This paper titled ‘Kutsen Miyagun Al’adu Cikin Al’ummar Hausawa: Waiwaye a Cikin Wakar Jiya da Yau ta Kyaftin Umaru Da Suru’. The paper through lights on how the Europeans uses the advantage to down grdes the Hausa people’s culture through interactions between themselves, with the aim to make their own superior and that of others inferior.The paper extracted ample examples from the poem of Umaru Da Suru named ‘Jiya da Yau’ to make the argument valid. The Europeans try their best to see that they succeeded in their mission in downgrading some good behaviors of the Hausa people like, lack of respect to elders, lack of shame, traditional plays, local technology, drug abuse and others. Lastly, the paper also came out with the writer’s opinion and findings of the paper.
Kutsen Miyagun Al’adu Cikin Al’ummar Hausawa: Waiwaye A Cikin Waƙar ‘Jiya Da Yau’ Ta Kyaftin Umaru Ɗa Suru
Na
Dano
Balarabe Bunza,
Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya,
Tsangayar
Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci,
Jamia’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
07035141980
Tsakure
An sanya wa wannan takarda suna ‘Kutsen Miyagun Al’adu Cikin Al’ummar
Hausawa: Waiwaye a Cikin Waƙar
‘Jiya da Yau’ ta Kyaftin Umaru Ɗa
Suru. An samar da wannan takarda ta hanyar nazarin da
aka yi na al’adun Hausawa da suka salwanta sanadiyyar cuɗanya
da baƙin al’ummu kuma, aka sami al’adunsu sun
yi tasirin gaske a kan na Hausawa. An yi haka domin faɗakar
da Hausawa don su daina riƙon
al’adunsu kamar sakainar kashi saboda ganin al’adun baƙin al’ummu. An nazarci waƙar ‘Jiya Da Yau’ wadda Kyaftin Umaru Ɗa Suru ya rubuta domin gargaɗi
ga Hausawa don su riƙi
al’adunsu da muhimmantar da su a kan na kowa. Wanda ya yi watsi da al’adunsa ya
ɗauki na wasu mutane, ya muhimmantar da
na wasu a kan nasa ne. Irin wannan ke sanya a ga Bahaushe da sifar mutanen da ba
Hausawa ba. Takardar ta gano cewa, baƙin
al’adu sun mamayi na Hausawa sanadiyyar wayewar kai da aka samu ta zamantakewa
tsakaninsu da waɗanda ba Hausawa ba. A fahimtar takardar wannan
ba komai ba ne face ci gaban mai ginan rijiya. An kawo bayani tare da misalai
daga baitocin waƙar ‘Jiya
da Yau’ kan kutsen da miyagun al’adu suka yi cikin Hausawa da ire-iren raunin
da aka samu a ɓangarori da dama na rayuwar Hausawa.
1.0 Gabatarwa
Mu’amala
tsakanin Hausawa da Turawa ta daɗe
tana gudana tun kafin mulkin mallaka ya shigo ƙasar
Hausa. Mu’amalar ta ƙullu
sanadiyyar kasuwanci da yaɗa addini da leƙen asiri da sauransu. Haka kuma, an sami
kusantar juna tsakanin Hausawa da Turawa sanadiyyar yawon buɗe
ido don ɗaukar
sirrin ƙasa musamman a Arewacin Nijeriya in da
mafi yawan mazauna wurin Hausawa ne. Wani al’amari da ya ƙara ƙarfafa
cuɗeɗeniya
tsakanin Hausawa da Turawa shi ne mulkin mallaka da karatun boko. Sanadiyyar
hulɗar
da ta gudana tsakanin Hausawa da Turawa an sami miyagun al’adu cikin al’ummar Hausawa
da har aka wayi gari al’adun Hausawa sun yi rauni sanadiyyar muhimmantar da
al’adun Turawa a kan nasu ba tare da yin la’akari da kasancewar su miyagu ba. Wannan
ya faru tun lokacin duhun kai, kafin a fahimci kasancewar al’dun miyagu.. An
gano haka a cikin ‘Waƙar
Jiya da Yau’ ta Kyaftin Umaru Ɗa
Suru in da ya ambaci raunin tare da bayyana wuraren da raunin yake. A taƙaice an kawo wasu al’adun Hausawa da
Turawa suka raunana tare da maye gurabunsu da nasu. Wannan takarda ta tsaya ga
abin da Kyaftin Umaru Ɗa
Suru ya faɗa a cikin waƙarsa ta ‘Jiya da Yau’ ba
2.0 Ma’anar Wasu Kalmomi
Kalmomin
da aka kawo ma’anarsu da ke cikin takardar sun haɗa da
kutse da miyagu da kuma al’adu. An yi amfani da ma’anonin da masana suka bayyana
a cikin rubuce-rubucensu kamar yadda takardar ta nuna.
Kutse
Bahaushiyar kalma ce mai nufin cusa, yin shisshigi, ƙwala, burma, ruga (Ƙamusun Hausa, 2006:258).
Ita
kuma kalmar mugu na nufin mutum mai mummunan hali na cuta, macuci, ɓarawo,
ƙwaro (Ƙamusun
Hausa, 2006:348). Miyagu na nufin jam’in mugu da ke nufin mutane masu munanan
halaye na cuta, macuta, ɓarayi da ƙwari.
Kalmar
al’ada ba Bahaushiya ba ce, ta aro ce daga Larabci. Ba za mu bi diddigin
tarihin aron kalmar ba, domin are-aren kalmomi tsakanin harshen Hausa da na
Larabci daɗaɗɗen
abu ne a tarihi (Ibrahim, 1982). A lugar Larabci al’ada na nufin wani abin da
aka saba yi, ko ya saba wakana, ko aka riga aka san da shi. A harshen Hausa ma
haka abin ke nufi kuma, akwai kalmomin da suka fi kusa da kalmar al’ada da suka
haɗa da
‘sabo’ da ‘gado’ da ‘hali’ da ‘sada’ da ‘gargajiya’. Duk waɗannan
kalmomi na da ma’ana makusanciya da kalmar al’ada a wuraren da ake amfani da su
cikin maganganun yau da kullum. A ko’ina mutum ya samu kansa duk wata ɗabi’a
da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko ake
rayuwa, ita ce al’adar da za a ce ita ce tasa. Tare da haka, saboda tasirin
Musulunci ga rayuwar Hausawa an sami suna amfani da kalmar al’ada da nufin wani
abu na addini wato, jinin haila. Idan aka lura mafi yawan Hausawa Musulmi na
kiran jinin haila da suna, jinin al’ada.
3.0 Kutsen Miyagun Al’adu Cikin Al’ummar Hausawa: Waiwaye
a Cikin Waƙar Jiya da Yau ta Kyaftin Umaru Ɗa Suru
Miyagun
al’adu a nan na nufin ɗabi’u da ayyukan da mutanen
da ba Hausawa ba suka kawo har Hausawa suka ɗauka
suna amfani da su tamkar nasu. Wannan ya yi daidai da maganar Hausawa ta cewa “Zama
da maɗauki
kanwa shi ke sa farin kai”. A dalilin zamantakewa wuri ɗaya
da aka samu tsakanin Hausawa da Turawa an sami yaɗuwar
miyagun al’adu da yawa da suka kutsa cikin Hausawa har suka zamo tamkar nasu.
Kutsen da takardar ta duba ya shafi na rusa al’adun Hausawa ba na ciyar da su
gaba ba. Abin da ake nufi a nan shi ne, waɗanda
suka maye sanannun al’adun Hausawa da nufin rinjayar da nasu al’adu a kan na
Hausawa a rayuwar yau da kullum. Ga wasu da aka samu a cikin waƙar ‘Jiya da Yau’ kamar yadda Kyaftin
Umaru Ɗa Suru ya bayyana:
3.1 RaunanaTarbiyya
Asalin kalmar ta aro ce daga Larabci,
wato ‘Attarbiyyat’. Tarbiyya na nufin (i) koyar da hali na gari. (ii) hali
nagari. (Ƙamusun Hausa
2006:428). Bayan wannan, an sami ma’anonin tarbiyya da dama daga wasu masana
kamar haka: Alhassan da wasu (1982) sun bayyana ma’anar tarbiyya da cewa, renon
halayen abin da aka haifa don ya zama nagari, kuma ya iya kama kansa idan ya
girma.
A cewar Funtu’a (1983), tarbiyya horo ne
da iyaye da manya kan yi wa yara domin su tashi da halayen kirki.
Gusau (1999), ya kawo cewa tarbiyya wata
hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan
Adam domin shirya shi zuwa ga halaye da ɗabi’u
masu kyau da nagarta. Ta yin haka zai sa ya tashi da ƙima da kwarjini da ganin mutuncin abokan
zamansa, sa’annan ya riƙa ba
kowa haƙƙinsa daidai yadda ya kamata
gwargwadon hali.
Yahaya da wasu (1992) sun ba da ma’anar
tarbiyya da cewa, cusa wa yara halaye da ɗabi’u
nagari da kuma sa su ƙyamaci
munanan halaye domin su rayu rayuwa ta gari wadda za ta amfane su da kuma
al’umma baki ɗaya.
A ra’ayin Bunza (2002), tarbiyya na
nufin samun kyakkyawan horo ga mutum ya zama masanin kyawawan abubuwa na ɗabi’un hulɗa da jama’a da ladabi da
biyayya da kamun kai da kasancewa mai jin kunya da kyakkyawan maƙasudi.
Shi kuma Bunza (2016) cewa ya yi, ana
iya fitowa da wata ma’anar tarbiyya da cewa, “Tarbiyya hanya ce ta kyautata
rayuwar mutum da daidaita ta domin ya kasance kammalalle mai halaye nagari da
zai amfani kansa, al’umma ta amfana da shi, ta kuma yi alfahari da shi,
musamman lokacin da ya cika girmansa”.
Akwai masu koyar da tarbiyya a cikin
al’umma da suka haɗa da
iyaye da malamai a makarantun ilimi da sauran waɗanda abin ya rataya a wuyansu. Ana koyar da tarbiyya
domin a sami al’umma tagari. Yin sake da rashin koyar da tarbiyya ke sanya a
sami al’umma ɓata
gari mai aikata abin da take so domin rashin bin umurnin iyaye, wanda magance
matsalarsu sai tare da sanya hannun hukuma. Maras tarbiyya shi ne mai bijire wa
kyawawan al’adu da karantarwar addinin Musulunci ba tare da jin kunya ko samun wata
damuwa ba.
A fahimtar mai bincike, tarbiyya na
nufin kira ko koyar da halayen kirki ga yara da manya domin su nisanci miyagun
halaye tare da rungumar kyawawa suna aikatawa.
Raunana tarbiyya na nufin raguwar
aikata halin kirki tare da rungumar halaye marasa kyau da wasu mutane suka kawo
sanadiyyar mu’amalar zamantakewa. Haka kuma raunanawa na nufin lalatawa wato,
rungumar miyagun al’adun da Hausawa suka yi ya kawo lalacewa da raguwar
kyakkyawar tarbiyyar al’umarsu. Kafin haɗuwar
Hausawa da wasu al’ummu tarbiyyar yara ƙanana
da matasa abin yabawa ce. Yara na girmama manya da aikata abin da al’ada ta
tanada na bin sawun magabatansu. Sanadiyyar haɗuwa da wasu mutane da ba Hausawa ba ya sanya aka sami
kyawawan halayen mafi yawan Hausawa musamman matasa da ƙananan yara sun yi rauni. Wannan ya faru
saboda nasarar da baƙin al’ummu suka
samu kan matasa na sha’awar al’adunsu da rungumar su ido rufe ba tare da tantance
dacewa ko rashin dacewa ba. A da, akwai biyayya da halayen kirki masu ɗimbin yawa a al’ummar Hausawa amma,
sanadiyyar haɗuwa da baƙin al’ummu sannu a hankali miyagun
halaye suka yawaita cikin al’umar Hausawa. Halaye da ayyukan ɗa’a da ‘ya’yan Hausawa ke aikatawa kafin
haɗuwarsu da baƙin al’ummu sun ragu ainun kuma, marasa
kyau sun maye gurabun na ƙwarai
a cewar Kyaftin Umaru Ɗa
Suru cikin waƙarsa mai suna
‘Jiya da Yau’. Tarbiyya babban fage ne da aka duba kamar haka:
3.1.1 Rashin Ladabi da
Biyayya
An sami ma’anar ladabi da biyayya daga
wasu masana irin Alhassan da wasu (1988) a cikin littafinsu mai suna ‘Zaman
Hausawa’ in da suka ce “Ladabi da biyayya manyan ƙusoshi ne a cikin tarbiyyar Hausa watau, muhimman halaye
ne da Bahaushe yake so ya ga ana yi. Girmama na gaba da kyautata wa na baya, su
ne halayen da ake kira ladabi da biyayya”. A nan, in an ce na gaba da kai, ana
nufin wanda ya fi ka a shekaru ko ta hanyar shugabanci. Ma’anar girmamawa kuwa,
ba wai sai ka rusuna ka gai da mutum ba. A’a, sassauta magana da saurara wa
mutum idan yana yin tasa, wannan ma girmamawa ce. Haka kuma, idan babba ya
tashi aiki a karɓe shi,
ita ma girmamawa ce. Bayan haka, a tarbiyyar Hausa, tsoma baki cikin maganar na
gaba da kai aibu ne. A wani wuri kuma, an bayyana cewa ladabi na nufin biyayya
(Ƙamusun Hausa, 2006:297). Biyayya kuma
na nufin ladabi da bin na gaba (Ƙamusun
Hausa, 2006:49). Ke nan ladabi da biyayya na nufin halaye da ɗabi’un kirki da al’adar Hausawa ta
aminta da su. Kafin Hausawa su haɗu
da wasu al’ummu suna cike da ladabi da biyayya. Bayan haɗuwarsu da wasu al’ummun ne aka sami
tarbiyyarsu ta fara rauni don daina aikata halayen kirki, marasa kyau suka maye
gurabunsu. Wannan ne ya raunana tarbiyyar Hausawa kai tsaye. Dangane da rashin
ladabi da biyayya ga abin da Kyaftin Umaru Ɗa Suru ya ce:
5. 'Ya 'yan yau ba biyayya,
In an yi karo a
hanya,
Yaro bai amsa kaya,
Shi riƙa in ya ga manya,
Al'adu sun yi rauni.
A cikin baiti na 5 da ke sama Kyaftin ya bayyana rashin biyayyar ‘ya’yan Hausawa na zamani ta hanyar cewa biyayyar da aka san ‘ya’yan Hausawa da ita ta yi rauni sosai idan aka yi la’akari da zamanin da ya gabata. Ya faɗi haka saboda barin kyawawan ɗabi’u da ‘ya’yan Hausawa suka yi, suka koma ga waɗanda ba su da tushe balle makama. Kalmar karo da Kyaftin ya yi amfani da ita a layi na biyu, haɗuwa yake nufi a kan hanya. Daga cikin halaye na ladabi da biyayya akwai karɓa wa babba kaya idan aka haɗu da shi yana ɗauke da su a kan hanya, musamman idan ya dawo daga jeji. Wannan ɗabi’a ta yi rauni ƙwarai da gaske face a wurare kaɗan. Karɓa wa babba kaya da yara ke yi na janyo ɗinbin albarka ga ‘ya’ya sanadiyyar addu’a da wanda aka karɓa wa kayan ke yi. Maimakon karɓa kayan, ko gai da wanda ke ɗauke da su bai samuwa a mafi yawan wurare. Don haka, maimakon karɓa kayan, abin ya koma kaya su kashe ka. Duk mai shekara 40 zuwa yau ya san da wannan kyakkyawar al’ada na gudana a cikin al’ummar Hausawa. Idan aka yi la’akari da wannan za a tarar cewa, ɗabi’ar taimakon na gaba ta hanyar karɓa masa kaya ta yi rauni ƙwarai a mafi yawan wurare na ƙasar Hausa. Kyaftin ya ƙara da cewa:
6.
Yau ba mai karya guiwa,
Wai don ladabi ga kowa,
Zamani ke jirkicewa,
Matsalolin da da shawa,
Ni kansu nake tunani.
Karya guiwa na nufin ɗan tsugunawar da ake yi a gai da na gaba domin nuna ladabi da biyayya.
Kalmar jirkicewa da ke cikin layi na uku na nufin sauyawa. Matsalolin da
Kyaftin ke nufi har ya ce suna da sha’awa, halayen kirki da ke gudana a da yake
nufi ba matsala ta koma baya ba. Duban yadda abubuwa ke tafiya lamui lafiya a
da da ganin yadda suka sauya ya sanya Kyaftin a cikin tunani na mamakin ganin
yadda suka komo a wannan zamani. A al’adance a da, idan yaro ya haɗu da na gaba gare shi yakan durƙusa ya gaishe su domin nuna ladabi da biyayya. Bayan haɗuwar Hausawa da wasu al’ummu sai aka sami akasin haka.
Babu wurin da aka samu Bature ya kai ziyara a fadar wani sarki, ya durƙusa ya gaishe shi. Irin wannan ɗabi’a ce yaran zamani
suka kwaikwaya daga Turawa har suka faɗa cikin halin rashin
ladabi ga na gaba. Gaisuwar Bature ga na gaba da shi da na baya gare shi duk
iri ɗaya ce domin, ba ta zarce hello da hi ba ta hanyar tayar da hannu ko yin shewa idan ana son a kira wani.
Idan aka duba sosai, haka rayuwar mafi yawan matasan Hausawa take. Wannan
matsala ce ta sanya Kyaftin tsunduma cikin tunanin abubuwan da ke gudana a yau
saɓanin jiya. Wannan ne sanadiyyar sanya wa
waƙarsa suna “Jiya da Yau” wato yana kwatanta abubuwan da ke
gudana a da da kuma yadda suka sauya a yau saboda wasu dalilai.
3.1.2 Raunana Al’adar
Kunya
Alhassan da wasu (1988) sun ce “In an ce ana jin nauyin
mutum ko ana jin kunyarsa, to ana girmama shi ke nan, kuma ba za a yi wasa da
shi ba, sa’annan duk wani abin wargi ba za a yi shi da shi a wurin ba. A wani
wuri cewa aka yi, kunya na nufin halin nuna kawaici da jin nauyi da rusunawa
saboda wata dangantaka (Ƙamusun Hausa, 2006:254).
Takardar na da fahimtar Kyaftin ya gwama lokuta biyu (Da da yanzu) domin nuna
bunƙasar kyawawan halaye da kuma rauninsu. Don haka idan ya ce
ana aikata wata ɗabi’a a da to, mai
kyau ce da ta yi rauni a wannan zamani. Za a ga haka a baitin da ya yi tsokaci
kan wata ɗabi’a ta rashin jin
kunyar aikata wasu ayyuka ga mutanen zamani kamar haka:
7.
Mutumin da na da kirki,
Kominsa cikin tsanaki,
Ga hula kai da aski,
Bai ci kuma kan ɗariƙi,
Sai dai ya je mazauni.
Abin da Kyaftin ke
nufi a cikin baitin da ke sama shi ne, duk abin da ke ciki na halin kamalar
mutanen da, na yanzu akasinsa ke gare su face kaɗan.
Ya yi haka domin ganin sunan waƙar zai yi wa mai karatu jagora ya
fahimci mutanen da na da kyawawan halaye ba kamar na wannan zamani ba da ke
aikata ganin damarsu ba tare da yin la’akari da dacewa ko rashin dacewa ba.
Kyaftin ya ce mutumin da na da kirki mai nufin kirkin mutumin wannan zamani na
da rauni. A layi na biyu ya ce duk abin da mutumin da zai yi ko yake yi
zai sanya natsuwa (Tsanaki) a ciki, saɓanin yau da idan aka
ga wani ya aikata wani abu za a fahimci akwai rashin natsuwa a ciki mafi yawa.
A layi na uku Kyaftin ya bayyana cewa, mutumin da zai yi aski kuma, ya sanya
hula a kansa saɓanin mutumin zamani.
A layi na huɗu Kyaftin ya bayyana
halin mutumin da na rashin cin abinci a kan hanya duk yadda yake jin yunwa har
sai ya sami wuri ya zauna. Abin nufi a nan shi ne, ba haka mutumin yau yake ba.
Shi kan, duk wurin da ya so ya ci abinci, yana cin abinsa domin ba ya tare da
kunya.
Wannan ya sanya Kyaftin ya fito ƙarara a baiti na tara ga wanda bai
fahimci abin da yake nufi a baiti na bakwai ba domin ƙara
fayyace maganar da ke ƙunshe a cikinsa yana cewa:
9.
Mutumin yau bai da kunya,
Da ido ƙulai na ƙarya,
Suruki bai kauce hanya,
Wai don suruki ya ɓuya,
Mata sun daina huni.
An ga ma’anar kunya a baya daga bakunan masana. A layi na biyu da ke cikin
baitin ƙulai na nufin buɗe mai nufin ba ya
runtse ido domin nuna jin kunyar kowa. Duk wanda ya kware masa ido shi ma zai
kware masa. Bayan haka ga baƙar ƙarya, idan ya ba da labari biyar da wuya
a sami uku na gaskiya. Bayan haka abin da aka sani tsakanin surukai, nuna jin
kunya. Idan suruki na magana da surukinsa da wuya su haɗa ido saboda jin kunya. Hasali ma, da wuya su haɗa hanya ɗaya, sai girshi da
rashin sani. A zamanin da, idan suruki ya tsinkayi surukinsa a kan hanyar da
yake tafe, zai bar wannan hanya , ya koma ga wata kai tsaye don tsananin nuna
kunya da nuna ladabi da biyayya. Surukan yanzu kuwa, ba a kunyar juna, hasali
ma, wani na jiran suruki ya shigo hannunsa domin ya ci mutuncinsa. Da zarar an
sami haka, al’adar kunya ta yi rauni ƙwarai ba kaɗan ba. Huni da ke layi na biyar a wannan baiti na nufin lulluɓi. Idan aka sami mace ta daina lulluɓe jikinta har ta fita waje da tufafin da ta ga dama, rashin
kunya ya bayyana kuma, ya kai in da ya kai. A baiti na 9 Kyaftin ya nuna akwai
rashin kunya ga mafi yawan ‘ya’yan Hausawa na wannan zamani musamman tsakanin
surukai. Wayewar da ta kai mutum barin ɗabi’arsa ta ƙwarai
ya koma ga ɗabi’a maras kyau ci
baya ne ba ci gaba ba. Shi kuma ɗan yau da yake zamani
ya juye tunaninsa, babu ɗan gaye sai shi kuma,
ba ya shakkar mahaifinsa, maimakon haka, mahaifin ke shakkar sa don kar ya
kunyata shi cikin jama’a. Wannan na yin hannunka-mai-sanda cewa, ɗan ya shiga halin ɓatuwar hankali irin na
shaye-shaye kamar yadda Kyaftin Umaru Ɗa Suru ya faɗa:
11.'Ya 'yan yau sai fa disko,
Ka ji suna wai
Ajasko,
Mata kai ba babu diko,
Wannan zamani na
boko,
Ya
hamɓare 'yan zamani.
Disko kiɗi ne da rawa irin na
Turawa da sauran ƙabilu amma, ba Hausawa ba. Haka kuma, za ka ji ana kiran ɗan Bahaushe da suna Ajasko wanda ba Musulmi ba. Wani lokaci
sunan da mahaifinsa ya sanya masa da ya yanka masa rago da shi na laɓewa saboda mafi yawan mutane Ajasko suka san shi da shi ko da
Ahmad ragonsa ya ba shi. Wannan rashin kunya ne a fili in da za a sami yaro ya
sanya wa kansa wani suna daban da wanda mahaifinsa ya raɗa masa kuma, na arna ba Musulmi irinsa ba. Wannan na tabbatar
da maganar Kyaftin ta cewa, al’adun Hausawa sun yi rauni matuƙar
gaske musamman idan aka dubi layi na uku da na huɗu
da kuma na biyar a wannan baiti, in da ya ce, mata kai babu diko dawannan
zamani na boko da kuma ya hamɓare ‘yan zamani. A ƙashin
gaskiya zamani ya yi mummunan tasiri a kan al’adun Hausawa idan aka dubi
abubuwan da ke gudana a cikin makarantun boko. Mafi yawan mata ‘yan boko ba su
sanya diko (Ɗankwali) a kansu sai dai wani ƙyalle ko gyale ko kuma
a bar kai sake don nuna an waye. Wannan wayewar ta sanya suka saki al’adun
kakaninsu suka kama na wasu. A nan, an sami ci gaban mai ginan rijiya. Saboda
haka maganar Kyaftin na nan ta cewa, al’adar kunya ta yi rauni ƙwarai
ba kaɗan ba.
3.3 Shaye-Shaye
Shaye-shaye
na nufin nanata shan abubuwa musamman masu sa maye (Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano,
2006:410). Haka kuma, shaye-shaye na nufin ɗabi’a
maras kyau da ake samu ga wasu ‘ya’yan Hausawa na ci ko sha ko shaƙe ko yin allura da sauran hanyoyin da
ake bi domin hankali ya ɗagu a sami damar yin abin da
ake so. Duk waɗannan shaye-shaye ba komai ba ne sai
wuce gona da iri na magungunan da ake amfani da su yau da kullum. Misali,
maganin mura da na ƙarfin
jiki da sauransu. Marubuci waƙar
ya kwatanta ‘ya’yan da da na wannan zamani dangane da shan abubuwa masu gusar
da hankali, in da ya ce:
12. Ɗan da bai kunna taba,
Abada bai buɗa kwalba,
Disko ba a san shi da ba,
In ba sallah ta zo ba,
Kiɗa ganga sai ga rani.
A
cikin baitin da aka kawo a sama Kyaftin Suru ya bayyana ‘ya’yan da ba su shan
abubuwa masu gusar da hankali kamar na wannan zamani. Ba mashaya ne babu ba a da. A’a. Akwai su amma, ba
su da yawa kamar na yau. A wannan zamani kuwa, mashaya sun yi yawa ƙwarai da gaske ka ce wani aiki da ake ba
mai yin sa lada. Ba komai ya kawo wannan ba sai haɗuwa
da baƙin al’ummu da al’adarsu ba ta hane su da
aikata wannan ba. Akwai shaye-shaye iri daban-daban da suka haɗa da
na ruwa da kuma sandararre. Mafi yawan mahaukatan da ke kan tituna a yau ba
haukar Allah ba ce, shaye-shaye ya haddasa hakan. Idan aka ƙara komawa ga baitin za a fahimci
maganar da Kyaftin ya fito da ita cewa, mashaya taba da giya sun yi yawa a
cikin Hausawa. Hasali ma, ko waɗanda suka kawo shaye-shaye a
ƙasar Hausa ba su sha kamar yadda Hausawa
ke sha. Tabar sigari Kyaftin ke nufi a layin farko na cikin baiti na goma sha
biyu. Buɗa
kwalba kuma, shan giya yake nufi. Kiɗan
disko kuwa, Turawa suka zo da shi har suka yi sanadiyar ‘ya’yan Hausawa suka yi
watsi da kaɗe-kaɗensu
na gargajiya suka rungumi na zamani.
An wayi gari namiji
da mace, babba da yaro sun tsunduma cikin ɗabi’ar
shaye-shaye ka’in-da-na’in, wanda shi ya kawo ƙaruwar
mahaukata a kan titunan ƙauyuka
da birane. Tabar da ba irin ta yau ba ce domin akwai wuiwui da ake kira tabar
aljannu mai saurin haukata mai shan ta. Magungunan asibiti da yawa an mayar da
su shaye-shaye sanadiyyar wuce gona da irin da ake ke yi a wajen amfani da su.
Misali, maganin mura da likita ke cewa a sha marfi ɗaya
da safe, ɗaya da dare, sai mashayi ya kafa kai ya
tsotse kwalbar baki ɗaya don maganin ya fita daga
zama magani ya koma masa barasa. Akwai hodar aljannu da ake amfani da ita a
matsayin shaye-shaye sai dai wannan ta masu hali ce.
A
cikin baitin ana iya gano cewa, cikin kowane lamarin rayuwar Bahaushe Bature ya
yi iya ƙoƙarin
da yake yi domin ganin ya raba Hausawa da al’adunsu tare da cusa musu nasa ko
ta halin ƙaƙa. Wannan maganar da marubucin ya faɗa
babu ƙarya ko ƙari
a ciki domin, komai a fili yake ba sai an tambaya ba. Duk wanda ya san yadda
ake a da, ya kuma kula da abin da ke gudana a yau, zai tabbatar da abin da
Kyaftin ya ce dangane da kutsen miyagun al’adu cikin na Hausawa gaskiya ne ba ƙarya ba.
3.3 Raunana Wasu Wasannin
Gargajiya
Wasa
na nufin abu da akan yi don raha ko nishaɗi (Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero,
Kano:470). A gargajiyance Hausawa na da wasannin da suke yi a wasu keɓaɓɓun
lokuta na shekara, musamman lokacin kaka. Wasannin gargajiyar Bahaushe sun haɗa da
dambe da kwankwanba da wasannin tashe da kokawa da wasannin dandali na yara maza
da mata irin kalankuwa da wasan hawan ƙaho
na rundawa da sauransu. Idan aka yi la’akari da zamani za a fahimci cewa, sun yi
rauni matuƙa in da wasunsu sun
kama hanyar ɓacewa. Ba komai ya kawo wannan ba sai ƙoƙarin
Bature na ganin ya raba Bahaushe da al’adun kakaninsa kuma, ya maye su da nasa.
Alal misali, Turawa sun kawo dambensu a cikin kasakasai da suka sanya wasu
Hausawa barin nasu wasanni suka raja’a ga na Turawa. Haka wasan ƙwallon ƙafa
ya haddasa barin kallon wasanni da yawa na Hausawa. Wasan tashe lokacin azumi
ya yi rauni ƙwarai idan aka yi
la’akari da yadda ake gudanar da ita a da da kuma yanzu. A taƙaice, mafi yawan wasannin gargajiya na
Hausawa sun yi rauni sanadiyyar wasannin fim da Turawa suka kawo. Akwai wasu
wurare a cikin waƙar
Kyaftin da ya kawo cewa wasannin gargajiyar Hausawa sun yi rauni sanadiyyar
ganin na Turawa kamar haka:
64. Ƙwara ta ɗiyan kaɗanya,
Ita
ce ƙwan
yin fasayya,
Ƙwallon ragga tawayya,
In an jefe a goya,
Wasar dale sai ga rani.
Daga
cikin wasannin gargajiyar Hausawa da yara ke yi akwai ta fasayya da ɗiyan
kaɗe da
kuma wasan jefayya da ƙwallon
raga wadda tsoffi ke kira tawayya. Wasa ce mai ban sha’awa ƙwarai da gaske kuma, mai haɗa
zumunta tsakanin yara matasa. A zamanin da ake ciki yanzu kuma, Turawa sun kawo
wasan ƙwallon ƙafa
da ake gudanarwa ko’ina har Hausawa suka daina sha’awar tasu wasa suka koma ga
na Turawa. Wanda duk ya san wasannin gargajiyar Hausawa na da kuma ya ga abin
da ake yi a yau, zai tabbatar da akwai shigowar miyagun al’adun wasu mutane ga
abubuwan da Hausawa suka saba aiwatarwa kuma, shi ya haddasa raunin da ake
zance a kai.
Wani
dalili da ke ƙara tabbatar da
Turawa sun yi sanadiyyar raunin al’adun Hausawa shi ne a wurin da Kyaftin Umaru
Ɗa Suru ya ce:
86.Can da in za a
taro,
Aka
ce an ba da goro,
Sai ‘yan wasa su jero,
Ka ga mai doka da tsoro,
Tukkaye dama hauni.
87. Yau ko duka sun ji
tsoro,
Kowa ya aske tsoro,
Da wuya ka ga masu rero,
Fillani ba su sharo,
Al’adu sun yi rauni.
A
baiti na 86 Kyaftin ya kawo hoto cikin bayani na abubuwan da ake gudanarwa idan
ana buƙatar yin wani taro. Ya ce akan raba wa
jama’a goron gayyata kafin ranar taron ko bukin. Idan ranar buki ta zo za a ga
‘yan wasa cikin shiri sun jero wani bayan wani an nufi filin wasa. Daga cikin
‘yan wasan za a ga wasu sun gyara gashin kansu ta nau’i daban-daban. Wasu za su
yi kitson da ake kira doka (Kitson da namiji ke yi idan zai tafi wurin wasa da
ake raba gashin kai kashi uku ko huɗu a ɗaure).
Tsoro kuma na nufin a aske gashin kai na ɓangaren
dama da na hagu tare da barin gashi a tsakiyar kai daga goshi har zuwa ƙeya. Tsoro gashi ne da ake bari lokacin
da aka yi wa yaro aski, siriri a tsakiyar kansa daga goshi zuwa ƙeya. Tukkaye kuwa gashi ne da ake bari a
wasu wurare ga kai lokacin da aka yi wa ɗan
wasa aski. Ana yi wa yaran ƙauye
irin wannan aski musamman na goye da waɗanda
ba su yi wayo sosai ba. Ana iya yin tukkuwa biyar a kan ɗan
wasa kamar yadda marubucin ya faɗa
cewa, tukkaye dama da hauni. Idan aka kalli wannan bayani, aka yi la’akari da
yadda abubuwan suke a da, za a tabbatar da wasannin da sun yi rauni ba kaɗan
ba. Marubucin ya fayyace wannan magana a baiti na 87 in da ya ce, duk ‘yan
wasannin gargajiya sun daina. Haka kuma da wuyan gaske a sami ‘yan dambe da
rero (Kewayayyen farin gashin wuyan rago ko wata dabba) wanda ke nuna ƙawar ɗan
wasa. Ganin haka ya sa marubucin ya yi hukunci a layin ƙarshe cewa, al’adun wasannin gargajiya
sun yi rauni, kuma gaskiya ne domin duk wanda ya rayu a lokacin da marubucin ke
magana a kai, kuma ya ga abubuwan da ke gudana a yau zai tabbatar da abin da ya
faɗa
gaskiya ne domin komai a fili yake.
3.4 Raunana Fasahar Hausawa
ta Gargajiya
Fasaha
na nufin gwaninta ko ƙwarewa
(Ƙamusun Hausa, 2006:136). Allah ya ba
kowace al’umma fasahar da za ta rayu a doron ƙasa
kuma, kowace al’umma da nau’in fasahar da aka ba ta. Hausawa mutane ne da Allah
ya hore wa fasahohi daban-daban. Wasu an ba su fasahar gine-gine, wasu ta ƙere-ƙere,
wasu ta saƙe-saƙe, wasu ta ɗinki,
wasu ta gyare-gyaren wasu abubuwa da sauransu. In da za a gane kutsen da Turawa
suka yi da miyagun al’adunsu cikin na Hausawa shi ne, da sun fahimci wani na da
wata ƙwarewa sai su ɗauke
shi daga sunan aro su mayar da shi ƙasarsu
yana yi musu aiki, suna amfana da fasaharsa Hausawa sun rasa ke nan. An sami
wani ɗan
Nijeriya da ya ƙera
jirgin sama a shekarar 1979-80 da aka ba da labari a cikin jaridar Gaskiya ta
fi kwabo amma saura tashi. Nan take Turawa suka yi kudun-kudun suka ɗauke
mutumen zuwa ƙasarsu. Daga wannan
lokaci ba a sake jin labarinsa ba. Haka kuma akwai wani Bahaushe da Allah ya ba
fasahar fitar da siffar mota shi ma, sun ɗauke
shi. Shi da gida sai dai wata lalura ba ya yi wa ƙasarsa
aiki da fasaharsa. Akwai irin waɗannan
misalai da dama dangane da kutsen Turawa a cikin fasahar ‘yan ƙasa a wurare daban-daban a fagen raunana
fasahar gargajiyar Hausawa. Bayan haka, Turawa sun ci nasarar yin haka ta in da
suke ba mutanen da suka ɗauka zuwa ƙasashensu albashin da ba a iya ba su a ƙasarsu tare da ɗauke
wasu ɗawainiyarsu
da ta iyalinsu. Wannan ne ya sanya mutanen amincewa da su tafi su yi wa Turawa
aiki domin more rayuwarsu. Don haka a nan ana iya cewa idan ɓera da
sata, daddawa ma da wari. Irin wannan ya sanya marubucin faɗar
cewa::
61
Mu mun bar tamu ƙira,
Kuma
kanmu akwai basira,
Ku
tuna da namu yara,
Da
kara suka tasu ƙira,
Ko laka kun fa sani.
Ƙira na nufin sana’a ce ko aikin sarrafa ƙarfe a mai da shi makami, ko ma’aikaci da dai sauransu. Ana narka ƙarfe ko tama ko sanholama ko gaci ko
azurfa ko zinari da wuta, a mayar da ita wani abin amfani. Akwaai kayan aikin ƙira daban-daban da suka haɗa da
zuga-zugi da gawayi da uwar maƙera
da guduma da masaba da gizago da awartaki da sauransu. Ƙira na ɗaya
daga cikin sana’o’in fasaha na Hausawa da rini da dukanci da sauransu. Yaran
Hausawa na da fasahar yin motar kara da ta laka. Wannan na nuna irin basirar da
Allah ya ba Hausawa. Daga nan ne wasu suka gwada basirar yin fanka da sauran
abubuwa irin rediyon laka da sauransu da suke cin lamba da su a wuraren tarukan
gwadin amfanin gona da wasu irinsu. Da ilmin boko ya ƙara samuwa sai fasaha ta ƙasa bunƙasa.
Idan babu nufin raunanawa kama wa Hausawa ya dace Turawa su yi ta hanyar
taimaka wa masu basirar don ƙasa
ta amfana da su. Maimakon hakan, sai suka ɗauke
mutanen suka mayar ƙasarsu
don su yi musu aiki. Bayan haka ga abin da Kyaftin ya ƙara faɗa
dangane da fasahohin Hausawa:
62:
Yaranmu akwai basira,
Mota ta kara su ƙera,
Laka kwali su tara,
Dabba da mutum su ƙera,
Da wayar iska ɗayani.
Ba
Turawa kaɗai Allah ya ba fasahar ƙere-ƙere
ba, ya ba kowace al’umm irin nata. Yanayin zamantakewar da ke tsakanin Turawa
da sauran al’ummomi na mulkin kama karya ya sanya suka danne kowa suka gina
kansu. Yawon buɗe idon da suka zo tun farko
da wata manufa ne ta daban ba domin a taimaka wa kowa ba. Yawon leƙen asirin wasu ne a san yadda za a fito
musu a yaudare su. Marubucin ya kawo misalai ƙwarara
da hankali ke ganewa cewa, al’ummar Hausawa mai fasaha ce da basira musamman
idan aka lura da bayanin da ya gabata na wani da ya ƙera jirgin sama saura tashi. Ba wannan
lokaci kaɗai ba, ko yau idan Turawan Yamma suka
fahimci akwai wani mai basirar da zai amfane su, za su bi duk hanyar da ake bi
domin su raba ƙasarsa da shi ta
hanyar aron da ba na mayarwa ba. Bayan sun ɗauke
shi sai su tafi su yi yarjejeniya da shi cewa, za su biya shi abin da ƙasarsa ba ta iya ba shi domin ya tsaya
ya yi musu aiki. Ina ƙwarrarrun
likitoci ‘yan Nijerya waɗanda daga cikinsu akwai
Hausawa ? Ina suke aiki na dindindin? Mafi yawan lokuta da marasa lafiya ke
zuwa ƙasashen waje jinya, su ne ake samu a
matsayin ƙwararru. A san da cewa
idan ɓera
da sata, daddawa ma da wari. Duk da haka dai, sai mutum ya yi sake ake yi masa sakiya.
3.6 Ra’ayin Marubuci
Bisa
ga hangen marubuci waƙar,
rayuwarsa na cike da haushin yadda Turawa suka bi hanyoyi daban-daban na
raunana al’adun Hausawa ta kowane hali. Marubucin na da ra’ayin Hausawa su riƙe gargajiyarsu kuma, kar su aminta kowa
ya raba su da ita. An ciro ra’ayin a bakin marubucin in da ya faɗi
cewa:
93. Turawa kar su ja ka,
Ka
bi nasu ka ya da naka,
Ya zan wauta gare ka,
Al’adun kakanninka,
Ka riƙe su su zan ma’auni.
Kyaftin
Umaru Ɗa Suru ya kawo shawarwarinsa a cikin
baiti na 93. A cikin baitin ya ba da
shawarar cewa, kar mutum ya bi abin da Turawa suka kawo har ya yi wa nasa riƙon sakainar kashi. A maimakon hakan,
kowa ya riƙe gargajiyarsa ya bar
wa Bature nasa. Idan kuma aka rungumi al’adun Bature aka yi sakacin barin na
gargajiya, ba komai aka yi ba sai wauta. Ba a wannan baitin kaɗai
Kyaftin ya ba da shawara ba, akwai a cikin wasu baitoci sai dai, na 93 ya fi
dacewa da haɗe komi a wuri ɗaya
fiye da sauran baitocin kuma ya zan sara a kan gaɓa bisa
ga maudu’in takardar. Haka kuma, idan aka yi aiki da shawarar da ke cikin baitin
komai zai gyaru ya daidaita, a kuɓuta
daga matsalolin da Turawa suka saka Hausawa a ciki dangane da abin da ya shafi
al’adun gargajiyarsu.
3.7 Sakamakon Bincike
Takardar
ta gano cewa, shigowa da Turawa suka yi a ƙasar
Hausa ba domin taimakon Hausawa ba ne, domin yauradara ne. Sun yi hanyoyin mota
da jiragen ƙasa domin amfanin
kansu ba don kowa ba sai dai, ba ya yiwuwa ne kawai a dafi gawa a tashi babu
hawaye. Ma’ana, ko ba don kai aka yi abu ba idan aka yi shi wurin da kake, wani
amfani zai shafe ka. Haka kuma, binciken ya gano cewa, lokacin da Hausawa suka
fara haɗuwa
da Turawa ne tarbiyyarsu ta fara rauni har ta raunana. Babu shakka ladabi da
biyayya sun yi rauni da al’adar kunya a kan kutsen da al’adun baƙi suka yi a cikin na Hausawa. An gano
haka ne dalili da shaye-shayen da Hausawa suka sami kansu a ciki. Takardar ta
gano rauni ga sana’o’in gargajiyar Hausawa da wasannin gargajiya da kuma sace
fasahar Hausawa ana kai ta ƙetare
har da masu ita. Haka kuma, takardar ta
gano cewa, Kyaftin na ɗaya daga cikin Hausawa masu
son al’ummarsa ta ci gaba ba baya ba tare da gano cewa yana ra’ayin ana aiwatar
da al’adun gargajiya gwargwadon hali musamman wasanni irin dambe da kokawa da sauransu.
4.0
Kammalawa
A
cikin wannan takarda mai suna ‘Kutsen Miyagun Al’adu Cikin Al’ummar Hausawa:
Waiwaye a Cikin Waƙar
Jiya da Yau’ ta Kyaftin Umaru Ɗa
Suru’ an bayyana yadda Turawan Yamma suka yi ƙoƙarin ganin sun canza al’adun Hausawa domin
su maye da nasu, ba don komai ba sai don ganin sun ɗaukaka
a kan kowa. Da farko an yi gabatarwa sannan aka biyo da ma’anar wasu kalmomi da
suka fito a cikin taken takardar. A cikin gundarin bayanin takardar an tattauna
abubuwa da suka haɗa da raunana tarbiyya da ya ƙunshi rashin ladabi da biyayya. Haka
kuma an kalli raunana al’adar kunya da raunana wasannin gargajiya da raunana
fasahar Hausawa ta gargajiya. Shaye-shaye na cikin abubuwan da aka bayyana da
ke cikin hanyoyin da Turawa suka yi amfani da su wajen raunana al’adunsu
al’ummar Hausawa tare da cusa nasu domin al’ummar Hausawa a su tamkar su ne
nasu na ainihi. An kawo ra’ayin marubuci da sakamakon binciken da takardar ta
yi a ƙarshe.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda. Duba lambarsa a sama.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.