Nazarin Waƙar Sani Sabulu Mai Taken “Harkar Duniya” Duba Zuwa Ga Mazahabar Sigar Adabi

A wannan takarda an yi nazarin waƙar Sani Sabulu ta “Harƙar Duniya.”

Sani Sabulu


Nazarin Waƙar Sani Sabulu Mai Taken “Harkar Duniya” Duba Zuwa Ga Mazahabar Sigar Adabi

Huwaila Abubakar

Gabatarwa

          Wannan mazahaba ta sigar Adabi tana binciko tsari ko siga ta wata al’ada ta amfani da wasu dokokin aiwatarwa (codes), ko ta yin fashin baƙin tsarin saututtukan harshen. Tsarin sautin ya haɗa da matanin adabi da sassansa da kuma wasu harƙoƙin al’ada kamar tallace-tallace da salon kwalliya da batsa da sauran ɗabi’u da halaye (Hernedi, 2009). Wannan aiki yana ƙunshe da tarihin sigar Adabi, yaɗuwarsa da kuma manufofinsa ta yadda zai yi bayanai dalla-dalla kan kowanne daga ciki kamar yadda aikin zai nuna.

Samuwar Mazahabar Sigar Adabi

          Mazahabar sigar adabi ta samo asali ne a dalilin yadda wasu matarka suka lura da yadda aka yi amfani da wasu ra’ayoyi na nazarin kimiyyar harshe wajen gano wasu sassa na ɓoye masu bayar da ma’ana a cikin adabi da al’adun al’umma, wanda ya kai matsayinsa a ƙasar Faransa a cikin 1960.

          Mazahabar sigar adabi ta faro ne daga wasu ra’ayoyin nazarin harshe da kimiyyar harsuna, kuma tana lura da wasu sassa masu ɓoyayyar ma’ana a cikin al’adu da adabin al’umma. Wannan sassa an danganta su don su samar da sharhi game da aikin adabi da irin tsarin da aka bi aka fito da shi. Hasali ma, mazahabar sigar adabi na da ra’ayin cewa kowane abu muka yi na aikin ɗan’adam to, ana bayyana shi cikin harshe ne. mazahabar sigar adabi ta yi imani da cewa waɗannan alamomi ko wakillan furuci suna faɗaɗa ne su ma wuce aikin sadarwa na baka ko rubutacce.

          Wannan mazahabar ta tarken sigar harshe da masana da matarkan adabi suka ɗauki hannu daga gare ta ta samo asali ne daga ayyukan wani mai suna Ferdinand de Saussure (1857-1913) da ya zama uban masu nazarin kimiyyar harshe na zamani da suka yi fice wajen gano wasu tsare-tsare na fito da dokoki da ma’anar ɓoye a cikin nazarin harshe. Ya fito da waɗannan manufofin ne a cikin wasu ayyukansa da ya yi masu suna, La Langue La Parole (Language and Speech Act) (1914) da kuma course in General Linguistics (1923) da sauransu (Macey, 1965:364).

          Bayan wannan ƙoƙarin nasa ne aka sami wasu da suka ɗauki fannin tarken adabi don su samar da wata hanyar tarke ta dubam, da yadda tarken tarihin adabi da tarken tarihin mawallafi suka mamaye fannin tarken a jami’o’in Faransa (Junge, BsB: 983). A cikin shekarar 1940 ne wani mai nazarin baibayi (Anthoropologist) Claudio Leɓistrauss, da wani matarki Roland Berths da taimakon wasu masana suka ƙirƙiro da mazahabar sigar adabi ta Faransa (Mukhtar 2004:7).

          Ruby (1985) a cikin aikinsa na nazarin gajerun labarai ya nuna cewa, a cikin ƙarni na 20 ne aka sami wata mazahabar da ke tarken sigar adabi. tana duba yadda matanin adabi ke iya samar da ma’ana maimakon ma’anar kanta.

Bunƙasar Mazahabar Sigar Adabi

          An ƙirƙiro wannan mazahaba ne a Faransa a wajen shekarar 1960. Amma ta tsiru ne a dalilin wani aiki da Ferdinand De Saussure (1857-1913) ya yi a Faransa a kan nazarin harshe tun a farkon ƙarni na 20, mai suna, La Langue La Parde (1914) da kuma Course in General Linguistics (1923).

          Mazahabar ta ci gaba da bunƙasa har ta zama ta nazarin adabi a Faransa ta kuma ƙara bunƙasa a wajen 1960. Waɗanda suka ƙirƙiro ta sun haɗa da Charles Sanders Peirce da Roland Barthes da Treztan Todoroɓ da Gerard Genette da Roman Jackobson da Claudio Leɓi-Strauss da Mikhtin da sauransu. Da kuma ta faro daga Faransa kuma ya yaɗu zuwa Rasha da Ingila da Amurka a wajen 1960, sannan ta yaɗu tare da yin tasiri a kan irin bincike-binciken mazauna Amurka masu magana da Ingilishi, waɗanda suke kiranta da semiotics ko tarken adabi. ta kuma rikiɗa ta zama mazahabar bi-ƙa’ida da Rasha.

Manufofin Mazahabar Sigar Adabi

          Wasu daga cikin manufofin wannan mazahaba sun haɗa da:

1.     Tana siffantawa da feɗe tsarin da aka rubuta adabi kansa.

Wannan waƙa ta Alhaji Sani Sabulu an tsara ta ne daki-daki ta hanyar bayyana al’amuran rayuwa, wato yanayin duniya. Ga misali daga cikin waƙar kamar haka:

 

“Ka ji harƙar duniya ɗaku

Ka ga Annabi

Don shi aka yi duniya

Domin nai aka yi lahira

Ka ga Annabi ya barku ya bar duniya,

Balle ni Sani Sabulu na Hajara”.

2.     Tana kula da nazarin kimiyyar harshen da aka ɗora kan zubi da tsari, ba kan ƙunshiya ba.

Ita dai wannan waƙa ba ta da wasu ƙai’dodi na tsari na musamman da aka ɗora ta sai dai a iya cewa an rera ta ne gunduwa-gunduwa ta hanyar jeranta tunani domin akwai gangara, wato dangantakar ɗango da ɗango a cikin waƙar. Misali:

“Naushi ɗaya na yi mishi,

Ko da na duba ya faɗi,

Ya tashi yana faɗa da diri”.

3.     Tana ɗaukar adabi kamar yadda yake da tasiri ko ake aiwatar da shi, ta bar lura da tasiri da zamantakewar jama’a.

A taƙaice dai, za a iya cewa wannan waƙa za a iya ɗora ta kan wannan batu, domin akwai hikima wajen isar da saƙon cikinta sannan an samu ƙayataccen salon sarrafa harshe a cikin waƙar. Misali:

“Ina Musa na Hadizatu,

Gaishe ka mijin Kulu,

Gaishe ka Sakataren kiɗa,

Mamman mijin Aisha da A’i,

Baban Abdul’azizi, Sani Kantoman kiɗa”.

4.     Tana fito da tsarin ɓoye tubalan gina aikin adabi (ƙwarangwal) ko wasu dokoki na aikin adabi. misali, akwai maƙasudin bayyana kowane irin abu wadda yawanci akan bayyana shi kafin abin ya fara nisa. Ga dalilin wannan waƙa daga cikin waƙar kamar haka:

“Ni na ji ana faɗi,

Alhaji Sani ya mutu,

Harƙar duniya”.

5.     Tana kula da yadda ake shirya matani don a samar da jerin ma’anoni a cikinsa

A nan ana magana ne game da batutuwa da suka haɗu suka tayar da adabi. Don haka a wannan waƙa an yi ta kawo bayanai ne na neman tsari game da harƙoƙin duniya, ta hanyar kwatanta al’amuran da suke faruwa a cikinta. Misali:

“Na ji ana faɗi,

Alhaji Sani ya mutu,

Wai Alhaji Sani Sabulun Bauchi,

Harƙar duniya,

Ku masoyana kuka dai kuke,

An ce musu Sani Sabulu babu shi

Ai ba haka nan ba ne

Ku daina kuka Allah bai ba

Alhaji Sabulu

Su maƙiya sai murna suke,

Masu adawa na ta farin ciki,

Sun ji an ce Sani Sabulu ya rasu”.

6.     Tana duba wasu dokoki na musamman masu samar da aukuwar ma’ana a cikin matani, wanda kuma ke nuna aukuwar a cikin tsarin matanin ko a cikin al’umma.

Idan muka duba waƙar Alhaji Sani ta ‘harƙar duniya’ za mu ga cewa abin da yake aukuwa ne a tsakanin al’umma ya sanya shi rubuta waƙar, wato ana raɗe-raɗin Sani Sabulu ya mutu kamar har wasu suna murna. Wannan ya sanya shi tunanin yin wannan waƙa don ya shaida wa duniya cewar bai mutu ba, wato yana raye. Ga misali daga cikin waƙar kamar haka:

“Na ji ana faɗi,

Alhaji Sani ya mutu

Wai Alhaji Sani Sabulun Bauchi,

Harƙar duniya.

Ku masoyana ku kaɗai suke

An ce musu Sani Sabulu babu shi

Ai ba haka nan ba ne

Ku daina kuka Allah zai ba Alhaji Sabulu

Sun maƙiyi sai murna suke

Masu adawa na ta farin ciki

Sun ji an ce Sani Sabulu ya rasu”.

7.     Tana kallon matanin adabi a matsayin wani tsari da ke tantance ma’ana (haɗe-haɗen abubuwa na alamomi da lambobi da makaranci ke fahimtar matani da su)

A nan babu wani tsari ko alamomi da za a iya fitowa da su daga cikin wannan waƙa. Amma za a yi bayanin abin da ke da alaƙa da su daga cikin waƙar, tun da ana jan numfashi a matsayin hutu a cikin waƙar. Don haka za a iya cewa takan zo ne gunduwa-gunduwa amma ba ta da wani ma’auni, wato daidaiton ɗango (layi) a cikinta. Misali:

“Sani kantoman kiɗa,

Ɗan ruwan gora Shehu na kan kudu,

Ya insifektan kiɗa,

Birgediyan jangyale farin mijin Hassana”.

8.     Tana mayar da hankali kan ra’ayin kimiyyar harshe da ya danganci sadarwa da fashin baƙinsa; da kuma ra’ayin adabi mai samar da dokokin da za a yi amfani da su a rarrabe tsakanin maganar adabi da wadda ba ta adabi ba.

A nan za a tsunduma ne cikin waƙar domin zaƙulo maganganun hikima. Don haka ga misalen wuraren kamar haka:

Kirari:

“Sani daraktan kiɗa,

Ina Musa na Hadizatu,

Gaisheka mijin Kulu,

Gaisheka sakataren kiɗa,

Mamman mijin Aisha da A’i,

Baban Abdul’azizu,

Sani kantoman kiɗa,

Dan ruwan gora Shehu na kan tudu,

Ya insifektan kiɗa”.

Habaici/zambo

“In ƙara faɗa maka,

Abin da ba ka iyawa,

Kar ka yi shi haushi za ka ji in ka yi,

Adona ɗan Kano,

In ƙara faɗa maka,

Ko dambe dan mai ƙarfi yanada,

Wani ya ja sabulun Hajara,

Sani na Aminatu,

Naushi ɗaya mai mishi,

Ko da na duba ya faɗi ya tafi biki,

Ya tashi yana faɗa da diri,

Ba ka ji irinta ba,

Ka ji wadda ake gudu”.

Karin Magana:

“Idan ruwa ya ɗauke fa kainuwa”.

9.     Tana mayar da hankali ga abin da ya kamata makarancin matani ya sani ko wanda yake buƙatar sani game da fashin baƙin kowace kalma ko alama ko salo da sauransu.

A nan za a zaƙulo kalmomi ne da suka dace a yi fashin baƙi a kansu. Don haka a cikin wannan waƙa akwai ire-iren kalmomi da za a yi fashin baƙi a kan su kamar haka:

-         Insifekta (inspector)   - mai bincike, fannin tsaro

-         Birgediya

-         Darakta (director)       - jagora

-         Bauchi                       - Gari, jihar Nijeriya da ke yankin Arewa

-         Wahidun Jallah          - Mai girma ɗaya, ubangiji

-         Ɗan’adam                  - Mutum

Dangane da salo kuwa, salon wannan waƙa yana da armashi domin ana fahimtar saƙon cikin sauƙi. Daga ka saurara za ka fahimci cewa ana magana kan harƙoƙin duniya.

Sannan an yi amfani ne da karin harshen Gabas.

10. Tana ƙarfafa komawa ga sigar adabi don gano ƙwarangwal na cikin adabi

Kasancewar wannan waƙa ce ta baka. A ƙwarangwal na aikin adabi ta zamo ɗaya daga cikin rassa na adabin baka wato adabin gargajiya. Adabi ya ƙunshi zube, wasan kwaikwayo da waƙa. A ƙarƙashin waƙa ana samun waƙar baka da rubutacciya. Waƙar baka tana ƙunshe da waƙoƙin tashe, bukukuwa, wasanni da sauransu. To a cikin waɗannan rassa aka sami waƙar baka. Don haka wannan waƙa ce ta baka, fannin makaɗan jama’a.

Madogara

Tuntuɓi masu gudanarwa.

 

Rataye

Waƙar Sani Sabu ‘Harƙar Duniya’

Harƙar duniya

Allah jalla ubangijin kowa

Allah wahidin jalla sarki mai komai na har abada

Allah wahidin

Gyara jalla ubangijin dukkadu

Ku tar da zamani

Allah wahidin

Allah mai duniya

Shi ya yi saman bakwai

Kuma shi ya yi ƙasan bakwai

Kuma ya yi su domin annabinku

Allah wahidun

Allah kai ka yi mu

Ka hana mu da kunyar lahira ko kaɗan

Harƙar duniya babu daɗi, ba niyyar bari

Kulluma tafiya take tanan

Haruna na Mamman

Ga jikan Ali mai kiɗa

Haruna baban Garba na Amadu

Sannu daraktar kiɗa

Ina Musa na Hadizatu

Gaishe ka mijin Kulu

Gaishe ka sakataren kiɗa

Mamman mijin Aisha da A’i

Baban Abdul’azizu

Sanu kantuman kiɗa

Ɗan ruwan gora Shehu na kan kudu

Ya Insepetan kiɗa

Birgediyan jangyale fari mijin Hassana

Na ji kai ne kan kula indi

Na so ka riƙamini

Saboda da ku na gane kiɗa aikinku ne

Allah wahidim jalla Sarki mai iko har abada

Yau ga Sani Sabulu na Kanoma

Baban su Nafisatu

Yau ga Sani Sabulu ɗan Musa

Baban Murjanatu

Sani mijin Hajara mijin Amina

Sarai babban kada ɗaku

Sarai babban kada ɗaku

Ka huce kifi sai gungumin rago

Sarai babban kada

Ka huce kifi sai gungumin rago

Haɗari taso da gabar kasuwar

Mu ga ‘yan gishiri suna tafe

Kasan harƙar duniya da an samu sai a rasa

Ta yi wahala daɗi na nan tafe

Ka ji harkar duniya

Babu daɗi ba a niyan bari

Ba ka ji irinta ba

Wai wasu sunce na Sabulu ya tafi

Don naji ana faɗi

Wai dan naji ana faɗi

Wai ance Sani ya mutu

Ni naji ana faɗi

Alhaji Sani ya mutu

Wai Alhaji Sani Sabulun Bauci

Harƙar duniya

Ku masoyana ku kaɗai suke

An ce musu Sani Sabulu babu shi

Ai ba haka nan ba ne

Ku daina kuka. Allah bai ba Alhaji Sabulu

Su maƙiya sai murna suke

Masu adawa na ta farin ciki

Sun ji an ce Sani Sabulu ya rasu

Ai ba haka nan ba ne

Ku daina murna Allah bai ba

Harƙar duniya

Ku masoyar Sani Sabulu

Ku daina kuka Allah bai ba

In ƙara faɗa muku

Dukkan Musulmi na duniya

In ya samu ya yi hamdala

In ya rasa ma kuma ya yi hamdala

Baiwa da rashi kyauta huwallahu ne

Wasu sunce na mutu

To ni nasan zan mutu

Ko ban mutu ba, nasan zan mutu

Ban ƙi ba ance Sani na mutu

Ni a sani na mutu

Ni Sani Sabulu

Ka ga Annabi ya barku

Annabi ya barku ya bar duniya

To bari ni Sani Sabulun Hajara

Malam me kake nufi

Malam ni kake nufi

Indon wani iko duniya

Fir’auna ya mutu ya bar duniya

Iyakacinsa da daɗi duniya

Gobe ƙiyama ba zai kurɓi kausar ba

Ka ji harƙar duniya

Malam me kake nufi

Kana ta murna an ce na mutu

In kuka dukiya kake

In hanje dukiya kake

Ƙaruna ya mutu ya bar duniya

Ko da ya mutu bai riƙe ko kwabo uku ba

Ka ji harƙar duniya ɗaku

Ka ga Annabi

Don shi aka yi duniya

Domin na yi aka yi lahira

Ka ga Annabi ya barku ya bar duniya

Bale ni Sani Sabulu na Hajara

Harƙar duniya babu daɗi ba niyyar bari

Kullum tafiya take

Don Allah Ɗan’adam

Don Allah Ɗan’adam

Ana sha’ani dan lahira

Akan ajiye a yi harƙar duniya

Tun da na taɓa zance lahira

Bari in taɓa zance duniya

Don Allah Ɗan’adam

In ƙara faɗa maka

Kasan harƙar duniya

Kowa yasan da wuya take

Kamar kogi da ruwa take

Wani ya faɗa ya kai tudu

Wani ya faɗa bai kai iyakarta ba

Ka ji harƙar duniya ɗaku

Don Allah Ɗan’adam

In kara faɗa maka

Sha’ani ra’ayi muke

In ba a’ayi huce kar ka ba mu abin

Ka ka je ka ajiye shi

Ka ji harƙar duniya ɗaku

Don Allah Ɗan’adam

In ƙara faɗa maka

Abin da baka iyawa

Kar ka yi shi haushi za ka ji in ka yi

Ado na ɗan Kano

In ƙara faɗa maka

Ko dame ɗan mai ƙarfi yana da wuya

Wani ya je Sabulun Hajara

Sani na Aminatu

Naushi ɗaya na yi mishi

Wawa ko da na duba ya faɗi ya tafi bikita

Ya tashi yana faɗa da diri

Ba ka ji irin ta ba

Ka ji wadda ake gudu

Idan ruwa ya ɗauke fa kainuwa nasan

Ka ji harƙar duniya ɗaku

Don Allah Ɗan’adam

In kara faɗa muka

Sha’ani ra’ayi muke

In ba ra’ayi wuce kar ka ba mu abin

Doka ka je ka ajiye shi

Ka ji harƙar duniya ɗaku

Don Allah Ɗan’adam

In ƙara faɗa maka

Abin da baka iyawa

Kar ka yi shi haushi za ka ji in ka yi.

Post a Comment

0 Comments