Ticker

Ranar Rubutacciyar Waƙa Ta Duniya

Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta kasa.

Ranar Rubutacciyar Waƙa Ta Duniya

Sulaiman Salisu Muhammad

Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jami'ar Jihar Kaduna.
Email: sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740

Wakoki


Matsayin Rubutacciyar Waƙa Jiya Da Yau:

Assalamu alaikum, 'yan uwana marubuta da manazarta waƙoƙi. Ina taya mu murna da zagayowar wannan rana ta: 21-03-2021, wato RANAR RUBUTACCIYAR WAƘA TA DUNIYA.

Kamar yadda aka sani, wannan rana, majalisar dinkin duniya ta kebe ta ne domin yin bitar matsayin rubutacciyar waƙa: Jiya da yau da makomarta gobe.

Bahaushe ya fara dandanar zakin rubutacciyar waƙa tun a wajen karni na 17. A wannan karni an sami rubutattun waƙoƙi kamar na: Shi'ir Hausa  da Jamuyah dukkansu na Sheikh Ahmad Tila.  Sai Tarihi El-Sudan, ita ma waƙa ce ta Hausa da sunan Larabci ta Sheikh Abdulkadir Tafa. 

Duk dai a karni na 17, an sami waƙoƙi irin na su: Wali dan Masani da Wali dan Marina a Katsina. Da sauransu.

A karni na 18, an ci gaba da samun marubuta waƙoƙi irinsu: Malam Muhammadu Bn. Muhammadu al-Katsinawi wanda ya shahara a wajen shekarar 1732.

A karni na 18 zuwa na 19, an sami bunkasar marubuta waƙoƙi irinsu: Malam Muhammadu na Birnin Gwari 1758-1878. Wanda yana daya daga cikin wadanda ake alakanta shahararriyar waƙar nan ta GANGAR WA'AZU, zuwa gare shi.

Sannan akwai Shaihunnan Malamai irinsu: Malam Shitu dan Abdurra'uf mawallafin waƙar Jiddul ajizi Ba'ajamiya, da Jimiyya, d.s.

Haka nan akwai waƙoƙin madahu na masu jihadi irinsu: Shaihu Usmanu bn. Fodiyo da kaninsa Abdullahin Gwandu da dansa Muhammadu Bello, da Nana Asma'u da autansa Isan Kware, da sauransu.

A karni na 19 zuwa na 20, an sami fitattun marubuta waƙoƙi kamar su:  Sarkin Zazzau Alu dan Sidi, da (DR) Aliyu na Mangi da (DR) Akilu Aliyu da (DR) Alkali Bello Gidadawa da (DR) Mudi Sipikin, da Mal. Ummarun Gwandu, da Malam Sa'adu Zungur a Bauchi, da Malam Mu'azu Hadeja da Abubakar Ladan Zariya da sauransu.

 

A sakamakon kwazo da nuna kishi da kwazo na waɗannan Shaihunnan Malamai, an sami habakar rubutacciyar waƙa a kasar Hausa.

Rubutacciyar Waƙa A Yau:

A karni na 19-20, rubutacciyar waƙa na kamshin turare dan goma. Bayan tumbatsar marubuta waƙoƙi da aka sami, akwai litattafai da wallafe-wallafe da suka shafi rubutacciyar waƙa da dama.

Misali, irinsu waƙoƙin Imfiraji, da Fasaha Akiliyya, da waƙoƙin Mu'azu Hadeja, da Sababbi da tsofaffin waƙoƙin Mudi Sipikin, da Baje Kolin Hajar Tunani na Alkali Bello Gidadawa, da waƙoƙin Sa'adu Zungur, da waƙoƙin Hausa, da sauransu.

Amma maimakon a karni na 21, a ce rubutun litattafai ya yi tashin gwauron zabo,  sai aka sami ci gaban mai Hakim rijiya. Rubuce-rubuce sai ya koma a kafafen Sada zumunta ko social media. Wannan ya kawo koma baya a fannin nazarin rubutacciyar waƙa.

Misali, a sakamakon dukafa wajen nazarin rubutacciyar waƙoƙin magabatanmu, mun rabantu da samun Farfesoshi a fannin rubutacciyar waƙa kamar su: 1. Farfesa Dalhatu Muhammad 2. Farfesa Dandatti Abdulkadir 3. Farfesa Abdulkadir Dangambo 4. Farfesa Bello Sa'id 5. Farfesa Haruna Birniwa 6. Farfesa A.B Yahya 7. Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa da 8. Magaji Tsoho Yakawada 9. Farfesa Bala Usman 10. Farfesa Zulyadaini, da sauransu.

Kusan dukkan waɗannan Farfesoshi na fannin rubutacciyar waƙa, za ka ga ayyukansu, ya jibanci ayyukan marubuta waƙoƙi ne mazan jiya.

Matsalolin Da Rubutacciyar Waƙa Ke Fuskanta A Yau:

Zamani: A duk lokacin da wani abu ya yi tashin gwauron zabo, ana da ran wata rana zai yo kasa.

Buga litattafai: Ta fannin buga litattafai, za ka iske kusan dukkan litattafan magabata, kamfanoni ne suka buga su. Da wuya ka ji wani marubucin waƙa ya buga littafinsa da kansa.

Akwai kamfanoni masu buga litattafai irinsu: NNPC da Gaskiya Corporation, da University Press da Alhudda-hudda da Amana da Ahmadu University Press, da sauransu.

 

A yanzu waɗannan kamfunan buga litattafai kusan in ce sun daina karbar litattafai da suka shafi rubutacciyar waƙa domin bugawa.

A wannan karni na 21, litattafai da suka jibinci rubutacciyar waƙa kalilan ne masu shi suka buga. Misali, Daurayar gadon fede waƙa, na Farfesa Abdulkadir Dangambo, da Gadar zare na Dr. Awwal Anwar, da Salo asirin waƙa na Farfesa AB Yahya, da Bayanin rubutacciyar waƙa na Farfesa Isa Mukhtar, da Nazarin waken Hausa na Dr. Sulaiman A.S. Sarbi, da Guzurin marubucin waƙa na Malam Nasiru G.Ahmad 'Yan Awaki sai Matakan Nazarin rubutacciyar waƙa na Malam Sulaiman S.M.Mai Bazazzagiya.

Wani abin da ke ci wa rubutun rubutacciyar waƙa tuwo a kwarya, shi ne rashin nuna goyon baya ga al'umma, da hukumomi.

A da idan gwamnati na bukatar fadakarwa, ko wayar da kan al'umma a kan wani abu da ya shafi ci gaban al'umma, ana bukatar marubuta waƙoƙi su ba da tasu gudummuwa wajen rubuta kasidu a kan batun da ake bukata. A yanzu ba a yin haka. A yau in ka ga haka, sai dai yabo ga 'yan siyasa.

A tarukan al'umma na cikin gari, a da a kan bukaci marubuta waƙoƙi su baje kolinsu. Wato su yi maraba da baki. A yanzu wannan ya yi karanci.

A Jami'o'i kuwa, a da dalibai na da zummar nazatar rubutacciyar waƙa. Amma a yanzu abin sai a hankali. Dalibai na guje mata saboda sun shak'a cewa tana da wuya.

A jiya akwai gasa da Kungiyar Marubuta da Manazarta Rubutacciyar waƙa ke shiryawa duk shekara. A karshen gasar ana ba da Kofi da sauran kyaututtuka ga zakarun gasar. Wannan kan shajja'a mawaƙa wajen dagewa na inganta waƙoƙinsu.

Duk da yake a yanzu akwai yunkuri da ake yi domin farfado da ayyukan da wancan kungiyar ke yi. A karkashin GAMAYYAR MARUBUTA DA MANAZARTA RUBUTATTUN WAƘOƘIN HAUSA TA KASA, a bisa jagoranci Sulaiman S.M. Mai Bazazzagiya.

Shawarar Yadda Za A Farfado Da Rubutacciyar Waƙa:

1. Kamfunan buga litattafai su dawo da karbar buga litattafai na waƙoƙi. Ko a sami wani sabon kamfani na buga litattafan Hausa.

2. Hukumomi su rika daukar dawainiyar buga litattafan Hausa  masu ma'ana. Kamar yadda ake yi a kasar Masar, da sauran kasashe. Wannan zai zaburar da marubuta waƙoƙi.

3. Jami'o'i da gwamnatoci su rika daukar dawainiyar shirya gasar rubutacciyar waƙa. Ana ba da kyaututtuka ga zakarun gasar.

 

 Alhamdulillah, a yanzu wajen shekara hudu zuwa biyar, ana ta yunkurin karfafa ko inganta rubutun kagaggun labarai. Akwai cibiyoyi da ke daukar wannan, kamar: B.B.C da Aliyu Gusau Library, da gasar Dangiwa  da na Darma Library, da gasar gajerun labarai na Aminiya Trust da sauransu.

To a yanzu ya kamata a mayyazo zuwa ga rubutacciyar waƙa. Kamar yadda aka sani ne, tubalan ginin adabin zamani uku ne: Rubutacciyar waƙa, da Rubutun zube, da Wasan kwaikwayo.

Waɗannan su ne tubala ko murahun adabin zamani. Idan ya kasance a kullum ana ta gina kafa daya daga cikin murahun, sauran biyun na zagwanyewa, ko an dora tukunyar ci-maka, ba za ta zauna. Dafuwar za ta tuntsure ta kashe wutar murhun.

4. Marubuta waƙoƙi su dage su hada kansu. Makwabcinka ko dan kwadigo, ba za su maka kaftu, da noma, da cirbe, da girbi ba, a gonarka kamar yadda za ka yi da kanka.

Godiya ga Malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi, wanda bisa jagorancinsa ne muke wannan tattaunawar.

Wata godiyar zuwa ga Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, bisa gasar rubutattun waƙoƙi da suka shirya a kan tsaro.

Ba za mu manta da gwamnatin jihar Bauchi bisa karrama daya daga cikin magabatanmu, wato Malam Sa'adu Zungur. Na canza sunan Bauchi state University, zuwa Sa'adu Zungur University.

Mun tattauna da Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu Tilde. Akwai shiri wanda suke yi na karrama marubuta waƙoƙi a jihar Bauchi. Muna matukar godiya bisa wannan albishir.

Post a Comment

0 Comments