Takardar Da Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa-Da-Ƙasa Karo Na 5 a Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe Na Jami’ar Jihar Kaduna. Ranar 14 Zuwa 17 Ga Nuwamba, 2019.
Sir Hanns Vischer Ɗan
Hausa (1875-1945): Gudummawarsa Ga Ƙa’idojin Rubutun Hausa
Na
Hadiza
Usman
Ɗaliba a: Sashen Harsunan
Nijeriya Da Kimiyar Harshe,
Jami’ar Jihar
Kaduna
Lambar Waya: +2348165933830
Imel: hadizanananitr@gmail.com
Tsakure
Batun daidaita ƙa’idojin
rubutun Hausa batu ne da ya sha rubdugu tun lokaci mai tsawo. Ɗaiɗaikun mutane da
hukumomi sun yi ƙoƙari tare da bayar da gagarumar gudummawa wajen samar da ƙa’idojin
rubutun Hausa a mabambantan zamunna. Gudummawar sun haɗa da fitar da adadin
baƙaƙe da wasulan da ake amafani da su, da kuma fasalta
sautukan da suka dace da harrufan da babu su a harshen Ingilishin da aka ɗora lafazin Hausa a kan harrufansa. Alƙiblar
wannan maƙala ita ce tattauna gudummawar da Baturen Switzerland
jam’in mulkin mallaka kuma tsohon ɗan mishan wato Hanns Vischer wanda aka yi wa laƙabi da Ɗan
Hausa ya bayar ga samuwar ƙa’idojin rubutun Hausa. Maƙalar ta jaddada cewa Ɗan
Hausa shi ne tsittsige ko tushe ko asalin samuwar ƙa’idojin
rubutun Hausa, musamman abin da ya shafi baƙaƙe masu
lanƙwasa(ɓ, ɗ, ƙ).
1.0 Gabatarwa
Ƙa’idojin
rubutu dokoki ne da ake so mai karatu ya kiyaye domin daidaita rubutu ya dace,
da kuma fito da ma’ana da samun sauƙin fahimta. Bahaushe kan ce; “Gaba da gabanta, aljani ya taka wuta”.
Saboda haka, idan aka ce Sir Hanns Vischer (Ɗan Hausa)[1] shi ne limamin samuwa da kuma daidaita
ƙa’idojin
rubutun Hausa, ba a sharara ta ba. Ta la’akari da cewa Ɗan Hausa ɗaya ne daga Turawan mishan
wanda daga bisani ya rikiɗe aikin mulkin mallaka a ƙasar Hausa. Shi ne ya buɗe
makarantar boko ta farko a Arewa, wato Makarantar Ɗan Hausa a Nassarawa Kano. Nazarce-nazarce
da dama (Yahaya, 1988; Malumfashi, 2009; Bunza, 2015; Malumfashi da Mujaheed,
2018; da sauransu) bisa mabambantan manufofi sun taɓo
ayyukan Ɗan Hausa, ta fuskar aikin mishan da
aikin mulkin mallaka da kuma gudummawarsa ga karatun boko da rubuce-rubucen
Hausa. Saboda haka, a wannan maƙala an yi ƙoƙarin fito da gudummawar Hanns Vischer ne musamman ta fuskar
daidaita ƙa’idojin rubutun
Hausa.
2.0 Rubutun Hausa a Taƙaice
Rubutun boko tsarin rubutun abacada ne wato baƙaƙe
da wasula a jere wanda ya samo asali daga Latin,
wato harshen Romawa kimanin shekaru 3,100 da suka wuce. Asalin rubutun boko na
Romawa ne kuma yanzu da shi Turawan Italiya da Faransa da Fotugal da Ingila da
sauransu suke amfani, (Yahaya, 1988).
A ƙasar Denmark ta Turai ce aka fara
rubuta kalmomin Hausa cikin rubutun boko, inda wani Baturen Denmark mai suna
B.G Neighbuhr ya riƙa rubuta kalmomin Hausa yayin da yake
koyon Hausa. Misali yakan rubuta kalmomi kamar haka:
-
dudsji
maimakon dutse
-
ghurassa maimakon gurasa
-
berni maimakon birni,
da sauransu. (Yahaya, 1988).
Turawan bincike da na Mishan sun rubuta
harsunan Afirka da dama ta yin amfani da baƙaƙen Latin ciki har da Hausa. Waɗannan Turawa sun fara ziyartar Afirka
ta yamma a cikin Ƙ18 ƙarƙashin wata ƙungiya
mai suna Ƙungiyar
Gano Afirka.
Har ila yau, wasu ƙungiyoyin
addinin Kirista na ƙasashen Turai sun cigaba da aiko Turawa
daban-daban tun daga Ƙ18 zuwa Ƙ19 irin su Henrich Barth da James
Frederick Schon da sauransu, domin
binciken al’adu da harsuna da kuma yaɗa addinin Kirista a Afirka ta yamma,
(Yahaya, 1988).
Akwai wasu Turawan da suka yi
rubuce-rubuce cikin Hausar boko kafin Ƙ20 waɗanda suka haɗa da William Baikie wanda ya rubuta Letafi Zabura (1881) da J. Lippert ya
rubuta Hausa (1886) da kuma J. Numa
Rat ya rubuta The Elements of the Hausa
Language (1889), (Yahaya, 1988; Bakura, 2018; Bunza, 2018).
Kenan, tun kafin Turawan mulkin
mallaka, Turawa masu bincike da masu yaɗa addinin Kirista daga ƙasashen
Ingila da Faransa da Jamus da Denmark sun yi amfani da baƙaƙen
Latin sun yi rubuce-rubuce cikin Hausa. A lokacin da suke waɗannan rubuce-rubuce, Hausawa ba su fara
rubuta Hausa cikin boko ba kuma Hausawa ba su san ma akwai wani irin rubutu na
boko ba, sai da Turawan mulkin mallaka suka kafa makarantun boko a ƙasar
Hausa, wanda Ɗan Hausa yana shi ne ja-gaba a wannan fagen.
3.0 Taƙaitaccen Tarihin Hanns Vischer (Ɗan
Hausa)
Sir
Hanns Vischer wato Ɗan Hausa Bature ne wanda ya ba da
gagarumar gudummuwa sosai a sha’anin aikin mishan da kuma mulkin mallaka.
Kazalika, a ɓangaren samuwar ilimin boko da
rubutaccen zube; Ɗan
Hausa shi ne ya buɗe makarantar boko ta farko
(ta gwamnati) a Kano, kuma yana daga cikin malaman da suka fara koyarwa a ƙasar Hausa. Haka kuma da shi aka aza
harsahin samar da ƙa’idojin
rubutun Hausa da samar da littattafai ta hanyar fassara da ƙagawa da gasa, (Malumfashi da Mujaheed,
2018).
An
haifi Hanns Vischer
ranar 14 ga watan Satumba, shekarar 1876 a yankin Basle na ƙasar Switzerland. Ya yi karatu a makarantar St. Lawrence’s College da ke
Cambride a shekarar 1896 bayan ya yi taƙaitaccen
karatu a ƙasar Jamus. Bayan ya kammala karatunsa a kan Harsunan
Zamani a shekarar 1899, ya yi karatu na shekara ɗaya
a Ridley Hall kuma ya nazarci Hausa a Tripoli. Sannan ya yi kwas a kan lafiya a
wani asibiti da ke Berne a ƙasar
Switzerland a shekarar 1900. Ɗan
Hausa ya yi digiri na biyu a jami’ar Cambridge a 1903. Ya yi aure a shekarar
1911, sunan matarsa Isabelle de Tscharner, (Malumfashi da Mujaheed, 2018).
Har
ila yau, Hanns Vischer ya
yi ayyuka da suka haɗa da aikin Mishan na sa-kai lokacin
da yake karatu a Ridley da kuma ƙungiyar
yaɗa
addinin Kirista ta C.M.S ɓangaren Hausa a Cocin Ingila.
Daga shekarar 1900 zuwa 1902 ya yi aiki da tawagar mishan a Arewacin Nijeriya.
Daga bisani kuma Hanns Vischer ya
koma ƙasar Birtaniya ya zama ɗan ƙasa ya dawo Nijeriya a shekarar 1903 ya
koma aikin mulkin mallaka, (Malumfashi da Mujaheed, 2018).
Ɗan Hausa ya riƙe muƙamin
Razdan, kuma ya taimaka wajen aza harsashin buɗe
makarantar gwamnati ta farko a Kano, ya zama jami’in ilimi daga bisani kuma ya
zama Daraktan Ilimi na Arewacin Nijeriya. Ya yi ritaya a aikin mulkin mallaka
ne a shekarar 1919 a ƙashin
kansa, kuma ya cigaba da yin wasu aikace-aikacen da suka shafi nahiyar Afirka bayan
ya koma Birtaniya har zuwa shekarar 1941. Sir Hanns Vischer (Ɗan Hausa) ya mutu ne ranar 19 ga watan
Fabrairu na shekarar 1945, (Malumfashi da Mujaheed, 2018).
4.0 Gudummawar Ɗan
Hausa Ga Ƙa’idojin Rubutun Hausa
A
shekarar 1903 lokacin da Ɗan
Hausa ya dawo Afirka a matsayin Mataimakin Razdan a Arewacin Nijeriya, ya zauna
a yankin Borno kuma yana da ƙwarewa
a harshen Larabci da Hausa, (Malumfashi da Mujaheed, 2018).
A
shekarar 1912, Hanns Vischer ya
rubuta wani littafi mai suna Rules for Hausa Spelling inda ya
zayyana ƙa’idojin rubutun Hausa a cikinsa, ya
kuma bayyana irin kalmomin da suka kamata a raba da waɗanda
suka kamata a haɗa. Sa’annan ya sauya ƙa’idojin rubuta waɗannan
sautuka kamar haka:
-
Maimakon b,
a rubuta ‘b, wato ɓ
-
Maimakon d,
a rubuta ‘d, wato ɗ
-
Maimakon k,
a rubuta ‘k, wato ƙ
Waɗannan
ƙa’idojin, su Mr. G.P Bargery ya bi wajen
rubuta ƙamusunsa mai suna ‘Hausa-English Dictionary and
English-Hausa Ɓocabulary.’
Har ila yau kwamitin daidaita Ƙa’idojin
Rubutun Hausa na shekarar 1932 ya shafe kusan shekara 5 kafin cim ma
yarjejeniyar yi wa b da d da k ƙugiya suka koma ɓ da ɗ da ƙ,
maimakon ɗige-ɗigen
da Hanns Vischer ɗin
ya kawo a cikin littafin nasa, (Yahaya, 1988; Malumfashi da Mujaheed, 2018).
Kenan, idan ana batun ƙa’idojin
rubutun Hausa, wannan littafi na Rules for Hausa Spelling na Hanns Vischer
shi ne tsittsige ko tushe ko kuma asali. Saboda haka, wannan ya jaddada cewa Ɗan Hausa shi ne limamin samuwar ƙa’idojin rubutun Hausa. Kuma idan an bi
zaren tarihi tun daga shigowar boko ƙasar
Hausa zuwa yau akwai ɓurɓushin
gudummawar Ɗan Hausa a musamman a
fagen ƙa’idojin rubutun Hausa na boko.
5.0 Kammalawa
Bahaushe kan ce; “kowa da gwaninsa”.
Shi ya sa ma a fagen samuwa da adaidaita ƙa’idojin rubutun Hausa na zaɓi Sir Hanns Vischer, wato Ɗan
Hausa a matsayin gwanina wanda gudummawarsa ta fi ɗaɗa ni. An yi tsokaci kan rayuwar Ɗan
Hausa a taƙaice, an kuma waiwayi taƙaitaccen tarihin rubutun Hausa cikin
boko, sai kuma aka jaddada gudummuwar wannan jami’i (Sir Hanns Vischer, wato Ɗan
Hausa) a fagen samuwar ƙa’idojin rubutun Hausa.
Manzarta
Tuntuɓi
mai muƙalar (bayananta na sama).
[1] Tsananin soyayyar
da yake nuna wa harshen Hausa da sha’awarsa kan nazarin Hausa da kuma yadda ya
ji Hausa kamar jakin Kano, su ne dalilan da suka sa aka yi wa Hanns Ɓischer laƙabi da Ɗan Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.