Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).
Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 1)
Sulaiman
Salisu Muhammad
Sashen
Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar
Jihar Kaduna.
Email:
sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740
Gabatarwa
Wato na lura a cikin wannan Tsangaya tamu,
kowa ya iya rubutun Hausa, amma ba kowa ya san ka'idojin rubutunta ba. Saboda
haka za mu yi iyakacin bakin kokarinmu na ganin kowane dalibi ya koyi ka'idojin
rubutu, ta yadda a ko'ina zai iya rubutu ba tare da wata fargabar za a ci
gyararsa ba.
Wannan darasi yana da muhimmanci ga duk wani
mai rubutu da harshen Hausa a kowane fanni. Sau da yawa za ka ga mutum ya yi
zurfi a karatun Hausa, amma idan ka kalli rubutunsa, sai ka ga akwai
gyare-gyare da dama. Wannan ga waɗanda ma suka nazarci harshen Hausa a Jami'o'i
ke nan. Ina ga waɗanda ba su nazarci
harshen ba.
A wannan fagen ma, ni kaina ƘOLO nake. A duk in da
aka ga kuskure, sai a ankarar da ni. Na sani a ka'idojin rubutu akan sami sami
'yan bambance-bamcen fahimta a tsakanin masana.
Sai dai mun yi sa'a a yayin wannan darasi, a
gaban babban Shehinmu Farfesa Aliyu Muhammad Bunza za mu rika yi. Da bazarsa za
mu rika rawa. Saboda ya riga ya dama mana hurar, sai dai mu ɗiba mu sha a cikin
littafinsa mai suna: RUBUTUN HAUSA.
Mene Ne Rubutu?
Masana da dama sun yi bayanin abin da rubutu
ke nufi a tasu fahimtar. Misali:
"Rubutu wata dabara ce ta yin wasu 'yan
alamomi da za su wakilci magana..." (A.M. Bunza 2002)
Ƙa'idojin Rubutun
Hausa:
Idan ana magana a kan ka'idar rubutun Hausa,
ba wani ne shi kadai ya zauna ya ƙaga ya ce dole sai
kowa ya bi ba. Masanan harshe ne ke zama daga lokaci zuwa lokaci suna kawo
matsaloli da suka shafi rubutun Hausa ana tattaunawa domin a sami daidaito a
tsakanin marubuta harshen Hausa.
A shekarar 1932 ce aka fara yunkurin samar
samun ingantacciyar hanyar rubutun Hausa, saboda muhimmancinta a wajen
wallafe-wallafe. Wannan yunƙuri ya taso ne a lokacin da Bargery ke
yi na rubuta Ƙamusun farko na Hausa.
A shekarar 1951 an kafa kwamitin inganta
Hausa wanda ya dukufa wajen ganin an sami ingantacciyar hanyar rubutun Hausa. A
lokacin an yi bitar ƙa'idojin, sannan aka cim ma matsaya gamsasshiya game da
su.
A shekarar 1972, an sake zaunawa an duba waɗannan ka'idoji in da
aka daidaita wasu matsaloli da aka ga sun taso.
A shekarar 1980, an sake bitar ƙa'idojin a wurare
guda biyu: ɗaya a Jami'ar Ahmadu
Bello Zariya. ɗayan kuma a Niyame ta
Jumhuriyyar Nijar. Duk dai da nufin samun hanyar rubutun Hausa amintacciya.
(Bello: 2005).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.