Wannan ɗaya ne daga cikin jerin bidiyoyin taron gabatar da rubutattun waƙoƙin gasar da Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato ta shirya. Jigon waƙoƙin gasar shi ne "Tsaro a Arewacin Nijeriya." A cikin bidiyoyin taron za ku kalli yadda fasihai 30 daga jahohi daban-daban a faɗin Nijeriya suka fafata. Daga ƙarshe an ba da kyaututtuka masu tsoka ga waɗanda suka taka rawar gani.
Wani abun burgewa shi ne, bayan rubutattun waƙoƙi da aka gabatar, akwai kuma gasar "ja-in-ja" da "ga-ni-ga-ka." A wannan gaɓar haziƙan sun nuna bajintarsu nan take.
Duba sauran bidiyoyin domin kallon sauran ɓangarorin taron.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.