Maƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani Na Ƙasa da Ƙasa Na Uku Wanda Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe Ta Shirya a Ranakun 18-22 Mayu, 2017. Kuma an Buga ta a cikin Mujallar KADAURA Jounal of Hausa Multiti Disciplinary Studies Vol.1, No. 4, 2018 Special Edition.
Ɓullar Wasu Fasahar Baka Na Hausa
A Ƙarni Na
Ashrin Da Ɗaya: Taƙaitaccen Nazari A Kan Sababbin
Kirari Da Karin Magana
Rabi Mohammed
Jami’ar Jihar Kaduna, Nijeriya.
Email: rabimohammeddatti@gmail.com
G.S.M: 08060771666/08080381801
Tsakure
Nau’oin fasahar baka
na Hausa su ne a matsayin adabin baka na azancin magana, kamar karin magana, da
tumasanci da kirari, da arashi, da baƙar magana, da
barkwanci, da salon magana/ƙarangiya, da gatse, da kacici-kacici,
da shaguɓe, da ba’a da
gugar-zana, da sara, da dungu, da waskiya, da santin magana, da zambo, da
zaurance, da habaici, da sauranau. A Wannan maƙala za a yi ƙoƙarin nazarin wasu
kirari da karin magana ne na Hausa da suka bayyana a wannan ƙarni na ashirin da ɗaya. Da ma kamar
yadda aka sani kirari da karin magana jiyo su kurum ake yi daga bakin mutane,
sannu a hankali su fantsama cikin rubuce-rubuce ta fuskoki daban- daban. Waɗanda za a yi nazari a
nan, sun samu ne ta kafar sadarwa ta zamani (whatsApp) a bisa wasu dalilai waɗanda ke da muhimmanci
a tabbatar da nazarinsu a rubuce ta yadda komai tsawon zamani za a samu abun
dogaro idan wasu nazarce-nazarce sun taso. An gano lallai yana da kyau a dinga
taskace kirari wuri ɗaya a rubuce, saboda
yara manyan gobe, ko kuma don gudun kada wata rana a wayi gari a neme shi a
rasa shi sam. Ana fata wannan nazarin
har wa yau, zai taimaka wajen daɗa fito da fasalin kirari da karin magana da
yadda ake gina su da saƙon da suke dunƙulewa. Za kuma a yi ƙoƙarin rarrabe waɗannan sababbin kirari
da karin magana da aka kawo da waɗanda suka wanzu tun asali.
1.0 Gabatarwa
Manufar wannan takarda ita ce, ta taskace
kuma ta yi nazarin wasu sababbin kirari da karin magana a Hausa. Domin cim ma
wannan ƙuduri, za a fito da bayanai gida-gida. Za a bibiyi
ayyukan da suka gabata a fito da ma’ana da asali da dalili da kuma
fasalce-fasalce na kirari a Hausa. Bayan an yi haka, sai a kawo kirarin da aka
samo sannan a yi nazari da sharhi a kai. Idan an juyo ga karin magana, nan ma
za a yi bayanai ne ta yadda aka yi game da kirari.
2.0 Kirari a Hausa
Ma’anar Kirari
Masana da dama sun
bayyana ma’anar kirari daban-daban, ga kaɗan daga cikinsu:
Alhassan da Zarruƙ (1976), sun bayyana
kirari a matsayin nau’i na fasahar shirya taƙaitaccen kwatance,
wanda ya ƙunshi bayanin abubuwa ko halaye ko al’aumura. Sun ƙara da cewa kirari
yana cikin rukunnan nan na zantuttukan Hausa masu hikima da zurfin ma’ana da
nasiha. Kuma kirari koyaushe akwai mai shi, wato akan lanƙaya kirari ga mutum
ko wani abu da ba mutum ba, mai rai ko mara rai, kamar aljani ko ƙasa da sauransu.
Gusau, (1979/80), shi kuma ya ce: “Kirari
shi ne faɗin wasu kalmomi ga
wani waɗanda za su yi masa daɗi da cicciɓa shi a idon jama’a.”
Ƙamusun Hausa
(2006:246) ya bayyana ma’anar kirari da cewa, “Zaɓaɓɓun kalmomin da ake furtawa a tsare don zuga
ko kambamawa”.
Bunza kuwa, (2009: 140), ya ce: “Za a fi
fayyace ma’anar kirari idan aka nazarci waƙoƙin `yantauri ko
manoma ko maƙera ko mafarauta ko ɓarayi da sauransu.”
A taƙaice kirari nau’i ne
na fasahar shirya taƙaitaccen kwatance wanda ya ƙunshi bayanin abubuwa
ko halaye ko al’amura. A iya cewa kirari shi ne kuɗa da kurari cikin
hikima, ishara da isar baka, rurawa da razanarwa da ruba (cika baki). (Alhassan
da Zarruƙ 1982).
Asalin Kirari
Haka kuma masana ba su yi ƙasa a gwiwa ba, sun
kawo asalin kirari. Ga abin da wasu suka ce:
Kafin Hausa, (1985), ya bayyana cewa
“Asalin kalmar kirari daga kira ne, watau a nemo mutum ya zo ya fito fili ya
nuna kansa ko kuma wani ya fito ya nuna shi.” Har wa yau ya danganta asalin
kirari da Kalmar ‘ƙira’ wadda ke nufin aikin sarrafa ƙarfe a wuta. Idan ƙarfe ya yi ja a wuta
maƙeri
yana fito da shi ya yi ta makar sa da guduma har sai ya biyu. Sannan ya sa
zarto ya koɗa shi yadda zai zama
wani abu daban da siffarsa ta asali. To a cewar Kafin Hausa, kamar yadda maƙeri ke wannan aiki,
haka ɗan ma’abba kan wasa
mutum ya sa kaifinsa ya tashi yadda ba tsoro a gare shi. Ya kuma ƙara bayani da cewa
wasu manazarta sun danganta kalmar kirari da iƙirari. Watau mutum ya furta
abu da kansa, wanda shi Kafin Hausa, (1985) ya ce, bai yarda da ra’ayinsu ba
domin wani ma yana yi wa wani kirari. Sai dai yana ganin al’adar nan ce ta
manazarta da masana adabi da harshen Hausa ta a kullum Hausa ba ta da abin
kanta sai dai ta yafo na Larabci.
Shi ma Bunza, (2009: 140), ya nuna cewa
asalin kalmar kirari ‘kira’ take nufi, inda akan sa kalangu ko ganga ko murya a
kira wani da ƙarfi don ya fito a ɗebe tababan abin da ake faɗa a kansa. Idan da kiɗa aka yi kiran, to
take ke nan. Yayin da kuma aka sa baki aka fara kiɗa, shi ne an yi
kirari. A can gaba ya ƙara cewa: “Asalin kirari yaƙi, da faɗa, da nuna bajinta.”
Ya kuma tabbatar da cewa idan aka lura da waƙoƙin Narambaɗa mafi yawan gindin
waƙoƙin sigar kirari gare
su.
Shi kuwa Malumfashi, (2014:20), game da
asalin kirari ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce: “Kirari yana ɗaya daga cikin
rukunnan adabin bakan Bahaushe da ya gada tun kaka da kakanni, don haka ba wata
al’umma da za ta yi iƙirƙrin cewa ita ta koya wa Bahaushe hikimar aiwatar da
kirari.”
Dalilan Yin Kirari
Ana yin kirari saboda
waɗannan dalilai:
●Don
razanar da abokan gaba.
●Don koɗa wani a yi masa washi ko talla ko zuga.
●Don a yi nuni, a yi wa mutane hannunka-mai-sanda.
●Don a inganta azancin magana. Kirari ba ya inganta sai bisa
tafarkinsa na al’adu da sana’o’i. ana yin sa don a nuna hikimar zantukan Hausa.
●Don a nuna cewa da ma can shi zance ne ginanne da ake ɗabowa daga rumbun adabi kana a zo a ƙawata adabin da shi.
Matsayin Kirari
Kirari na ɗaya daga cikin manyan rukunan adabin
baka na Hausa. Ana gina kirari ne cikin fasaha da tsari don a kambama mutum ko
wani abu da ba mutum ba. Bunza, (2009: 140), ya bayyana cewa: “Kirari a nazarin
adabi abu ne wanda ya fi zambo da habaici faɗi da rassa da jiigogi da kayan ciki.” Har wa
yau Bunza ya nuna shi kirari ma’auninsa yana da zubi irin na waƙa amma ya fi waƙa shiga jiki. Abin da
ya bambanta kirari da waƙa, zaɓen kalmomi masu nauyi da shiga jiki da mamaye zuciya.
Ta wata fuskar, Alhassan da Zarruƙ, (1982), sun
tantance suka nuna lallai kirari wani babban ginshiƙi ne a rukunin adabin
baka wanda ke bayyana al’adar al’umma. Haka kuma suka nuna kirari na ciyar da
al’umma gaba ta fuskar ilmantarwa da faɗakarwa gami da nishaɗantarwa. Daga cikin
furucin da Zarruƙ, (1982), ya yi a gabatarwa, ya ce: “A fagen nishaɗi kam babu wanda bai
san matsayin kirari ba. domin kirari shi ne gishirin kiɗa da waƙa da sauran al’amuran
da suka shafi bukukuwa. Shi ne kuma sinadarin take da zambo. Bayan haka, kirari
nau’i ne na fasahar harshen Hausa.
Lokacin Yin Kirari
Kirari ba kodayaushe ne ake yin sa ba, sai
da dalili. A al’ummar Hausawa, ana yin kirari bisa dalilai na bukin aure, da
bukin suna, da shagulgulan sallah, da naɗin sarauta, da ayyukan al’umma, da wasanni
irin su dambe da kokowa, da wasu sana’o’i irin su ƙira da saƙa da rini da saye da
sayarwa. Haka kuma kirari na wanzuwa a ayyuka irin na rubutaccen adabi. Mode,
(2013:279-280).
Fasalin Kirari
Manzarta daban-daban sun fasalta kirari zuwa
gida biyu, wasu uku, wasu huɗu waɗanda Mode (2013: 279), ya yi bitar su, sannan ya tabbatar
da ra’ayinsa cewa, kirari za a iya kallonsa ko raba shi gida biyu ne: Kirarin
mutane da kirarin waɗanda ba mutane ba.
Bisa fahimta dai in an ce ‘kirarin
mutane’, to ya shafi mutum ɗin ne kai tsaye. Ko dai shi mutum ɗin ya yi wa kansa
kirari, ko wani mutum daban ya yi wa wani mutum ko mutane kirari. Kirarin da ya
shafi mutane an fasalta shi zuwa na maza da na mata. Na matan an sake fasalta
shi zuwa na uwargida da na amarya da na `yanmata. Sannan akwai kirarin yara
maza da mata da dai sauransu.
Idan kuwa an ce ‘kirarin waɗanda ba mutane ba, to
akwai masu rai da marasa rai. Masu rai kamar aljannu ko dabbobi ko ƙwari; marasa rai
kamar wurare ko ma duniyar kacokan, da duwatsu da koguna da sammai da hadari da
ruwa da zafi da sanyi da sauransu ba iyaka.
Kowane irin kirari dai, shi mutum ɗin ne ke tsara shi.
Kuma yana la’akari da abubuwa da dama ne na daga siffa ko halayya ta mutum ko
wani abu, sai ya fito da shi ƙarara ta fuskar kambama shi ko ɗaga dajarsa bisa wani
abu daban. Alhassan, (1982), ya faɗi cewa: “Idan aka sami wata halitta mai
tsananin jaruntaka ko gwaninta ko mai yawan rikiɗa, wacce ba ta iya tsayuwa a kan
halinta da aka sani, akan shirya mata kirari na musamman, saboda ya nuna
siffofinta da halayenta a fili, a karɓi na karɓa, a guji na gudu.”
Shi kuma Zarruƙ, (1982) ya ce; “Duk
abin da ya burge Bahaushe, ko wanda ya ba shi tsoro, ko ya iya gagarar sa, ko
ya ba shi mamaki, to lallai za ka ji ya yi masa kirari. Saboda haka dabbobin
daji, kamar su zaki da giwa da damisa da kura da sauransu, duk suna da kirari.
Wani kirarin yana gwada ƙarfin dabbar ne, ko faɗanta, ko wasu halayenta na tsoratarwa.” Ya ci
gaba da bayyana cewa: “A muhimman abubuwa na ƙasar Hausa, kusan
babu wanda ba shi da kirari. Garuruwa da sauran nau’o’i da mutane maza da mata,
yara da manya, duk suna da irin nasu kirari. Ana yi wa namiji kirarin mazakuta.
Mace ana yi mata kirari game da halayenta na mata. Haka nan tsoho da yaro, duka
akwai abin da ake faɗa game da su a cikin
kirari. Da aure da haihuwa da mutuwa, duka babu wanda bai sami kirari ba.
kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa, in ka
ji tarin kirare-kiraren da aka yi masa, zai ba ka mamaki.”
3.0 Wasu Samfurin
Kirari a Ƙarni na Ashirin da Ɗaya
Kirarin Mata
An samu wannan kirari ne ta kafar sada
zumunta ta zamani (WhatsApp) a watan Okotoba, 2016. Amma a rubuce ya zo kamar
haka:
Mata masu duniya, ku ba da tuwo ku ba da
other rum!
Mata masu mulkin di oda rum, komai iko da taƙamar mutum a oda rum
sai ya bi!
Mata hidimarku na da kyau, balle a oda rum!
Mata iyayen kowa komai mulkinsa!
Mata in babu ku inkomplit!
Mata a jinjina maku, rashinku asarar namiji,
rashinku hargitsewar namiji, rashinku a oda rum garari ne!
4.0 Nazari da Sharhi
Zarruƙ, (1982), ya nuna a
fagen nazari dai kirari wani rukuni ne na fasahar harshen Hausa da al’adun
mutanenta. Ita kuma wannan fasaha ta harshe, ta baka ce ko rubutacciya ce, ita
ake kira adabi. Watau idan an ce adabin Hausa, an kira dukkan fasahar harshen
Hausa ke nan. Adabin Hausa kuwa, da ma fanni ne guda wanda ake tsayawa a yi
nazarin sa a makaranta. Saboda haka idan an yi nazarin kirari, kamar an ɗauki wani rukuni ne a
cikin adabin Hausa.” Don haka a nan za a yi nazari da sharhi game da wannan
sabon samfurin kirarin da aka kawo ta fuskar bayyana dalilin samuwarsa da
fasahar da aka dunƙule a ciki gami da saƙon da kirarin ya
samar.
Wannan kirari ya samu ne a dalilin kalaman
da shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ya yi. Ya mayar da raddi
ne game da maganganun da matarsa (A’isaha Buhari) ta yi a kafar yaɗa labarai na BBC
Landan. Shi dai shugaba Buhari ya ce (cikin harshen Ingilishi): “I don’t
know which party my wife belongs to, but she belongs to my kitching, and my liɓing room, and the other
room.” Wannan
al’amari ya faru ne a watan Okotoba shekarar dubu biyu da goma sha shida (2016
Miladiyya), wanda ya zo daidai da watan Muharram shekarar 1438, bayan hijirar
Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina. Ita dai A’isha Buhari ta yi ƙorafi ne game da salon mulkin
maigidanta, shugaba Buhari. Shi kuma aka bi diddigin jin ta bakinsa, shi ne ya
furta kalaman da aka gani da Ingilishi. Waɗannan kalamai waɗanda a cikin harshen Hausa ke nufin, “Ban san
jam’iyyar da matata take ba, amma na san dai ita ke kula da madafata da ɗakin hutawata da kuma ɗayan ɗakin.” Wannan ne ya jawo
hankalin `yan Nijeriya suka yi ta cecekuce kowa yana faɗin ra’ayinsa. Kwatsam sai ga ɓullar wannan kirari ta kafar
sada zumunta (Whats App), wanda shi ma ya ja hankulan mata da dama ta inda suka
riƙa nuna
gamsuwarsu da wannan sabon kirari.
Wannan kirari dai an tsara shi ne da ka,
amma ya riski mutane ne a rubuce ta kafar sadarwa ta zamani. Idan aka kalli
yadda aka yi watanda da harshe a wannan kirari, farko za a fahimci an yi abin
da ake kira ‘Ingausa’, wato gwama harshen Hausa da Turanci wajen isar da saƙo. Wannan shi aka
sanya a rukunin Hausar `yanboko. Sai dai bisa fahimtar wannnan nazari, kalaman
Turancin da suka shigo cikin kirarin su ne suke ƙara tabbatar da
dalilin tsara wannan kirari lallai sanadin furucin shugaba Buhari ne wanda ya
yi maganar oda room wanda ya fito mana da Buharin a fili a gane ko shi
wane ne. Wato ya yi kinaya (saye) a maganarsa kasancewarsa daga al’ummar Hausa
waɗanda aka san sun gaji
kunya. Faɗin wannan magana ta
ja hankalin ai’umma ciki da wajen ƙasar Nijeriya. Bisa
fahimta ‘The other room’ na nufin ‘ɗakin kwanciyar bacci’ wanda a Hausance ake
cewa ‘turaka’. Buhari ya tabbatar matarsa kaɗai take da `yancin
shiga ta kwana tare da shi bisa yadda aka sani a al’adar zaman aure na mata da
miji. Haka kuma ta fuskar addini, maganar tasa dutse wanda ya tabbatar da cewa
shi musulmi ne kuma zuciyarsa na nan a ɗarfane da abin da addinin ya tabbatar.
Misali, an tambayi Annabi Muhammad (SAW)
cewa:
“Wace mace ce ta fi?”
sai ya ce: “Wadda take sanya mijinta farin ciki idan ya dube ta, take yi masa
biyayya idan ya umurce ta, kuma ba ta ƙin yi masa biyayya
saboda son zuciyarta ko dukiyarta ta inda ba ya so.” (Nasa’i).
A wani hadisi kuma
Annabi (SAW) sai ya ce:
“Idan mutum ya kira
matarsa zuwa ga shimfiɗarsa kuma ta ƙi zuwa, ya kuma yi
fushi game da hakan a wnnan dare, to mala’iku za su yi ta tsine mata har zuwa
safiya.” (Bukhari/Muslim)
Addinin musulunci ya tabbatar da matsayin
ma’aurata. Namiji shi ne ke jagorantar gidansa gaba ɗaya. Wajibi ne kuma
mata ta yi wa mijinta cikakkiyar biyayya wadda ba ta saɓa wa Allah ba. Yin
wannan shi zai ba matar aure damar shiga Aljanna bayan ta koma ga mahaliccinta.
Annabi Muhammad (SAW) ya ce:
“Idan mace ta mutu
alhali mijinta yana farin ciki da ita, to za ta shiga aljanna.” (Tirmidhi).
Wannan kaɗan ke nan daga cikin ɗimbin Hadisai
ingantattu daga hasken Alƙur’ani game da matsayi da muhimmancin miji a wajen matarsa.
Don haka maganar Buhari ta auna koyarwar addinin musulunci kasancewarsa musulmi
da kuma al’adarsa ta Hausa.
Ta wata fuskar kuma, idan muka dubi
ainihin ƙunshiyar kirarin da aka gina ta dalilin kalaman shugaba
Buhari, za mu iya cewa wannan ba sabon kirari ne na mata ba. An daɗe ana yi wa mata
kirari wanda ke nuna isa da muhimmancin mace kamar yadda Allah ya halicce ta.
Idan babu ita to rayuwar namiji garari ɗin ne; kuma namiji inkompilit yake, wato bai
zama cikakke ba a cikin al’umma. Faɗin haka ya yi daidai tunda ko shugabanci
mutum zai nema ba ya samun goyon bayan al’umma matuƙar ba shi da matar
aure. Wato su mata Allah ya ba su
darajar da babu mai ƙarfin ƙwace masu a duk duniya in ba
mahaliccin nasu ba. Shi ya sa a kirarin aka ji an ce:
Mata masu mulkin di oda rum, komai iko da taƙamar mutum a oda rum
sai ya bi!
Mata hidimarku na da kyau, balle a oda rum!
Mata iyayen kowa komai mulkinsa!
Wato wannan kirari a
fakaice an isar wa shugaba Buhari saƙo. Mata suna ganin ya
nuna wa duniya shi ne jagorar matarsa, har ma wasu suna ganin ya tauye mata
`yanci a siyasance. Don haka suke tuna masa komai isarsa a matsayin namiji idan
ya zo oda rum (turaka), to sai ya lallaɓa matarsa. To ba ga Buhari kaɗai ba, ko ma wane ne
namiji a rukunan al’umma sai ya bi mace ya lallaɓa ta don ya samu biyan bukata. Wannan
daraja da Allah ya ba mata suna alfahari da shi tun zamani mai tsawo. Tuntuni
da ma akwai kirarin mata da ke cewa:
●Sannunku mata masu kayan daɗi,
Mata masu abun bayarwa,
Dare naku safiya ta mazajenku,
Ku kai mutum lahira ku dawo
da shi,
Mata
ku sha wuya ku yi kuka, ku ji daɗi ku yi
kuka,
Mata masu kukan da ba
hawaye ko tsino,
Sannunku mata iyayen kowa,
In ba ku ba gida,
in kun yi yawa gida ya ɓaci
Mata cikinku damina,
gefenku ciyawa mata,
A auro ku don ana son ku, a sake ku don takaicinku mata,
Dariyarku ta fi sata ciwo mata,
Ku kira
namiji yayanku, ku yaye masa aljihu mata,
Mazanku
su yi mulki a waje, su zo gida ku mulke su,
Malami ya ba
da karatu ya zo gida ku ba shi darasi,
Mata masu lilon shillawa,
Mata masu fitillun tagulla a gaba,
Masu yawo da kujerun
zamansu,
Maza su ɗau nauyin wasu, su zo gida ku ɗau nauyinsu,
A ba ku ku raina, a hana
ku ku yi Allah ya isa,
A bar ku, ku
sangarce, a yi maku faɗa ku yi yaji,
A kore ku a je
bikonku,
Ciyawa ba ta ka da ku sai yaryaɗi mata,
Butulu maganin kangarar namiji,
A ci
da ku; a sha da ku; a yi maku sutura; amma gobe ku ce me aka
taɓa yi maku?
Ku
auri mutum idan kuna son sa, gobe ku ce da shi ƙaddara ce ta sa
zama da shi,
Ku
zalunci mutum kuma ku kai ƙararsa,
Ku
yi laifi a ba ku haƙuri mata,
Mata masu mayar da
sarki Bafade,
Mata dangin iblis, ko iblis na tsoron ku,
Mata a ci yau a ci gobe sai ku mata,
Ku sha sha’aninku mata dole a
zauna da ku,
Dole
a nemo a ba ku,
Dole
a lallaɓa ku mata,
In
kuwa an ƙi, dare ya yi
jiki yai tsami!
`Ga kuma wani kirarin da ya jima a tsakanin
al’ummar Hausawa:
Yanmata adon gari,
In ba ku ba gari,
In kun yi yawa gari ya ɓaci.
A
ba ku, ku raina a hana ku, a ji kunya.
A so ku, ku wahalar,
a ƙi ku, a tagayyara.
A amince maku ku yi
yaudara, a yaudare ku, ku rama.
`Yanmata ƙarfen ƙafa mai wuyar cirewa,
A kula
ku, ku yi wulaƙanci, a bar ku ku wuce a kwana ana da- na-
sani!
Mata gumbar
dutse; murucin kan dutse ba ku fito ba sai da kuka
shirya.
Idan an lura waɗannan kirare-kirare
sun daɗe da ginuwa a tsaknin
al’ummar Hausawa. Don haka idan an kwatanta da wanda aka kawo a matsayin sabo,
za a tabbatar ba sabo fil yake ba saboda fasalinsu ɗaya; ƙunshiya ko saƙonsu ɗaya ne duka kamar
yadda aka faɗa. Kirarin da
aka gina a dalilin kalaman Buhari ya tabbatar mana da kalmomin da ya furta na
Ingilishi wato ‘oda rum’ (other room). In ban da wannan, za a iya cewa kirarin
tamakar bita ne na kirarin mata da ya daɗe ana yin sa. Ba kuma zai kankaru ba domin an
jingina kirarin ne bisa yanayin halitta da kuma ɗabi’u irin na mata ɗin.
Kirarin Uwargida
Wannan nazari har wa yau ya yi kiciɓis da wani kirarin da
ya shafi mata ta kafar sada zumunta (WhatsApp), a ranar 02 ga watan 02,
shekarar 2017. Kirarin ya zo ne cikin
murya ba a rubuce ba, sai aka shifce kamar yadda aka ji daga bakin wata mace
kamar haka:
Ke amarya mara galihu
Ke amarya mara `yanci
Ke amarya `yar cin arziki
Ke amarya mai kwaɗayi
Ke amarya me ƙananan `ya`ya
Ki ba uwargida fili ga ni nan
fitowa
Uwargida sarautar mata
Uwargida zuciyar miji
Uwargida sirrin miji
Uwargida rayuwar miji
Uwargida ɗawainiyar miji
Sai ni nan uwargida wadda na raba mijinki
daga Ahmad ya koma baban Abba
Sai ni nan uwargida wadda na raba shi da
tuzuru ya koma magidanci
Sai ni nan uwargida wadda na koya mai farin
ciki fiye da zaman dakali
Sai ni nan uwargida wadda na hana shi jin
sanyin waje ya koyi jin ɗumin cikin gida
Sai ni nan uwargida wadda ni ce farko kafin
ke, kuma `ya`yana ne farko kafin naki, kuma tirenin ɗina za ki zo ki tadda.
Ke amarya karere! Kar fa ki manta Nana A’isha
matar Annabi Muhammad (SAW) ta ce ba ta taɓa kishi da wata mace
ba, face Khadija uwargidan Manzon Allah (SAW), kuma bai daina maganarta, bai
daina tunaninta, bai daina labarinta, Nana A’isha tana baƙin cikin wannan abu,
tana kishi da matar da ba ta taɓa gani ba, domin isa na uwargida.
Ke amarya! Matsa ki ba masu gida su samu
wucewa,
Amarya! Matsa ki ba ni wuri, in a gida ne sai
an ba ni fyf bedrum saboda ɗakina da `ya`yana, na jama’ana, gefen
`ya`ya maza, `ya`yanki ko ƙanana suna gefen masu
aiki amarya! Allah Sarki amarya! Ki yi haƙuri, wanda ya riga ka
barci, dole ya riga ka tashi.
Amarya sabuwar zuwa, amarya baƙuwa! Zauna ki ga
tirenin ɗin da na wa mijinki,
haka za ki hau ki ci gaba da tafiya a kai, domin kuwa ke macijiya ce ba ki da
raminki sai dai in wani ya haƙa ki shiga. Ke
macijiya ce ba ki san sanda muka taho a kan gada ba muna tafiyarmu, sai da muka
zo bakin birij mun zo mun tsallake, kafin a gan ki. Ba ki san ta wace Katanga
muka taho ba, me kika sani game da mijina? Me kika sani game da jin daɗinsa? Me kika sani
game da rayuwarsa? Komai ne kika zo kika samu, tirenin ɗina kika bi a kai. Ya
za kiyi? Ya za ki yi sabuwa? Ya za ki yi karere?
Sai ni nan uwargida sarautar mata! Mulkin
gida, farin cikin mijina, abin shawararsa, daga uwarsa sai ni. Ni ne abokiyar
shawararsa, ni ne farin cikinsa,
Ke karere mai ƙananan yara! Ki yi
biyayya manyan `ya`ya su sa naki a makaranta, ki yi biyayya manyan `ya`ya su
taimaki naki, ki yi biyayya manyan `ya`ya su duba ki
Haba amarya! Haba amarya karere! Haba `yar
Basakkwaciya! Haba `yar Basakkwaciya! Ki kwantar da kanki! Ki kwantar da kanki
a inda aka fi ƙarfinki ki ba uwargidanki fili ta sanar da ke
waye mijinki domin ki samu wurin tsugunnawa!
5.0 Nazari Da Sharhi
Kamar yadda aka faɗa, an yaɗa wannan kirari ne
cikin muryar mace ta kafar sadarwar zumunta (WhatsApp). Ba a ambaci sunan wadda
ta yi ba, sai dai ɗan bayani a rubuce
tare da wani hoto da ke nuna mace da namiji bisa kan gado suna sumbantar juna.
Kuma hoton ya nuna suna cikin kwalliya irin ta amarci da angonci. Wannan hoto
shi aka alaƙanta da wannan kirari cewa wai wata amarya ce ta tura wa
uwargidanta hoton da nufin takalar hankalinta. Ita kuma da ta gani, sai aka ce
ta yi wannan raddin kalamai na kirari ta tura wa amaryar da mijinta ya auro.
Sannan kuma bayan haka ta faru, sai aka sake yaɗa wata magana ta muryar wata mace, ba
a rubuce ba mai cewa:
Ke kuma uwargida, me
kike taƙama da shi ne da za ki wani karanto, kina haɗa kanki da Nana
Khadija ma, kya ma hwara? Za ki ce wani Nana Khadija kaza-kaza? Ibadan da take
yi kina yi ne, in ban da bin bokaye da abun nan da rawan kai ba abun da kike
yi. Sannan kina wani cewa Nana A’isha! Ai Nana A’isha ita ce mafi soyuwa ga
Annabi, ballantana har ki ce wani Nana A’isha kaza-kaza, kaza-kaza. Da kike
zancen `ya`ya da wani mene ne? to wa ya san gawan fari, in Allah ya tashi ɗaukewa sai ya ɗauke duka `ya`yan
naki, ko kuma ya shiryar da `ya`yan na amarya ya bar naki uwargida, ballantana
ki ce wani abu. Uwargida! Uwargida! Uwargida in ban da ma hauka ba abun da kika
riƙa faɗi. gaba ɗaya tsantsan haukanki
ne da jahilci kika faɗi kawai, (tsaki).
Wannan martini da aka ce amarya ta yi, in
an lura ba kirari ba ne. Ana zaton ba amaryar gaske ba ce ta yi tunda karin
harshen ba tsantsan karin Sakkwatanci ba ne wanda aka sa rai a ji saboda a
kirarin da uwargida ta yi, ta ce “`yar Basakkwata”. Sai dai lallai raddi ne ga
wannan kirari da uwargida ta yi.
Duk da cewa wannan kirari kwanan nan aka
haife shi, bai kai ma ga iya zama ba, ballantana rarrafe da tafiya, to ba za a
iya tabbatar da haƙiƙanin dalilin yin shi ba. Bisa bincike da mai wannan maƙala ta faɗaɗa ta kafar sada
zumunta, an gano cewa mata da yawa sun ji wannan kirari. Wasu sun tafi a kan cewa
akwai matsala babba ta yaɗa ƙarya a kafar sada
zumunta ta zamani (soshiyal midiya). Abun da za a turo a bidiyo daban, abun da
za a haɗa daban, ko
rubutaccen bayani ko hoto. Wannan matsalar kuma na faruwa ne kila, saboda wasu
ba su rufe auto midiyansu, sai kawai su shiga cikin ma’ajiya hotunansu, su zaɓo hoton da ya dace da
batun, su haɗa su watsa don tsabar
son su zama na farko wajen yaɗa zance. Ana gane hakan ne ta inda jama’a sun san wannan
hoto da muhallinshi kila tun shekara biyu ko fiye, kwatsam kuma sai ga shi an
liƙa
shi da wata magana an ce ai yau ko jiya ma abun ya faru.
Ko ma dai mene ne, da ma
kirari da karin magana, idan sun ɓulla da wuya ne
a yi saurin cafke gaskiyar wanda ya fara furtawa. Wannan kirari a iya cewa ko
haka nan ma, saboda kishi irin na mata, ba sai amarya ta takali uwargida ba. Za
ma a iya samun macen da ita kaɗai ce wajen mijinta, kuma ta
zauna ta shirya wannan kirari, ta kuma watsa da nufin cusa wani saƙo a zukatan mutane.
A bisa faifan nazari, kirarin da uwargida
ta yi wa kanta na nuni da cewa lallai mace ta farko a gidan miji ita ce kan
gida. Babu tantama lokacin da suka yi auren saurayi da budurwa kowa bai san
kamun ludayin zaman aure ba. A hankali ana kwana ana tashi ake shaƙuwa da juna ta
fuskoki iri-iri. Za a haifi `ya`ya waɗanda tabbas babu kankara, dole ne ka ji ana
wa uba laƙabi da baban wane; ko kuma uwa a ce mata maman wane. Babu
yadda za a yi a ce daga baya idan namiji ya ƙaro aure a ce amarya ɗaya take da uwargida
a wurin miji ta wannan fuska. Dole ne ta saurari uwargida ta koyi wani abu. A
bisa al’adar Bahaushe ma, ai babu yadda za a yi ne amarya ta kira sunan
uwargida saboda wannan daraja tata. A dole ne amarya ta ce da uwargida ‘yaya’.
To amma a wannan ƙarni da muke ciki, wannan tarbiyya ta Bahaushe ta mutu
murus musamman a birane. Idan aka lura ai kalaman da amarya ta aika a matsayin
raddi ga kirarin uwargida babu hikima sam kuma babu tarbiyya a ciki. Kirarin
uwargida kuwa ya nuna hikima da ilimi da tarbiyya duka.
Dangane da hikima dubi waɗannan kalamai daga
cikin kirarin:
Uwargida sarautar mata
Uwargida zuciyar miji
Uwargida sirrin miji
Uwargida rayuwar miji
Uwargida ɗawainiyar miji
Sai ni nan uwargida sarautar mata! Mulkin
gida, farin cikin mijina, abin shawararsa, daga uwarsa sai ni. Ni ne abokiyar
shawararsa, ni ne farin cikinsa,
Akwai hikima da ta
kira kanta masarauciya, zuciya, sirri, rayuwa ko ɗawainiya duka ga mijinta. Sarautar
mata na nuna matsayin matar farko a wajen miji cikin kishiyoyi. Zuciyar miji na
nuna cewa ita ce ta fara shiga ransa a matsayin matarsa, kuma ita ta fara sanin
duk wani sirrinsa kafin wata ta shigo gidan. Ita ce ma rayuwarsa gaba ɗaya na nufin komai
mijin zai aiwatar sai da shawararta. Ta riga ta shiga jini da tsokar mijinta,
ta saba da dangisa waɗanda ko su ba su iya
cewa wani abu na game da ɗan nasu, ba tare da
sun shawarce ta ba. Ɗawainiyar miji kuwa na nufin wahalhalu duk uwargida ta fi
juriya a kai. Misali kila ta aure shi tun ba shi da komai har Allah ya azurta
shi, a cikin haka sai kwatsam ya ƙaro aure. To babu
yadda za a tantance gaskiyar uwargida a kirarinta, sai lokacin da Allah ya
jarabci mijin da rashin kuɗi ko wata rashin lafiya mai tsanani ta kama shi, face an
ga uwargida ta jure ɗawainiya da mijin
nata. A wannan ƙarni da muke ciki mata da yawa ba su da juriya ta fuskoki
da dama ga ɗawainiya da miji.
Kila da ma abun hannunsa ya sa ta aure shi, don haka za ka ga ta fara noƙe-noƙe da cewa ita ba za
ta iya wahala ba.
Haka kuma, wata hikimar a kirarin sai inda
ta ce:
Allah Sarki amarya! Ki yi haƙuri, wanda ya riga ka
barci, dole ya riga ka tashi
Ma’ana ita uwargida
da ta riga auren mijin nasu, dole ne ta fi ta sanin komai na gidan mijin nasu.
Kuma dole ne sau da dama a ba ta matsayinta na babba.
Idan muka ɗauki batun ilimi, a cikin kirarin an
ji inda uwargida ta tunatar da amarya mai rawar kai da cewa:
Ke amarya karere! Kar fa ki manta Nana A’isha
matar Annabi Muhammad (SAW) ta ce ba ta taɓa kishi da wata mace
ba, face Khadija uwargidan Manzon Allah (SAW), kuma bai daina maganarta, bai
daina tunaninta, bai daina labarinta, Nana A’isha tana baƙin cikin wannan abu,
tana kishi da matar da ba ta taɓa gani ba, domin isa na uwargida
Wannan yana nuna mana
uwargida mai yin kirari ba jahila ba ce tunda ta ɗauko misali daga rayuwar gidan manzon
Allah (SAW), don ta tabbatar wa amarya maganarta dutse ne.
Batun tarbiyya kuwa a cikin kirarin, za mu
iya duba waɗannan kalamai:
Sai ni nan uwargida wadda na raba mijinki
daga Ahmad ya koma baban Abba
Sai ni nan uwargida wadda na raba shi da
tuzuru ya koma magidanci
Sai ni nan uwargida wadda na koya mai farin
ciki fiye da zaman dakali
Sai ni nan uwargida wadda na hana shi jin
sanyin waje ya koyi jin ɗumin cikin gida
Sai ni nan uwargida wadda ni ce farko kafin
ke, kuma `ya`yana ne farko kafin naki, kuma tirenin ɗina za ki zo ki
tadda.
Lokacin da mace ta
auri mjin fari ba su da ɗa, a tarbiyyar ɗan Bahaushe mace ba
ta kiran sunan miji, sai dai ta ce malam ko maigida da sauransu. A wannan ƙarni kuma an samu
sauyi inda za a ji mace tana kiran mijinta da baban wane, kamar yadda ya fito a
kirarin cewa ta raba mijinta da Ahmed ya koma baban Abba. Ke nan kafin su samu ɗa, tana kiran mijin
nata da sunansa, wanda a da Bahaushiya wane ita. Sannan akwai kunya musamman ɗan fari, a da uba ko
uwa wane su! Sai dai a alƙanta ɗa da ƙanin uba ko wan uba. Amma a wannan
kirarin an gwada irin sauyin da wannan ƙarni ya zo da shi.
Sai dai duk da haka ba za a ce tarbiyya ta rushe ba. Watakila saboda ci gaban
samun ilimin addini ga mata ya sa suka fi cewa baban wane kamar yadda akan ji
Larabawa na cewa abu wane. Akwai alamun tarbiyya ke nan tunda ta daina
kiran mijinta da sunansa, sai dai ta ce baban Abba. Sannan tarbiyya ce ƙarara a inda kirarin
ya nuna uwargida ta iya bi da mijinta ta yadda kullum idan ya dawo daga aiki,
to yana liƙe da ita a cikin gida, babu zaman dakali wajen hira. Da
ma idan ka ga mjin aure yana yawan zaman waje, to gaskiya bai samu tarbiyyar ƙwarai daga matarsa
ba. Uwargida ta ƙara da cewa tirenin ɗinta dole amarya za ta tarar. Wannan haka
yake domin akan samu rikici a tsakanin kishiyoyi inda sau da dama amarya takan
yi ƙorafin
wasu abubuwa da ta tarar ana gudanarwa a gidan mijin idan ya saɓa wa ra’ayinta. Sai
ka ga ana ta rikici tana nuna uwargida ta cutar da gidan tunda ba ta bi da
mijin ya saba ba. A yayin da aka samu uwargida ta gari, za ta tarbiyyantar da
miji yadda ake so. Amarya idan ta shigo za ta samu sauƙi wanda shi ne ya
fito a kirarin. Kalaman uwargida a kirarin akwai lumana tunda ta ce:
Ke karere mai ƙananan yara! Ki yi
biyayya manyan `ya`ya su sa naki a makaranta, ki yi biyayya manyan `ya`ya su
taimaki naki, ki yi biyayya manyan `ya`ya su duba ki
Haba amarya! Haba amarya karere! Haba `yar
Basakkwaciya! Haba `yar Basakkwaciya! Ki kwantar da kanki! Ki kwantar da kanki
a inda aka fi ƙarfinki ki ba uwargidanki fili ta sanar da ke
waye mijinki domin ki samu wurin tsugunnawa!
Ta yi kira ga amarya da ta kwatar da
hankalinta domin ta ci arzikin gidan. Wannan haka yake tunda sau da dama manyan
`ya`ya su ne suke ɗauke wa uba ɗawainiyar iyali ko
yana raye ko a mace. Idan a raye ne, kila rauni na shekaru ya zo, ga shi yana
da ƙananan
yara `ya`yan amrya. Idan amarya ta sa tsiya a gidan miji kuwa, ta ƙi mutunta uwargida,
ya za a yi `ya`yan uwargida su kyautata wa na amarya? Ai zuciya an halicce ta
ne da son mai kyautata mata. Shi ya sa uwargida ta jaddada wa amarya a matsayin
nasiha, in ta ji ruwanta. Don haka wannan ya nuna uwargida tana da tarbiyya
daidai gwargwado a kalamanta. Kalmar da za a iya cewa ta bayyana ɓacin zuciyar uwargida
ita ce, ‘karere’, wadda take nufin `yar karo. Za kuma a iya fahimtar
cewa kirarin ya nuna mana akwai buɗewar ido saboda kila tasirin al’adun Turawa.
Wato in an kwatanta kirarin da wanda ya daɗe cikin al’ummar Hausawa, za mu fahimci akwai
zaƙewar
mata a yau. Domin nazarin Kafin Hausa, (1985) ya nuna cewa ba safai mata kan yi
kirari ba a ƙasar Hausa, watau su fito fili su yi ihu suna kirari.
Amma sukan yi wa wani abu kirari, shi ma ba sosai ba. A wasu kalaman kuma aka
nuna cewa mutum yakan yi wa matarsa kirari idan ta yi masa wani abu wanda ya ba
shi sha’awa. A yau kuwa sai ga shi mace na aikawa da muryarta ta kafar sada
zumunta ta zamani tana yi wa kanta kirari. Saɓanin da, kunya ba ta barin mata su
fito da kansu haka, har su fayyace abin da ke zuciyarsu. Har wa yau, za mu iya
fahimtar kirarin da aka gina na uwargida a da ya fi ɗaukar zurfin ma’ana.
Dubi dai inda aka ce:
Uwargida sarautar
mata
Uwargida uwar katarere
Kwari tankarin gida
Fara gutsura mai farar akaifa,
Kin ga ta kowa taki ta yi wuyar gani.
Wannan kirarin ya dunƙule duk abubuwan da
uwargidan ƙarni na ashirin da ɗaya ta bayyana. Babu dai wanda zai bugi ƙirji ya ce ga wanda
ya gina wannan kirari domin ya sha bamban da na wannan ƙarni da muke ciki.
Kirari ne wanda ya daɗe kuma babu kalmar da
ta fito a ciki wadda za ta iya fayyace mana jinsin wanda ya gina kirarin. Saɓanin wanda aka kawo ɗan yau, akwai
kalmomin da suka tabbatar da cewa mace ce ta gina kirarin. Kamar inda aka ce;
“Sai ni nan uwargida.” Sannan ya tabbata mace ce saboda ta sigar murya aka gina
kuma aka sadar wa jama’a ta kafar sada zumunta ta zamani (whatsApp). Idan an
lura sabon kirarin ya ginu amma bai zo a bisa sigarsa ta asali ba wanda za a
iya cewa sabon salo aka samu ke nan.
6.0 Karin Maganar
Hausa
Ma’anar Karin Magana
Karin magana nazari ne na halin rayuwa a
dunƙule
cikin maganganu gajeru irin na hikima. Masana da dama sun tofa albarkacin
bakinsu game da ma’anar karin magana. Misali:
Yunusa, (1977) ya kira ko ambaci karin magana
a matsayin Dunƙulalliyar Magana ne. A cikin
gabatarwar littafin nasa sai ya bayyana abin da ake nufi da Hausa a Dunƙule da cewa: “Hausa a dunƙule zance ne dogo a
dunƙule
wuri ɗaya, wato taƙaitacce.”
Ɗangambo, (1984) kuma
y ace: “Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a
cikin zance ko `yan kalmomi kaɗan cikin hikima.”
Furniss, (1997) ya dubi ma’anoni
daban-daban na masana da manazarta game da karin magana wanda shi kuma a nasa
kalmomin ya tabbatar da cewa, karin magana na nufin dunƙulƙlliyar magana ce
wadda take ƙunshe da ɓoyayyiyar ma’ana wadda kuma mai sauraronta sai ya nemi ciko
ko ƙarin
bayani a kanta.
Karin magana na nufin magana ta musamman
wadda sai an yi tsokaci ake ganewa. Ƙamusun Hausa (2006:
235).
Asali Karin Magana
Malumfashi da Nahuce (2014:31), a bisa
fahimtarsu da bayanan wasu manazarta, sai suka ce ce: “Karin magana ta samo
asali ne tun lokacin da Ɗan Adam ya ƙirƙira fasahar mayar da
zance mai tsawo ya zuwa gajere. Babu wani takamamman lokaci da aka keɓe cewa nan aka fara,
sai dai babbar hikimar da ke tattare da wannan shi ne karin magana ta ratsa
kowane fanni na rayuwar Bahaushe.
Matsayin Karin Magana
An ɗauki karin magana a matsayin wani gishiri mai
ba da ɗanɗano a cikin zance na
yau da kullum ga duk wanda ya iya harshen Hausa. Sannan mawaƙa da sha’irai suna
yawan amfani da wannan hikima a cikin waƙoƙinsu. Wannan na nuna
lallai karin magana ya kai ƙololuwa domin irin matsayinsa ta
fuskar adabi. Ga shi dai asalin karin magana adabin baka ne, to amma za a gan
shi yana karakaina a dukkan wani nau’i na rubutaccen adabi ko na baka. Waɗannan sun shafi waƙa da zube da kuma
wasan kwaikwayo. Kai ba a nan zancen ya tsaya ba, idan an duba mutum yakan
siffanta kansa da wani karin magana har ya rikiɗe ya koma kirarinsa, maimakon kowa da
kowa. Misali:
●Ko
ba a gwada ba, linzami ya fi ƙarfin bakin kaza: Karin magana ke
nan.
●Yaro
duban ni da kyau! Ko ba a gwada ba, ka san cewa linzami ya fi bakin kaza: Kirarin ke nan.
Lokacin Yin Karin
Magana
Karin magana kamar yadda aka faɗi, gishiri ne a cikin
zance, ya tabbata koyaushe ake yin shi. Amma ba kowa yake da fasahar baka ba.
Sai dai duk lokacin da mutane biyu ko fiye suka haɗu kuma magana ta
shiga tsakaninsu, da wuya ne ba a ji wani ya yi karin magana ba. Kafin Hausa,
(1985), shi ma ya ratso kalamai cikin nazarinsa game da kirari, ya ce: “Kirari
ya yi kama da karin magana ta fuskar cewa, duk lokacin da bukata ta taso a
cikin taɗi ana iya sa su don
mutum ya nuna gwanintarsa kan harshen.” Wannan ya tabbata cewa kowane lokaci ya
kama ana wanzar da karin magana.
Fasalin Karin Magana
Yunusa, (1977), bai fasalta karin magana
yadda wasu masana suka yi daga bayansa ba, ya dai ce suna da yawan gasken
gaske. A cikin littafin dai ya kawo karin magana fiye da ɗari shida ya bayyana
ma’anonin wasu daga ciki. Ya dai jero su ne bisa tsari na Abjadin boko, wato
tun daga kan waɗanda suka fara da
harafin ‘A’ a jere har zuwa harafin ‘S’.
Masana irin su Malumfashi da Nahuce (2014)
kuwa, sun fasalta karin maganar Hausa bisa dalili ko yanayi ko bigire na yadda
aka gina ta. Sun dai nuna rabe-raben karin magana suna da yawa, amma kaɗan daga waɗanda nazarinsu ya
kalato kuma suka kawo misalansu su ne:
Fasali
Misali
Karin magana mai ƙwar ɗaya: Matambayi ba ya ɓata
Karin magana mai ƙwar biyu: Kowa ya ci zomo, ya ci
gudu
Karin magana mai
labari: Gaba
ta kai ni, gobarar Titi a Jos
Karin magana mai ‘In
Ji’: Zama
wuri ɗaya tsautsayi ne, in
ji Kifi
Karin mgana mai ‘Sai’: Sai bango ya tsage
ƙadangare ke samun wurin fita.
Karin magana mai ‘An
ce’: Ba dole
ba, an ce wa ɓarawo ruga.
Karin magana mai ‘Daga’: Daga ƙin gaskiya, sai ɓata.
Karin maga mai ‘Ko’: Ko kurum, Magana
ce.
Karin magana mai ‘Dole’: Dole uwar na ƙi.
Karin magana mai ‘Har’: Cin danƙo har da su kaza.
Karin magana mai ‘Ta’: Ta malam ba ta wuce amin.
Karin maga mai ‘Tun’: Tun ranar gini,
ranar zane.
Karin maga mai ‘Ana’: Ana so, ana kai
kasuwa.
Karin maga mai ‘Wanda’: Wanda ya gani, shi
ka faɗa.
Karin maga mai ‘Da-na-sani’: Da-na-sani ƙeya ce, a baya take.
Karin maga mai ‘A’: A dafa a
daka, sai kalwa.
Karin maga mai ‘Da’: Da kai da kaya
duk mallakar wuya ne.
Karin maga mai ‘Ba’: Ba a canza wa
tuwo suna.
Karin maga mai ‘Tasirin
Gargajiya’: Sanin wurin
bugu, shi ne ƙira.
Karin maga mai ‘Tasirin
Musulunci’: Azumi ba salla,
holoƙo.
Karin maga mai ‘Tasirin
Zuwan Turawa’: Jirgin sama ba
ruwanka da kwalta.
Idan an duba littafin nasu za a ga sun
kawo misalai na karin magana da yawa a ƙarƙashin kowane fasali.
A nan kuwa an zaɓo ɗai-ɗai ne don a gwada
misali. Bayan hakan, sai suka rattabo ratayen karin magana sama da dubu shida bisa
tsari na Abjadin boko. Wato tun daga harafin ‘A’ zuwa harafin ‘Z’ don amsa
sunan littafin nasu.
7.0 Wasu Samfurin
Karin Magana a Ƙarni Na Ashirin da Ɗaya
Su ma waɗannan karin magana an tsince su ne
suna yawo a kafar sadarwa ta zumunta (WhatsApp) a watan Maris ta shekarar 2017.
Su ne kamar haka:
i) Boka
ya ci kuɗinmu, `yan Shi’a sun
ji saukar Buhari a Nijeriya.
ii) Haƙuri dole, wai ɗan Shi’a ya ga Buhari
a Bila
iii) Ka
ji ɗan albarka, matar
talaka ta ji muryar sarkin Kano.
8.0 Nazari da Sharhi
Da yake an ce wani abu game da nazari a
sama, yanzu kai tsaye sai a ce kamar yadda aka gani, waɗannan karin maganganu
guda uku suna cikin fasalin karin magana mai labari waɗanda sun samu ne ta
dalilin salon mulki a Nijeriya. Karin magana ta farko da ta biyu ta ambaci
sunan Buhari. To ba wani ba ne face shugaban ƙasar Nijeriya
Muhammadu Buhari. Abin da ya wakana shi ne, shugaban ƙasa ya yi tafiya zuwa
ƙasar
Landan (Birtaniya), domin hutawa da kuma duba lafiyarsa. Wannan ya sanya `yan
Nijeriya da dama cikin zulumi, wasu kuma cikin farin ciki. Masu farin cikin
tafiyarsa su ne suka yi ta fatar Allah ya sa sai gawarsa ce za ta dawo. Cikin
ire-iren waɗannan mutane, akwai
`yan Shi’a waɗanda suke ganin baƙin shugaba Buhari
saboda ƙarƙashin mulkinsa ne aka kashe masu mabiya Shi’a da yawa a
Zariya. Kuma an kame masu shugaba (Ibrahim El-Zakzaky) wanda har zuwa lokacin
tattara wannan bincike yana tsare. An yaɗa jita-jitar suna tsaface-tsaface don dai
Buhari ya mutu, kada ya dawo. Ikon Allah kuma da ya sha ƙarfin kowa da komai,
sai ya ƙaddara dawowar Buhari sumul bayan ya kwashe fiye da wata
guda a Birtaniya. Wannan lamari shi ya sa masu zulumi a lokacin tafiyar Buhari
suka maye gurbin `yan Shi’a wato farin ciki. Wannan farin ciki ya sa an ƙago waɗannan karin magana
mai cewa:
“Boka
ya ci kuɗinmu, `yan Shi’a sun
ji saukar Buhari a Nijeriya.”
“Haƙuri dole, wai ɗan Shi’a ya ga Buhari
a Bila”
Wato ga Buhari ya
dawo, sai dai wanda ya so mutuwarshi ya ɗauki haƙuri, tunda ya shiga
fadar gwamnati da nufin ci gaba da aiki. Kuɗinsu da suka ba bokaye kuma sun sha ruwa.
Mutane sun gina waɗannan karin magana da
nufin miƙa saƙonsu ne ga maƙiya shugabancin
Buhari. Suna tabbatar masu cewa Allah ya fi ƙarfinsu tunda ya
hukunta dawowar Buhari ba tare da ya mutu kamar yadda suka so ba. Shi ya sa
karin maganar ta ce haƙuri dole, da kuma boka ya
ci kuɗinmu.
Karin magana mai cewa: “Ka
ji ɗan albarka, matar
talaka ta ji muryar sarkin Kano.” Ta samu ne saboda salon mulkin sarkin Kano
na yanzu, wato Sunusi Lamiɗo Sunusi II. Mulkin nasa ya kalli matsalolin zamantakewar
aure ne tsakanin musumi a jihar Kano. Don haka ya kafa kwamiti na malaman
addinin musulunci don su kawo masa rahoto game da sharuɗɗan musulunci ga yin aure ko ƙara aure. Sannan
mulkinsa ya jaddada a matsayin doka wadda kowa zai bi don a sama wa mata sauƙi na wahalhalun da
suke samun kansu a ciki sakamakon gallazawar mazajen aurensu. To da yake
talakawa sun fi shan wahala, sarkin ya fi karkata a gare su. Wannan yunƙuri na sarkin Kano ta
faranta wa jama’a da dama rai muasamman mata. Shi ya sa kwatsam sai ga wannan
karin magana. Ita dai matar talaka babu abin da ya fi mata face ta sa wa sarki
albarka, in ji masu hikimar magana.
Masana sun tabbatar
da cewa karin magana tana ƙunshe da muhimmin saƙo. Misali Yunusa,
(1977) ya ce: Ita irin wannan magana sau da yawa takan faɗakar da mutane ko
kuma ta yi masu habaici. A wani lokacin kuwa takan yi kama da kirari.” Da haka
kuwa za mu tabbatar da cewa karin maganganun da wannan maƙala ta kawo ta yi
nazari a kansu, an yi hannunka mai sanda ne ga al’umma don su fahimci
kurakurensu.
9.0 Kammalawa
A Wannan maƙala an yi ƙoƙarin kawo wasu kirari
ne da wasu karin magana da aka tsinto ta kafar sada zumunta kamar dai yadda
bayani ya gabata. Haƙiƙa an fahimci lallai harshen Hausa da adabinsa da ma
al’adunsa, na tafiya tare da kowane irin zamani. Game da kirare-kiraren da aka
kawo, an tabbatar akwai asalinsu da daɗewa. Sai dai an fahimci akwai tasirin irin
zamanin da ake ciki a kirare-kiraren. An gano kuma an tabbatar da cewa a
tattare da kirari da karin magana har yanzu akwai ɗimbin hikima da
zurfin ma’ana mai ɗauke da saƙo na musamman. An
kuma ƙara fahimtar cewa kirari koyaushe akwai mai shi, wato
kullum akan lanƙaya kirari ga mutum ko wani abu da ba mutum ba; yayin da
karin magana ta kasance gishiri ne a cikin zance. Sai dai dukkansu ana aiwatar
da su a duk lokacin da bukata ta taso a cikin zance don mutum ya nuna
gwanintarsa ta fuskar sarrafa harshen Hausa da isar da saƙo cikin hikima.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai takarda.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.