"Ba wani abu ne ya sa na kira ku ba, abin da na ke so game da ku shi ne ku yi shiri ku tafi ku yiwo mini hari a ƙasar Gwari. Ina da wata babbar buƙata ne, saboda haka ina son ku yi shiri maza ku tafi”.
Tarken Littafin Shaihu Umar Na Sir. Alhaji Abubakar Tafawa Bisa Mazahabar Makisanci
Idris Abubakar
Hafsat
Muhammad
Hauwa
Mu’azu
Huwaila
Abubakar
Fatima
Muhammad Haruna
Hafsat
Alhaji Yaya
Department
of Nigerian Languages and Linguistics
Bauchi
State University Gadau
Gabatarwa
Wannan takarda da za a gabatar, za tai
bayani ne kan tarke/nazarin littafin “Shehu Umar” Na Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa. Sannan za a ɗora
aikin ne kan tsarin mazahabar Makisanci. Amma kafin mu kai ga yin wannan
nazari/tarke yana da matuƙar muhimmanci mu
haskaka masu sauraru hanya dangane da wannan mazahaba da za mu ɗora
aikin mu a kai, akwai buƙatar mu yi bayani
dangane da wannan mazhabar tare da kawo wasu daga cikin manufofinta, domin
hakan zai taimaka gaya wajen fahimtar madosar wannan aiki.
Mazahabar Markisanci ta samo asali ne
daga tunanin wani Bajamushe mai rajin neman sauyi a sha’anin tattalin arziki da
zamantakewar al’umma da kuma siyasar duniya mai suna Karl Henreich Marɗ (1818-1883). Shi dai mafalsafi ne kuma masanin tattalin arziƙin ƙasashe na ƙarni na 19. Ya fito da wannana ƙidar ne a cikin wani littafinsa mai suna, The German Ideology
(1845). Wannan mazahabr tana da wasu manufofinta, kaɗan
daga cikin irin wannan manufofi na markisanci su ne kamar haka:
1.
Tana duba sha’anin wasu rukononin jama’a da ake danne su, ko
ake ware su, ko ake ɗora musu wani nauyin da bai dace ba, akamr wariyar launin
fata, ko tauye ‘yancin mata ko mulkin mallaka ko ƙyamar ‘yan luwaɗi
da ‘yan maɗigo.
2.
Tana duba rikice-rikicen neman iko da na matsayi a cikin
al’umma.
3.
Sannan tana bayyana irin rikicin tattalin arziƙi da na mulki da zamantakewar al’umma tsakanin masu mulki da
waɗanda ake mulka (Talakawa).
4.
Tana gano sababbin hanyoyin fahimtar danganatak tsakanin
tattalin arziki da adabi da dukkan abubuwan da al’ada take samarwa.
5.
Tana amfani da fasahar fiɗar
adabi mai ƙunshe da batun aƙidoji da fito da yadda taurarin littafi ke mu’amala a
tsakaninsu ta la’akari da tattalin arzikinsu da yadda suke neman matsayi a
al’umma.
A
taƙaice wannan mazahabar tana lura da
sha’anin tattalin arziƙi da zamantakewa
da shugabanci (siyasa) da tarihin al’umma da kuma adabinta shi ake kira da
markisanci. Don haka mazahabar markisanci ta tarken adabi na lura da wasu
muhimman sassan nazari guda huɗu da suke ƙunshe da irin halayen rayuwar al’umma, kamar haka:
1.
Ƙarfin tattalin
arziƙin al’umma
2.
Rikicin neman matsayi a al’umma
3.
Abubuwa na zahiri da na ɓoye
4.
Aikin fasaha da adabi da aƙidoji
Daga
ƙarshe bisa ga wannan jawabi da ya gabata
a sama ya isa ya yi mana jagora wajen wannan aiki na tarke na littafin “Shehu
Umar” Na Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa.
Tarken
Littafin Shehu Umar Duba Zuwa Ga Mazahabr Markisanci
Dangane da wannan mazahabar kamar
yadda muka ambata a manufofinta a baya, ta fi mayar da hankali kan halayen
rayuwar al’umma da suka shafi ƙarfin
tattalin arziƙi da rikicin neman
matsayi a al’umma tare da duba sha’anin wasu rukunonin al’umma da ake danne su,
ko ware su, ko ake ɗaura musu wani nauyin da bai dace ba. Don haka wannan littafi
na “Shaihu Umar” Na Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa
zai iya hawa wannan mazahabar in muka duba cikin littafin tun daga farko har
zuwa ƙarshe kamar haka:
“Da dukkan mutane suka hallara, kowa
ya ba da abin da ya kawo, sai sarki ya ce “kai, ina Makau? Ko an kashe shi ne a
can ku ka ɓoye mini?”.
Jama’a duka suka amsa “A’a! Ranka ya
daɗe, ai ka san halin mutanen duniya. Mu ta ma mun yi shiru ne
kawai tun da farko da muka ga ka ɗauke
shi mu ga yadda za ku ƙare. Domin mun san
duk wanda aka ba shi amana ya ci lalle Allah yana kama shi, balle ma kamar kai
da Makau wanda ya ke ka yarje masa kamar naka. Bari dai mu feɗe
maka biri har wutsiya, a cikin garin nan ba ka taɓa
samun wanda yake cin amanarka kamarsa ba. Ai Makau ne ya ke fallasa ka a wajen
talakawa da ka ke ganin suna girman kan nan yanzu. Kuma babu asirin da za ka yi
da shi waɗansu ba su ji ba. Ka gani tun da muka fita zuwa harin nan har
muka dawo bawan Allah nan bai bar zaginka ba, a kan haka ma har sarkin zagi ya
ji haushi ya zare takobi zai yanke kansa, sai da barde ya ba shi haƙuri. Yanzu ma abin da ya sa ba ka gan shi ba a nan ya bi ta
gidansa ne domin ya ɓoye waɗansu daga cikin bayin da ya samo, gama dai bawa huɗu
ya kama, mata biyu da yara maza biyu; amma dai ba mu sani ba, ma ga abin da zai
kawo”.
Da sarkin ya ji waɗannan
maganganu sai ya ce “Daidai ne, amma Makau ya kyauta”.
Idan muka duba wannan jawabi da ya
gabata a sama za mu ga cewa tun a kanun littafin “An Ɓata Tsakanin Sarki da Makau”. Za mu ga cewa rikicin neman
duniya ya fito ƙarara a fili a
tsakanin taurarin cikin littafin. In kuma muka kwatanta wannan lamari da
abubuwan da suke faruwa a cikin rayuwar al’umma na yau da kullum, za mu iya
cewa wannan rikicin neman matsayin ba wai a iya kan ƙulla makirci ya tsaya ba, har da kisan kai, da asirce-asirce
duk dan dai mutum ya ga ya samu matsayi a cikin al’umma.
Dangane da taurarin cikin littafin
kuwa sun yi haka ne domin su raba tsakanin sarki da Makau, kuma haka abin ya
kasance har ma sarki ya kori Makau daga ƙasarsa.
Don haka wannan manufa ta mazahabar makisanci da take magana kan rikicin neman
matsayi da iko ya dace ko zai iya hawa kan wannan littafi na Shaihu Umar kamar
yadda muka ambata ko muka gani a shafi na biyar.
Dangane da wannan mazahabar ta
makisanci har iya yau tana duba sha’anin wasu rukunin al’umma da ake danne su,
ko ake ɗaura musu nauyin da bai dace ba. Za mu ga a cikin wannan
littafi na Shaihu Umar an samu wasu rukunin al’umma da aka mayar da su bayi ake
tauye musu hakki ake ɗora musu nauyin da bai dace ba, za mu tabbatar da haka in
muka dubi shafi na talatin da ɗaya (31) kamar haka:
“Da fitowata daga ɗakinsa,
in dai duba haka, sai na ga bayi cikin ƙangi
an shanya su kawai a rana. Da na daɗa
dubawa cikin bayin nan, sai na ga uwata da uban nan nawa, waɗanda
aka kamo ni da su daga gona. Daga nan sai zuciyata ta karaya, tsorona kuma ya
yi yawa. Ai da na ga haka sai na sunkuyad da kai na wuce, hawaye yana zuba a
idona. Na tafi gida, aka ba ni abinci, ga shi ina jin yunwa amma dole na bar
shi. Ba abin da nake tunani sai bayin nan. Yayin da duk na sunkuyar da kai sai
in gan su, kai na dai zama sai ka ce wanda aka kawo masa labarin ubansa da uwa
tasa sun mutu”.
Don haka a nan bisa hali ko yanayin da
Umar ya shiga a sakamakon ganin yadda bayanin nan suke ya isa cewa wannan littafin
yana magana ne a wani ɓangaren da ya shafi yadda ake danne wasu rukunin al’umma kuma
ake ɗora musu nauyin da bai dace ba a matsayinsu na bayi kawai.
Har ila yau, a wannan mazahaba ta
makisanci tana bayyana irin rikicin tattalin arziki da na mulki da zamantakewar
al’umma tsakanin masu mulki da waɗanda
ake mulka (talakawa). Idan muka dubi wannan littafi da muke tarkensa bisa
la’akari da wannan amzahabar za mu iya cewa kusan duk an gina wannan labarin ne
kan ƙarfin tattalin
arzikin al’umma, za mu tabbatar da haka in muka shiga wannan littafin kamar
haka:
“Tun a shafi na uku (3) za mu ga yada
ake fafutukar neman arziki tsakanin masu mulki da talakawa inda sarki ya sa aka
yi kiran dukkan fadawansa. Da suka taru ya ce musu, “Ba wani abu ne ya sa na
kira ku ba, abin da na ke so game da ku shi ne ku yi shiri ku tafi ku yiwo mini
hari a ƙasar Gwari. Ina da
wata babbar buƙata ne, saboda
haka ina son ku yi shiri maza ku tafi”.
Da fadawan nan suka ji wannan magana
ta sarki duka sai suka zama kamar mahaukata sabili da farin ciki, suka yi ta
murna suna cewa “Da ma mai neman kuka, balle an jefe shi da kashin awaki”!.
Dalilin farin cikinsu kuwa shi ne don ka sani a wajen harin nan za su yi samuwa
da yawa na dabbobi har zuwa bayi. Kuma in sun dawo sarki zai sam musu rubu’i
daga cikin abin da suka samo. Ko wataƙila
in mutum ya kama bayi uku sai sarki ya ɗauki
biyu daga ciki, shi kuma bar shi da ɗaya.
Don haka a nan za mu iya cewa an samu
rikicin tattalin arziƙi a cikin wannan
littafin tsakanin masu mulki da waɗanda
ake mulka (Talakawa). Wannan hari kuwa da sarki ya shirya, dalilinsa wai dan
yana son ya sami waɗansu bayi ne waɗanda
zai gama da nasa ya aika da su Kano, domin a sayo masa tufafi da kayan doki waɗansu
kuma ya aika da su Bida domin a sayo masa bindigogi.
Saboda haka, yanayin tattalin arzikin
al’umma yana nuna irin halin da take ciki da wanda za ta iya kasancewa a nan
gaba. Mawallafin yana nuna yadda ake da ƙarancin
samuwar wasu abubuwan rayuwar kamar su kayayyaki, sutura, da dawakai da kuɗi
na masarufin yau da kullum cikin jama’a. sannan waɗannan
abubuwa da aka lissafo talakawa ne dalilin samar da su amma ba su da halin
mallakar su, to in suka gane ana tauye musu haƙƙi lallai za a samu rikici. (Dobe, 2009:93).
Saboda haka, a wannan littafi na
Shaihu Umar an nuna haka a fili domin kamar yadda aka nuna a shafi na uku su
kansu talakawa su ne silar samar da abubuwan more rayuwar na yau da kullum zuwa
ga masu arziƙi. Kenan an nuna
ko mawallafin wannan littafin ya nuna cewa talakawa a cikin kowanne rukunin
al’umma su ne suke samawa masu arziƙi
ko masu mulki matsayi da suke tinƙaho
da shi.
Haka zalika an ƙara fito da rikincin neman matsayi a wannan littafi na Shaihu
Umar a shafi na takwas (8) inda sarki ya sa aka yaso kayan Makau har da
dabbobin Umar na gado, sai Makau ya tashi ya cewa sarki “Ranka ya daɗe,
ina roƙon a cikin kayan
nan akwai waɗansu waɗanda suke ba nawa ba, kayan maraya ne”.
Da jin haka sai fadawa suka ɗauka
gaba ɗaya “Mhm kun ji ya fara irin ƙaryan nan tasa! Ina ka ga wata dukiyar maraya har da za ka ce
tana wurinka? Allah ya daɗe da sarki, ƙarya
ya ke yi, ita dukiyar marayan da ya ke faɗi
ba wurinsa ta ke ba. Tana wajen uwar yaro, ita ta san inda ta kai abinta.
A wannan wuri fadawa sun yi waɗannan
maganganu ne domin su sake samun wurin zama ko gindin zama a wajen sarki. Don
haka a nan wurin ma za mu iya cewa an samu rikice-rikice na neman matsayi a
tsakanin taurarin littafin.
Dangane da sha’anin tattalin arziki
kuwa in muka dubi shafi na 11-15 inda Makau ya sadu da maharbi, ya masa nuni da
ya zauna a Maƙarfi sakamkon
Makau ya ce yana son yin sana’ar nema ne. za mu ga cewa wannan littafi ya
shafir harkan tattalin arziki kamar yadda mazahabar makisanci take magana a kai
in muka dubi shafi na 12 inda Makau ya ce, “Wai da ni buƙatata ina so in tafi wani ɗan
ƙauye ne wanda ya ke tsakanin Zazza da
Kano in yi zamana. Domin buƙatata
yayin da na sami matsuguni sosai sana’ar da zan yi ita ce noma.
Saboda haka ke nan mawallafin wannan
littafin ya fito ƙarara ya nuna
harkan tattalin arzikin al’umma a wannan labarin. Domin noma a wannan zamani
kusan babu wata hanya ta bunƙasa
tattalin arziki da ya wuce sana’ar noma don haka ne ma ake mata kirari da cewa
“Noma tushen arziki”. A wannan littafin an ambaci wuraren noma da lambuna da
dama kamar a shafuka kamar haka:
A shafi na 4 an ambaci gona a lokacin
da ‘yan hari suka isa ƙauyen nan da sarki
ya tura su ƙasar Gwari domin
yin hari. Su Makau sun ɓuya a bakin gonaki ne, da sassafe wajen goshin asalatu, sai
arna suka fara fitowa daga gidajensu suna zuwa gonakinsu. A lokacin nan kuwa
ruwan sama ya fara sauƙa dukan manoma za
su yi ta gyaran gonakinsu”. Kenan mawallafin ya ambaci abubuwan da suke bunƙasa tattalin arziki kamar su noma a cikin labarin kamar yadda
muka faɗa.
Haka a lokacin da kura ta cinye ɓarawon
Umar a shafi na 21 nan ma an ambaci gona a matsayin wurin da ake samar da
arziki za mu tabbatar da haka in muka shiga littafin a shafi na 21 kamar haka:
“Kura ta cinye ɓarawo
na”.
Lokacin da masu nemana suka koma
tsakar dare ta yi da mutumin da ya sace ni ya ji daji ya yi shiru, sai ya ce da
ni, “yanzu mun huta ko? Mu tashi mu tafi. “Sai ya ɗauke
ni a wuya ya yi ta tafiya da ni a cikin daji har muka kawo wani ɗan
gona”. Kalmar gona ta sake bayyana a cikin wannan labarin.
Haka zalika, wannan littafi na Shaihu
Umar ya dace da wannan mazahaba ta makisanci domin har yanzu in muka duba shafi
na 35 mawallafin ya fito da ƙarfin
tattalin arzikin al’umma a wannan shafin domin kanun shafin ma ya tabbatar da
haka “Mun Taɓa Ciniki”. A lokacin da su Umar suke tafiya a cikin hamada
sun zo wani gari inda suka yada zango a buɗe
harkan saya da sayarwa kamar haka:
“Bayan an jima kaɗan
sai na ga mutanen garin mata da maza suna ɓarkewa
zuwa gare mu. Kuma in duba haka sai na ga kowane bafatake daga cikinmu ya
kwance kayansa ya fito da baƙaƙen rawuna da zannuwa irin waɗanda
a ke yi a Kano. Daga nan kuwa sai na ga wurin duk ya hargitse sai ciniki a ke
yi. Fataken nan suka yi ta ciniki har rana ta yi sanyi, zuwa can wajen la’asar
sai na ga kowa ya kama kayansa ya ɗaure.
Da almuru ta fara kusantowa sai kuma aka buga kuge muka tashi.
Idan muka duba wannan wuri a shafi na
35 sai Alhaji Abubakar Tafawa Ɓalewa
ya bayyana irin ƙarfin tattalin
arzikin da al’ummar take da shi a wannan lokacin. Domin masana ilimin kasuwanci
sun bayyana cewa “Duk ƙarfin/kuɗin
mutum ba zai iya rayuwa shi kaɗai ba”. Ta wannan hanyar
saya da sayarwar ita ce hanyar da wani zai taimaki wani, abin nufi wannan
hanyar ta zama wajibi a cikin al’umma sai an bi ta. Sannan tana bunƙasa/haɓaka tattalin arzikin al’umma ta ƙasa baki ɗaya.
Baya ga ƙarfin tattalin arzikin al’umma, wannan mazahaba ta makisanci
tana duba abubuwan zahiri da na ɓoye
da suka fito a cikin labarin/adabin. Dangane da abubuwan na zahiri waɗanda
mai karatu ba zai manta da su ba, da suke faruwa a cikin wannan labarin sun haɗa
da:
1.
Shaihu Umar shi asalin mutumin Kagara ne
2.
Yadda aka ɓata tsakanin sarki da
Makau
3.
Haɗuwar Makau da Maharbi
4.
Yadda ɓarawo ya sace Umar da kuma yadda aka yi kura ta cinye ɓarawon
Umar
5.
Sayar da Umar ga Balarabe (Abdulkarim)
6.
Karatum Umar a Ber Kufa
7.
Fitan gyatumar Umar zuwa nemansa
8.
Haɗuwar Umar da mahaifiyarsa
9.
Tasowar iska ta turniƙe
su Umar da Abdulkarim
A
taƙaice waɗannan
su ne irin abubuwan da suka faru na zahiri a cikin wannan littafin na Shaihu
Umar waɗanda masu karatu ko masu sauraro ba za su taɓa
mantawa da su ba.
Har yanzu wannan mazahabar tana duba
irin abubuwa ko aikin fasaha ko aikin ɓoye
da suke faruwa a cikin adabi. dangane da wannan littafi na Shaihu Umar akwai
abubwa da dama da suka faru a ɓoye tare da nuna aikin
fusaha kamar haka:
“A shafi na 22 an samu aikin fusaha a
daidai lokacin da kura ta cinye ɓarawon
Umar lokacin da mijin matan nan ya zo lambu ya tarar da abin da ya faru, kamar
yadda ya faru a shafin kamar haka: “Da zuwansa sai suka labarta masa duk abin
da ya auku. Bayan haka sai ga tufafin mutumin ya shiga binciken abin da ke
akwai. Da buɗe rigar mataccen sai ga wata babbar zabira, ba kome a ciki
sai soyayyen nama, da danda ƙwarya,
da garin soye, da wani ɗan ƙoƙo. Kuma ya duba ‘yar ciki sai ya ga waɗansu
layu guda biyu, ɗaya an mata rufi da fatar goshin damisa da sasari a hancinta.
Ɗayar kuwa da fatar minjiyar aka rufe,
aka ɗinke da jijiyar biri. Ita layan nan ta biyu kuma a cikin wani
yankin tsumman saƙi aka ƙunshe ta. A nan kuma ya sa kitsen mutum wanda ya ke milke ta da
shi”.
“A taƙaice in gajarta maka magana dai, da ya dudduba kayan mataccen
nan sarai sai ya ajiye zuciya ya ce, “lalle wannan mutum ba uban yaron nan ba
ne, ba shakka ya sato shi ne daga wani wuri, domin waɗannan
kaya babu mai irin su sai masu sane ko ‘yan ƙwance”.
Saboda haka a wannan wuri aikin fasaha ya tabbata.
Dangane da abubuwan ɓoye
kuma “spiritual life” da suka faru a cikin wannan adabin/labarin in muka duba
shafi na 47 lokacin da su Abdulkarim da Umar da mutanensu suna cikin tafiya,
sai suka ji kuwwa daga wajen ‘yan’uwansu da suka tafi yawo, sai suka hango su a
guje-rudididi kamar wasu garken uda. Da suka duba sama sai suka ga hadari ya
tokare sararin smaaniya ɓaƙi-ƙirin. Ashe ba hadari ba ne. iska ce kawai ta girma ta zama
hadari. A cikin iskar kuwa ba kome sai yashi. Yayin da iskar ta kawo wajensu
nan sai wurin ya hargitse, ba sa iya ganin kome balle su san inda wani yake.
Iskar nan ba ta tashi yin sauƙi
ba sai bayan wani lokaci mai tsawo, kana ta ɗan
kwanta. Da idon Umar ya buɗe sai ya duba cikin
sararin nan sai ya ga babu kowa sai shi ɗaya”.
Saboda haka za mu iya cewa wannan wani
ɓoyayyen labari ne da ubangiji ya zantar da hukuncinsa a
lokacin da ya so. Sannan kuma wannan ba wani abin mamaki ne don ya faru ba.
An sake samun wannan ɓoyayyun
al’amura a shafi na 48 lokacin da iskar nan ta rufe kowa sai Umar shi kaɗai
ya rasa inda zai yi, ya tsaya kawai yana jiran mutuwarsa. “A rana ta huɗu
wajen la’asar yana kwance sai ya ji kuka kamar na raƙumi sai gabansa ya faɗi,
ya ɗaga kai, sai ya hango wani raƙumi daga nesa da labtu ya nufo inda yake. Ashe raƙuminsa ne wanda ya gada, sai ya ga ya durƙusa a gabansa na kai gare shi na dubi salkar ruwa na sha.
Hankalinsa ya komo, sai ya yi godiya ga Allah.
Saboda haka, wannan al’amari ma za a
kira shi da “spiritual life”.
A taƙaice wannan shi ne tarken littafin Shaihu Umar wanda aka ɗora
aikin a mazahabr makisanci, wanda muka duba wasu daga cikin manufofin wannan
mazahabr kamar su: Ƙarfin tattalin
arzikin al’umma, abubuwa na zahiri da na ɓoye
tare da aikin fasaha. Duk waɗannan batutuwa mun fito
da su a cikin wannan littafin tare da kafa hujja mai ƙarfi.
Manazarta
Tuntu masu gudanarwa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.