Ticker

Wakar Zaura Ta Sanin Baldo: A Tsakanin Gaskiya Da Karya

In Kadaura Journal of Hausa Multi-Disciplinary Studies, Vol. 1, No 3, Department of Nigerian Languages and Linguistics Kaduna State University, Kaduna. Pp 146-159/ISSN: 2536-7609.

Kayan kwalliya

Waƙar Zaura Ta Sanin Balɗo: A Tsakanin Gaskiya Da Ƙarya

Rabi Mohammed
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harsuna,
Jami’ar Jihar Kaduna, Nijeriya.
Email: rabimohammeddatti@gmail.com
G.S.M: 08060771666/08050311800

1.0 Gabatarwa

Da yake Hausawa a al’adance da addinance, suna ƙoƙarin assasa tarbiyya mai kyau, sai ya kasance suna da hanyoyin  gyara tarbiyya maras kyau a adabance, ta inda za a sami waƙoƙi daban-daban da karin magana da tatsuniyoyi da sauransu, waɗanda suke gargaɗi ko faɗakarwa ta hanyar nuna illar wasu halaye tare da nuna sakamakon mai aikatawa don ya daina. Haka ma sukan nuna sakamako mai kyau ga wanda ke da kyawon hali don wanda bai siffantu da shi ba ya yi koyi. Ire-iren waɗannan ayyukan adabi akan yi nazarinsu ta fuskoki daban daban. Ɗangambo  (2007:6-7), ya bayyana cewa, “akwai hanyoyi guda biyu manya na nazarin waƙa. (1) Hanyoyin Gargajiya da (2) Hanyoyin Zamani.”  Hanya ta farko wadda kai tsaye ita ta shafi wannan nazari ita ce ya bayyana ta a matsayin  wadda malamai da sauran suke amfani da ita don su bayyana ra’ayinsu game da ingancin waƙa, littafi ko wani rubutu. Wato zantuuttuka ne na yabo ko kushewa inda za ka ji idan an saurari waƙa wani ya ce ‘ta burge shi’ ko’ ta ƙayatar’ ko’ ba laifi’ ko ‘ga a nan dai’ ko ‘ba yabo ba fallasa’ ko ba ta yi kyau ba’ ko ‘ai sha’ani’ da dai sauran kalamai makamantan hakan. Don haka ne wannan nazari zai yanke hukunci ya sa waƙar Zaura ta Sanin Balɗo a sahun waƙar da ta ƙunshi gaskiya da ƙarya da rayuwar masu  aikin adabi suka gada yau da kullum.

2.0 Wace ce Zaura?

    Wannan kalma ‘Zaura’ kamar yadda mawaƙin ya yi amfani da ita, a Hausa dai an fahimci ana danganta ta ne da mace kuma a wani yanayi da ta riski kanta, musamman a yankin Sokoto da Zamfara da Kabi. A sauran sassan kamar Kano da Katsina zawara ko bazarawa suke kiran ta. Robinson (1913:439), ya bayar da ma’anar wannan kalma zuwa kalma biyu da Ingilishi, wato ‘widow’ da ‘diɓorced woman’. To idan an bi diddigin waɗannan kalmomi, za a ga a ƙamusun Ingilishi, kalmar ‘widow’ na nufin macen da mijinta ya rasu ya bar ta musamman a lokacin da ba ta yi wani auren ba. Ita kuwa kalmar ‘diɓorcee’ na nufin wadda mijinta ya sake ta, kuma ba ta riga ta yi wani auren ba. A ƙamusun Bargery (1934), ya bayar da ma’anar kalmar Bazawara da cewa wadda ba ta da miji. Shi kuma mai neman auren Bazawara shi ne Bazawari. Ta ɓarayin Ingilishi, ƙamusun shi ma ya bayyana kalmar ‘widow’ a matsayin Bazawara ko Zawara ko Gwauruwa. Sannan Ƙamusun Hausa (2006), ya ambaci zawara wadda ya nuna ita ce dai bazawara. Bazawara kuma na nufin, “matar da aurenta ya mutu, ko mijinta ya mutu ta gama idda tana zaman gida kafin ta sami wani mijin.    

     Shi kuwa Abdullahi  (1999:45), cewa ya yi “wannan kalma ta zawarci ta samo asali ne daga kalmar zaura. Wato matar da ta rabu da mijinta saboda wasu dalilai, amma ba ta riga ta auri wani mijin na daban ba. Sai dai saboda bambancin karin harshe a waɗansu wurare (kamar Jihar Kebbi) sukan bambanta da cewa Zaura ita ce wadda mijinta ya mutu, wasu na ƙarawa da cewa mai zawarcin tilas. Amma wadda ta rabu da mijinta saboda wasu dalilai, ana kiran ta da sunan gwauruwa.”

     Sarkin Sudan (2008:124), ya bayyana ko wace ce zaura da cewa, “ A al’adar Maguzawa idan mace ta rabu da mijinta, ko ya sallame ta, ko kuma mijinta ya mutu, to ta zama bazawara ke nan. Wannan zama da za ta yi a wani lokaci tsakanin fitowarta gidan wani da kuma yin wani auren shi ake kira zawarci.”

    Dangane da waɗannan bayanai game da ko wace ce zaura, an fahimci lallai Bahaushiyar mace ba za a taɓa kiran ta bazawara ba sai dole ta taɓa yin aure, kuma auren ya ƙare a sakamakon mutuwar miji ko mutuwar auren ta dalilin saki. Amma da zarar ta yi wani auren, to ta fita a muhallin zawarci kuma.

3.0 Mawaƙi Sanin Balɗo Da Alaƙarsa Da Bazawara

   Nazarin Abdullahi (1999:51), ya bayyana dalilin yin wannan waƙa cewa a sakamakon neman wata Bazawara  da Sanin Balɗo ya yi ne a garin Nasarawar Burƙullu, a ƙaramar hukumar Anka, Jihar Zamfara mai suna Fati wadda kuma suka yi alƙawari a kan ba za ta auri kowa ba sai shi. Daga baya kuma sai ta yi ƙaryar cewa ita mijinta bai sake ta ba, har ma ta gaya wa sauran manemanta. Ashe sun yi alkawari ne da wani daban ya sa ta faɗa wa abokin Sanin Balɗo haka. Shi kuma ya je ya faɗa wa Sanin Balɗo, don haka sai ya ɗauki kayan kiɗa ya zambace bazawarar. Daɗin daɗawa ya je har ƙofar gidan su Fati Bazawara ya sanya kaset ɗin mutane suka ji.

4.0 Waƙarsa Ta Zaura A Faifen Nazarin Adabi

    Adabi wani katafaren fage ne mai ƙunshe da harshe da al’adu na dunƙulalliyar al’umma, amma bisa sigarsa ta sanya nishaɗi ta hanyar amfani da salo iri-iri waɗanda suke taimaka wa mai aikin adabin ya isar da saƙonsa ga al’umma. Wannan hoto na adabi da ya bayyana a waƙar Zaura ta Sanin Balɗo ya sanya manazarta adabin Hausa sun yi sharhi a kanta. Misali:     

  Nazarin Abdullahi (1999), da na su Sarkin Gulbi (2013), sun yi sharhin waƙar filla-filla musamman game da jigonta da salonta. Babban jigon da aka nuna shi ne zambo. Akwai kuma ƙananan jigogin da suka taimaka wajen fitowar babban jigon wato habaici da zagi a cewar Abdullahi Rabi’u. Ya kuma nuna wannan waƙa cike take da salo da azanci, domin tana da salon buɗewa da salon kamance na daidaito da na fifiko da na kasawa. Haka ma akwai salon siffantawa da salon dabbantarwa da salon labartawa da salon washi da kuma salon maimaitawa, duka a cikin waƙar. 

    Mode (2002), ya yi tsokaci ne game da wasu munanan halayen bazawara. Shi ma ya alaƙanta nazarin nasa ne da wannan waƙa wadda Sanin Balɗo ya yi wa Bazawara musamman saboda munin halinta a gare shi (mawaƙin) da wasu. Waƙar ta feɗe bindin munanan halayen bazawara har wutsiya. Ya dubi waƙar ta Sanin Balɗo ya karkasa yanayin ɗabi’un bazawara daban-daban.  Haka ya nuna cewa ita bazawara ba ta da zaɓi, tana dai yaudarar rukunan mutane mabambanta kamar tsoho ko yaro; mai lafiya da naƙasasshe; mai kuɗi ko talaka;  duk tana sauraron su, in ya so in ta sami biyan buƙatarta ta zanzare.  Ya nuna kamar a waƙar ta yaudari kurma da ɗan garuwa da mai alawa da ɗan tireda da mahauci da maƙeri da wanzami da Bafillatani da malami har da shi kansa mawaƙin.

   A nazarin Rabi (2011), an yarda cewa lallai ana samun mace maƙaryaciya mai cin amana inda cikin misalan da aka kawo daga bakin mawaƙan baka na Hausa, har da wannan waƙa ta zaura da Sanin Balɗo ya yi.  Babu shakka wannan waƙa tana da matsayi a adabin Hausa domin tana da manufa ta huce haushi ko takaici na mawaƙin ga zawarawa, sannan uwa uba cike take da gwanintar kwatance da ke ɗaukar hankalin mai sauraro har ya tasirantu da ita, ta fuskar sa shi nishaɗi ko kuma akasin haka.

5.0  Wasu Waƙoƙi Masu Turken Faɗakarwa

    Gusau  (2008:384-387), ya nuna waƙoƙin baka babu shakka suna taimakawa wajen yi wa jama’a sanarwa da wa’azi da gargaɗi da jan kunne da kuma wayar da kai. Ire-ien waɗannan waƙoƙi suna da yawa. Daga cikinsu akwai masu gargaɗi kan gyaran rayuwa kamar yadda ya kawo misali:

Mu gargaɗi mai gina ramin mugunta

(Shata: Hana yin mugunta)

 

Kuɗi a kashe su ta hanya mai kyau

(Shata: Tsawatawa kan almubazzaranci)

 

Allahu mafi girma

Wanda babu irinai ai,

Ya la’anci malalaci

(Ɗanmaraya Jos: Hana lalaci)

 

Allah Wahabu Sarki’

Sarkin da ba kamatai,

Ya Allah mai gumi da ɗari.

(Ɗanmaraya: Tsawatarwa kan Duniya II)

 

Jawabin aure za na yi

(Ɗanmaraya: Riƙo da yin aure)

 

Amma mai akwai da babu,

Duk dangantakarku daidai.

(Ɗanmaraya Jos: Matsayin Daraja a Rayuwa)

 

Mun jiyo labarin ta zubar

(Shehu Ajilo: Kwaɗaitarwa kan yin aure da tsawatarwa kan aukawa cikin karuwanci)

   

    Umar M.B (1987:40), shi ma ya bayyana Ɗanmaraya Jos a matsayin wanda waƙoƙinsa suke ƙunshe da gargaɗi da wa’azi da faɗakarwa da nasihar rayuwar duniya a dukkanta. Ya kawo misali da waƙar Jawabin Aure wadda take nuna tsarin zamantakewar iyali a ƙasar Hausa musamman ma ta fannin haƙƙin miji a kan matarsa, da kuma haƙƙin mata a kan mijinta bisa tafarkin addinin musulunci. Mawaƙin , daga nan ne ya ja zaren warware jigon wannan waƙa inda ya fito da hoton ɗabi’ar mace mai haɗa husuma ta hanyar yaɗa gulma a tsakanin ma’aurata har ya zama sanadin mutuwar auren. Da zarar aure ya rabu, sai Ɗanmaraya yake nusar da mace ta gane saboda wahalhalun a kanta zai koma. Shi ma maigida yana samun matsala idan har ba shi da wata matar saboda kula da gida da ya rataya a wuyan matarsa.

 6.0 Waƙar Zaura A Matsayin Tsakanin Gaskiya da Ƙarya

    A cikin wannan waƙa an muzanta mace bazawara ba don komai ba sai don rashin alƙawari da ƙarya da ta yi.  A gaskiya duk wanda ya saurari wannan waƙa musamman ma dai mata zawarawa,  za su ce, an cuce su saboda muzantawar ta isa matuƙa, wadda za ta iya sa wani namijin ba zai amince wa mace bazawara ba in har ya bi ta wannan waƙar saboda ba lallai ne ya fahimci cewa wannn adabi ba ne. 

     A duba wannan ɗiyar daga cikin waƙar:

                                      Kuma kowa am mabiɗin zaura

                                      Hasara ukku shina yin ta ko shi aw wa

                                     Sani ɗan Balɗo faɗas su mu gane in kan san su

                                     Ka ga dai na san sallar mabiɗin zaura

                                     Ni san koyaushe ƙala’i ta sanƙira

                                     Har yau bai shiga jam’i ba, wa shi nan

 

Sanin Balɗo dai ya ci gaba da tsinar bazawara a kan ƙarya da saɓa alƙawari inda yake cewa :

Mai guntun alƙawali,

Mai guntun keso,

Mai guntun luddai,

`Yar Inna da Baba ɗiyak Kawu,

Zaura ke kam lamarin,

`Yebabbar Allah,

Ban ra’ayin zaura,

Kuma ni nan ba ni biɗar zaura,

Amma kuma ban hana yarona nema ba.

     Ya ƙara bayyana tsananin ƙiyayyarsa da bazawara a kan wannan hali inda ya ce:

 To don tsananin ban ra’ayin zaura,

 Don ta gaishe ni da aiki,

 Gwamma ya zam na ɗakko sumogal,

 Kwali goma,

`Yansanda goma su kama ni,

 Moba Polis goma su iske mu,

 Can daji a yi ta duka ta,

 Sai ka hwaɗi,

 To Alhaji Sani ya hi ɗumin Zaura.

 

 Tsaya ka ji Zaura mun ruhe hulɗa.

  Sam- sam Alhaji Balɗo mijin Dije,

  Don tsananin ɗai ban ra’ayin zaura,

  Ni nan da a ce mini ga zaura,

  An ba ni tare da mota 505.

  Sai an gina gida na gilashi du,

  Sai  an  shahe da siminti swal,

  An ba ni.

  Ga ɗinki  goma na shadda,

  Dun ni ad da,

  Ga hula goma ta sokewa du ƙube,

  Kai ni!

  Da  agogo goma na ɗarmawa,

  Ni ad da,

  Ah!

  Takalmi goma na takewa dub Bata,

  An haɗa ɗan Balɗo,

  An ban Tibi da Rikoda ta jibisi, (JƁC)

  Ga Janareta sabo an ban,

  Ai  mani burtcatce na ruwan sha,

  Ga kuma firinjin,

  Sabo an ban an yi ma Mamman,

  Don sanyinsu.

  Sannan ɗakina kowane fanka,

  Sai ta tashi.

 

  A ba ni naira dubu ta sayen magi ,

  Da naira dubu ta sayen manja,

  A ce mani ka gan su nan,

  Kyauta an ba ka,

  To kuma ga zaura,

  Kai ad da!

  Alhaji don tsananin ɗai ban ra’ayin zaura,

  Wajen motag ga ta hwarin nai,

  Ni gwamma a ba ni aron keke ,

  Ko tsoho na duk da na sata na,

  In ciyo mil goma cikin rairai,

  Dan Sani Balɗo mijin Dije.

 

            ` Yansanda da suka gane ni,

  In shekara goma ga `Yansanda,

  Sun riƙe,

  Alhaji na san ban yi asarar,

   Kwanana ba,

    Ya ka!

 

    Don na san ta kowaj ji wuyaz zaura na hi shi,

    Kai!’irin wanga hali mu ɗan Balɗo,

    Kamak kura ta irke farin rago,

   An turke yamma garai danni ya hwaɗi,

   Ɗauki abincinki,

   Banza ne.

   

    A duba irin abubuwan  da ya faɗi saboda munin hali na rashin alƙawari da ƙarya da bazawara ta yi masa. Yadda yake  nuna irin ƙinsa da bazawarar, shaci faɗi ne irin na aikin Adabi wanda ya saɓa wa tunanin Bahaushe.

    Don  ƙara nuna wa jama’a irin wannan munin ɗabi’a, akwai inda ya yi mata zambo kamar haka:

Ni dai ni niy yi kiɗin zaura,

`Yar Inna da Baba shiririta nomanki,

`Yak kicihin darga,

Mai sa dattijo a raina mai dattako,

Zaura `yab Baba,

Mai kai tsohonta ga rantsewak kaffara,

Zaura `yab Baba,

Mai sa shiyyarsu ta rummace,

Ke wuta ƙanenki ɓarawo tsoho murhu.

        Idan aka yi nazarin wannan waƙa za a ga kuma ta shafi sauran mata zawarawa waɗanda ke da irin halin da ma waɗanda ba su da shi, domin shi ya yi amfani da karin maganar nan mai cewa ‘wake ɗaya shi ke ɓata gari’. Hakan kuma ya faru ne garin gudun gara sai aka faɗa wa zago. Wato tun farko shi mawaƙin bai ambaci sunan wadda ya yi waƙar domin ta ba, bai kuma yi ƙoƙarin a sakaya ta  ba,  sai ya yi fyaɗar `ya`yan kaɗanya  har lokacin da uwar bazawarar ta nemi cewa don Allah idan zai yi waƙar kada ya sa sunan `yar tata saboda kada waƙar ta yi tasiri a kanta kawai. Ba ta san cewa da ma bai sa sunanta ba!

7.0  Dangantakar Waƙar Da Wasu Waƙoƙi Ta Fuskar Turke

    Idan aka bi ƙwaƙƙwafi game da maganar turke a nazarin waƙar baka, to za a ga Gusau  (2008:369-392), ya tsettsefe nau’o’in turke a waƙoƙin baka na Hausa waɗanda suka haɗa da na yabo zalla da na zuga zalla da na yabo surke da zuga da na zambo da na ta’aziyya da na wayar da kai da tarihi da na siyasa da na kishin ƙasa da na soyayya da na wasa kai ko koɗa kai da na taya murna da sauransu. Da farko ya nuna cewa “Turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba.” Dangane da yanayin turke a waƙar baka kuwa, Gusau ya nuna cewa makaɗi ne yakan lura da halayyar rayuwar zamantakewar  al’ummar da zai yi wa waƙa. Don haka sai Gusau ya ce, “Nagartacciyar waƙar baka ta Hausa ita ce wadda take ɗauke da turke mai ƙarfi ba rarrauna ba, mai kyau ba maras kyau ba, wanda ya dace da kyawawan al’adu da ɗabi’u, ba wanda ya kauce masu ba.”

    Dangane da waƙar da Sanin Balɗo ya yi wa bazawara ta fuskar turke dai ba ta zama wadda ta fuskanci cikakkiyar gaskiya kai tsaye ba. Waƙar tun daga farkonta har ƙarshenta, kai tsaye turkenta zambo ne na wulaƙanci wanda zai iya haddasa wasu maza su ci gaba da mayar da mace ba komai ba a idon al’umma.  Amma ire-iren waƙoƙin baka daban-daban waɗanda aka ga misalansu suna faɗakar da mata da sauran jama’a a game da wasu munanan ɗabi’u, ba tare da aibata su ta yadda za su sami  illa ba.

Don haka wannan waƙa tana da raunin turke bisa waɗannan hujjoji da dalilai:

Haruna Uji yana faɗin:

                                                 Na kaɗa `yar gangata

                                                 Za na faɗa wa mata

                                                 Ku kama tafarkin aure

                                                 Aure shi ya fi daɗi

 

                                                 Kai ga wa’ai zan bayar

                                                 Bayan haka in kun dubo

                                                 Yara ku kama tafarkin aure

                                                 Wai ko kun san aure?

                                                 Miye ya fi uba kuma?

                                                 Kuma miye ya fi uba?

                                                 Wallahi shi ko aure.

 

Amma shi Sanin Balɗo  a tasa waƙar ya yi ta ƙoƙarin dakushe kimar zawarawa a idon maza, kamar a inda  ya ce:

                                            To fa maza mabiɗa Zaura,

                                            Don Allah ku kakkaɓe kunnenku,

                                            Ga Alhaji nan wa’azai kai ma malam,

                                            Kana gidanka ka sauraran na fara 

 

                                           Don ka gani kowace zaura na san halinta

Ya ci gaba a inda ya ce:

                                  Zaura duk ad da ɗiya goye,

                                  Sannan ga wani yaro ta jawo shi,

                                  Ita ta nika ce ma kwaramgwanki

                                  Wannan dum mai biɗatta ba ya da hutawa,

                                  Ya hwaɗa ma kwaramgwamki,

                                  Ya shiga ƙumci da kwaramgwamki,

                                  Ya isko damisa da ɗiya kwance,

                                   Ko ka san da wuya ko za ya fita wannan mirkizza.                     

 

A wani ɗan waƙar kuma ya nuna cewa:

                                

                                 Ta ci mazan jiya, ta ci mazan yanzu,

                                  Bale ta kai ga mazan yau mu,

                                  In mun kai ga katifa sai ta waye,

                                  Ka ji zaura ta hwasa malamman Ƙur’ani

                                  Mai kwana wuridi zamne

                                  Modibbo ya kwana kiɗan tasbi,

                                  Ya tafi biɗar zaura ta ƙi shi,

                                  To bale ta sadu da malamman boko

   

   A nan za a iya fahimtar akwai alaƙar turke tsakanin waƙoƙin ta inda akwai kira game da amfanin yin aure, da kuma neman karya lagon auren ta wani ɓarayi, duka dai a adabance. Kuma wannan ya tabbatar da cewa shi fa adabi a wasu lokuta ba wai yana bayyana gaskiyar lamurra ba ne, sai dai ya samar da nishaɗi. Amma kuma kash! Wannan waƙa ta zaura ba ta zama mai nishaɗantar da mata ba. Watakila saboda yanayin turken nata ne na zambo kai tsaye wanda kuma ya shafi kowace bazawara.

    A nazarin Abdullahi (1999:48), an nuna wannan waƙa ita ce Bakandamiyar Sanin Balɗo domin ita ta fi shahara a cikin waƙoƙinsa kuma jama’a suka fi karɓar ta. To a nan in an lura da kalmar ‘jama’a’ a Hausa jam’i ce wadda ta haɗe rukunan mutane maza da mata. Kuma a nazarin an nuna cewa shi kansa mawaƙin ya bayyana cewa zaurori ba su buƙatar wannan waƙar, har ma idan zaura ta biyo hanyar da ta ji an sa kaset ɗin waƙar, to sai ta yi sauri ta sake hanya. (Abdullahi, 1999:54).

    Bugu da ƙari wannan maƙala ta gano mata waɗanda suka haɗa da zawarawa da masu aure da kuma `yan mata da yawa waɗanda suka tafi a kan cewa wannan waƙa da suka saurara sam ba ta yi masu daɗi a ransu ba. Daga cikin ra’ayoyinsu game da hakan akwai budurwa `yar shekara ashirin da uku, da ta ce:

“Ba na fata in zama bazawara saboda ba kowace bazawara ba ce take da wannan halin haka. Kuma gaskiya bai ma zawarawa adalci ba domin kamar yadda ya faɗa ai shi bazawara ɗaya ce kawai ta yaudare shi.”

    A ra’ayin wata matar aure `yar shekara talatin da bakwai, cewa ta yi:

“Waƙar ta baƙanta min rai don ba faɗakarwa ba ne sai dai zambo da habaici wanda sai dai ya hassala zawarawa saboda ba kowace bazawara ba ce ba ta ƙwarai ba, akwai wacce mijinta mutuwa ya yi, wata kuma ba tai sa’ar miji ba ne, shi ya sanya ta zama bazawara. Ni a ganina ba ai ma zawarawa adalci ba.”

    Sai misali na ra’ayin wata bazawarar `yar shekara arba’in da shida wadda mijinta ya rasu, inda ta ce:

“ Da na saurari waƙar, a raina na ji haushi. Waƙar ba faɗakarwa take yi ba don abin da yake faɗa ba gaskiya ba ne, don mutum ba zai iya yanke wa mutane da yawa hukunci a kan halin da ya gani a wajen mutum ɗaya ba.”

    Kuma ba Sanin Balɗo ne ya fara waƙa mai turken zambo ba. Akwai su da dama. Sai dai abin da wannan takarda take son tabbatarwa shi ne, mata a matsayinsu na iyayen al’umma, ba sa buƙatar irin wannan salon waƙar. Daga cikin matan da suka bayyana ra’ayoyinsu, sun nuna lallai akwai waƙoƙin da suka yi tasiri a gare su, wato suna son sauraronsu kuma suna amfana da su wajen guje wa munanan ɗabi’u. Ire-iren waƙoƙin kuwa sun haɗa da:

●Waƙar Sana’a da kuma waƙar Gwarne na Barmani Coge

●Waƙar Gangar Wa’azu

●Waƙar Gidan Haya ta Babangida Kakadawa

●Waƙar Jami’a ta Aminu ALA

●Waƙar Labbaika Rasulullah ta Ramla

●Waƙar Rayuwa ta Fati Musa

●Waƙar Matar Jami’a da Waƙar  Ba Zan Sake Ki Ba ta Naziru

●Waƙar Aure ta Ɗanmaraya Jos

●Waƙar Gwauro ta Shatan Nijar

 ●Waƙar Gwauro ta Ahmadu Doka

●Waƙar Aure ta Haruna Uji, da dai sauransu da dama

    Babu shakka idan aka bibiyi waɗannan waƙoƙi, aka daganta da wadda aka yi wa bazawara, sun bambanta ta fuskar turke, amma  kuma ta wani ɓarayi za a ga mummunar ɗabi’ar wata mace ta sa aka yi ta. Kamar misalin waƙar da Barmani ta yi ta Sana’a da wadda Shehu Ajilo ya yi ta Halin Ɗan Adam (karuwa) da sauransu, duk sun fito da munin ɗabi’ar wasu mata amma ta fuskar neman su da su gyara ne cikin azanci, ba tare da ta shafi matan kirki ba. Amma waƙar zaura ta nuna duka zawarawa ba su da halin kirki ko kaɗan.

        Wata hujjar mai nuna waƙar tana da raunin turke ita ce, ta inda mawaƙin ya fallasa kansa a lokacin da aka gaya masa abin da Fati ta ce, sai ya ce, “Wanda ke bisa sa ai bai kwaɗayin tozo.” Dalili kuwa, ko da yake neman bazawarar nan, to yana sha’awar barin ta ya koma wajen wata yarinya mai suna Matuna wadda kuma ya aure ta ɗin. Mawaƙin ya nuna cewa har gardama ake yi a kan wadda ta fi kyawo daga cikinsu. Wani lokaci ma idan gardamar ta tashi, sai ya hau mashin ya tafi ya dubo Matuna, ya zabura kuma ya tafi wajen Fati (zaura) don ya gwada ya ga wadda ta fi kyawo. (Abdullahi 1999:52).

     Bisa fahimtar waɗannan maganganu za a iya cewa ke nan, shi ma mawaƙin, da ya so ya yaudari zaurar da yake nema. Allah bai nufi hakan ba, sai tata yaudarar ta riga bayyana. Don haka ya dai huce haushinsa ne kawai ba wai duka abin da ya faɗi a waƙar haka ne ba.

7.0 Kammalawa

    Bisa taƙaitawa, wannan takarda ta yi ƙoƙari ne ta nusar da al’umma  game da matsayin yin zambo irin wannan, musamman ma ga mata waɗanda suke iyaye masu daraja. Mace kamar yadda Allah ya nufe ta, `yar lele ce wadda take buƙatar a kula da ita ta kowace fuska ta yadda shi kuma namiji zai more mata. A maimakon in ta nuna munin hali a yi mata zambo na ɓatanci, kamata ya yi a yi mata gargaɗi ko nasiha ko wa’azi ta yadda za ta amshi saƙon. Idan ma za a yi zambo mai kaushi, zai fi zama daidai ga ɗabi’ar mata ta karuwanci saboda babu abin kala ga macen da take cikinsa. Zawarci kuwa wata ƙaddara ce da take faɗa wa mata ba kuma lallai sai da laifinsu ba. Nazarin Abdulmumin (2002) ya fito da irin wannan yanayi a rubutattun wasannin kwaikwayon Haausa, a inda ya yi nuni da yadda iyaye ke nuna fin ƙarfi don kwaɗayin kuɗi su tilasta wa `ya`yansu mata auren da ba sa so.  A wasannin guda biyu, mazan da aka ba `ya`yan sun kasance mashaya giya kuma su ma sun tauye wa matan nasu haƙƙinsu na ciyarwa da sauransu.  In matan sun  nemi `yancinsu sai su lakaɗa  masu duka kuma ba damar su kai ga iyayen nasu.  Don haka dole sun zama tamkar bayi sai yadda ta Allah ta kasance. Haka ne kuwa domin Baturiya bayan wahala a ƙarshe sakin ta mijin ya yi tun tana ƙaramarta. Yayin da a wasan ‘Uwar Gulma’ Halima a ƙarshe mutuwa ta yi a sakamakon wahalhalun  da iyayenta da mijinta suka jefa ta.

       A ƙarshe, wannan maƙala za ta rufe da Basakkwaciyar waƙa daga bakin Hafsatu Guliliya wadda  ta kasance ruwan wanke dauɗar Bazamfarar waƙar zaura da aka yi sharhinta.

Ga irin abin da take cewa:

Kuma can ga wurin magana ku daidaita,

Ta hairi ko ta sheri ta.

 

Magana mai ba da kunya ta,

Ka hwaɗinta  ana ta dibin ka.

 

Kuma in magana mai ba da shawa,

Ka ga hwaɗe ta ana ta shawak ka.

 

Kyawon magana in za ka yo ta,

Ka san wada za ta hita ga halshenka.

 

Kuma in ka yo ta ka san zamanta,

In ba ka san ta ba kak ka hulta ta.

Tun da dai magana na yanke kan,

Wanda yay yi ta ko ba ta yanke halshenai,

Magana zagal bunu ga ɗaki.

Kan tah hita ba ta komawa.

 

Wai  ashe magana tamkah halitta ta,

Wada duk ka ƙi ba a canza ta .

 

Ke  mai waƙa dena yin zambo,

Zambo  bai waƙe halkata.

Kuma masu habaici sai ku daina,

Mai ƙazahi ke ma ki bar yi nai.

 

Kuma ke mai waƙa dena yin zambo,

Ba zambo ad da samu ba.

Azziki ke san na Allah na,

Samu da  rashi na Allah na.

      

        Da wannan kira da `yar`uwa ta yi wannan nazari ke fatar mawaƙa za su lura. Masu nazari kuma su ci gaba da sa ido su yi rubuce-rubucen da za su ciyar da al’umma gaba. Su kuma zawarawa, su danne zuciyarsu, su ƙara ƙaimi wajen kyautata ɗabi’unsu. Maza kuma idan sun ji irin wannan waƙa su tuna, ba a taru an zama ɗaya ba, kada su bari shaiɗan ya sami kafa ya cusa masu ƙyamar bazawara domin waƙa kamar kowane aikin adabi ba gaskiya ba ne tamke a ciki, akwai shaci-faɗi da ƙirƙira.

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.

Post a Comment

0 Comments