ta amince da saurayi da budurwa su rungumi juna yayin da suke soyayya, Bahaushe bai yarda da haka ba a al’adarsa. Ba kamar sauran AKK ba, Aminu ALA yana cusa ƙyama ga irin wannan ɗabi’a cikin rubuce-rubucensa. Misali, a littafin Baƙar Aniya 1, muryar mai bayar da labarin ta nuna cewa Hauwa’u da Auwalu:

Suna ƙaunar junansu kamar su haɗiye junansu don soyayya, amma daidai da second ko minti ba su taɓa haura iyaka ba, a fagen soyayya, hannunsa bai taɓa saɓanin ya gogi nata ba ko da wasa, saboda kawaici da tsantseni gami da tsoron Allah na kowannensu…. (Baƙar Aniya, shafi na 11).

Wannan ya jaddada yadda marubucin ke tsarma saƙonnin faɗakarwa game da taka-tsantsan a harkar soyayya domin tabbatar da al’umma tagari.

5.1.3 Nuna Muhimmancin Riƙo da Asali

Asali shi ne mafari ko tushe ko salsala (CNHN, 2006: Sh. 20). Asali abin tutiya ne a wajen Bahaushe, shi ya sa kowa ke tinƙaho da asalinsa. Muhimmancin riƙo da asali ya sanya Bahaushe yake da karin magana irin su ‘kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi’; ‘kowa ya bar gida, gida ya bar shi’, da sauransu. A littafin Tarzoma, ALA ya faɗakar da al’umma kan muhimmancin riƙo da asali a lokacin da Ayuba yake bayar da labarin rayuwarsa a Ikko, inda ya ce:

Sai a lokacin ne na gane kuskuren mahaifina, na kuma ci gyaran kaina da kaina, a sa’ilin da na tuno, sau biyu kaɗai mahaifina ya taɓa kai ni yankin Sakkwato ganin gida, duk kuma a lokacin da ba ni cikin hankalina na sake tuna lokacin da ya rinƙa gaya mini cewa ya kamata in fara shirin zuwa gida zai mini kwatance, ko domin in hutar da shi ya rage tafiye-tafiye, saboda matsalar basur da ke addabarsa. Na yi takaici mai tsanani a lokacin da ƙarairayin da na rinƙa yi suka faɗo min, a inda na rinƙa togaciya da karatu ina zuzzuƙewa, kuma a zahirin gaskiya ba ni ko sha’awar zama garin da Bahaushe yake a wannan lokaci. (Tarzoma, shafi na 11-12).

A nan, marubucin ya nuna duk matsalolin da Ayuba ya fuskanta a rayuwarsa ta rashin makoma da faɗawa tarkon rikice-rikicen ƙabilanci duk sun faru ne sakamakon shi da mahaifinsa ba su ba asalinsu muhimmanci ba. Domin kuwa da ya san asalinsa, kai-tsaye daga Anambra can zai koma zama cikin ‘yan’uwansa bayan da aka kashe iyayensa. Amma da yake bai san ina zai dosa ba, sai ya sake nausawa duniya.

5.1.4 Nuni da Kyawawan Ɗabi’u

A cikin littattafansa, ALA yana ƙoƙarin faɗakar da al’umma kan kyawawan ɗabi’u. Misali, a labarin Tarzoma, tauraron labarin wato Ayuba a zamansa na Kaduna, ya bayar da labarin yadda rabuwarsu da Sarkin Fawan da ya zauna a wajensa a kasuwa ta kasance cikin kewar juna, sakamakon kyawawan ɗabi’unsa:

Sannu a hankali muka sanya ranar tafiya, a lokacin ne kuma na je na yi bankwana da Sarkin Fawa, ina kuka yana tausar zuciyata tare da shi mini albarka, Sarkin Fawa ya ji ɗadin zama da ni matuƙa saboda biyayyata da riƙo da sallah ga ganin girman na gaba, kuma har ya zuwa lokacin barina ba ni da abokin sa-in-sa, balle faɗa.” (Tarzoma, shafi na 23).

A nan ALA ya nuna muhimmancin riƙo da kyawawan ɗabi’u irin su biyayya da girmama na gaba da zaman lafiya da riƙo da addini, waɗanda su ne ƙashin bayan zama lafiyar da Ayuba ya yi da Sarkin Fawa a Kaduna har suka rabu cikin kewar juna.

5.1.5 Nuna Damuwa da Halin da Ƙasa Take Ciki

Ko a waƙoƙinsa, ALA ya shahara wajen damuwa da halin da ƙasa take ciki, musamman sha’anin mulki da siyasa da tattalin arziƙi da tsaro. An lura cewa a rubutaccen labarinsa ma haka batun yake, yana tsarma irin waɗannan saƙonni domin faɗakar da al’umma muhimmancin kishin ƙasa. Misali, a littafin Baƙar Aniya 1, a tattaunawar Auwalu da Hawwa’u, Auwalun ya nuna damuwa da irin halin da ƙasar Nijeriya take ciki, inda ya ce:

Yau a duniya mun makara, mun zama koma baya, a harkar ƙere-ƙere (technology). Bayan kuma Allah ya albarkace mu da komai na mu tafi kafaɗa-da-kafaɗa da sauran ƙasashen duniya. Ƙasashen da suka zama (super powers) ƙashin bayan arziƙinsu a yau (Technology). Da akwai ƙasar da ba su da isasshiyar rana, Nijeriya muna da ikon ƙere-ƙere, ta (sun light) akwai ƙasar da ba ta noma, akwai ƙasar da ba su da ruwa, akwai ƙasar da ba su da ma’adinai na ƙarƙashin ƙasa, ke hatta fatar dabbobin Nijeriya ta fi ta sauran ƙasashen duniya nagarta, babu abin da Allah ya rage mu da shi, face mu muka tauye kanmu, muka tare a ɓangare ɗaya, a ɓangare ɗayan ma shugabanninmu kansu suka sani da ‘ya’yansu.

                         (Baƙar Aniya 1, shafi na 6-7).

 

Daɗin daɗawa, a littafin Tarzoma marubucin ya kawo irin wannan saƙon faɗakarwa kan halin da ƙasa take ciki. Misali, yayin da Ayuba yake ba Aminuddeen labarin rayuwarsa cewa ya yi:

Zan ba ka cikakken labarina Aminuddeeen, ko domin ka yi amfani da damar da Allah ya ba ka ta rubutu, ka isar da saƙon gurin al’umma, wala’alla yin haka zai iya zame wa mutanen arewacin Nijeriya darasin da zai sa su fuskanci tsari da mulki da mu’amalar da ta cancanci rayuwarsu. Rayuwata kacokan tana ɗauke ne da saƙonni masu fa’ida, ga shugabanni da talakawa na ƙasarmu baki ɗaya. (Tarzoma, shafi na 8).

Ire-iren waɗannan saƙonni suna jaddada yadda ALA ya damu da halin da ƙasa take ciki, domin haka yake faɗakar da al’umma cikin rubuce-rubucensa na labarin Hausa.

6.0 Kammalawa

Alƙiblar wannan takarda ita ce nazarin ayyukan ALA na rubutattun ƙagaggun labarai, duk da cewa an fi sanin sa a fagen waƙa.  Da yake masu iya magana sun ce ‘tushiya mafarin dawa’, shi ya sa wannan maƙala ta yi nazarin rawar da Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya taka a fagen kiɗan rubutaccen labarin Hausa. An nazarci yadda ALA ya kasance marubuci kafin mawaƙi, tare da bayyana gurbinsa cikin marubutan Hausa. An kuma kawo sharhin rubutaccen labarinsa da saƙonnin da suka yi karakaina a cikin littattafansa. An bi diddigi an fito da gudummawarsa fili a fagen rubutaccen labarin Hausa, inda a nan ne ya fara baje-kolin fasaharsa a adabance kafin waƙa. Nazarin ya tabbatar cewa akwai auratayya tsakanin saƙonnin da suke kimshe cikin littattafan ƙagaggun labaran da ALA ya rubuta da kuma waƙoƙinsa.

 

Manazarta

 

Tuntuɓi mai takarda. Duba bayanansa a sama.

 



[1] A daidai wannan zangon rayuwa ne ɗaliban UPE, shirin Gwamnatin Tarayya da aka soma daga 1976 domin ba kowane yaro damar samun ilimin furamare kyauta, suka fara shiga kasuwar rubutu da karatu da rububin abubuwan karantawa, domin ɗaliban farko na wannan shiri sun baro firamare a shekarar 1982, daga wannan lokaci har zuwa 1984, an yaye dalibai har kashi hudu. Saboda haka an samar da sababbin makaranta da suke buƙatar abin karantawa.

Haka wannan zango ya zo daidai da lokacin da babban kamfanin wallafa da dab’i a ƙasar Hausa wato NNPC ya soma shiga tasku, ya soma sukurkucewa da neman durƙushewa. A daidai wannan lokaci kamfanin NNPC ya daina buga littattafan hira da nishaɗi, bayan kuma ga dubban matasa da aka yaye daga shirin na UPE sun antayo cike da  shauƙin irin wadannan littattafai da babu su.(Abu Sabe, 2008; 2018).

 

[2] Wato rubuce-rubucen littattafan Adabin Kasuwar Kano (AKK)

[3] Wasu manazartan suna bayyana Adabin Kasuwar Kano (AKK) da sunan littattafan soyayya la’akari da cewa soyayya ce ta mamaye kaso mafi tsoka na jigogin littattafan. Saboda haka, idan ALA ya bayyana cewa ya kasance marubucin so da ƙauna, kenan ya jaddada cewa shi marubucin AKK ne.

[4] A duba tattaunarwar ALA da marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino ta hanyar saƙon wayar salula, ranar 10/11/2012  da misalin ƙarfe 11:26 na dare. Kamar yadda Gidan Dabino ya kawo a cikin (Malumfashi, 2018).

[5] Har zuwa lokacin da aka kammala wannan takarda littafin  Ceto Ko Cuta bai zo hannu ba, ballantana a fayyace shekarar bugunsa  da abin da ya ƙunsa.

[6] Hakan ba ya rasa nasaba da cewa bai daɗe ana damawa da shi a  fagen rubutaccen labari ba, kuma an fi jin ɗuriyarsa a fagen waƙa, sa’annan littattafan nasa ba su shahara kamar waƙoƙinsa ba.

 

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.