In Zauren Waƙa Journal of Hausa Poetry Studies, Vol. 1 No 2, Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto. Pg 15-34/ ISSN: 2384-5139
Salo A Waƙar Baka Ta Hausa:
Misali Daga Waƙoƙin Makaɗan Jama’a Waɗanda Suka Yi Wa Mata
Rabi Mohammed
Jami’ar Jihar Kaduna, Nijeriya.
Email: rabimohammeddatti@gmail.com
G.S.M: 08060771666/08080381801
Tsakure
A Hausa an san waƙa iri biyu ce a dunƙule,
wato ta baka da kuma rubutatta. Waƙar baka kuwa, ita Hausawa
suka daɗe da
sanin ta wadda kuma tana daga cikin manyan rukunan adabin baka ɗin. Umar M.B
(1987:7), a tsammaninsa ya ce, “ Adabin ya faro ne tun sa’ar da Bahaushe ya
fara buɗe baki
ya yi magana a fahince shi. Wato tun tasowarsa, ƙafa da ƙafa
suke tafiya da al’adun gargajiya na Hausa.” Ta wata fuskar kuma, an ayyana waƙa ko ta
baka ko rubutatta, a matsayin wadda take taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙo, a
lokaci guda kuma ta nishaɗantar (Furniss G 1996). Kuma an tabbatar da lallai masana
manazarta waɗanda suka gabata sun yi bakin ƙoƙari
wajen fito da nau’o’in adabin ta fuskar
feɗe
jigoginsu da salonsu. Kama ya zuwa yanzu abin tubarkalla tunda har da su kaza a
cin danƙo . Domin nazarin mata a Adabin Hausa ya fara tsayawa da ƙafafunsa
tunda har a wasu Jami’o’in ƙasar nan ana nazartar fagen a matsayi kwas tare da
gudanar da rubuce-rubuce game da gudummawarsu da kuma kula da abin da ake faɗa a kansu wanda a
farkon al’amari, masu nazarin Adabin Hausa ba
su ba ɓarayin mata muhimmanci ba saboda mayar da su tun
farko saniyar ware a cikin al’umma. Ga
shi kuma mata sun mamaye wasu nau’o’in adabin baka. Har ma ya zuwa lokacin
jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da bayan jihadin duk sun bayar da gudummawa a
rubuce.( Balbasatu I.1998). Tunda ana fito da jigogin da suka shafi mata a
adabance, to manufa a nan kuma ita
ce nazarin salon da ke cikin wasu waƙoƙin don
ci gaba da faɗaɗa wannan fanni yadda al’umma za su amfana.
01.Gabatarwa
Wannan
nazari zai yi tsokaci ne game da irin salon da mawaƙan baka (musamman
makaɗan jama’a) ke amfani
da su wajen isar da saƙonsu ga al’umma. Tsokacin zai tsayu ne ga waƙoƙin da aka gina
jigoginsu game da rayuwar mata. Yin hakan na da muhimmanci domin in ba don salo
ba, da wataƙila hankali ba zai karkata ga waƙoƙin ba balle mata su
saurare su har su amfana da su. Ire-iren salon da za a nazarta sun shafi salon
sarrafa harshe da ma wasu nau’o’in salon da suka haɗa da na hira ko
labari da kuma ƙarangiya.
02. Ma’anar Salo
Kalmar
salo ba baƙuwa ba ce ga Bahaushe, don haka masana, kuma manazarta
harshe ta fuskar Adabi sun ba da gudummawa wajen bayyana ma’anar salo cikin
jimloli dogaye da gajeru.
Yahya,
(2001) ya bayyana ma’anar Salo da:
“Dabara ko hanya ko wayo” ko kuma: “Salo kwalliyar magana ce mai tasiri kan mai
jin ta” ya ci gaba da cewa a dunƙule “Salo dabara ce
ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana”.
Gusau
(2002: 54) cewa ya yi “salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin
furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin
harshensa da zaɓar abubuwan da suka
dace da abin da yake son bayyanawa”.
Emilda
(2003:32), ta ayyana ma’anar salo da cewa, “salon Adabi wata hanya ce da
marubucin Adabi ke amfani da ita wajen isar da saƙonsa ga masu
sauraronsa / `yan kallonsa”
Ɗangambo
(2007:37), ya ba da ma’anar salo da cewa “Bisa jimla, muna iya cewa salo shi ne
hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”
Idan da za a bi
diddigin yadda waɗannan malamai suka ba
da ma‘anar salo, za a iya cewa lallai salo na nufin dabara ko hanya da kan sa
hankali ya karkato har ya fahimci abin da ake nufi. Alal misali, su kansu waɗannan malamai da aka
ambata, kowannensu ya yi amfani da salo wato dabararsa wajen ƙoƙarin gamsar da mai
karatu ya fahimci ma’anar salo.
Misali Yahya, (2001:1-2) ya kwatanta ma’anar salo da bin diddigin ƙuruciyar yaro a tsakaninsa da mahaifiyarsa inda takan
ce da ɗanta “Kai raba ni da
salo” musamman idan yaron na buƙatar wani abu. To a nan ne ya nuna
lallai salo shi ne dabara ko hanya wadda a cewarsa ita ce dahir. Ya ci gaba da
bayaninsa cikin dabara inda, ya danganta ma’anar salo da ƙaulin Hausawa inda
sukan ce “Salon Magana” ko “Sabulun Salo” wato magana ba wadda aka saba ji ba,
ko kuma, sabulu ba wanda ake saurin kawowa a zuciya ba.
03. Salon Sarrafa Harshe
Bisa yadda aka fahimci ma’anar Salo, sai a iya cewa, salon sarrafa
harshe na nufin dabara ko hanya da ake bi a yi wa harshe ado ko kwalliya domin
a isar da saƙo ko manufa. In mawaƙi bai yi amfani da
dabarun zaɓo kalmomi ba waɗanda zai gina ko tsara
waƙarsa
ta kasance mai jawo hankali ba, to akan ce ya yi amfani da lamin salo wato salo
mara karsashi.
Mawaƙan baka gwanaye ne
wajen yin amfani da salon sarrafa harshe ko adon harshe a cikin waƙoƙinsu. Yayin da kuma
akan sami wasu jefi-jefi suna yin amfani da lamin salo wajen isar da saƙonsu ga jama’a. Daga
cikin dabarun da ake amfani da su don yi wa waƙoƙi na baka ado akwai,
kinaya da kamance da jinsarwa da alamtarwa da zayyana da salon hira ko labari
da Ƙarangiya
da dai sauransu. Waɗannan nau’o’in salon
da aka ambata, su za a yi bayani tare da misalai daga cikin waƙoƙin da aka yi su domin mata.
03.1 Kinaya
Salon kinaya dabara ce ta sakaya ko lulluɓe magana ta zauna a
madadin wata maganar wato in an yi kinaya akan nashe ma’anar asali zuwa ga
sabuwar ma’ana mai kama da ta asalin don dai a isar da wata manufa. Don ƙarin bayani, duba
Yahya, (2001 :59-67) da Gusau, (2003:60).
Mawaƙan baka, gwanaye ne a
fagen amfani da salon kinaya cikin waƙoƙinsu. A dubi abin da
Babangida Kaka Dawa ke faɗi a cikin waƙarsa ta matsalar
aure:
Matan garin
ga sun yi yawa
Kuma sun cika
tumɓulɓul
Kuma ba su
son aure,
Sai
sun biɗi mai kuɗɗi
Kalmar tunɓulɓul kinaya ce da ta nashe ko ga lulluɓe ma’anar cikar
budurcin mace wato mace wadda ta balaga
ke nan. A maimakon ya yi ta zayyano alamomin balagar `ya`ya mata sai ya dunƙule a kalma ɗaya.
Shi ma Shehu Aljilo,
a cikin waƙarsa da ya yi ta ‘Aure’, akwai salon kinaya a inda yake
cewa:
Yara na yi Gabas na yi Yamma,
Na dawo Tsakiya na Zauna,
Har nai kudu na tai Arewa,
Na dawo tsikiya na zauna,
Na ga du ban ga wuyar
aure ba,
In ka tuna da matar
aure,
Yo komi taka yi lada
ne
A ƙashen
wannan ɗiyan sai ya
ce:
In ta gyara gado lada
ne,
Balle a ce dare ya
raba biyu,
Ta zo
ku fara bautar Allah
A farkon wannan ɗiyan, ya yi amfani da
kalmomin gabas da yamma kudu da arewa a matsayin wuraren da ya kewaya don ya
nuna cewa ya ƙure tunaninsa ko ya yi nazari ya gano cewar aure ba wata
wahala ba ce illa ma lada da ake samu a cikinsa. Sa’ananan ya ƙara yin kinaya inda
ya ɗauki bautar Allah a
tsakiyar dare a matsayin jima’i tsakanin
miji da mata, wanda kuma shi ne ainihin ruhin
aure, kuma ladansa ya ɗara duk wasu nau’ukan ayyukan lada a gidan aure.
Har ila yau, a ɗiya ta gaba, Shehu
Ajilo ya ƙara amfani da salon
kinayar inda ya ce:
Babban abin mamaki
Jaki da kaciya, Sa babu.
Wato ya kwatanta, ya siffanta karuwa a
matsayin Jaki, matar aure a matsayin Sa, Jaki dai dabba ne mara daraja ta fuskar haramcin cin namansa
kuma ɗabi’ar Jaki a
matsayinsa na dabba, in an kwatanta da sauran dabbobi, shi daƙiƙi ne wanda sai da
bulala ake shawo kansa. Duk da wannan ƙasƙancin sai ya zama
Allah Ya yi masa wata daraja ta kaciya wadda shi kuma Sa ba shi da ita. Shi
kuma Sa duk da rashin wannan daraja ta kaciya, sai ya zama mai daraja ta fuskar
halaccin ci da kuma sarrafuwa cikin sauƙi. Hikimar a nan ita
ce, ita karuwa komai kyaunta, da kwalliyarta da wasu aikace aikace da za ta yi
don mazan da take hulɗa da su, duk banza ne
domin kuwa tana cikin muhalli ne na haramcin da babu lada sai dai zunubi. Ita
kuwa matar aure, duk da an ba ta matsayin Sa mara darajar kaciya, sai ya zama
karuwa ba ta kai darajarta ba. Saboda matar aure tana cikin muhallin halaccin
da komai ta aikata mai kyau ga mijinta, lada za ta samu daga wurin Allah.
03.2 Kamance
Salon kamance salo ne na babban salon
siffantawa wanda ke bayyana wani abu ta fuskar kwatanta shi da wani abu daban.
Wato siffanta mutum da cewa ya yi kama
da wani abu, amma ba shi ne abin ba,. Yahya, ( 2001: 67) A irin wannan salon ana
amfani da kalmomi irin su kamar, ya, fi, wuce, zarce, kasa da dai makamantansu.
Kamantawa tana iya kasancewa ta daidaito ko
fifiko ko kasawa, waɗanda akan gane su ne
da irin kalmar da aka yi amafani da ita wajen kamanta abubuwa. Shehu Karamba mai Gurmi ya yi amfani da kamancen
fifiko a cikin waƙar da ya yi wa
mata ta reno kamar haka:
Uwa ta ɗar ma,
Kai uwa ta ɗar ma rainawa,
Cewar Usman mai tambarin Gurmi yaro!
Wato mawaƙin ya yi ƙoƙarin kamanta irin
muhimmancin mace a tsakanin al’umma da cewa, ita ba banza ba ce, abar a
girmama ce, ta wuce raini.
Haka shi ma Haruna
Uji a waƙar da ya yi ta ‘aure’ yana cewa:
Wai ko kun san aure?
Wai daɗi na aure,
Meye ya fi uwa
kuma?
Kuma miye ya fi
uba,
Wallahi shi ko aure.
A ƙoƙarinsa na nuna irin
muhimmanci aure shi ne ya kamanta wato ya siffanta darajar aure da ta iyaye
cewa auren shi ne ya fi. Ke nan shi ma ya yi amfani da salon kamancen fifiko.
Har ila yau, mawaƙin nan Alhaji Sanin
Balɗo, a waƙarsa ta zaura, ya yi
amfani da salon kamancen a ɗiyoyin waƙar daban- daban. Misali, akwai inda ya
ce:
To don
tsananin ban ra’ayin zaura,
Don ta gaishe ni da aiki,
Gwamma ya zama na ɗakko sumogal
Kwali goma,
`Yansanda goma su kama ni,
Moba Polis goma su irke mu,
Can daji a yi ta duka ta,
Sai ka hwaɗi.
To, Alhaji Sani ya hi ɗumin zaura.
A wata ɗiyar kuma sai
yake cewa:
Don tsananin ɗai ban
ra’ayin zaura,
Ni nan da a ce mini ga zaura,
An ba ni tare da mota 505.
Ya ci gaba a can
gaba:
Ni gwamma
a ba ni aron keke,
Ko tsoho na, duk da na sata na,
A ra’ayin mawaƙin saboda irin
sharrin da bazawara ta yi masa ya sanya ya ƙi jinin ta inda har
yake kamanta cewa, gara ya faɗa wasu sharrukan kamar zama ɗan sumogal ko aron
kayan sata, duk a ma kulle shi a kan hakan, ya fi da halayen bazawara, don a
cewarsa, ba su kai sharrin bazawara ba.
Haka kuma akwai inda Sanin Balɗo ya yi amfani da
salon kamancen daidaito da ma na fifiko kamar haka:
Don na san
ta, kowaj ji wuyar zaura na hi shi,
Kai irin
wagga hali mu Ɗan Balɗo,
Kamak kura ta iske farin rago,
An turke
yamma garai dannai ya hwaɗi,
A tunanin mawaƙin, ya fi duk wani
wanda ya yi hulɗa da bazawara shan
wuyar ta da kuma sanin halinta wanda har ya sanya ya kwatanta sanin halayyar
bazawara da ya yi tamkar kura ce da ta iske rago ba tare da wani shamaki ko
kariya ba, Ka ga ta sami garaɓasa ke nan. Farin rago don ko a duhu ne, nan da nan za a
gan shi, ballantana ga kura mai biɗar nama, ta same shi ba kariya, ai ta sami
banza.
Har ila yau, akwai wani misalin na kamancen
daidaito da za a iya gani, inda Sale Mai Gambara ya yi amfani da shi a waƙar da ya yi ta
Alkalin Tsafe, kamar yadda ya ce:
Na je roƙon mai gari,
Na duba fadarshi,
Ban ga turken doki ba,
Da matansa guda uku,
Uwag gidan sai ta fito mana,
Tsawon baya sai ka
ce azara ɗaya kan gada,
Ma bi uwag gida kuma ta fito mana,
Cikin nan a waje ɗaya,
Ya tsoho ya sa
tsala,
Da
kaka ya ɗau dami.
Mawaƙin ya kwatanta ko ya
kamanta bayan uwargida da azarar da ke shimfiɗe ko miƙe bisa gada. Ita kuma
ma bi da uwargida ya siffanta cikinta tamkar tsoho ne ya sanya wando tsala,
wato ɗamammen wando ba tare
da ya sa riga ba, za a ga cikinsa a waje.
03.3 Jinsarwa
Amfani da harshe a ɗauko halayya ko
darajar wani abu a liƙa wa wanda ake magana a kansa, shi ake nufi da, jinsarwa.
Misali, akan ɗora wa wani abu da ba
mutum ba, darajar mutum, wadda ake kira salon mutuntarwa. Ana kuma ɗaukar hali ko yanayi
ko daraja ko ɗabi’a ko aikin da aka
fi sanin dabba da shi a ɗora wa mutum,
wanda shi ake kira da salon dabbantarwa.
Haka kuma, akwai salon jinsarwa da akan ɗauki hali ko ɗabi’a ko daraja ko
yanayi na wani abu wanda ba dabba ba, a liƙa wa mutum. A irin
wannan sai a ce an yi amfani da salon abuntarwa ke nan. Don karin bayani, duba
Yahya, (2001:79-88).
Mawaƙan baka na Hausa, su
ma gwanaye ne wajen yin amfani da wannan salon
jinsarwa. Ga misali:
Hajiya Barmani Coge,
a waƙar da ta yi ta kishiya, ta yi amfani da salon dabbantarwa
inda ta ce:
Ku tsaya ku ji sunan kishiya,
Baƙin maciji mai cizon tsiya
Karya, matsattsaku mai baki ɗari,
Mai haƙorin cizo,
shegiya,
In ta kama, sai ta girgiza.
Mawaƙiyar ta kwatanta, ta ɗauki halayyar muggan ƙwari da dabbobi
musamman maciji irin baƙin nan mai cizo, ta liƙa wa mutum (kishiya).
Sannan ta liƙa ma kishiya siffa ta karya da kuma matsattsaku.
Shi ma Musa Ɗan Goma, ba a bar shi
a baya ba wajen amfani da salon dabbantarwa. A cikin waƙar “Karuwa Gamsheƙa”, akwai inda ya ce:
Allah raba
mu da gaurakar gari,
Sarkin yawo tsohuwar karuwa,
Zuwa daga
Legas ta ɓullo Gusau.
Ya kwatanta ko ya siffanta ɗabi`ar wata tsuntsuwa
wato ‘Gauraka’ mai yawo da irin halin karuwa na yawon tsiya, ba ta a wannan
gari, ba ta a wancan gari.
Baya ga dabbantarwa, a salon jinsarwa, an
ambaci salon mutuntarwa wanda shi ma za a iya ganin misalai daga cikin ire-iren
waƙoƙin baka. Kamar
Babangida Kakadawa mai kiɗan kuntugi, daga
cikin waƙar da ya yi ta ‘Matsalar Aure’ yana faɗin:
Duniya! Ban zo da garaje ba,
Duniya! Kuma ke nika son aure,
Duniya! Kuma ke nika wa kuka,
Ba kukan kuɗɗi ba,
Ba kukan
riga ba,
Raina nika
wa kuka,
Idan wata
ran kai ne,
Wata ran ba
kai ba.
A nan yana nuna duk
wani abu mai daraja a duniya ba a samun shi cikin sauƙi. Saboda haka, sai
ya kawo mace a matsayi wadda ke da
daraja kuma a Bahaushiyar al’ada akan
tsananta wajen aurenta don mai aurenta ya riƙe ta da mutunci. Don
haka sai ya ɗauki duniya kacokan
ya mutunta ta, ya nuna cewa, ita yake son aure, ga shi kuma ita ba matabbata ba ce.
Har ila yau, a can gaba ya fito da
wannan salon mutuntarwar, ya ce
Malaman ƙasarmu sun yi
kiran,
Aure ya rage kuɗɗi,
Sarakunanmu sun yi kiran,
Aure ya rage kuɗɗi,
Iyaye ku duba,
Ku hango matsalar aure.
A madadin mawaƙin ya ce iyaye su
rage kuɗin aure sai ya ce
auren ne da kansa, ake kira da ya rage kuɗin. A nan aure ya komo tamkar mutum ke nan.
Ita ma Barmani Coge
ta yi amfani da salon mutuntarwa mai jawo hankali kamar yadda ta ce:
Kuma ran asabar na sha daɗi
A gidanta ta Sani da Alhaji Sambo,
Na ci alkakin sunan Rahaman,
Na ji hantata na guɗa,
Rannan na ji
hanjina na shewa
Mawaƙiyar a ƙoƙarin cin ma manufarta
a wannan waƙa don ta jawo hankalin jama’a su saurari waƙar sai ta mutunta
hanta da hanji, ta ba su matsayin mutum
inda ta nuna hanta ta yi guɗa hanji kuma na shewa a sakamakon cin alkakin da ta yi
duka a gidan bikin suna don nuna tsananin farin cikin wannan haihuwa da Bilki
ta yi ta gwarne, kuma don dai ta ƙarfafa wa mata gwiwa
su saki jiki da mazansu su yi ta haihuwa don ko arziki ce.
Idan aka karkata ga ɗaya nau’in jinsarwar
wato salon abuntarwa, nan ma mawaƙan baka na Hausa na
badali a ƙoƙarin da suke yi don isar da saƙo, misali in muka
waiwaya ga waƙar Babangida Kakadawa wadda aka ambata, ta matsalar aure,
a wata ɗiyar waƙar yana cewa.
Isah gurgu Allah ya kiyaye sa,
Tsohon gwado mai ƙai-ƙai,
In anka taɓa ƙura,,
In anka rufa zahi,
Mawaƙin ya siffanta mutum
da wani abin da ba shi da rai wato gwado wanda yake tsoho ne da aka yi amfani
da shi tsawon lokaci, kuma yana ajiye ya sha ƙura, A irin wannan
hali, in an ɗauko gwadon nan za a
iske saboda kaurinsa ya ƙunshi ƙura. Da za a rufa da shi, to zai sa
mutum ya ji ƙaiƙayi a jikinsa. To wannan yanayi ne ya ɗauko ya liƙa wa mutum wato Isah
Gurgu, don ya siffanta halayensa na rashin ɗaukar wargi. Amma wannan hali na Isah, bai
hana ya saurari mawaƙin nan, ya kuma yarda da maganarsa ba.
Shi ma Musa Ɗangoma a cikin waƙarsa ta “Gamsheƙa”, a wata ɗiya ya yi amfani da
salon abuntarwa, yana faɗin:
Tsohuwar karuwa gamsheƙa
Baƙar ashana ƙona-gari,
An ce ki aure ƙauye
Kin ce niƙan dawa da
wuya.
A tunanin mawaƙin ya yi ƙoƙarin siffanta irin
illar tsohuwar karuwa wadda ita ce take
tattara yaran mata a gidanta ta ɗaure masu gindin yin karuwanci kuma saboda ƙwarewarta a harkar,
komai tsufanta, ta san yadda za ta jawo hankalin yaro, su taru su lalace. Wanan
illar ce ya nuna daidai take da baƙar ashana, wadda ƙwaya ɗaya in an ƙyasta, ta za ta iya ƙone gari in ba a yi hattara
ba.
03.4 Alamtarwa
Alama ko alamci na nufin nuni ko bayyana
abu. Alamtarwa wata hanya ce da ake bayyana wani abu da abin da ya yi kama da
shi na abin da ya shafi siffa ko yanayi
ko ɗabi’a ko asali ko
jaruntaka ko ƙasaita da sauransu. (Gusau, 2003: 60 – 61).
Yanzu dubi wannan misalin daga bakin
Hajiya Barmani Coge, a cikin waƙarta ta ‘Sana’a’,tana faɗin:
Kuma an je wurin barka
Ga uwargida bisa wundi
Ɗayar a kan `yar kanti,
Da wadda ba ta sana’a
Ta ɗauki guntun keso
Ta
kakkaɓe shi ta zauna.
Mawaƙiyar ta yi nuni
da nau’o’in tabarma wato wundi da `yar
kanti da keso ta danganta matan
da ta ambata guda uku, kowacce daidai da siffarta ko ɗabi’arta. Ballagaza
daga cikin matan uku, tunda ƙazama ce an alamta tabarmar keso
(lalatacciyar tabarmar kaba) da ita. Ma bi uwargida aka alamta ta da tabarmar
kanti (tabarmar roba ta zamani). Yayin da Uwargida aka alamta ta da wundi
(Babbar tabarmar kaba kewayayyiya). Bisa tunani, uwargida ita ce matar farko, matar asali, ta zauna a tabarmar
asali ta Hausawa.
A can gaba kuma, Hajiya Barmani Coge ta yi
amfani da alamci da ke nuni da muhalli ko wurin da ke da shuke- shuke, inda ta
yi amfani da kalmar kurmi. Tana cewa:
Da na gaya ma matan kurmi,
Kowa ya kama sana’a.
Haka ma a waƙar da ta yi ta
Gwarne, akwai inda ta yi amfani da alamci mai nuna irin halin da rai ke ciki na
farin ciki ko murna tana cewa:
Ayye ɗiyar wakili salamu alaikum
Ga ta Ƙadiri Sannu da niyya
A can gaba kuma ta
ce:
Alalo-alalo na gode
Hajiya Ladi alalo na gode.
Shi ma Babangida Kaka Dawa a waƙar da aka ba da
misalai a baya, akwai inda ya yi nuni da kalmar maɗaci da ke ɗaukar makwafin wuya,
yayin da zuma ke alamta daɗi yana cewa:
Ko an ba ni maɗaci ma,
In aka ba ni zuma nish sha
Ba na iya jin zaƙi.
In ban ga masoya ba.
Wato abin da mutum
yake shauƙin gani saboda sonsa da abin, idan har ba ya ganinsa, to
ba ya jin daɗin rayuwar tasa gaba ɗaya. Duk abin da kake
tunani zai yi masa daɗi baran zuma ne. To
amma ita ma zumar ba ta kai daɗin ganin abin da mutum ke so ba.
03.5 Zayyana
Salon zayyana salo ne da ke tafiya da wasu
salalai kamar na kinaya da na hira da sauransu. Salon zayyana salo ne da mawaƙi ke amfani da
kalmomi domin ya ƙirƙiro hoton zuciyarsa ta yadda mai saurare ko karatu zai ga
hoton da idon zuciyarsa Yahya, (2001:89-90).
Sale Mai Gambara ya yi ƙoƙarin amfani da salon
zayyana don nuna yadda shari’a ta ƙare a tsakanin matan
mutum guda, su uku, inda aka nuna hoton
sigar mace mai tsoro da mara tsoro, aka tabbatar da mai tsoron nan ita ce ta
cika `ya mace. Kamar inda mawaƙin ya faɗa:
In
dai shari’a ce,
In
dai ta gagara,
Ba
mai yanke ta,
Sai
alƙalin
Tsahe.
Shi
ya nemi kwatanniya,
Mai
cin tulu shida,
Ya
kamo kifi da rai,
Sai
ya saka nan,
Ya
ce uwargida taso kamo,
Ko
da ta laliba kifin ya taɓa ta,
Sai
ta maƙaro
kifi,
Ya
ce dawo mai da.
Ma
bi uwaggida ke kuma taso,
Ko
da ta laliba kifin ya taɓa ta,
Sai
ta maƙaro
kifi,
Ya
ce dawo maida,
Amarya
ke taso,
Ko
da ta laliba,
Kifin
ya taɓa ta,
Sai
tai wani lwai-lwai,
Ta
ce za ya kashe ni
Ya
ce ke ce mai Sa.
Za a iya ganin salon zayyana a waƙar Dr. Alhaji Ɗanmaraya mai ɗauke da salon hira da
za a iya gani a gaba kaɗan. Da kuma waƙar nan ta Nana mai
Tafasa ta kishiya, da waƙar sana’a ta Hajiya Barmani Coge.
04. Salon hira ko labari
Salon hira ko salon labari, salo ne mai ban
sha’awa mai kuma sa karsashi ga masu sauraron waƙa. Ana iya gane salon
hira a cikin waƙa a yayin da mawaƙi ke sarrafa harshe
cikin muryoyi mabambanta ya ƙaddarta tamkar yana magana da wani ko
kuwa wasu ne daban suke maganar ba shi ba. Idan kuwa salon labari ne, mawaƙi na ƙoƙarin bayyana abin da
ya gudana ne a tsakanin mutane biyu ko
fiye. Duba Yahya,(2001:108–112) don ƙarin bayani.
Makaɗan
baka gwanaye ne wajen amfani da salon hira ko na labari (Habarce) a cikin waƙoƙi. Idan aka dubi waƙar da Dr. Alhaji Ɗanmaraya Jos ya yi ta ‘jawabin
aure’, za a ga ta ƙunshi
salon hira da salon labari gaba ɗaya kamar inda yake cewa:
Sannan
kun san boka daban,
`Yar
korar boka ma daban,
Gulmawiya
mai sha’anin tsiya,
Mai
son raba sunnar Rabbana,
Kwatsam!
Sai ga ta cikin gida
Maigidan nan na nan kin jiya,
Shin a’a koko ya fita?
Sai
ka ji `yar matar gida ta cane,
Ai
malam ya fita.
Ta
samu kujera nan da nan,
Ga
labari ɗan kaɗan,
Na
jiyo ne can ko a anguwa,
Malam zai miki kishiya
Sai
ka ji ai matar gida,
Ta
buga ƙirji
nan da nan:,
Yanzu
Malam zai min kishiya?,
Sai
ka ji `yar kore kuma,
Ta
ce mata lallai ai kuwa!
Wannan
ba shakka kuwa.
Daga
nan sannan in na tuna,
Sai
ka ji ai matar gida,
Ta
ce. yaya za na yi?
`Yar
kore ta faɗa mata:
Akwai
wani baƙo tun
jiya,
Baƙon boka na nan a can,
Can
layin su magajiya,
Ki
tamabayi maigida,
Za
ki je kuma barkar haihuwa,
Mu
haɗe layin su magajiya.
Maigida
in ya zo nan gidan,
Sai
ka ji ai matargida ta cane:
Malam zan tafi anguwa,
Zan
je barkar haihuwa,
Sai
ta kwashi gyalenta ta lulluɓa
Su
haɗe layin su magajiya.
Wani kuma kyakkyawan misali na amfani da
salon labari a waƙar baka shi ne inda mawaƙiya Nana mai Tafasa,
ta yi waƙar kishiya cikiin hikima take nuna tamkar ita ce a wannan
matsayin macen da aka ce za a yi wa kishiya. Ga yadda ta nuna salon:
Kun
ga shekarata goma da ni da shi,
Ina
zamana lamui lafiya,
Ya
ce muni za shi wurin batu,
Daga
nan niz zabura nij jawo zane,
Ni
ebo kuɗɗi hwam biyar,
Ga
ni Malam Audu ka agaje ni,
Kam
mijina yai min kishiya,
Yanzu
Nana zuba min kuɗɗi hwam biyar,
Ina
raba ki da sherin kishiya.
Ki
zo ki amshi layu ukku ki turbuɗe
Na
anshi layunnan na turbuɗe,
Ran
da laya tak kwan arba’in,
Yac
ce mini za shi wajen batu.
Haka mawaƙiyar ta tafi da
wannan salon labari har zuwa ƙashen waƙar da ta nuna irin
rashin cin nasararta na hana yi mata kishiya.
05. Ƙarangiya
Akan yi wa wannan kalma laƙabi da ‘gagara gwari
faɗa’. Ƙarangiya salon
sarrafa harshe ne da Bahaushe kan yi cikin hikima ya sarrafa haruffa ko kalmomi masu fitar da amon
sauti kusan iri ɗaya a kai-a kai,
misali Bahaushe kan ce:
Turmi ture kura,
Kura ture turmi.
Sai a buƙaci wani baubawa (wanda ba Bahaushe ba) ya faɗa a cikin sauri don a
gwada ko ya ƙware da harshen. To irin wannan salon magana, ana samun
ta birjik a cikin waƙoƙin baka. Ga misali daga bkin Barmani Coge:
Ballagaza bazaar-bazar ta ɓarza,
Kana kan ta tausa har ta talga,
Kana kan ta ɓarka har ta tuƙa,
Shi ma Alhaji Ɗanbawa Ƙaura ya yi amfani da
salon ƙarangiya a waƙar nan tasa ‘Matan
Nijeriya’ kamar haka:
Raggo
da gara da ragga.
Shin
wane kaf fi so?
Raggo
ba ya tumu,
Ragga
juji yake
Kai
gara kuma ɓarna takai,
In an lura da wannan misali na ƙarshe, mawaƙin ya yi amfani da
luguden kalmomi masu amo kusan iri ɗaya wato ‘Raggo’ da ‘gara’ da kuma ‘ragga’
don nuna isar harshen Hausa wajen gwanintar kwatance. Ire-iren waɗannan na nan birjik a
waƙoƙin baka.
07. Kammalawa
An dai fahimci lallai su ma mawaƙan baka (makaɗan jama’a) gwanaye ne
wajen amfani da salailai iri-iri a waƙoƙinsu. An yi tsokaci
tare da misalai na salon sarrafa harshe da aka san mawaƙan baka na amfani da
su wajen cin ma manufarsu. An kuma fahimta cewa lallai salo dai a waƙa tamkar ado ko
kwalliya ce da ke sa a yi sha’awa. Don haka sun tabbata a wasu waƙoƙin da aka yi su don
nuna yadda mace take rayuwa a nan duniya, kamar yadda aka ga misalai.
A ƙarshe, ana fatar
wannan nazari ya kasance ƙarin haske ne ga manazarta waƙoƙin Hausa musamman ta
fuskar nazarin salo a Adabin Hausa. Da yake akwai makusanciyar alaƙa tsakanin salo da saƙon da waƙa take ɗauke da shi, za a ga
cewa akwai ɓirɓishin saƙon waƙoƙin da aka yi nazarin
salonsu a nan. Ke nan ana fatar wannan nazari ya tunatar da mata waɗanda aka yi domin su
su amfana wajen karɓar saƙon don gyaran ɗabi’unsu marasa kyau
da kuma dagewa a kan masu kyau.
Manazarta
Tuntuɓi mai takarda.
1 Comments
Aikin ya bayar da ma'ana sosai, musamman da aka bayyana inda mai karatu zai samu Ƙarin bayani a cikin aikin.
ReplyDeleteSani Adamufaskari
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.