Ticker

Waƙa a Bakin Mai Ita: Fashin Baƙin Karin Maganar Nan Ta "Ka Fi Ɗandakon Jega Sani" a Bakin Ɗan Jega

 Ka Fi Ɗandakon Jega Sani!

Abbas Musa Jega
abbasmusajega750@gmail.com
08036152617
Dan dako

A ɗan binciken da na yi, zan iya hasashen cewa karin maganar bai jima sosai ba, domin ana iya  duk wani mai shekaru talatin da wani abu zuwa sama, zai iya tuna wani abu game da labarin wani shahararren ɗan dako da aka yi a Jega wanda ya yi suna da "Ɗanhwarin" ke nan idan haka ne zan iya cewa karin maganar zai iya dangantuwa kai tsaye ga shi wannan sanannen ɗandako da aka yi a Jega wanda aka fi sani da suna Ɗanhwari. 

Shi dai Ɗanfari kamar yadda waɗanda suka san shi sosai suka bayyana, "Mutum mai dakon harawa wadda ake baiwa dabbobi, kusan a iya cewa duk da faɗi da girman garin Jega, idan aka yi masa kwatancen wani gida zai iya gane wajen ba tare da wata wahala ba, mutum ne mai matuƙar basirar gane kwatance, daga cikin abin da ke tabbatar da basirarsa shi ne, ga shi dai mutane suna yi masa kallon marar cikakken hankali amma duk yadda aka yi masa kwatancen gida zai iya gane gidan, zai iya kuma gane gidan ko da bayan kwanaki ne, matuƙar ya ga wanda ya yi masa kwatancen a baya. Kuma idan ka saba ba shi dakon kaya ya kai gidanka, aka yi kwanaki ba ku haɗu ba, zai iya bayyana maka adadin juma'a nawa aka yi ba ku haɗu ba, da an yi lissafin kuma sai a dace da abin da ya faɗa. Bugu da ƙari  kuma an tabbatar da cewa idan ya saba kai harawa ko haki (ciyawa) a wani gida, a bar maganar mutanen gidan hatta dabbobin gidan zai iya shaida su idan ya gan su a wani waje. 

Wani abu ya taɓa faruwa da tunkiyar wani da ya saba kaiwa harawa, aka sace ta, aka yi neman duniya ba a ganta ba, wata rana, Ɗanfarin ya je Turaku (Kara) sai ko ya ga tunkiyar, ya kuma shaida ita ce dai wadda ya sani, wato wadda yake kaiwa harawa, sai ya je gidan da ya saba kai wannan harawa ya gayawa matar gidan cewa ya ga tunkiyar a kasuwa;  "Ajiya ajiya na ga tunciyam nuko" (Hajiya na ga tunkiyar Miko) sai ko Hajiya ta bi shi a baya sai karar Jega, ya kurɗa nan ya kurɗa nan da Hajiya, sai ga tunkiyar, Hajiya na ganin tunkiyar, ta je ta kamo ta, ta kwance mata ɗaurin da aka yi mata, ba ko wanda ya ce mata komai, ta yi gida da ita. 

Saboda wannan basira ta wannan ɗandakon sai ya zamto idan mutum na magana da wani a kan wani abu da kowa ya san shi a tsakaninsu, sai ɗayan ya ce masa ai ka fi "Ɗandakon Jega Sani". Yau da gobe sai abin ya zama karin maganar da ake amfani da shi a Jega har da wasu manyan garuruwan da ke kewaye da ita. sanadiyyar wannan rubutu shi ne; wani malamin adabi ne da ke aikin a Kwalejin ilimi ta Shehu Shagari a Sakkwato mai suna Shamsuddeen Isma'il (Ph.D in view), ya yi min tambayar asalin karin maganar.

Post a Comment

0 Comments