Takaitaccen Tsokaci Game Da Mawallafan "Diwan Wakokin Aminu Ladan Abubakar (ALA)"

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, da ke Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. A halin yanzu shi ne mataimakin shugban Ƙungiyar Masu Fassara da Baddala ta Ƙasa (Nijeriyan Institute of Translators and Interpreters, NITI). Daga cikin rubuce-rubucensa akwai: Translation: An Introductory Guide (1993) da Jagoran Ilimin Walwalar Harshe (2012) da Taskar Al’adu da Tarihi da Nishaɗi (2012) da The Rights of Widows and Divorcees in Hausa/Fulani Society (2002) da kuma Sanin Makamar Fassara (2018).

Abu-Ubaida SANI ɗalibin Hausa ne. Yana koyarwa a Sashen Harsuna da Al’adu da ke Jami’ar Tarayya Gusa, Jihar Zamfara. Ya kasance edita a mujallun da suka haɗa da Tasambo Journal of Language, Literature and Culture (FUGUS, Nigeria), THE AFRIKANIST: International Journal of African Studies (University of Georgia, USA) da Global Academic Journal of Linguistics and Literature, United Arab Emirates. Ya yi wallafe-wallafe da suka shafi littattafai da muƙalun da aka buga cikin mujallu. Ya kuma gabatar da muƙalu a tarurrukan ƙara wa juna sani daban-daban. Shi ya yi sanadiyar samuwar babban kafar intanet ɗin nan ta Hausa wato www.amasohi.com.   

Diwan Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)


Post a Comment

0 Comments