Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).
Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 5)
Sulaiman Salisu Muhammad
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar Jihar Kaduna.
Email: sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740
Amfani Da Wakilin Suna Da Aikatau:
Ana amfani da wakilin suna a maimakon suna a cikin jimla.
Kalmar aikatau na ishara ga faruwar wani aiki a cikin jimla.
A duk in da aka sami haduwar wakilin suna da aikatau, to ba a hade su, a rarrabe suke.
Misali:
Na yi ba Nayi ba
Ka yi ba Kayi ba
Kin yi ba Kinyi ba
Ya yi ba Yayi ba
Ta yi ba Tayi ba
Mun yi ba Munyi ba
Kun yi ba Kunyi ba
Sun yi ba Sunyi ba
An yi ba Anyi ba
Na ci ba Naci ba
Ka ci ba Kaci ba
Kin ci ba Kinci ba
Ya ci ba Yaci ba
Ta ci ba Taci ba
Mun ci ba Munci ba
Kun ci ba Kunci ba
Sun ci ba Sunci ba
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.