Tsinkayar Wasu Marubuta Waƙoƙi Kan Makomar Arewa

Mutuƙar a Arewa da Karuwai, Wallah za mu yi kunyar duniya. *** Mutuƙar ‘yan iska na gari,  Ɗan Daudu da shi da Magajiya.*** Da samari masu rowan kuɗi, Ga maroƙa can a gidan giya. *** Babu shakka ‘yan Kudu za su hau, Dokin mulkin Nijeriya.*** Su yi ta kau sukuwa bisa kanmu ko, Mun roƙi zumuntar duniya...

Damuwa


Tsinkayar Wasu Marubuta Waƙoƙi Kan Makomar Arewa

Yahaya Idris
Sahen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato
yahayaidris33@gmail.com

 

1.0  Gabatarwa

 Waƙa wata ƙololuwar magana ce ta hikima da ɗan’adam ke iya yi, ita ce ta fi ingancin tacewa kuma ita ce mafi tasiri kai tsaye ga zuciyar taliki. Waɗannan siffofi ne suka sa waƙa ta fi saurin isar da saƙonni daban-daban game da al’amuran rayuwar al’umm (Usman 2009:2). Wannan takarda za ta yi waiwaye ne dangane da hasashe da tsinkayar da wasu marubuta waƙoƙin Hausa suka yi a kan mutanen Arewa, sannan za ta fito da wuraren da suka yi musu kandarko da hannunka mai sanda. A takardar za a yi misalai da waƙar ‘Arewa Jamhuriya ko Mulukiya’ (AJM) ta Sa’adu Zungur da waƙar ‘Tutocin Shehu da waninsu’ ta Mu’azu Haɗeja (TSW) da kuma waƙar ‘Muhimmancin Al’adunmu: Haɗarin  Rungumar na Ƙasashen Waje (MAHRƘW) ta Alƙali Haliru Wurno.

2.0 Tarihin Rayuwar Marubuta Waƙoƙin a Taƙaice

2.1Malam  Sa’adu Zungur

Malam Sa’adu Zungur wanda yake ya fito daga gidan ililmi a Bauci, yana ɗaya daga cikin haziƙan ‘yan arewa da kwalejin Katsina ta taɓa haihuwa. Shi ne na farko da aka taɓa aikawa zuwa babbar kwaleji ta Yaba, a Ikko daga jihar arewa. To, zuwansa Yaba ya ƙara sa shi zama gogaggen ɗan siyasa bisa ilimi. A taƙaice dai ana iya cewa shi ne fitila ta farko da ta fara haskaka arewa cikin siyasar zamani. Shi ne farkon wanda tun wajen 1940 ya tara waɗansu abokansa a Zariya, ya yi lacca a kan amfanin jam’iyya. Saboda haka aka kafa jam’iyyar abokai, watau (Zarias Friendly Society). Haka kuma yana cikin manyan shikashikan kafa jam’iyyar malaman makaranta ta arewa. Ya je Ingila a 1947 tare da Zik a kan sha’anin siyasa, tun ma kafin ido ya buɗe sosai.

2.2 Malam Mu’azu Hadeja

An haifi Mu’azu Hadeja a shekarar 1918 a unguwar Kilabakori, a cikin garin Hadejia. A bisa al’adar Musulmi, yaro yakan fara samun tarbiyya tun yana ƙarami, ya sami tarbiyya da horo masu inganci daga iyayensa. Cikin irin wannan yanayi ne Mu’azu ya tashi. Daga wannan mataki ne iyayen Mu’azu suka kai shi makarantar allo, inda ya yi karatun addinin Musulunci. A lokacin ƙuruciyar Mu’azu, wajajen 1910, ilimin boko ya kunno kai domin haka ya shiga makarantar Elementare a makarantar Dalla a garin Haɗejia daga 1928-1931, daga nan sai Mu’azu ya shiga Midil ta garin Kano a 1932 zuwa 1934. Saboda basirarsa da ƙoƙarinsa wajen karatu, lokacin da Mu’azu da ya gama Midil a 1934 sai ya sami nasarar shiga kwalejin horar da malamai ta Bauchi daga 1935-1937. Duk lokacin da Mu’azu yake karatu a waɗannan makarantu na boko bai taɓa dogara da wannan karatu shi kaɗai ba, domin a kowane lokaci yana ɗaukar gafakarsa ta karatun addini ya tafi ɗaukar karatu cikin gari wajen malamai. Haka yake yi kuma duk lokacin da ya zo hutu. Bayan mu’azu ya sami wadataccen horo na karantarwa sai ya fara aikin karantarwa a elementare ta Wudil a shekarar 1938 zuwa 1940. Aikin malam Mu’azu a Wudil ya ci gaba domin ya zama shugaba ‘Teacher in charge (IC). Bayan zamansa na Wudil, malam Mu’azu Haɗejia ya yi aiki a makarantar Ringim Katutu Elementare School, daga 1944 – 1947. Daga Ringim sai aka dawo da Mu’azu Kano a matsayin visiting Teacher (Mai duba Makarantu), wanda ake taƙaitawa da V.T. daga 1947 – 1958 wanda a wannan lokaci ne Alah ya karɓi ransa.

2.3 Alƙali Haliru Wurno

An haifi Alƙali Haliru Wurno a ƙauyen Kwargaba cikin ƙaramar hukumar mulki ta Wurno a shekarar 1925. Lokacin yana ƙarami an saka shi makarantar allo ta liman Macciɗo na masallacin Sarkin Musulmi Bello a cikin garin Sakkwato. Alƙali Haliru Wurno ya halarci makarantar koyon aikin alƙalanci ta Sakkwato daga shekarar 1943 zuwa 1947. Daga nan sai ya wuce zuwa makarantar koyon aikin shari’ah ta Kano a inda ya yi shekara huɗu, ya gama a shekarar 1951. A gwagwarmayar neman ilimi, Alƙali Haliru ya yi karatun littatafai kamar littafin al-Izziyya da al-Akhdari da al-Tafsir Jalalain. Ya kuma yi karatun wasu daga cikin littatafan magabatansa wato Fodiyawa. Daga cikin waɗanda ya karanta akwai ihy al-Sunna da Siraj al-Ikhwan da Tanbih al-Ikhwan. Haka kuma ya nazarci Diya al-Hukkum da kuma Diya al Tawil. Bayan gama karatunsa a makarantar koyon aikin shari’ah a Kano, Alhaji Haliru ya zama malami a makarantar Elemantare ta Maru, ya zauna a can tsawon shekara ɗaya da rabi. Bayan nan sai ya kama aiki da hukumar kula da harkokin shar’ah ta jihar Sakkwato a shekarar 1952. Ya ci gaba da yin wannan aiki har zuwa shekarar 1965 lokacin da ya yanke shawarar komawa aikin malanta. A wannan lokaci ne ya kama aiki da makarantar Nizamiyya a Akija cikin garin Sakkwato, ya yi koyarwa ta shekara da watanni a wannan makaranta. To a lokacin ne ya tsara fitacciyar waƙar nan tasa mai suna Fanda ko Danja. Cikinta ne ya bayyana irin yadda ya ji lokacin da suka sami hatsari kan Fanda, shi da ɗan uwansa Muhammadu Lema. Daga nan Alhaji Haliru ya sake komawa  ɓangaren shari’ah da aiki, ya yi aiki a matsayin Alƙali har zuwa lokacin da aikin ya ishe shi kamar yadda ya faɗa da bakinsa a shekarar 1981.

Alƙali Haliru Wurno ya fara tsara waƙa yana da shekaru sha biyar da haihuwa. Ya yi tafiye-tafiye da dama cikin Sakwkwato da wajenta. Allah ya karɓI rayuwarsa cikin 2003.

3.0 Wasu Mahangar Marubuta

3.1 Fifita Zama a Arewa

Alƙali Haliru Wurno ya faɗakar da mutanen Arewa su fahimci bambancin al’adu da ke tsakaninsu da mutanen Kudu. Irin kuma wannan bambanci ke haifar saɓanin na yanayin zama da yin zama a wurin da za ka sami damar yin al’adunka. Ashe ke nan akwai bukatar mutumin Arewa kada ya shantake a wurin da ba nasa ba ne ko ba nan ne asalinsa ba. Ga abin da Alƙali Haliru Wurno yake cewa:

7. Gidan wasu ba gidanku ba ne ka gane,

Uwar wasu ba uwarka ba ce ka barta.

8. Garin wasu ba garinku ba ne ka lura,

Zaman Gumi bai kama da zaman su Delta.

(Waƙar MAHRUW ta Alƙali Haliru Wurno)

3.2 Ƙarfafa Addinin Arewa

Addini yana nufin hanyar bauta wa Ubangiji, (CNHN, 2006:3). Wannan hanyar bauta wa Ubangiji ta haɗa da yadda za a gudanar da rayuwa baki ɗaya. Muddin mutane suka riƙi wannan hanyar bauta daidai da yadda Ubangiji ya sharɗanta a yi, lalle rayuwa za ta inganta, idan kuma aka saɓa to sakamako zai zama akasin haka. Dubi dai abin da Sa’adu Zungur ya faɗa:

                                              30. Ilimi, hikima, addini duka,

            Da dabarar sarrafa duniya.

38. In fa addini ya raunana,

            Babu alheri nan duniya.

48. Sai arnanci ya yi sallama,

            Dada har abada ba dawaya.

(W aƙar A J M ta Sa’adu Zungur)

3.3 Yi wa Arewa Addu’a

A taƙaice addu’a na nufin roƙon wani abu daga Allah shi kaɗai ta amfani da waɗansu lafuzza na musamman (Ainu,2007:52). A nan sha’irai biyu Mu’azu Haɗeja da Sa’adu Zungur sun yi addu’a ta musamman ga yankin arewa da kuma sarakunan arewa idan sun tsaya wa gaskiya. Ba komai ne ya kawo wannan addu’a ba sai don hasashen gudun yadda aka sami kai yanzu.

16. Addu’armu ga Allah Rahimi,

            Ya kiyaye Arewa gaba ɗaya.

                                 (Waƙar A J M ta Sa’adu Zungur)

39. Allah muna a gare ka,                        

Mun ko fake a gare ka,

     Muna biɗar ka taimaka                     

 Sarakuna su ɗaukaka,

                          In sun tsaya wa gaskiya.

                                            (Waƙar TSW ta Mu’azu Haɗeja )

3.4 Muhalli Bisa Gaskiya

Jan ragamar jama’a ko wata ƙungiya ake nufi da shugabanci (CNHN, 2006:415). Hikimar da take cikin waɗannan baitoci ta haɗa da nuna idan shugabanni suka sau gaskiya mulkinsu zai lalace. Misali, baiti na 29 a cikin waƙar “Arewa Jimhuriya ko Mulukiya” ta Sa’adu Zungur da wasu baitocin suna cewa:

 29.  Shehu Abdullahi hakikatan,

            Ya bar mana gadon gaskiya.

31. Muka lalata, muka wargaza,

            Ga shi yau sai anai mana dariya.

32. Babu tsuntsu ba tarko duka,

            Wallah mun yi hasarar duniya.

52. Kar ka bar arna su shige musu,

            Don su watsa dafin Jumhuriya.

54. In ji dai kun hangi mutan Gusun,

            Masu mai da ƙasa Jumhuriya.

Daga nan wasu baitocin suka yi kira ga sarakuna da su yi tsaye wajen tabbatar da shugabanci mai gaskiya mai aminci, duk abin da za a yi wanda zai tallafi mutanen Arewa a tabbatar da yin sa kada a bari a shiga cikin halin nadama. A kuma fahimci shirin mutanen kudu na son su ɗauki gaba ta su tarwatsa haɗuwar Arewa ta Musulunci. A dubi  abin da Sa’adu ya faɗa a baiti na 98 da kuma 100 da 107-108:

                                                97. Hakkin jama’a na kansu duk,

            Su riƙe igiyarsa da gaskiya.

98. In kunka sake jama;ar Kudu,

            Suka hau mulkin Nijeriya.

99. Daɗa ba sauran mai tambaya,

            Kowa ya san zai sha wuya.

100. An sha bamban bisa kan nufi,

            Na shirin mulkin Nijeriya.

107. Fatarmu Arewa ta farga duk,

            Don ta gane lamarin duniya.

108. Farfagandar makirci duka,

            Sai a bar ta, a bincika gaskiya.

                           (Waƙar AJ M ta Sa’adu Zungur)

 

Shi kuma Mu’azu ya yi kira ga shugabannin Arewa (sarakuna) da su riƙe jama’arsu da gaskiya domin mai biya yana bin sawun majiɓincinsu. Mu’azu Haɗeja yana cewa:

 

37. Ku kunnuwammu ne ku san,         

Ku ne idanummu ku san,

Ku ne ƙafafummu ku san,               

Ku bakunammu ne ku san,

Wuyanku munka rataya.

 

38. Inda baki ya karkata,                       

Ta nan miyau shi kan fita,

In ka ga kyalla ta ɓata                      

Mai bin ta ne ya sake ta,

Ƙafarta babu igiya.

(Waƙar TSW ta Mu’azu Hadeja)

3.5 Gargaɗi ga Mutanen Arewa

Kashedi ko horo shi ake nufi da gargaɗi (CNHN, 2006:159). Sa’adu Zungur da Mu’azu Haɗeja sun yi wa mutanen Arewa gargaɗi kan su lura su san kansu su kuma riƙa lura da abin da zai je ya komo. Abin da ka raina wata rana shi za ya ba ka tsoro musamman game da tafiyar da al’amuran ƙasa. Yana da kyau a fahimci waɗanda ake zaune da su. A ‘Arewa Jamhuriya ko Mulukiya Sa’du Zungur yana cewa:

113. Mu dai hakkinmu gaya muku,

                                     Ko ku karɓa ko ku yi dariya.

                                                          114. Dariyarku ta zam kuka gaba,

            Da nadamar mai ƙin gaskiya.

125. Kar ku ruɗu da zancen ja’irai,

            Masu son halakar Nijeriya.

130. ‘Yan Arewa ku daina gaganiya,

            Ku riƙe daularku da gaskiya.

135. In kun dage, kun shantake,

            Bisa al’adu na mazan jiya.

136. Za ku rera faɗar da-na-sani,

            Da na bi jawabin gaskiya.

                  (Waƙar AJM ta Sa’adu Zungur)

A wasu baitocin Mu’azu Haɗeja yana faɗin:

45 .Ka ji abin mamaki,                    

Ungulu zai  zai kashe maiki,

Dawa za ta ci doki,                             

Kare yi sannu da zaki,

Don juyi na duniya.

 

Sai kuma:

52. Abin ga ko da gaskiya?                                      

Kura ta iske tunkiya,

Ta ce su je su tsariya,                                    

Akwai tuwo akwai miya,

 Su yi shagali na duniya.

(Waƙar TSW  ta Mu’azu Haɗeja)

3.6 In ba a ji Bari ba

Masu iya magana suna cewa, “cikin ƙira ake ɗaɗi,” duk inda aka yi gargaɗi, to, ana sa ran mutum ya yi taka tsan tsan, ya kiyaye abin da aka yi masa magana a kansa. Rashin kiyayewar zai haifar da wani abu na ‘in ba a ji bari ba a ji hoho.’ Dubi abin da Sa’adu Zungur yake gaya wa Arewa:                                      

141. Mutuƙar a Arewa da Karuwai,

          Wallah za mu yi kunyar duniya.

142. Mutuƙar ‘yan iska na gari,

          Ɗan Daudu da shi da Magajiya.

143. Da samari masu rowan kuɗi,

          Ga maroƙa can a gidan giya.

144. Babu shakka ‘yan Kudu za su hau,

           Dokin mulkin Nijeriya.

145. Su yi ta kau sukuwa bisa kanmu ko,

          Mun roƙi zumuntar duniya.

                           (Waƙar AJ M ta Sa’adu Zungur)

Mu’azu Haɗeja shi kuwa yana cewa:

50. Ga shi muna son mulki,                             

Tsanimmu babu mataki,

Zancen awa na mafarki,                                   

Auren da babu sadaki,

Yana cikin haramiya.

 

51. Ƙasarmu ba masu sani,                                 

Idommu ma ba su gani,

Mu bar shiga zugar wani,                              

Da hankali da tunani,

Kadda mu koma baya.

 

65. Ana zato za a iya,                                         

Wataƙila za a sha wuya,

Don ƙarya da gaskiya,                                   

Ba su zama wuri ɗaya,

Kan ƙauli na gaskiya.

(Waƙar TSW ta Mu’azu Haɗeja)

 

4.0 Kammalawa

A cikin wannan takarda an kalato abubuwan da masana suka hango wa Arewa tun kafin wannan lokaci. Hakan ta sa suka yi bayani filla-filla cikin waƙoƙinsu kan cewa, muddin dai ba a tashi tsaye mun yi shiri ba, to babu shakka za ta kaimu ga faɗar da na sani kamar yadda aka sami kai yanzu. An fahimta daga cikin waɗannan waƙoƙi, masana sun yi wa al’umma hannunka-mai-sanda ta hanyoyin da suka haɗa da fifita zama a Arewa da Ƙarfafa Addinin Arewa da yi wa Arewa Addu’a haɗa da muhalli bisa gaskiya da gargaɗi ga mutanen Arewa da kuma nasihar in ba a ji bari ba a ji hoho. A cikin wannan takarda an fahimci cewa, duk “wanda bai ji bari ba ya ji hoho” a game da halin da Arewa ta sami kai a halin yanzu. Da mun kiyaye da duk irin jan hankali da hannunka mai sanda da waɗannan masana suka yi, da mun sami mafita duniya da lahira. Amma saboda halin ko o ho da muke da shi  sai faɗar da na sani muke yi.

 

Manazarta

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments