“An yi sa’a an haɗa waƙoƙin tun ALA yana raye…” Dr. Bukar Usman, M.IoD, D.Litt, OON
MUƘADDIMA
Farfesa
Sa’adiya Omar
Darakta, Cibiyar
Nazarin Hausa
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Godiya
ta tabbata ga Allah (Subhanahu Wata’ala) wanda ya halicci ilimi. Tsira da amincinsa
su tabbata ga Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi wa Sallam) wanda ya wajabta
neman ilimi a kan dukkan Musulmi maza da mata. Na yi matuƙar farin ciki da aka nemi na yi muƙaddima a wannan littafi mai suna DIWANIN
WAƘOƘIN
AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), littafin da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da
Abu-Ubaida Sani suka rubuta a kan ɗaya
daga cikin shahararrun mawaƙan
Hausa na wannan zamani.
Haƙiƙa
irin wannan aikin haɗin-guiwa tsakanin malami da ɗalibi,
wata sabuwar hanya ce ta taskacewa da kuma adana waɗannan
waƙoƙi
domin kada su salwanta. Abin lura a nan shi ne irin tagomashin da waɗannan
waƙoƙi na
zamani suke da shi, wajen isar da saƙonni
ta siga daban-daban domin inganta rayuwar al’umma. Bugu da ƙari, wannan Diwani ya zo da bayani mai
zurfi game da rayuwar Aminu ALA, wato tarihin ya fito da bayanai dangane da ƙimarsa a cikin al’umma da yanayin da ya
samar da waƙoƙi da kuma mutanen da aka yi waƙoƙin
domin su.
Wani ƙari
da aka samu kuma a wannan Diwani shi ne na tattara waƙoƙin a
bisa jigogin da suka dace. Wato kama daga jigon
ilimantarwa da wa’azantarwa da faɗakarwa
zuwa na siyasa da soyayya da sarauta da kuma na yabo da jinjina. Sauran sun haɗa da
jigogi na ganin dama da na talla da na aure da na ta’aziyya da ɗaukaka
da kuma na zagin kasuwa. Dukkan waɗannan
abubuwa sun zama shaidar da za a tabbatar da cewa wannan aiki na marubutan haɗaka,
wata gudummawa ce ga ci gaban nazari a fagen adabi, musamman ma fannin waƙoƙin
Hausa na zamani.
JINJINA
Alhaji
Aminu Ado Bayero
Mai
Martaba Sarkin Kano
Muna
godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya nuna mana fitowar wannan muhimmin
littafi da aka rubuta a kan waƙoƙin fasihi, gwani, rumbun hikima wato
Alhaji Aminu Ladan Abubakar (ALA). Haƙiƙa ALA wani babban jigo ne kuma jagora a
fagen adabin Hausa na zamani, domin shi ne fitila mafi haske a cikin fitilun da
ke haskaka wannan sabon jigo na waƙoƙin Hausa na zamani.
ALA
ya yi amfani da ɗimbin basirar da Allah ya yi
masa wajen ɗabbaƙa
sabon salo a waƙar
Hausa ta yadda tilas ya ja hankalin masana da manazarta adabin Hausa.
Diwani
wata taska ce ta adana ayyukan fasaha da suka danganci waƙa, da zube, da wasan kwaikwayo, da
sauran ayyukan adabi. Muna maraba da wannan diwani na waƙoƙin
Alhaji Aminu Ladan Abubakar, da fatan littafin zai amfanar a fagen bincike da
nazari ga malamai da kuma ma’abuta sha’awar waƙoƙin Hausa.
Marubutan wannan littafi wato Prof. Salisu Ahmad Yakasai da
ɗalibinsa Abu-Ubaida Sani, haƙiƙa sun
yi tsinkaye da hangen nesa wajen yin wannan gagarumin aiki domin
ƙara fito da wannan sabon fanni na adabi
da taskace waƙoƙin ALA domin amfaninmu baki ɗaya.
Allah Ya albarkaci wannan littafi, ameen.
ALLAH
SAN BARKA
Ado Ahmad Gidan
Dabino, MON
Tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya, ANA
Reshen Jahar Kano
Samar da littattafai a kan waƙoƙin
fasihan mawaƙan Hausa na Arewacin Nijeriya babban abin jin daɗi da kuma alfahari ne, saboda ana
adanawa da killace ire-iren waɗannan
ayyuka domin gudun ɓacewarsu
wata rana. Diwanin waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA), na
tabbata zai zama abin so ga jama’a musamman masu son waƙoƙinsa
da kuma manazarta.
TSOKACI
Alhaji Kabir Assada
Babban Edita, Mujallar Muryar Arewa
Littafin Diwanin Waƙoƙin
Amini Ladan Abubakar (ALA), wani kundi ne da ya zamo ɗaya-tamkar-da-goma idan ana maganar
taskace tarihin mawaƙan Hausa na wannan zamani da kuma
ayyukansu. Mawallafan littafin sun nuna ƙwarewa da naƙaltar
sanin ƙabli
da ba'adin wannan fage na adabi, musamman idan aka yi la'akari da tsari da
zubin littafin.
GOYON
BAYA
Hajiya
Fati Nijar
Mawaƙiyar Hausa
Waƙa tana taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka
harshe da kuma bunƙasa al'adun
al'umma. Samuwar DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), tanadi ne
na kare wannan aiki na adabi daga salwanta. Marubuta
littafin sun nuna ƙwarewa
cikin hikima.
YABAWA
Malam Sulaiman Salisu Muhammad
(Mai
Bazazzagiya)
Yau
Farfesa Salisu Yakasai,
Sani
Ubaida kun yi aiki sosai,
Gun
Diwanin nan na ALAN Waƙa.
Babbar
gona ce ciki ga shuka,
Kwanyar
ALA ga ta nan fa ta waƙa.
Har
al’ada ba a bin sa fa bashi,
To haka
harshen walwala gun waƙa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.