Ticker

Mu Koyi Ka'idojin Rubutu (Kashi na 2)

Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).

Ka'idojin Rubutu

Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 2)

Sulaiman Salisu Muhammad
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar Jihar Kaduna.
Email: sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740

DALILIN ƘIRƘIRO RUBUTU A DUNIYA:

Daɗaɗɗiyar hanyar sadarwa a duniya ita ce maganar baki da baki, a tsakanin mutum biyu ko fiye.

Ita sadarwa ta baki da baki, kafin ta gudana dole sai an hadu da mai magana da wanda ake son yi wa maganar. Idan akwai tazara a tsakaninsu, kamar wani yana wani gari, shi kuma wancan yana wani gari, ya zama dole ɗaya daga cikinsu ya tashi ya je ya sami dayan ya fada masa, sannan ya dawo. Ko kuma mutum ya tashi wani ɗan aike ya faɗa masa saƙon, shi kuma ya je ya isar da saƙon da fatar baki.

A irin wannan tsarin sadarwa akwai gajiyarwa a cikinsa. Sannan idan abin ya haɗa da aiken ɗan saƙo ne, a nan kuma babu sirri a maganar da za a fada. Sannan kuma akwai yiwuwar mantuwa, ko ƙarin gishiri ko ragewa ga ɗan saƙo. To wannan a magana ke nan, ina a ce wasu nau'o'in maganar hikima ta adabi, kamar waƙoƙi ko labarai da sauran hanyoyin ilmantarwa.

Ire-iren waɗannan matsaloli ne suka sabbaba wa ɗan Adam ya ƙirƙiri hanyoyin rubutu. Wannan ya ba shi damar rubuta saƙonsa, ko tunaninsa ko wasu darussa ko dai wasu muhimman abubuwa a kan takarda da yake son adanawa, ko aikawa daga wani wuri zuwa wani ba tare da tangarda ba, ko tauyewar abin da yake nufi ba.

 

SAMUWAR RUBUTU A KASAR HAUSA:

Wadancan matsaloli da aka ambata a baya, kowace al'umma ta duniya ta fuskance su. Wasu sun sami wayewar kai sun kirkiri hanyoyin magance su. Sun kirkiri hanyoyin rubutu kuma sun adana su ana amfani da su har zuwa yanzu. Akwai mutane kamar: Romawa da Chaina da Sipaniyawa da Larabawa.

Masana harshen Hausa suna nan sun dukufa domin gano ko Hausawa suna da nasu hanyar rubutu kafin zuwan Larabawa da Turawa kasar Hausa.

Akwai wasu alamomi gadaddu da ke nuna cewa Hausawa su ma akwai yunkuri da suka yi a can baya na yi wa wasu abubuwa zane. Misali, zanen da Bahaushe ke yi a fuskarsa, da wanda yake yi a kwarya da akushi. Ko wanda yake yi a fadojin Sarakunan gargajiya. Dukkan waɗannan zanuka ko alamomi, akwai abin da suke nufi a cikin al'aldar Bahaushe. Misali zanen kalangu na Katsinawa da na Gobirawa duk akwai abin da suke nufi.

Waɗannan abubuwa suna nuni da cewa Bahaushe ba a bar shi a baya ba wajen kirkirar tasa hanyar ta magance matsalar sadarwa. Rashin sa'ar da aka yi shi ne, magabata ba su tsaya sun inganta su ba kamar yadda saura al'ummomin duniya suka yi ba. Larabawa da Turawa sun yi mana shigar gaggawa, muka shantake muka ringumi nasu.

Post a Comment

0 Comments