Wannan muƙala mai suna “Kwaɗayi Mabuɗin Wahala: Nazarin Kwartanci da Ayyukan Kwarto a Mahangar Makaɗa Ɗanladi Mai Kiɗin Kwartaye”, an bayyana wasu dalilai da ake ganin suna daga cikin abubuwan da ke haddasa wasu mutane yin kwartanci. An samo hujjojin abin da aka faɗa daga waƙar kwartaye ta Ɗanladi. Dalilan da aka hango da ke sanya wasu mutane zama kwartaye sun haɗa da kwaɗayi da gado da kasancewar mutum hariji da yin abota da kwarto da mallakar magani da sauransu kamar yadda aka ciro daga waƙar kwartaye ta makaɗa Ɗanladi. Haka kuma an bayyana wasu ayyukan da kwartaye ke aikatawa da suka haɗa da kwartanci da gudu da fasa darni da neman magani da neman matan maƙwabta da sauransu. An yi hira da wasu mutane da dama da ba a ambaci sunayensu ba da sunayen garuruwan da suke domin guje wa ta-da-zaune-tsaye, domin idan aka ba da bayanin wani ta hanyar ambatar sunan wanda aka yi hira da shi, zai ga an ci mutuncinsa. Domin guje wa hakan aka sakaya sunayen waɗanda aka yi hira da su da sunayen garuruwan da suke. An kawo abubuwan da muƙalar ta hango a matsayin sakamakon bincike da shawarwarin da ake ganin za su taimaka wajen rage matsalar kwartaye da kwartanci
Muhimman Kalmomi: Kwaɗayi; Kwartanci; Kwarto; Kwartaye
Kwaɗayi
Mabuɗin Wahala: Nazarin Kwartanci Da Ayyukan Kwarto A Mahangar Ɗanladi Mai Kiɗin
Kwartaye
Bello Bala Usman
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
08027459617
And
Dano Balarabe Bunza
Department
of Nigerian Languages
Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto.
07035141980
1.0
Gabatarwa
Masana
da manazarta da suka feɗe biri har wutsiya a harakar waƙoƙin baka na da yawa.
Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Gusau, S.M. (1988) da Abba da Zulyadaini (2000)
da Bunza A.M. (2009) da sauransu. Kiɗin kwartaye kiɗin tonon silili ne da ake
yi wa wanda asirinsa ya tonu a lokacin da ya tafi wajen aikinsa na neman matan
wasu mutane, a garin da yake ko a wani gari. Kiɗin kwartaye kiɗin kunya ne da
ake yi wa makunyatan da abin kunya ba ya ba su kunya. Kiɗi ne da ake yi wa
wanda aka kama ko aka tayar a gidan da ba nasa ba, da niyyar neman matar wani
domin ya yi lalata da ita. Babu magidancin da ke murnar wani mutum ya yi wa
matarsa kwartanci ko da kuwa shi kwarto ne. Kiɗan da ake yi wa kwartaye ba da ra’ayinsu
ba ne. Wannan ke sanya kwarto ba makaɗi komai domin kar ya kaɗa masa gangar
kunya. Idan dai yadda ake so bai samu ba, tilas a yi haƙuri da abin da aka samu.
Kwarto da ayyukansa duk abin ƙyama ne ga kowace al’umma. Takardar za ta kawo
bayanin abubuwa da dama da suka shafi kwarto da ayyukansa da suka haɗa da dalilan
da ke haddasa yin kwartanci da ayyukan kwarto kamar yadda muka hango a cikin waƙar
makaɗa Ɗanladi mai kiɗin kwartaye. Za mu kuma yi amfani da hirarrakin da muka
yi da waɗansu mutane sai dai, ba za mu ambaci sunan waɗanda muka yi hira da su ba,
da na kwartayen da muka sami labari daga hirar da muka yi da su ba. Za mu kafa
hujjoji da ɗiyan waƙar Ɗanladi waɗanda ya rera wa kwartayen da ya ambaci
sunayensu a cikin waƙarsa.
2.0 Dalilan Bincike
Kowane
bincike na da dalilin da ya sanya aka yi shi sai dai, dalilin ya kasance mai
karɓuwa ko raunana. Dalilin aiwatar da wannan bincike shi ne, ba mu sami
takardar da ta kalli kwarto da kwartanci ta fuskar nazarin waƙar kwartaye ta Ɗanladi
ba, face ta Aliyu Muhammad Bunza. Shi ma Aliyu ba waƙar ya nazarta ba domin ya
yi amfani da ɗiyan waƙar kwartaye uku kacal a cikin takardarsa sai kuma ratayen
waƙar da ya kawo. Hasali ma, taken takardarsa shi ne: Kwartanci: (Fashin Baƙinsa,
Mafarinsa da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin Bahaushe). Ita kuma takardarmu
ta kalli kwarto da kwartanci yadda makaɗin ya fito da su a cikin waƙarsa ta
hanyar kafa hujja da ɗiyan waƙar. Ƙarin da aka samu shi ne hirarrakin da muka
yi da wasu mutane a kan kwarto da ayyukansa kuma, ya sanya armashi a takardar.
Na biyu shi ne, makaɗin ya rasu, waƙar na a kan hanyar ɓacewa kai tsaye ko kuma
a rasa samun wanda ya yi tunanin rubutu a kan kwarto da kwartanci. An yi wannan
bincike domin ciyar da al’amarin adabi gaba da masu tasowan da ba su san kwarto
ba, balle kwartanci. A fahimtarmu idan aka yi bayanin kwarto da kwartanci a
rubuce, wanda bai san shi ba idan ya karanta zai fahimta.
3.0 Dabarun Bincike
A
cikin kowane bincike akan sami dabarar da aka yi amfani da ita, ko a faɗa ko
kar a faɗa. A lokacin rubuta wannan takarda mun yi amfani da dabarun binciken
da suka haɗa da sauraro da nazarin waƙar da kuma bincike a ɗakunan karatu tare
da yin hira da masana fannin adabi da al’adun Hausawa. Sai dai kuma, ba mu sami
aikin da aka yi kacokan a kan kwartanci ba, balle nazarin waƙar kwartaye ta Ɗanladi.
Haka ba mu sami kwarton da ya ba da haɗin kai domin a yi hira da shi ba, face
waɗanda suka san abin da ya faru dangane da kwartanci a gabansu. Wannan na da
alaƙa da kasancewarsu cikin garuruwan da tashin-tashinar kwartanci ta faru a
gaban idonsu.
4.0 Hanyar Bincike
Hanyar
da aka aza wannan bincike a kai ita ce karin maganar Hausawa da ke cewa “Kwaɗayi
mabuɗin wahala”. Takardar ta lura da duk rayuwar kwarto a ɓangaren kwartanci
wahala ce da babu ranar hutu face an daina. An lura daga gudu sai gudun ceton
rai kwarto ke fama da shi bayan barazanar halakarwa da yake fuskanta daga
al’ummar da yake taɓa matansu. Idan ba ya da rabon mutuwa, zai sha kasha tamkar
damen dawa na ƙarshe da aka fitar a cikin rumbu.
5.0 Kwarto
Masana
sun bayyana wanda ake kira kwarto a cikin rubuce-rubucensu gwargwadon hali. Ga
bayanin wanda ake kira kwarto kamar haka:
A ganin wasu masana kwarto na nufin mutumin da
yake neman matar wani (CNHN, 2006:267).
Aliyu
Muhammadu Bunza cewa ya yi, kwarto shi ne wanda yake da aure, kuma ya yi hulɗar
ɓatanci da matar aure a cikin takardarsa, (Kwartanci: Fashin Baƙinsa, Mafarinsa
da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin Bahaushe).
A
fahimtarmu duk bayanan da suka gabata sun yi wa ma’anar kwarto susa gurbin ƙaiƙai
kuma, sun wadatar da mai neman ma’anar kwarto. Tare da haka muna da ra’ayin
cewa kwarto na nufin mutumin da ya yi ko ke hulɗa da mata/matan wasu ta hanyar
saduwa cikin ɓoyo/sirri ba tare da buƙatar sanin kowa ba. Aliyu Muhammadu Bunza
ya bayyana cewa babu mace kwartuwa domin mai zuwa ake ba suna ba wanda ake je wa
ba. A tunanin takardar wannan a da ne kuma a al’adance, ba kamar yau da aka waye
ba, inda wasu matan aure ke kai kansu a gidajen wasu maza domin a yi hulɗar kwartanci
da su. Idan a da namiji ke zuwa wurin mace shi ya tabbatar masa da sunan
kwarto, to yanzu kuma da mace ke kai kanta wurin namiji kuma duk domin buƙata
iri ɗaya, me zai hana a kira ta kwartuwa ko kwartanya?
6.0 Kwartanci
Kamar
yadda masana suka bayyana ma’anar kwarto, haka sun bayyana kwartanci kamar
haka:
A
wani wuri cewa aka yi, kwartanci na nufin neman matar wani (CNHN, 2006: 267). Shi
kuma wani cewa ya yi kwartanci na nufin immorality
between adults (zina). Haka kuma ya bayyana cewa kwarto na nufin 1. Aprofligate, immoral p., a paramour. (Bargery).
Har
yanzu an sami wani masanin al’adar Hausawa ya bayyana ma’anar kwartanci da
cewa, hulɗar soyayya tsakanin mace mai aure da wani namiji ma’auraci ko yana
tare da matarsa ko sun rabu sunan namijin kwarto. Sunan wannan soyayyar ko da ɓatanci
bai bayyana ba, aka kama su, sunanta “kwartanci”. A al’adar Bahaushe, da an yi
aure an katangance ango da amarya. Hulɗa da wani miji da ba nata ba, ko hulɗa
da wata matar aure da ba tasa ba, shi ne kwartanci. Wanda duk aka samu cikin
wannan ƙazanta sunansa kwarto.
A
fahimtarmu, kwartanci na nufin zuwan wani namiji ga matar da ba tasa ba a cikin
gidanta ko gidansa ko wani wuri da amincewar juna domin yin lalata tsakaninsu.
Bayan haka ana iya cewa, kwartanci shi ne haɗuwar mijin wata da matar wani a
kan wata yarjejeniyar biya wa juna buƙata kuma, akan sami hakan ko ba tare da
yarjejeniya ba a wasu lokuta. Je wa mace ba tare da yin yarjejeniya da ita ba,
shi ake kira shige. A taƙaice, kwartanci shi ne hulɗar fasiƙanci tsakanin wani
mijin aure da matar auren da ba matarsa ba da saninta ko ba tare da saninta ba,
an gan su ko ba a gan su ba.
7.0 Taƙaitaccen Tarihin
Makaɗa Ɗanladi
Ba
a sami tarihin makaɗa Ɗanladi ba domin ba a taɓa aikin bincike a kansa ba a
matakin digiri na farko ko na biyu ba balle na uku. Haka kuma ba a sami wani aikin
NCE da aka gudanar a kansa ba. Abin da aka sani game da shi kawai shi ne abin
da ya ambata a cikin waƙarsa ta kwartaye. Ba a san waƙarsa ba sai da baya-bayan
nan kuma, manazarta ba su ahama da yin rubutu a kan waƙar kwartaye ba sai da
baya-bayan nan. Abin da aka sani dangane da shi kawai shi ne, mutumin ƙasar
Neja ne kamar yadda ya ambata a cikin wani ɗan waƙarsa kamar haka:
Bari in koma ƙasarmu
in mai da bilata dai,
Garba sana’a na
Salka bai bak kasada ba,
Kasuwad daji Garba
yay yi gaba da Hilani,
……………………………………………
A
cikin ɗan waƙar da aka kawo a sama, makaɗin ya faɗi cewa, a bari ya koma ƙasarsu
ya faɗi wani abu dangane da wani kwarto mai suna Garba Sana’a na Salka. Garin Salka
na cikin jihar Neja a yankin Kwantagora. Yana can gaban garin Nasko idan an
fito daga Yawuri. An ƙuduri a haɗu da makaɗin domin yin hira da shi, sai aka
sami labarin ya rasu. Wannan shi ne ƙarshen tarihin da aka samu na makaɗa Ɗanladi
mai kiɗin kwartaye a taƙaice.
8.0 Dalilan Da Ke Haddasa Yin Kwartanci
Ko
a hankalin tuwo bai dace a yi tunanin faruwar abu ba tare da dalili ba. Idan
aka sami mutum na sata (ɓarawo ne) tilas a sami sanadin kasancewarsa ɓarawo.
Hausawa dai cewa suka yi “Ruwa ba ya tsami banza”. Ma’ana, ba a san ruwa da wani
ɗanɗano ba. Idan aka ji su da wani ɗanɗano akwai abin da ya faru gare su. Haka
idan aka tarar mutum maye ne ko mai yin fashi ya ƙwace kayan mutane ko ma wane
iri, tilas a sami dalilin kasancewarsa hakan. A kan haka ne takardar ta duƙufa
don gano dalilan da ke haddasa mutum ya kasance kwarto har ya yi kwartanci. Ba
shakka an sami wasu dalilai daga bakin Ɗanladi a cikin waƙarsa da ya kawo wasu
dalilai da takardar ta yanke hukuncin cewa su ne suka yi sanadin kasancewar
kwarto da wannan aiki. Ga dalilan kamar haka:
8.1 Kwaɗayi
Kwaɗayi
na nufin tsananin son wani abu, musamman abin da za a ci ko za a sha, wanda
mutum bai mallaka ba. Haka kuma yana nufin sha’awar ci ko shan wani abu. Bayan
wannan an ce kwaɗayi na nufin son karɓar wani abu cikin sauƙi a wajen mutane (Ƙamusaun
Hausa, 2006:260).
Makaɗin
kwartaye ma ya bayyana abin da ake nufi da kwaɗayi a cikin wani ɗan waƙarsa
inda ya ce:
Shekaranjiya Kawoje yag
ganan yay yi kira na nit tai,
Yarinya tai madaddake ta
yi magarzai,
Kuma ga dogon wuya kamat
ta yi ma kanta,
Ta sa lallen ga nata
daidai da idon swai,
Kitson kiliya ag ga kanta
mai jehwa mazaje,
Alhaji Mamman da yag gani yaɗ ɗahwa rainai,
Ya ce min dalumag ga ab ba ta wuce shi,
Lahira in ya tai matambayan nan su kashe shi.
Idan aka yi la’akari da layuka uku na ƙarshen ɗan waƙar da aka
kawo a sama, makaɗin ya bayyana abin da ake nufi da kwaɗayi a fahimtarsa a kuma
fahimci abin cikin sauƙi. Ya ce mutum ya ga abu ya ɗahwa (sanya ransa gare shi)
kuma ta kowace hanya sai ya sami abin daga baya duk abin da ke faruwa gare shi
ya faru. Haƙiƙa wannan shi ne kwaɗayi. Wannan yasanya Hausawa faɗar “Ƙuda wajen
kwaɗayi aka mutuwa”.
A
fahimtarmu kwaɗayi na nufin tsananin buƙatar wani abu a rayuwa da mutum bai
mallaka ba da ƙoƙarin ganin ya same shi ta kowane hali. Ana iya cewa, kwaɗayi
na nufin ƙallafa rai (Ɗahwa rai) ga abin da ba a mallaka ba da nufin a same shi
ta kowane hali. Abin na iya kasancewa abinci ko abin sha ko wata ƙawar duniya
da Sheɗan ya ƙawatar da zukatan bil Adam da ita.
A
binciken da aka yi an sami makaɗin kwartaye ya kira kwarto makwaɗaici a cikin
wasu ɗiyan waƙarsa. Wannan ya sa aka sanya wa takardar suna “Kwaɗayi Mabuɗin
Wahala”. Hausawa sun ce “Idan da kwaɗayi da wulaƙanci”. Makaɗin da kansa ya
kira su makwaɗaita a cikin waƙarsa, duk da yake shi ma makwaɗaicin ne. Ga wuraren
da ya kira kansu makwaɗaita:
Ina sarkin raɓe-raɓe kwarto makwaɗaici?
Kwarto mai shan jinin jikinai ya bi darni.
Allah hi kiyaye,
To ko can sai sha biyun dare za ta rabawa
zak kyau,
Yakin in sa kiɗin mazana makwaɗaita
An ce min ɗan alaru ya
kai makwaɗaici Audi,
To bari in tai buhuhuwa
can in hwake su,
Ana son a yi ɗandako
mutane na ƙiya min,
An ce Sarkin alaru ya
rataya darni.
Shekaranjiya Kawoje yag ganan
yay yi kira na nit tai,
Yarinya tai madaddake ta
yi magarzai,
Kuma ga dogon wuya kamat
ta yi ma kanta,
Ta sa lallen ga nata
daidai da idon swai,
Kitson kiliya ag ga kanta
mai jehwa mazaje,
Alhaji Mamman da yag gani
yaɗ ɗahwa rainai,
Ya ce min dalumag ga ab
ba ta wuce shi,
Lahira in ya tai
matambayan nan su kashe shi.
Ɗanladi
ya kira kwarto makwaɗaici kuma, shi ne makaɗinsu. Ya san su domin mutanensa ne.
Hasali shi ma kwarto ne. A taƙaice, ya san kansa kuma ya san waɗanda yake tare
da su. Idan aka lura kwaɗai da ɗahwa rai ga abu, duk ɗaya ne. Kwaɗayi irin na
Audi ya kai gaya saboda ya amince wa kansa komai zai same shi ya same shi idan
dai ya cim ma buƙatarsa ga dalumad da makaɗin ya siffanta. Mutum ya amince wa
kansa halaka a lahira saboda wani abin duniya, ba shakka kwaɗayi ne kuma wanda ya
kai gaya.
8.2 Ɗan Burgu/Gafiya Bai Rasa Farin Bindi
(Gado)
Gado
na nufin muƙami ko hali ko sifa ko kaya da mutum ya gada (Ƙamusun Hausa,
2006:149). A fahimtarmu, gado a nan na nufin a sami mutum ya ɗauko hali ko ɗabi’a
ko aikin da wani ko wasu daga cikin iyayensa ko kakanninsa ke aikatawa, har
idan aka gani a fahimci halin ya samo shi daga gare su. Wannan ya sa Hausawa
suka ce “Gado ba ya wofinta”. Ma’ana tilas a sami wani ya ɗauko halin wani daga
cikin iyaye ko kakanninsa. Wannan ya sanya Hausawa faɗar “Kyawon ɗan ƙwarai ya
gadi ubansa”. Wannan ya sanya muka yi wa kan labarin suna ‘Ɗan burgu ba ya rasa
farin bindi’. Idan akwai kaka ko uba da ke wata ɗabi’a mai kyau ko akasinta, aka
sami daga cikin ‘ya’ya ko jikokinsa/ta wani ya tashi da ita kuma yana aikatawa,
ba shakka gado ya tabbata. Dangane da wannan ba sai an je nesa ba domin makaɗin
ya faɗi cewa yana da wani tsoho (mahaifi) a gidansu da ya tsufa yana kwartanci
bai daina ba. Haka kuma ya nuna ya sha jan hankalin tsohon ya rage ko ya bari
baki ɗaya domin kar ya bar musu abin faɗi/faɗe. Amsar da tsohon ya ba shi ita ce,
abin da duk za a yi musu faɗe da shi sai dai ya kashe su, ba zai bar wannan
jaraba ba. A sanadiyyar gado sai aka sami ɗan (Ɗanladi) ya yi aron hannu (ya
gadi) ɗabi’ar kwartanci daga wannan tsoho. Wannan shi ya sa aka ce ɗan burgu ba
ya rasa farin bindi/wutsiya. Ga wuraren da hoton gado ya fito a cikin waƙar
kuma, shi abin ya shafa kai tsaye ba wani ba. Dangane da haka ga abin da ya ce:
Daɗa yaƙi ya ci gwamna
‘yan soja a watsu daji,
Ganga ta ci mai gari ta
ci talakka,
Kiɗi daɗa ya ɓaci tunda ya kai ga su baba.
Akwai wani tsoho gare ni bai bak kasada ba,
Kullum nit tai gida ina
zai masa horo,
Baba baƙin kwaɗan ga na so ka rage shi,
Yac ce, tai taka haraka
ni in yi tawa,
Ka san horonka bai hana
min jarabag ga,
Tsoho in kam mace ɗumi mu aka wa shi,
Sai yac ce min yawan ɗumin nan shi kashe mu.
Daɗa tsoho na zaton kiɗin ba ni buga mai shi,
Da nic ce kasa kunnuwanka
in ba ka tahwashenka,
Lalle bana ban hana ma tsoho ya ji ganga,
To baba ka sha kiɗinka don ɗanka ka yi nai.
Yarinya ta da tay yi
laihi ga mijinta,
An ce tsoho maji kira zo tahi bikon ta,
Baba da yash shigo dawa yac cire wandonai,
Ko da ta waiwayo dawa ya
zube wando ƙasa,
To sun sha kewayal labaye
da ƙahwahu,
Ai babban azzikinta sayyu
na tare shi,
Da niz zo can inda yai
gudun anka gwada min,
Jama’a swan baba gun labu ba hi ɓacewa,
Mata kwalhen ruwa sukai
nan bisa swan nan.
Idan
aka duba Ɗanladi ya yi amfani da kalmar tsoho da baba a wuri goma sha ɗaya a
cikin ɗiyan waƙar da aka kawo a sama. Babu kwarton da ya kira baba in ba wannan
ba don haka, wannan ya nuna mahaifinsa ne ba wai tsufar haihuwarsa ko yawan
shekaru kaɗai ba. Haka kuma ko makaɗa ya fi shi shekaru yana zama ɗansa saboda
dangantakar da ke tsakaninsu. Idan aka dubi ɗan waƙa na biyu da na uku da aka
kawo a sama za a fahimci haihuwar gaske ce ke tsakanin Ɗanladi da tsohon. A taƙaice,
makaɗa ya yanke hukuncin ana gadon kwartanci daga iyaye kamar yadda ya tabbatar
a cikin ɗiyan waƙar da ke sama. Bayan haka, daga cikin kwartaye talatin da biyu
da Ɗanladi ya ambata a cikin waƙarsa babu wanda ya kira baba/tsoho sai wannan
tsoho kurum. Wannan ya nuna gado na ɗaya daga cikin dalilan da ke sanya a sami
mutum ya zama kwarto kai tsaye.
8.3 Harijanci
Hariji
shi ne mutum namiji mai tsananin jarabar son saduwa da mata. Ita kuma harija,
ita ce matar da ke da tsananin jarabar son saduwa da namiji (Ƙamusun Hausa,
2006:197).
A
fahimtarmu, hariji shi ne mutumin da Allah ya jaraba da ƙarfin yi da yawan son
jima’i da kuma ƙoƙarin yin sa kuma wannan daga jini ne ba ta hanyar shan wani
magani don aiwatar da hakan ba. A taƙaice hariji shi ne wanda mace ba ta gane kasawarsa
a wurin jima’i. Ita ma mace wadda aka halitta da wannan haka take.
A cikin waƙar Ɗanladi an
sami wurin da ya ambaci wani da sifanta shi da zama hariji a cikin wasu ɗiyan waƙarsa.
Ga abin da ya ce:
To bari dai in kiɗa ma
sarkin majarauta duka,
Kwamandan ‘yan nema ko
tawa ba hi ragawa,
Bari in koma ƙasag gabas
inda Namanke,
Na Nabara anne na Bawa
kura a ci wawai,
Jan anne ya biya ni
jingaj jarabatai,
Ya sai doki da keke ya ba
ni Namakau.
Ga shi mata huɗu ag gare
shi bai baj jaraba ba,
Mata huɗu ba isan Namakau
suka yi ba,
Wai dub bakin karin
kumallo ya aje su.
Tun farko makaɗin ya ba kwarton sarauta ko shugaban kwartaye
na zama kwamanda. A layi na biyu ya ce matar kowa ba ya bari idan ya samu. A ɗan
waƙa na biyu ya bayyana cewa mata huɗu mutumin ke da amma ba su hana shi neman
wasu mata ba ta hanyar kwartanci. Ma’ana, duk matan huɗu ba su isarsa ko gamsar
da shi, hasali ma a matsayin karin kumallo ya aje su. Idan haka ne, ina na rana
da na dare? Harijanci halitta ce, ba girman jiki ba ne ko rashinsa. A nan makaɗin
ya bayyana mutumin da cewa hariji ne musamman idan aka yi la’akari da ma’anonin
da aka bayyana a sama.
8.4
Zama da Maɗaukin Kanwa (Abota da Kwarto)
Akwai
abotakar kusa da ta nesa cikin sha’anin zamantakewar yau da kullum tsakanin mutane
‘yan ƙabila ɗaya ko akasin haka. Sanin sirrin zamantakewa tsakanin mutane ya sa
Hausawa suka ce “Zama da maɗaukki kanwa ke sa farin kai”. Su kuma Hausawa faɗa
kaɗai suka yi ba maganarsu ba ce. Wannan zance daga Annabin rahama ya samo
asali a inda ya ce “Ɗabi’a na satar ɗabi’a”. Abin nufi a nan shi ne, matuƙar
mutum biyu na zaune tare, tilas ɗabi’ar ɗayansu ta yi tasiri a kan ta ɗaya.
Wannan ya ƙara sanya Hausawa faɗar cewa “Abokin cin mushe ba a ɓoye masa wuƙa”
Dangane da wannan maganar babu tantama domin an sheda ba ɗaya ba, ba kuma biyu
ba. Mai abota da mai shaye-shaye ƙarshensa ya zama ɗan ƙwaya. Abokin ɓarawo, ɓarawo
ne inji Hausawa. Idan aka sami abota tsakanin mutane babu shakka akwai wani
al’amarin da suke gudanarwa tare mai kyau ko akasinsa. Bayan haka, Hausawa sun ƙara
da cewa “In hali bai zan ɗaya ba ba a yawo tare”. A taƙaice abin nufi a nan shi
ne, abota da kwarto na daga cikin dalilan da ke sanya aboki ya ɗauki ɗabi’ar
kwartanci ya ci gaba da yi. Ana ɗaukar ɗabi’un ƙwarai daga abokai kamar yadda
ake ɗaukar waɗanda ba na ƙwarai ba. A hirar da na yi da wani ya gaya min cewa
aboki na farko kwarto ne. Na biyu ba kwarto ba ne. Yau da gobe har kwarton ya
janye ra’ayin abokinsa ya sanya shi cikin kwartanci. Wannan misali ne da ke
tabbatar da maganar zama da maɗauki kanwa shi ke sa farin kai. Ma’ana, duk mai ɗaukar
kanwa ba ya rasa fari a kansa, don haka wanda duk ya yi abota da shi, kansa zai
yi fari shi ma, domin zai taya shi ɗaukar ta wata rana. Sanadiyyar abota Allah
kaɗai ya san waɗanda suka ɗauki ɗabi’ar kwartanci, suka zama kwartaye. A taƙaice,
zama da kwarto ta hanyar abota na sanya aboki ya zama kwarto kamar abokinsa
musamman aiki ne na kunya da duk mai yin sa ya yi bankwana da kunya, ba ya jin ta,
ba ya gudun ta domin gonarsa ce dole ya nome ta. Allah ya kare mu.
8.5
Mallakar Magani
Magani
na nufin abin da ake sha ko shafawa a jiki ko ɗurawa a jini ta hanyar yin
allura, don neman samun lafiya. Haka kuma an ce magani na nufin abin da
samuwarsa ke kore wani abu daban. An ƙara da cewa, magani na nufin sammu, wato
harhaɗa wasu abubuwa da yin surƙulle da nufin cutar da wani, musamman abokin
gaba. Har wayau an ce magani shi ne harhaɗa ko yin wasu abubuwa don shawo kan
wani, ko samun galaba a kan wani abu (Ƙamusun Hausa, 2006:316). Irin maganin da
takardar ke magana kansa shi ne ma’anar ƙarshe da aka kawo ta Ƙamusun, wato
harhaɗa ko yin wasu abubuwa don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu.
Wannan ma’ana ta yi canjaras da maganin da kwartaye ke nema domin ganin sun
biya buƙatarsu da duk matar da suka ɗahwa ransu gare ta. Wannan dalili ya sanya
makaɗin ambatar wasu kwartaye haɗi da kansa a fagen neman magani da amfani da shi
ga ayyukansu na fasadi a bayan ƙasa. Ga abin da ya ce:
Ina Sanin Sani magani sai da gwadawa,
Daɗa Sani ka biya mawaƙin
makwaɗaita,
Da mai mata nab bige shi
yar rama bugunai,
Kuma an amshe zanenshi ya
amso zanenai,
Sani bai ɗaɗɗaka ba bai
kau da ƙahwatai ba,
Nic ce tai ka yi ɗam maza
hag ga uwaye.
Bari ni ma mai kiɗinsu
bam bak kasadab ba,
Bana na kwan Unashi can
anka tare ni,
Sauƙi don na ci baduhun kau da ido na,
In ba don na ci baduhun kau da ido ba,
Da ko am ba ni rai dubu na rasa raina,
Mai mata na bugun gado na tahiyata,
‘Yag gangata ta dauri can sunka kashe ta.
Akwai Mamman ɗan Amina
kura a ci wawai,
Mamman mai kankare
idanunka da kwalli,
Amina ki ja ɗanki kam maƙwauta
su kashe shi.
A
ɗiyan waƙa uku da aka kawo a sama makaɗin ya yi bayanin kwartanci ba ya yiwuwa
sai tare da magani, kuma maganin da aka tabbatar da aikinsa ba wanda ake tababa
ba. A ɗan waƙa na farko da aka kawo makaɗin ya yi wa wani kwarto kirari a kan
maganin da ya samu na yin buga in buga da mai mata ba tare da mutanen unguwa ko
gari sun kawo wa mai matar agaji ba. Zanen da mai matar ya karɓe hannunsa, ya
karɓi abinsa, duk a sanadiyyar tambayar (maganin) da yake da. Haka a ɗan waƙa
na biyu makaɗin ya nuna shi ma an taɓa rutse shi a cikin wani ɗaki, inda ya
bayyana cewa da ba ya da ba-duhu a wannan rana da kwanansa sun ƙare, ko da kuwa
rayukkansa sun kai dubu balle ɗaya ne. Idan ba aiki da magani ba, yaya mai mata
ke rutse kwarto cikin ɗakinsa kuma a ce ya fita lafiya? Wani aiki sai magani! Kamar
faɗar da aka yi a cikin wata ma’anar magani cewa, ana shafawa. Kwartaye na
amfani da kwalli/tozali ta hanyar haɗa magani mai suna idonki-idona. Wannan ya
sa ake kyautata zaton mutumin da ke amfani da tozali (kwalli) idan ba rashin
lafiyar idanu gare shi ba, a hukunta masa kasancewa kwarto, face idan ya yi
domin koyi da Manzon Allah (S.A.W.).
Mun
yi hira da wani mutum dangane da tabbacin ko kwartaye na neman magani?
Sanadiyyar haka ya ba ni labarin wani ma’aikacin gwamnati kuma kwarto da aka
kai wani gari aiki, sai ya gane matar wani. Da mutumin ya ji labari kuma ya
tabbatar da abin da ke faruwa, sai ya tafi ya nemo maganin da kullum yake buƙatar
matar ma’aikacin zai same ta. Idan ya je wajenta ya yi, idan bai je ba ita ke
kai kanta domin a yi da ita. Abin ya kai ko ƙaƙa, har mutumin ya faɗa wa
ma’aikacin cewa ai ba irinsa ake yi wa haka ba, don haka wallahi kullum sai ya hau
matar ma’aikacin matuƙar tana cikin garin. A ƙarshe, ma’aikacin ya gaji da
wannan ta’asa tilas ya mayar da matarsa wani gari domin ya raba ta da mutumin.
Me zai sa haka in ba magani ba? Za a kawo wasu misalai nan gaba a cikin ayyukan
kwarto danagane da neman magani domin wannan na cikin dalilan da ke sanya wasu
mutane yin kwartanci.
9.0 Ayyukan Kwarto
Ayyukan
kwarto na da bambanci da dalilan da ke haddasa yin kwartanci da aka yi bayani a
lamba ta 7.0 da sauran abubuwan da suka biyo bayansa. Duk da haka suna da alaƙa
saboda mutum ɗaya suka shafa. Misali, kwaɗayi na daga cikin dalilan da ke sanya
mutum ya zama kwarto sannan yana daga cikin halayen da aka san kwarto da shi da
wasu abubuwa da suka yi kama da hakan. A kan haka takardar ta hango akwai wasu
ayyukan da kwarto ke aikatawa kafin da kuma lokacin da ya je kwartanci kamar
yadda makaɗa Ɗanladi ya bayyana a cikin waƙarsa ta kwartaye sai dai, mafi yawan
ayyukan ba su bayyana sai a wurin kwartanci kamar yadda za a gani a cikin
bayanin da ke tafe .
9.1 Gudu
A wani wuri an ce gudu na nufin fyalle ko ruga (Ƙamusu Husa,
2006:171). A tamu fahimta gudu shi ne rugawa da hanzari saɓanin tafiya mai nuna
mai yin sa na cikin wani uzuri sanadiyyar faruwar wani abu da ya fi ƙarfin
tafiya sannu. Ba a yin gudu sai buƙatar yin sa ta kama. Babu shakka gudun da
kwartaye ke yi na uzuri ne da ceton rai. Duk kwarton da aka rutsa da shi har
aka kashe shi wajen kwartanci tamkar an kashe kare ne. Domin tabbatar da haka
ga abin da wani kwarto ya faɗa da bakinsa inji makaɗinsu kamar haka:
Barmu
mesin da yai gudu anka hwaɗa min bana,
Yuƙag
gina ga ƙyasuwa munka ishe ta,
Ka
dubi yawan kuwara ta kai ga cikewa,
Kaw
wani baƙon kada hi taso hi haye ka,
Yac
ce “Ba ta kada nikai ba in tcira da raina”.
Irin gudun da kwarto ke yi ba irin na kai ceto wurin da aka
yi gobara ba ne, ba ceton wasu mutane ba ne, gudun ceton rayuwarsa ne don kar a
kashe shi. Haka kuma duk lokacin da kwarto ya ruga da gudu, an tayar da shi ne
a wurin aikinsa na kwartanci. Idan ba a tayar da kwarto ba to, batun gudu bai
taso ba. Saboda haka gudu aikin kwarto ne da yake yi a kan tilas domin ya tsira
da rayuwarsa kar a kashe shi. Wannan ya sanya makaɗin faɗar:
Ashe kwac ci abin gudu
jiyoji ka biyanai,
Da duy yac ce bai gudu
jikinai ya hwaɗa mai,
In kag ga gudu da waiwaya
ce na ba’a na,
Gudu in ya ɓaci ko gida
ba a biyawa.
A fahimtar makaɗin duk kwarton da aka tayar ya ƙi gudu ya
amince da ya sha kashi tare da tonuwar asirinsa ko ma a kashe shi baki ɗaya. Ya
ƙara bayyana cewa, idan mutum na gudu yana waiwayar bayansa ba na rashin
gaskiya ba ne kuma, ba kwarto ba ne. Hasali ma idan aka biyo kwarto ba ya
waiwaya kuma ba ya shiga gidansa domin kar a kama shi. Yadda ɓarawo ke gudu
domin tsoron a kashe shi, haka kwarto ke yi domin duk gudun ceton rai ne suke
yi. Ga wani ɗan waƙa da makaɗin ya ce:
Wai kura ta yi lahiya
Daudu Madangyal,
Bari Daudu mutan Halala
nak kama wuyanai,
Ni ban aza Daudu na gudu
don wahala ba,
Sai ga hi sharaf-sharaf
da laka ga ɗuwayya.
Wani
kwarto ne mai suna Daudu Madangyal da mutanen garin da ake kira Halala suka
kama lokacin da ya je kwartanci a wani gida. Makaɗin bai zaci Daudu na gudu don
wahalar duka ba amma, da ya sha dukar da ta fi ƙarfinsa dole ya ara daga cikin
na kare. A lokacin da ya ji an fi ƙarfinsa sai ya yi shawarar rugawa da gudu
kar a kashe shi. Tare da haka shawarar gudu ba ta kama shi ba sai da ya sha
kashi, ana bugu yana faɗuwa ƙasa cikin laka sannan da ya fahimci babu sarki sai
Allah ya ce ƙafa mi na ci ban ba ki ba? Shi ma makaɗin da kansa ya bayyana cewa
an taɓa tare shi a wani gari mai suna Raha lokacin da ladan mai kiran salla na
assalatu amma, kafin mutane su tashi da safe su wanke ido ya kai garin Bena
saboda bala’in gudun da ya yi. Ga abin da ya faɗa da bakinsa ganin babu mai
gudun da ya fi kwarto. Ga ɗan waƙar duk da yake bayaninsa ya gabata a sama:
Garin Raha nis san gudun
kwarace da iyawa,
Ladan na assalatu sai
anka tare ni,
Ka diba sai ga ni Bena ba
a wanke ido ba.
Bayan haka akwai wani kwarto mai gudu sosai da an yi biyar sa
babu adadi ba a sami kama shi ba da makaɗin ya bayyana kamar haka:
Guntu na guntuwar kwana
ba a riƙe shi Yellow,
Jama’a guntun mutum hina
kyau bisa danni,
Yellow bana in kab buwaya karnai aka sa ma.
Bayanin
layin ƙarshe a ɗan waƙa na sama shi ne, an sha bin Yellow ba a kama shi a
shekarun da suka wuce. Don haka bana ko da ta kai a yi masa aji (A haɗa shi da
karnu domin a kama shi) sai an yi domin a ga cewa an kama an halaka shi. Mutum
ne mai gudu sosai da ba a taɓa kamawa a wurin aikinsa na kwartanci ba. A lura
sosai a nan cewa, gudun kwartaye ba irin na sauran mutane ba ne. Mun yi hira da
wani mutum, ya gaya muna cewa kwartaye na shan maganin da ke sa su yi gudu
sosai wanda idan suka shiga gaba, babu mai iya cim musu balle ya kama su. Daga
cikin abubuwan haɗa maganin gudu da kwartaye ke amfani da shi akwai shalla. Don
haka takardar na ganin Yellow na amfani da wannan magani har ya sa ya buwaya a ɓangaren
gudu inda mutane ba su iya kama shi, sai dai a sa masa karnuka. A gaida uban
gudu kwarto!
9.2 Fasa Darni
Darni na nufin shingen kara ko zana (Ƙamusun Hausa, 2006:99).
A wani wuri cewa aka yi darni/danni na nufin karan gero ko dawa ko maiwa da ake
tsarawa a gewaye gida (Aliyu Muhammadu Bunza, 2020 a cikin takardarsa mai taken
Kwartanci: Fashin Baƙinsa, Mafarinsa da Nauyinsa a Ma’aunin Al’ada da Adabin
Bahaushe). Duk ma’anonin da ke sama sun bayyana abin da ake nufi da darni/danni,
duk da haka a fahimtarmu darni shi ne tsarin gewaye gida ta hanyar amfani da
kara kuma mafi yawa karan gero ko na dawa ko duka ta hanyar yin killiya-killiya
(sashe-sashe) kafin a gewaye gida. Mafi yawan masu amfani da darni su ne manoma
da talakawa saboda rashin ƙarfi.
Fasa darni ko yakuce shi na daga cikin ayyukan kwarto kamar
yadda makaɗinsu ya ambata a cikin wasu ɗiyan waƙarsa kamar haka:
………………………………………
Don yanzu guda-guda ina
ba da mutane,
Kwartaye sun jima suna yaƙuce
danni.
Bana lisafi gida-gida
ukku yana nan,
Daɗa kowane yab biya
gidan ya hwashi danni,
Gidan Manu Tcirare yab
biya ya hwashi danni,
Gidan Malam Sani ya biya
ya hwashi danni,
Gidan Sarkin hwawa ya
biya ya hwashi danni,
Mugun ya ɗauko killiya
ukku ga bainai,
Hay ya iske Ɗanhaɗeja ya
take ƙahwatai.
Kwartaye na fasa darni a kan tilas ba da son rai ba. Hakan na
faruwa a lokacin da aka tayar da su cikin gidan wani lokacin da suka je kwartanci.
Idan aka tabbatar da suna cikin gida ko ɗaki, akan tsare hanyar fita gidan
domin a sami damar kama su. Kwarto ya tsani a kama shi don haka, ya zaɓi fasa
darni ya fita ba tare da ya bi hanyar shiga da fita gidan ba domin gudun a kama
shi. Idan ƙofar shiga gida na ɓangaren gabas da mutane suka fake idan ya zo a
kama shi, zai fashe darnin yamma domin ko an biyo shi akwai tazarar da da wuyan
gaske a kama shi saboda tsananin gudun da yake da kamar yadda aka bayyana a baya.
A ɗan waƙa na farko da aka kawo a zancen fasa darni makaɗin
ya bayyana cewa akwai kwartaye da dama da ke wannan aiki. Hasali ma, cewa ya yi
sun jima suna yakuce danni. A nan ana iya fahimtar cewa, duk wanda ya jima (daɗe)
yana yin abu, babu shakka aikinsa ne. Yakuce danni aikin kwartaye ne kamar
yadda takardar ta ciro daga bakin makaɗinsu a cikin ɗan waƙan da ke sama.
A ɗan waƙa na biyu kuma, makaɗin ya ba da labarin wani kwarto
da ya shiga gidaje uku lokaci ɗaya ta hanyar fashe wa masu gidajen danninsu.
Wannan ya faru sanadiyyar biyo shi da aka yi domin a kama shi. Babu abin da
kwarto ya tsana irin a kama shi hannu da hannu domin ya san makomarsa halaka ko
kashewa idan haka ta faru. A taƙaice fasa darni na daga cikin ayyukan kwartaye
na dole-uwar-na-ƙi da suke yi. Da yawa akan ga kussuwa ga sabo ko tsohon darni
a yi tsammanin dabbobi suka yi su don ɓarna amma kwartaye ne ba dabbobi ba.
Wani lokaci idan kwarto ya ga fasa darni na da wuya, sukan canza dabara su hau
killiya su ƙetare. Wannan ya sanya makaɗinsu faɗar cewa suna kyau bisa darni
kamar haka:
Guntu
na guntuwar kwana ba a riƙe shi Yellow,
Jama’a guntun mutum hina kyau bisa
danni,
Yellow
bana in kab buwaya karnai aka sa ma.
Layi na biyu da ke cikin ɗan
waƙa na sama na nufin bayan fasa darni da kwartaye ke yi, akwai dabarar hawa
darni a ƙetare musamman idan kwarto ya shiga rutsi.
9.3 Neman Matan Maƙwabta
Maƙwabci
shi ne mutumin da gidansa ko wajen zamansa yake kusa da na wani (Ƙamusun Hausa,
2006:327). Wannan ma’ana ta yi daidai da zancen da takardar ke yi domin, akwai
maƙwabtakar da kwarto ke yi da maƙwabtansa da ta shafi gida da wurin zama. A
nan, babu shakka kwartaye mutane ne marasa kunya da rashin jin tsoron Allah
dangane da cin amanar maƙwabtaka. Ana samu a cikin gida ɗaya wani ya nemi matar
wani ko a sami ya nemi matar maƙwabcinsa da lalata. Kai! Akwai wani mutum da ya
nemi matar ɗansa. Wannan maganar ba zaɓi-faɗi ba ce, makaɗin kwartayen ya faɗi
haka ga wani maras kunya kamar haka:
Akwai sheri Nabangu ya ja wata darga yap
pashe,
Auwal don ka jima kana cuta mutane,
To tsoho yo ma ɗanka aure ku ci tare,
Sai nic ce ka ga hurhure za ni gama ku,
Tai ka ci mai ƙurciya ka turo masa tsohhi,
Don mataɗ ɗanka ta hi matanka ɗuwayya,
Amma ci guminka kai kai wahalakka.
To! Ga wani uba saboda tsananin nisa cikin sha’anin kwartanci
har da sarukansa (Matan ɗansa) bai bari ba. Makaɗa ya faɗa cewa, mutumin ya yi
wa ɗansa aure amma, kowannensu na amfani da matar. Haba! Wannan rashin kunya da
rashin tsoron Allah har ina? Ba abin mamaki ba ne domin na yi hira da wani ya
gaya min cewa akwai irin wannan da ya taɓa faruwa a wani gari inda uba da ɗa
suna noma tare amma, ɗan yana da mata biyu kuma su ke kai musu abinci/abinsha a
daji. Idan ɗaya ta kai yau, gobe ɗayar ta kai. Daga cikin matan biyu ɗaya ta
amince uban ya yi amfani da ita, ɗayar kuma ta ƙi amincewa. Duk lokacin da suka
kawo abincin/abinsha (hurar) sai ya ce su tafi can bakin dutsi ya sama musu
iccen huri su koma da shi gida. Yau haka, gobe haka har ɗan ya fara zargin
akwai abin da ke faruwa. Wata rana wadda ke amincewa da uban ta kawo hura, suka
tafi wajen icce bakin dutsi. Jim kaɗan ɗan ya bi sawunsu. Isarsa ke da wuya sai
ya tarar da uban saman matarsa. Ganin haka ke da wuya sai ya juya ya koma gona
ya ci gaba da aikinsa. Ana komawa gida, ɗan ya gaya wa mahaifiyarsa abin da ya
faru kuma ya ce lallai ya bar wa uban matar har abada. Mutumin ya gaya muna cewa,
ɗan bai dawo ba tsawon lokaci sai da ya ji labarin uban ya mutu.
Wani ya ba mu labarin wani kwarto da ke neman matar wani ɗan
uwansa. Mutumin da ake neman matarsa basarke ne. Mai neman matar kuwa ba ya
neman matar sai ya tabbatar da mutumin ya tafi wurin kamun kifi. Ana nan wata
rana aka ba shi labari, ya ce babu komai a bari kawai. Har wurin da yake
kwanciya da matarsa an gaya masa. Wata rana ya fita zuwa wurin kamun kifi sai
matar ta fita zuwa wurin mutumin. Ana cikin haka kafin a jima ga mutumin ya komo
gida. Yana dawowa bai tarar da matarsa ba, ya san wurin da ta tafi. Da ma an
gaya masa wurin da suke sha’aninsu, bai tsaya ko’ina ba sai can yana riƙe da
mashi. Yana laɓaɓe har ya isa a kansu ba tare da saninsu ba, sai da ya kai gare
su kwarton ya kula da shi. Yana ƙoƙarin ya ruga sai mai matar ya nashe shi da
mashin. Nashinsa ke da wuya sai ya juyo ya komo gida, ya bar mutumin da mashi.
Daga wurin da aka nashi mutumin da mashi har cikin ɗakin matarsa jini ke zuba. Kafin
ya shigo gari ya karya gorar mashin, ya shigo da ƙarfen mashin jini na tsiyaya.
Matarsa na ganin haka sai ta tafi ta gaya wa ‘yan uwansa. Suka zo suka gani,
suka tambaye shi wanda ya yi masa wannan karen aiki, sai ya ce ɗan uwansa ne.
Ana cikin haka sai mutumin da aka nasa wa mashi ya ce ga garinku. Aka yi ta
shari’a daga ƙarshe aka raba wannan darga saboda akwai ɗan uwantaka kuma,
mamacin ba ya da gaskiya. Duk da haka har yau gabar wannan abu na tsakanin ‘yan
uwan wanda aka nasa da mashi da na wanda ya yi nashin. Haka kuma makaɗin ya
ambaci wani kwarto da ke neman matan maƙwabtansa kamar haka:
Akwai Mamman ɗan Amina
kura a ci wawai,
Mamman mai kankare
idanunka da kwalli,
Amina ki ja ɗanki kam maƙwauta
su kashe shi,
A
cikin ɗan waƙar makaɗin ya ambaci sunan kwarton da mahaifiyarsa tare da ba ta
shawarar ta hana ɗanta aikin da yake yi kar maƙwabta su kashe shi. Wannan ya
tabbatar da cewa, akwai kwartayen da ke neman matan maƙwabtansu da lalata. Wasu
ma har na ‘yan uwa suke nema a cikin gida ɗaya. Don haka neman matan maƙwabta
na ɗaya daga cikin ayyukan kwartaye da takardar ta hango a cikin waƙarsu. Ba
wannan kaɗai ba, dangane da haka akwai haddasa mugun zama tsakanin ‘yan uwa da
kwartaye ke yi. Allah ya kare mu ya kare muna.
9.5 Neman Magani
An bayyana ma’anar magani a lamba ta 7.4 mai taken “Mallakar
Tambaya (Magani)” a cikin dalilan da ke sanya mutum ya zama kwarto. Kwartanci
aiki ne da ba ya yiwuwa sai tare da mallakar magani don haka, neman magani na
cikin ayyukan da kwartaye ke fara yi kafin su fita fage a san su. Ƙaryar kwarton
da duk aka kama yana kwartanci ta ƙare, ta hanyar yi masa mummunan duka ko
kashi ke sanya kwartaye neman magani. Daga cikin magungunan da kwartaye suka
shahara da nema sun haɗa da ba-duhu da na gudu da ba-sanyi da idonki-idona da
sauran irinsu. Tilas kwarto ya nemi maganin shiga da fice da yake yi a ɗakunan
wasu magidanta domin, ko ba komai ya san da ana haƙon sa. Ba wannan kaɗai ba,
idan birinsa ya yi kuren reshe, aka kama shi sai wani ba shi ba. Makaɗin
kwartaye ya san da kwartanci ba ya yiwuwa sai da tanadar magani domin, shiga
kwartanci babu magani tallar rai ne. Haka kuma, maganar da ya faɗa cewa, magani
sai da gwadawa gaskiya ce domin, Hausawa ma cewa suka yi “Sai an gwada akan san
na ƙwarai”. Wannan ya sa makaɗin faɗar cewa:
Ina Sanin Sani magani sai
da gwadawa,
Daɗa Sani ka biya mawaƙin
makwaɗaita,
Da mai mata nab bige shi
yar rama bugunai,
Kuma an amshe zanenshi ya
amso zanenai,
Sani bai ɗaɗɗaka ba bai
kau da ƙahwatai ba,
Nic ce tai ka yi ɗam maza
hag ga uwaye.
A cikin ɗan waƙar da ke sama, makaɗin ya jinjina wa wani
tauraronsa saboda ya nemo magani har ya je gidan wani ya gwada ingancin maganin
inda maigida ya buge shi, shi kuma ya rama. An karɓe zanen da ya je da shi
wajen kwartanci amma, bai bar zanen can ba sai da ya karɓi abinsa. Wannan ya
nuna neman magani na daga cikin ayyukan kwartaye kamar yadda bayani ya tabbatar
dangane da ɗan waƙar da aka kafa hujja da shi daga waƙar kwartaye. Bayan haka
akwai iza mai kantu ruwa da makaɗin ya yi wa tauraronsa a inda ya ce “Tai ka yi
ɗam maza har ga uwaye” dommin idan duka ne ko kashi, kwarton ake yi wa ba makaɗin
ba. Ga kuma wata hujja da ta tabbatar da neman magani na daga cikin ayyukan
kwartaye kamar haka:
Bari
ni ma mai kiɗinsu bam bak kasadab ba,
Bana na kwan Unashi can
anka tare ni,
Sauƙi don na ci baduhun
kau da ido na,
In ba don na ci ba-duhun
kau da ido ba,
Da ko am ba ni rai dubu
na rasa raina,
Mai mata na bugun gado na
tahiyata,
‘Yag gangata ta dauri can
sunka kashe ta.
A cikin ɗan waƙar da aka kawo makaɗin ya tabbatar da shi ma
kwarto ne kuma, ya nemi magani domin aikinsa aikin tallan rai ne. Ya ce wata
rana ya kwana garin Unashi inda ya tafi kwartanci wani gida aka rutse shi cikin
ɗaki. Yana cikin ɗaki maigida ya tarar da shi bisa gadonsa kwance, kai tsaye
maigida ya ci gaba da bugu tsammaninsa kwarton yake bugu. Shi kuma kwarton ya
riga ya fita ɗakin, ya bar mai mata na bugun gado domin yana da maganin ba-duhu.
Idan bai nemi maganin ba yana samun sa? Kwarton ya faɗa da bakinsa cewa, in ba
domin ya ci ba-duhun ba da ko rai dubu gare shi da ya mutu a ranar. Domin
rainin wayo har da gangarsa ya tafi da ita cikin ɗaki wajen kwartanci. Duk da
ba a sami sa’ar kashe shi ba, an kashe gangarsa da ya bari a ɗakin. To, da ba
ya da ba-duhun fa? Wannan kaɗai na tabbatar da kwartaye na neman magani kamar
yadda bayani ya tabbatar a sama. Haka kuma, mun yi hira da wani a kan neman
magungunan da kwartaye ke yi inda ya gaya muna, dole ne su nemi magani domin
aikin tallan rai suke ciki kuma, sun san da zarar sun shiga hannu sai dai idan
da kwana gaba. Ya ƙara da cewa, akwai wani kwarto ba ya zuwa kwartanci sai
gidan mutumin da ke bugun gaba da babu kwarton da ya isa ya yi masa kwartanci
cikin gida. Shi kuma ya fi son irinsu, ya zo ya gaya maka da bakinsa cewa yana
nan tafe gidanka rana kaza kuma lokaci kaza. Mutumin ya ce ko mutum na kwance da
matarsa kwarton na zuwa ya yi amfani da ita ya wuce saboda samun baƙar tambaya
(Magani). Irin wannan maganinsa mugu ne domin, an ce da zarar ya taɓi mutum shi
ke nan sai ya kama kwana ba tare da ya san inda yake ba, ko an tada shi ba ya
iya tashi. A nan, mun zaci maganin ba-sanyi ke gare shi. Idan ba a nemi magani
ba ba a samun sa. Gaskiyar Hausawa da ke cewa “Mai nema yana tare da samu”.
9.5 Neman Mafaka (Wurin Ɓuya)
Kwartaye
na neman wurin fakewa idan aka tayar/koro da su a wurin kwartanci. Duk wanda
aka kama ƙaryarsa ta ƙare. Wanda aka tayar aka biyo shi ba a cim masa aka kama
shi ba, shi ke neman mafaka (Wurin ɓuya) domin ba ya zuwa gidansa kai tsaye.
Wannan ya faru domin gudun a gane shi/ko a waye da shi, duk da ai ana fahimtar/gane
wanda aka tayar domin zamantakewarsu da jama’a. A cikin waƙar makaɗin ya sha faɗin
an koro wane ya laɓe (Tsuguna) gindin ƙyasuwa ko a masussuki kuma sauro na
cizon sa babu halin korewa don gudun asirinsa ya tonu a gane wurin da ya laɓe.
Domin tabbatar da wannan magana ga abin da makaɗin ya ce dangane da neman
mafakar da wani mai shari’a ya yi cikin wani ɗan waƙa:
Shari’a ta anka sa ka ba
banye zane ba,
Ga shari’a ta tashi ban
ga kundin shara’atai ba,
Sai nac ce gobe kotu can
za ni da gangata,
Ga Alƙali ga ƙyasuwa ya
yi tsugunne,
Ga shi sauro na cin shi
babu halin ya bige shi.
A cikin ɗan waƙar da ke sama makaɗin ya tabbatar da kwartaye
na neman wurin da suka laɓe idan an koro su daga wurin kwantanci kamar yadda ta
faru ga wani alƙali, inda ya nuna alƙali ya sami ƙyasuwa ya tsuguna ƙarƙashinta
domin kar waɗanda suka biyo shi su gan shi. Dalilin da ya sa makaɗa na yawan
kawo ƙyasuwa a matsayin wurin ɓuyar kwartaye shi ne, ƙyasuwa haki ne da ke da tsawo
sosai da kuma duhun da ke hana a ga mutum ko yana ciki idan ba shigansa aka
gani ba, domin da dare suke aikinsu. Akan sami haka idan magani ya kwanta ko
kuma babu shi. Ba alƙali kaɗai ke kwartanci ba kamar yadda makaɗin ya faɗa.
Akwai nau’in mutane da dama da ya bayyana cewa suna kwartanci wanda idan aka
saurari waƙar ko aka karance ta, za a tabbatar da kwartanci ruwan dare ne game
duniya. Wannan zai ba mutum mamaki har ya yi niyyar musantawa idan da ba ga
bakin makaɗin ya ji maganar ba. Allah ya kare mu, ya kare muna.
9.6
Idan ba a Bar Zuwa Ruwa ba, ba a Barin Ɓari (Faɗawa Cikin Tarko)
Yadda
ake haƙon ɓèra da gafiya da sauran namun daji, haka ake haƙon kwarto domin a
kama shi. Idan aka kama ɓera da gafiya ko naman daji kashe shi ake yi sai wanda
Allah ya kuɓutar.
Kwarto
ma haka ake yi masa, face in ba a kama shi ba. Idan Allah bai nufi a kashe
kwarto ba, sai ya ƙaddari a tayar da shi ya ruga ya tsere, ya nemi wurin ɓuya.
Ba wannan kaɗai ba, akan kama kwarto a gwada wa jama’a cewa kwartanci aikinsa
ne, ko ana sake shi daga baya a sake bayan kowa ya tabbatar da matsayinsa na mai
neman matan mutane. Akwai tarkon da aka haƙa wa wani kwarto da makaɗin ya ce ba
a taɓa kamun kwarto da ya kai munin wannan ba. Ga abin da makaɗin ya ce:
Bakin Lanjeriyag ga in
dai a riƙe kwarto na,
Kamun kwarton Nabasa ab
babu irinai,
Basarke kwash shige shi
ya cimma iyaka,
Da yag gane kussuwad da
kwarto ka shigowa gidansa,
Ga mamurra cikin gida
anka haƙe su,
Mangariba ta wuce kurum
anka yi kora tai,
Da yaz zo zai kurɗa
kussuwa sunka riƙe shi,
Ɗan mamari ga su sui ɗari
bakwai nan bisa bainai,
Har rana tay yi tsakkiya
ga hi tsugunne.
Makaɗa Ɗanladi ya ce a cikin
Nijeriya baki ɗaya ba a taɓa kama kwarto irin kamun da aka yi a garin Nabasa
ba. Wani kwarto ne da ke zuwa kwartanci a gidan wani basarke da maigida ya gane
sai ya yi wa kwarton tanadin yadda zai kama shi, bayan ya gane hanyar da yake
bi ya shiga gidansa. Basarken bai yi wata-wata ba sai ya ɗauko mamari ya haƙa a
cikin gida kafin magariba. Bayan magariba dare na yi sai kwarton ya shigo
gidan. Ana ganin sa sai aka kore shi ba tare da ya san an haƙa mamari ba. Yana tasam
ma kussuwar da ya saba fita gare ta, bai kai can ba sai haƙo ya kama shi. Makaɗin
ya ce ɗiyan mamarin da suka shige wa kwarto ga jiki sun kai ɗari bakwai. Da
maigida ya tabbatar da kwarto ya kamu, bai yi masa komai ba, bai ce masa komai
ba sai da kowa ya gama ganinsa. Kwarton na nan sai da rana ta kai tsakiya
sannan aka zo wurinsa domin kowa ya gan shi. Idan mamari ya kama kifi, duk
lokacin da kifin ya motsa mamari ƙara shiga jikin kifin yake yi. Haka mamurran
suka rinƙa shiga jikin kwarton duk lokacin da ya motsa, kuma aka fita batunsa
sai da rana ta kai tsakiya. Ga abin da makaɗa ya ci gaba da cewa:
Da yaz zaka shi bai bugai
ba yat tarda mutanenai,
Ai ko an ɗauko wanzami
nashi na kainai,
To sai tcaga akai ana hid
da ɗiyan nan,
Mugun ya zo ta Bauci ya
sake kamannu,
Bana sun maisai Bakambare
ba hi ɓacewa.
Da maigidan ya zo wurin kwarton bai buge shi ba amma, ya kira
mutane domin su zo su gan shi. Kwrton na tsugune kuma ga mamurra cikin jikinsa
babu halin motsi saboda kaifinsu ga jiki, sannan ba su ciruwa da hannu sai da
aka kira wani wanzami domin ya cire wa kwarton. Dalilin tsagar da aka yi wa
kwarton ana ɗebe masa ɗiyan mamari har canza kama ya yi, ya koma kamar
Bakambare. Dangane da wannan akwai tabbacin faɗawa cikin tarkon masu gidaje da
kwartaye ke yi ba da saninsu ba. Wannan ne dalilin da ya sanya aka sa wa kan
labarin suna “Idan ba a bar zuwa ruwa ba, ba a barin ɓari”. Wannan na nufin
matuƙar kwarto na zuwa kwartanci wata rana sai ya shiga hannu a wulaƙanta shi
bainar jama’a. Babu shakka wannan kwarto ya faɗa tarkon maigida kuma, da wannan
aka sami asirin kwarto ya tonu da aka kama shi.
10.0
Sakamakon Bincike
Binciken ya gano cewa ana
sa kwarto hurumi sanadiyyar ƙyamar da ake yi masa kamar yadda makaɗinsu ya
bayyana abin da ya faru tsakanin wani kwarto da wasu Fulanin ƙasar Neja. Wannan
ya faru saboda tare wata Bafullata da ya yi a daji ya yi fasiƙanci da ita, duk
da yake ina da tunanin fyaɗe ne ba kwartanci ba domin, taron ta ya yi a daji ba
gida ya tarar da ita ba. Ga abin da makaɗin ya ce da ke tabbatar da sanya
kwarto hurumi:
Bari in koma ƙasammu in
maida bidata dai,
Garba sana’a na Salka bai
bak kasada ba,
Kasuwad daji Garba yay yi
gaba da Hilani,
Bahullata yat tare dawa
yac ci tsakanta,
Daɗa ya yi hwaɗin dara,
dara taƙ ƙi tsayawa,
Kai misallike kwangyal ga
ƙyasuwa za ya nasa ta.
Ko ga nono cikin gida ba
a saye mai,
Sai ya biɗo tsamiya ga ƙwarya
ya jiƙa ta,
In ba hi da tsamiya ƙwame
za ya hwashewa,
Nic ce ɗau anniya da mata
na Hilani,
Ga Hillani na Salka kau
sun game kansu,
Amma a yi langaru ka’ a
sarai da takobi,
Ka san langaru bai barin
kaɗo da hulla.
Haka kuma an gano cewa ana gadon kwartanci kamar
yadda makaɗin ya nuna a cikin wasu ɗiyan waƙa cewa yana da mahaifi kwarto, shi
kuma ɗa kwarto ne. Bayan haka binciken ya gano kwarto matsoraci ne kuma
matsoraci, ba ya tsayi ya fuskanci jama’a idan aka tayar da shi, sai dai ya
ruga domin ya tsira da ransa. Akwai ɗiyan waƙa da dama da suka tabbatar da haka
daga bakin makaɗin. Wani hali da binciken ya gano shi ne, kwarto bai kula da
addini ba a wurin da makaɗinsu ya ce, kwarto bai kula da wankan janaba ba. Domin
koyaushe suna cikin rashin tsarkin jiki da na tufafi bayan zuciyar ma ɓatatta
ce. Wannan na nufin ba su kula da yin salla ba. Wani abin da binciken ya ƙara ganowa
shi ne, kwarto ya yi ban kwana da kunya, bai san ta ba kuma bai yi kusa da ya san
ta ba. Bayan haka akwai rashin ƙyamar kowace irin mace ga kwarto inda aka nuna
yana yi da mai ido da makauniya da mai ji, har kurma bai bari ba. Wannan shi ya
tabbatar da kwaɗayin kwarto. Ga ɗan waƙar da makaɗin ya tabbatar da kwaɗayi da
rashin ƙyamar kowace irin mace ga kwarto:
To bari dai in kiɗa ma
sarkin majarauta duka,
Kwamandan ‘yan nema ko
tawa ba hi ragawa,
Bari in koma ƙasag gabas
inda Namanke,
Na Nabara anne na Bawa
kura a ci wawai,
Jan anne ya biya ni
jingaj jarabatai,
Ya sai doki da keke ya ba
ni Namakau.
Ga shi mata huɗu ag gare
shi bai baj jaraba ba,
Mata huɗu ba isan Namakau
suka yi ba,
Wai dub bakin karin
kumallo ya aje su.
Tun yana ciyo mai kunnuwa
hi dawo ma kurame,
Nic ce wata ran ham mar’
ido ba hi barin ta.
Haka
kuma binciken ya gano kwarto maci amana ne inda yake neman matan abokansa da na
’yan uwansa da na maƙwabta na kusa da nesa. Wannan ya nuna kwarto azzalumi ne
na ƙoli a cikin harakar zamantakewa. Kaɗan daga cikin abubuwan da binciken ya
gano ke nan dangane da kwarto da kwartanci.
11.0 Shawara
Shawarar
da muƙalar ke bayarwa ga al’umma ita ce, a ƙyamaci kwarto da aikinsa, sannan a ƙyamaci
zuriyarsa domin duk inda ɗan burgu yake ba ya rasa farin bindi. Kar a auri
‘ya’yan kwarto kuma kar a ba su auren ‘ya’yan al’umma domin ɗabi’ar raɓo take
yi face idan an tabbatar da rabuwarsa da wannan ɗabi’a. A ɓangaren hukuma kuma ya
dace a hukunta su daidai da shari’a. Idan aka yi haka, an ɗauki matakin da ke
kai al’umma ga tudun-na-tsira. A ƙarshe, kowa ya yi addu’a ya roƙi Allah tsari
daga kwartanci domin ganin al’umma ta gyaru baki ɗaya har a wayi gari a sami ɗabi’ar
kwartanci da kwartaye sun yi rauni. Haka kowa ya kula da iyalinsa da waɗanda
suke hulɗa da su. Abokai da ke kai abokansu cikin gidajensu su yi hattara kar
abota ta zama masifa gare su. Bayan haka, kowa ya kula da lalurorin iyalinsa,
kar ya bar su cikin halin ƙaƙa-nika-yi domin gudun kwaɗayin abin hannun wani
har a faɗa halin ƙuncin rayuwa da kuma da-na-sani. Allah ya kiyaye.
12.0
Kammalawa
An fara muƙalar da
gabatarwa, aka kawo dalilan bincike da dabarun da aka yi amfani da su a wajen
rubuta muƙalar. An kawo hanyar bincike da bayanin ma’anar kwarto da kwartanci
dangane da abin da masana suka faɗa da taƙaitaccen tarihin makaɗa Ɗanladi a taƙaice
ƙwarai. Bayan haka an bayyana dalilan da ke haddasa (sanya) mutum ya zama
kwarto da suka haɗa da kwaɗayi da gado da harijanci da abota da mai yin
kwartanci da mallakar magani da aka kafa hujjoji daga ɗiyan waƙoƙin makaɗin.
Takardar ta kawo wasu ayyukan kwarto da suka haɗa da gudu da fasa darni da
neman matan maƙwabta da rashin ƙyamar abokiyar fasiƙanci da neman magani da
neman mafaka da kuma faɗawa tarkon magidanta. An yi haka ta fuskar tsamo
ayyukan daga waƙar kwartaye ta makaɗin.
Manazarta
Tuntuɓi Masu takarda
(Lambobin wayoyinsu na sama).
1 Comments
Masha Allah. Malam Abu Ubaida kana kokari sosai. Allah ya taimaka.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.