Ticker

    Loading......

Waiwayen Ginshikan Bukatun Rayuwar Maguzawa

Cite this article as: Abdullahi, I. S. S. (2021) “Waiwayen Ginshiƙan Bukatun Rayuwar Maguzawa” Scholars International Journal of Linguistics and Literature ISSN 2616-8677 (print) ISSN 2617-3468 (Online) Scholars Middle East Publishers, Dubai, United Arab Emirates. Journal Homepage: https//saudijournals.com DOI: 10.36348/sijll.2021.v04i09.003

Waiwayen Ginshiƙan Bukatun Rayuwar Maguzawa
Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Department of Nigerian Languages
Usmanu DanfodiyoUniversity, Sokoto.

Maguzawa

Tsakure

Wannan bincike ya yi nazari ne a kan yadda al’ummar Hausawa suke gudanar da muhimman al’adun matakan rayuwarsu. A ƙoƙarin fayyace waɗannan ginshiƙai na rayuwa kamar yadda suke a kowace al’umma, nazarin ya kalli irin tanadin da Maguzawa suke yi musu a al’adance. Waɗannan abubuwa kuwa su ne abinci da muhalli da sutura da hanyoyin tattalin arziki da makamai da kuma hanyoyin samar da magunguna. Manufar wannan bincike ita ce a tabbatar da cewa, su ma Maguzawa al’adarsu ita ta tanadar musu yadda suka shimfiɗa rayuwarsu dangane da wasu ginshiƙai na rayuwa. Haka kuma nazarin yana da manufar fayyace yadda Maguzawa suke amfani da fasaharsu wajen samar wa kansu abin da ya zama dole su tanada kamar sauran al’ummu na duniya. Babbar hanyar da aka bi wajen gudanar da wannan nazari ita ce hira da dattijan Maguzawa ta fuskar shekaru domin tsamo abin da za su iya tunawa kuma waɗanda al’adunsu suka tabbatar dangane da waɗannan ginshiƙai na rayuwa. Haka kuma an yi   nazarin littattafai da kundayen da aka rubuta musamman waɗanda suka shafi al’adun Maguzawa. Daga ƙarshe, nazarin ya gano cewa, Maguzawa sun yi amfani da abubuwan da suka samu a wuraren da suke zaune wajen shimfiɗa wa kansu al’adu cikin sauƙi da kuma samar wa kansu duk abin da suke bukata waɗanda suka zama dole rayuwa ta amfana da su. Wannan tanadi da suka yi, ya yi tasiri a rayuwarsu kuma ya taimaka musu wajen dogaro da kai.

Fitilun Kalmomi: Maguzawa, Rayuwa, Al’ada, Bukatun Rayuwa

1.0 Gabatarwa

Maguzawa mutane ne da a kullum ake tunanin sun bambanta da sauran jama’a. Wannan tunani yana tuzgowa ne saboda ba a ganin suna mu’amala kai tsaye da sauran mutane. Abu ne mai sauƙi Bahaushen wannan zamanin ya iya bayanin komai a kan irin kallon da yake yi wa Yarbawa ko Inyamurai ko Gwari da dai sauransu. Hakan na faruwa ne saboda irin shaƙuwa da aka yi da juna musamman wajen gudanar da rayuwar yau da kullum. Amma da zarar an meni sanin ko wane ne Bamaguje, ba abin da za a ji illa arnan Hausawa ne. In ko haka ne, akwai bukatar kusanta da waɗannan mutane don wayar wa jama’a da kai a kan rayuwarsu.

 

Maƙasudin wannan nazari shi ne ƙoƙarin fito da abubuwan da suke ginshiƙai a rayuwar Maguzawa. Wato nazari ne aka yi na al’amurran da suka shafi rayuwar Maguzawa waɗanda ake ganin kowace al’umma ta duniya tana tinƙaho da su domin rayuwa ta gudana cikin sauƙi. Yin haka shi zai ba mutane haske a kan al’umar da ake kira Maguzawa. Haka kuma shi zai ba da damar a iya kwatanta fasaharsu da tunaninsu da duk wata al’umma ta duniya. Ta wannan hanya ce za a fahimci yadda suke gudanar da wasu al’adu nasu waɗanda za a iya kwatantawa da kowace alumma ta duniya saboda ingacinsu a matsayin hanyar gudanar da rayuwa.

 

2.0 Maguzawa

Ƙoƙarin sanin ko waɗanne mutane ake kira Maguzawa ba baƙon abu ba ne idan aka yi la’akari da ayyukan masana tarihin ƙasar Hausa da malaman al’adar Hausawa. Kaɗan daga cikinsu akwai Krusius (1915), Greenberg (1946), Adamu (1980) Last (1980) Ibrahim (1982 da 1985) Akodu (2001) Magaji (2002) Abdullahi (2008) da dai sauransu da dama. Duk da yake nazarin da waɗannan malama suka yi a kan Maguzawa sun bambanta, amma ba su yi saɓani ba dangane da bayanan da ke ba da haske a kan mutanen da ake kira Maguzawa. Wato dai duk sun aminta da cewa, Maguzawa Hausawa ne waɗanda ba Musulmi ba, kuma addininsu da al’adunsu na gargajiya su suke yi musu jagoranci wajen gudanar da wasu harkoki na rayuwarsu.

 

Wannan suna da ake yi musu a ganin masanan, ya samo asali ne bayan da wasu daga cikin Hausawan suka karɓi addinin Musulunci a matsayin addininsu. Wannan ya sa suka yi ƙoƙarin bambanta kansu da waɗanda ba su karɓi addinin ba ta hanyar kiran su da suna Maguzawa. Su kuma (Hausawa Musulmi) suka riƙi kalmar Hausawa don bayyana kansu. A taƙaice Hausawa su ne Musulmin da Hausa ita ce harshensu. Su kuma Maguzawa su ne Hausawan da ba Musulmi ba kuma addininsu da al’adunsu na gargajiya waɗannda suka gada daga iyaye da kakanni suka yi tasiri a rayuwarsu. Ta la’akari da wannan bayanin, ana iya cewa, Maguzawa Hausawa ne domin ba su da wani harshe illa Hausa, kuma ƙasar Hausa ita ce ƙasarsu.

 

3.0  Ginshiƙan Bukatun Rayuwar Maguzawa

Maguzawa kamar kowace ƙabila ta duniya, suna da waɗansu muhimmam abubuwa da rayuwa take bukata. Waɗannan abubuwa duk ɗaya ne da na sauran ƙabilu, sai dai sun bambanta ta fuskar hanyoyin aiwatar da su a al’adance. A wannan fasalin za a nazarci bukatun rayuwar Maguzawa waɗanda suka haɗa da abincinsu da muhallinsu da suturarsu da hanyoyin tattalin arzikinsu da makamansu da kuma hanyoyin da suke samar wa kansu da magunguna.

           

3.1 Abincin Maguzawa

Maguzawa ba wasu mutane ne daban da Hausawa ba. Duk abin da Bahaushe Musulmi yake ci, Bamaguje ma yana ci. To sai dai kasancewarsu a cikin daji koyaushe ya sa ba su saba da cin ire-iren abincin ƙwalama da ‘yan’uwansu Hausawa (Musulmi) suke ci ba. Wannan kuma bai hana su cin abin da su suke ɗauka ƙwalama ba.

 

Muhimmin abincin da ya fi tasiri a wajen Maguzawa shi ne tuwon dawa. Maguzawa sun fi shuka dawa fiye da kowane irin hatsi. Galibi a gidan Bamaguje da dare, tuwon dawa ake yi da duk miyar da ta sauwaƙa kamar miyar kuka ko kuɓewa ko karkashi ko ayayo. Da safe ma da sauran tuwon da ya rage jiya ake karya kumallo (ɗumame). Wasu su haɗa da kunu ko koko. Da rana kuma ba kowane gida ake yin tuwo ba. Akasari sukan yi dambu ne ko kwaɗon tsaki. Haka ma sukan yi kwaɗon ganyayyaki kamar na zogale ko rama ko dinkin ko tafasa ko yaɗiya. Idan aka sami dankali ko rogo su ma akan dafa a matsayin abincin rana. A wasu lokuta na musamman, Bamaguje yakan ci shinkafa ko tuwon shinkafa.

 

Ta fuskar nama kuma, kusan a ce ba irin naman da Bamaguje ba ya ci. Wato ba shi da haram dangane da nama. Suna samun naman ne ta hanyar kiwon da suke yi na dabbobi da tsuntsaye. Haka kuma sukan sami nama ta hanyar farauta. Wasu Maguzawan har mushe sukan ci idan ya samu. Da yake sun fi mu’amala da jinsin awaki musamman wajen bukukuwa da tsafe-tsafensu, to za a ga naman awaki ya fi saukin samuwa a gare su (Abdulahi, 2008)

 

Ta ɓangaren abin sha kuma, baya ga kunu ko koko da aka ambaci suna yin kalaci da su da safe, can ba a rasa ba suna shan hura da rana. Shan hura ya yi tasiri ga wasu daga cikin Maguzawa da yake suna samun nonon ne ta kiwon shanu waɗanda sukan tanada don tsaron lalura. Haka kuma ga waɗanda suke maƙwabtaka da ruggar Fulani, samun nono yakan yi musu sauƙi.

 

 Babban abin shan Maguzawa da suke ba muhimmanci ita ce giyar dawa (Abdullahi 2021). Bamaguje yana sha’awar giya matuƙa. Ba babba ba yaro wurin shan giya. Muhimmancin giya a wurin Bamaguje ya sa dole ne a kawo ta a matsayin kayayyakin da al’ada ta tanada don ƙulla aure. Haka ma a wurin bukin mutuwa, dole ne sai an sha giya. A taƙaice, a sakamakon mu’amala da giya da Bamaguje ke yi, da zarar an yi girbin dawa, an ɗaura damma, dole a fitar wa Maigida na shan giya a ajiye ta daban. Idan har ba a yin giya a gidan Bamaguje, to dawar da aka ajiye masa a cikin rumbu, ita yake ɗiba ya sayar don ya sha giya.

 

3.2 Suturar Maguzawa

A al’adance, Bamaguje ba ya da wata sutarar kirki. Maguzawa ba su gaji wata sutura ta musamman ba. Manya maza walki/warki aka san su da shi. Shi suke ɗaurawa a gida, kuma shi suke amfani da shi a wurin aikin gona. Idan za a tafi unguwa ko wajen cin kasuwa ko wani buki, sai a yi lagen gwado. Saboda haka, duk magidancin Bamaguje yana da walki da gwado. Har ’yan shekarun baya, wasu Maguzawan in za su tafi cin kasuwa da lagen gwadonsu suke zuwa.

 

Su kuma mata ɗan zane kawai suke ɗaurawa a kwankwaso (ƙugu). Ga Bamagujiya/Bamaguza, ba abin kunya ne ta saki ƙirjinta a gaban kowa ba. Yara maza kuma bante ake yi musu bayan an yi musu kaciya. Kafin wannan lokacin, haka za a riƙa ganin su zindir musamman a lokacin bazara. Daga lokacin da yara maza suka fara balaga za su fara sa walki. Yara mata su ma wani abu suke ɗaurawa mai kamar bante da ake kira durwa. Su ma suna tare da wannan durwar a kowane lokaci har su kai munzalin aure. A lokacin da suke isa aure suke fara ɗaura zani. Wasu masanan na ganin cewa daga wannan kalmar ta durwa aka sami kalmar budurwa. Wato a lokacin da aka cire durwa an zama budurwa ke nan, sai batun aure. Wasu masanan kuma kamar Abraham (1962) suna ganin ana yi wa yarinya durwa ne saboda hana a yi mata fyaɗe.

 

Duk da yake a yanzu suturar Maguzawa tana sauyawa, wato suna sa tufafin da kowane Bahaushe yake iya sawa, ba wani ado na a-zo-a-gani suke yi ba. Tsofaffi daga cikinsu dai ba a raba su da tsumma a jiki, sai fa in za a yi wani buki ko za a shigo gari ake sa rigar kirki. Matan aure kuma ba kowa ke sa riga ba, sai dai su ɗaura zani a ƙirji. Su ma sukan sa riga da zani idan bukatar hakan ta taso kamar idan ana buki, ko in za a shiga kasuwa. Samari daga cikin ’ya’yan Maguzawa sukan sa ‘yan ƙananan riguna, galibi irin shat ko jamfa da wando. ’Yan mata kuma in sun sami riga su sa, su kuma ɗaura zani. In kuma ba bukatar rigar kamar a lokucin bazara, haka za a gan su da zani ɗaure a ƙirji. Idan a cikin gida ne ko a kewayen muhallin da suke, mata manya da ƙanana ƙirazansu a sake suke. Mace ba ta kunyar kowa ya ga ƙirjinta, ko da kuwa suruki ne.

 

3.3 Muhallin Maguzawa

Kasancewar Maguzawa mutanen da yawanci suke zaune a ƙauyuka, muhallinsu ba wani abu ne da ya bambanta da wanda aka sani a ƙauyukan Hausawa ba. Sukan yi gini na laka/ƙasa, a daɓe ciki da tsakuwa. Wasu kuma ginin kara suke yi a yaɓe da ƙasa. Rufin sama kuma da ciyawa ake yi (jinka). Kowace matar aure a cikin gida akan ba ta ɗaki na musamman ita kaɗai sai ’ya’yanta ƙanana. Wasu masu gidajen sukan tanadi ɗakinsu na daban a cikin gida in da hali. Wasu kuma sukan riƙa bin ɗakunan matansu ne suna kwana daga lokaci zuwa lokaci.

 

Bamaguje a da, bai damu da killace gidansa ba. Duk da haka, akan sami fuskar gida. A nan ne ake gudanar da wasu tarurruka na gidansa. A yanzu za a ga yawancin gidajen Maguzawa an yi musu danni na kara ko a killace gidan da zana. Daga waje kuma a yi zaure. Masu hali daga cikin Maguzawa sukan yi katanga, amma ba mai tsayi sosai ba.

 

Yara maza da mata ƙanana sukan kwana ne a ɗakunan iyayensu. Idan kuma akwai tsohuwa a gida, to a ɗakinta sukan kwana. Wasu ma gidan maƙwabta suke kwana muddin dai akwai tsohuwa a gidan. Idan yara maza suka zama samari, akan tanadar musu ɗaki a wajen gidan. Idan kuma za su yi aure, sai a gina musu ɗaki na musamman a wani sashe na gidan.

 

Gidajen Maguzawa gidaje ne masu ɗauke da shiyoyi ko sassa da yawa. Magidanta uku ko fiye suna iya zama a gida ɗaya, kowa da iyalinsa komai yawansu. A ƙauyukan Maguzawa, babu wani abin nuna bambanci ko arziki dangane da tsari ko kyan gida, domin duk tsari ɗaya suke yi. Sai dai yawan jama’a ya bambanta girman gidajen.

 

3.4 Tattalin Arzikin Maguzawa

Tattalin arzikin Maguzawa ya dogara ne ga sana’i’o’in da suke gudanarwa a muhallin da suke zaune. A wannan fasalin, za a tsakuro ire-iren waɗannan sana’o’in da fayyace irin tasirin da suke da shi a rayuwar Maguzawa.

 

3.4.1 Noma

Maguzawa ba su da wata sana’a da ta wuce noma. Ita suka gada kaka da kakanni. Da ita suke alfahari fiye da komai a duniya. A ɗaukakar duniya, ba abin da Bamaguje ke sha’awa kamar a kira shi Sarkin Noma. Ta fuskar tsafe-tsafe, a dalilin noma ne sukan yi fice wajen sihirce-sihirce don hana satar amfanin gona, ko don yin maganin fari, ko maganin cika baki ko dabarun tara amfanin gona da yawa.

 

Baya ga abin da Bamaguje ya cire na cin abinci daga amfanin gonarsa, akan sami waɗanda sukan sayar don biyan wasu bukatu na rayuwa. Bamaguje yakan sayar da amfanin gonarsa ba don sha’awar kasuwanci ba, sai don musanyawa da wasu abubuwan more rayuwa da yake bukata ko samar wa kansa wasu kayayyakin noman.

 

Akwai dalilai da yawa da suka sa Maguzawa suka riƙe noma a matsayin mafi ingancin sana’a a rayuwa. Suna da tunanin cewa, babu sana’ar duniyar nan da ta fi noma albarka. Mutum ya shuka ƙwaya ɗaya ya girbi ɗari ba tare da ya roƙi kowa ba. Mutum ya wadata da abin da ya samu ta fuskar abinci da biyan bukatun rayuwa.

 

Yanayin ƙasar Maguzawa ita ta ba su damar riƙe noma a matsayin sana’a. Yankin da suke (ƙasar Hausa) yanki ne da yake da ƙasa mai kyau da yanayi mai armashi wanda ya dace da irin abincin da ɗaukwacin jama’ar wannan wuri suke ci.

 

Dabarar noman gandu da al’adar Maguzawa ta tanada, ta taimaka musu wajen riƙe sana’ar da samun yalwar abinci. Noman gandu noma ne da duk ilahirin mutanen gida (’ya’ya, mata, matan ’ya’ya, jikoki) za su taru a gonar maigida a noma ta gaba ɗaya. Irin wannan taron-dangi da ake yi wa gona ba tare da ƙyashi ko kasala ba, dole ya haifar da sakamako mai kyau, musamman da yake ana yin noman ne ta hanyar sha’awa da jin daɗi da alfahari.

 

A al’adar noman Maguzawa, ba bambanci tsakanin mace da namiji. (mai aure da mara aure). Dukkansu aiki suke yi a gona ba ji, ba gani. Abu ne mawuyaci a iya bambanta noman namiji da mace ta fuskar inganci a al’ummar Maguzawa. Rungumar da kowane jinsi ya yi wa noma, da himmar da ake bayarwa da ɗaukar sa abin kunya ga mace ko namijin da suka kasa, sun taimaka wajen dauwamar noma a matsayin sana’a ga Bamaguje.

 

Maguzawa suna da hikimar yin auren mata da yawa. Wannan hikima ba ta rasa nasaba da yin ficen a sana’ar noma. A nasu tunanin, mace ba a cikin gida kawai take da amfani ba. Haka kuma, babu wata hanya da za a more wa dukiyar auren da aka bayar in ba ta hanyar noman da za ta yi a gidan miji ba. Don haka, bunƙasar noman namiji, da samun wadatarsa ta fuskar noma, sun dogara da yawan mutanen da suke noma gonarsa. Wannan dalili ya tilasta wa Bamaguje auren mata da yawa domin gonarsa ta rayu har abada. Sakamakon da Maguzawa ke samu da irin alfanun da suke gani ta fuskar noma a dalilin auren mata da yawa, shi yake yi musu takunkumin karɓar wani addini kamar Musulunci ko Kiristanci inda ake ƙayyade yawan matan da namiji zai aura.

 

Daga cikin amfanin gona da Maguzawa suke nomawa akwai dawa, da gero da masara, da shinkafa, da gyaɗa, da auduga, da rake, da barkono da dai sauransu. Haka kuma wasu daga cikinsu musamman waɗanda suke zaune kusa da fadama, suna haɗawa da noman rani.

 

Duk da irin bunƙasar aikin gona da ake samu a duniya a yau, Bamaguje ya fi sha’awar amfani da kayan nomansa wurin yin aiki a gona, sai kuwa ɗan abin da ba a rasa ba kamar amfani da shanu wajen huɗa da sauransu.

 

 

3.4.2 Ƙira

Baya ga noma, ƙira ita ce sana’a mafi muhimmanci ga Maguzawa. Wannan ba ya rasa nasaba da alaƙar da take tsakanin sana’o’in guda biyu. Wato duk tinƙahon da Bamaguje yake yi da noma, ya dogara ne ga kayayyakin da maƙera suke ƙerawa. Wannan muhimmuncin na sana’ar ƙira shi ya tilasta wasu daga cikin Maguzawa suka ɗauki ƙira a matsayin sana’a. Duk da haka abu ne mawuyaci a sami maƙerin Bamagujen da ba ya noma. Wato dai ƙirar ana yin ta ne saboda biyan buƙatar noma ta samar da kayan aiki da gyara su, amma ba don a dogara gare ta a matsayin hanyar ɗaukar ɗawainiyar rayuwa ba.

 

Daga cikin kayayyakin noman da máƙèrán Maguzawa suke ƙerawa akwai fartanya, da galma/garma da kwasa da wuƙa da gatari da lauje da magirbi dai sauransu. Baya ga ƙera kayan aikin noma, maƙeran Maguzawa sukan ƙera da gyara ko wasa makaman da suke amfani da su wajen faraunta da tsaro. Irin waɗannan makamai sun haɗa da takobi, da mashi, da kwari da baka, da ma bindigar toka. Haka kuma sukan ƙera kayayyakin amfani a gida kamar wuƙa da masulla da kuma wasu kayayyakin gudanar da wasu sana’o’in.

 

Wani abin ban sha’awa da wannan sana’a a tsakanin Maguzawa shi ne ba lallai ne sai Bamaguje yana da kuɗi ƙasa kafin ya mallaki wani kayan aikin noma da maƙeri ya ƙera ba. Haka ma babu bukatar dole sai an biya kuɗin gyaran kayan noman. Idan babu halin biya kai tsaye, akan biya da amfanin gona a duk lokacin da aka sami hali.

 

Galibin maƙeran Maguzawa gado suke yi daga kaka da kakanni. Amma duk da haka ana samun waɗanda suke yi wa sana’ar haye don biya wa al’umma bukatar samar da kayan aikin gona da gyara su.

 

3.4.3 Farauta

Farauta ita ya kamata a fara ambata da farko a matsayin sana’ar Maguzawa, amma ganin yadda noma da ƙira suka yi mata fintinkau, shi ya sa aka jinkirta kawo ta. Farauta dai tana nufin shiga daji a kaso namun daji don ƙarin abinci. Masana irin su Alhassan da Sauran (1982) sun nuna cewa, wannan ita ce hanyar farko da ɗan Adam ya dogara da ita don neman abin da ya ci. Farauta ita ce sana’ar da ake hasashen ta kafa garuruwa da yawa na Hausawa.

 

A sakamakon samun sana’ar noma da ba ta muhimmanci da Maguzawa suke yi, wannan bai sa sun yi watsi da farauta ba, duk da yake hanyar abincinsu ba ta dogara kacokan a kan farautar ba. Kasancewar muhallin Maguzawa a cikin daji yake kusa da gonakinsu, shi ya ba su dama da ƙwarin guiwar yin farauta. Wasu daga cikinsu sun nuna suna farauta ne don tanadar dabarun kare jama’arsu daga barazanar namun daji, da inganta miya da kuma samun ƙwarewa don yaƙar abokan gaba.

 

Farautar da Maguzawa suke yi tana iya kasuwa zuwa gida biyu. Ana iya samun mafarauci shi kaɗai, ya ɗauki makamansa da karnukansa su shiga daji neman namun daji. Haka kuma ana samun jama’a da yawa su yi gangami, a hura ƙaho a ce a haɗu daji kaza, rana kaza, lokaci kaza, don a yi farauta. A irin wannan, akan kamo namun daji kamar zomo, da barewa, da gada, da tsuntsaye iri-iri.

 

Maguzawa ba su cika zuwa yawon farauta ba sai a lokacin rani, bayan an cire amfanin gona, maganin zaman banza. Baya ga cin namun dajin da ake farautowa, wasu sukan sayar domin biyan bukatunsu na rayuwa.

 

3.4.4 Kiwo

Kiwo sana’a ce ta ajiye dabbobi da kula da su don a amfana ta hanyoyi daban-dabam. Duk da yake Maguzawa ba su tara dabbobi da yawa kamar Fulani, ana iya cewa, kusan babu gidan da ba a ajiye wata dabba ko tsuntsu ana kiwo don biyan bukatar tsafi ko noma ko tsaro ko abinci ko kuma sha’awa ko don a saye a sayar a ci riba da dai sauransu. Daga cikin dabbobin da Maguzawa suka fi kiwatawa akwai shanu waɗanda suke amfani da su wurin noma da samar da taki. Sukan yi kiwon dabbobi dangin awaki don yankawa a lokacin tsafe-tsafe da bukukuwa. Karnuka kuma don tsaro da farauta. Baya ga waɗannan kuma, ba a raba gidajen Maguzawa da tsuntsaye kamar kaji da agwagi da dai sauransu. To sai dai Maguzawa ba su taɓa ɗaukar kiwo a matsayin sana’ar da rayuwa kan dogara a kanta ba. Sukan yi kiwo ne don taimaka wa rayuwar ko biyan bukata ta musamman. Duk da haka ana samun Maguzawan da suke turke dabbobi kamar shanu don su yi huɗa da su, su tara musu taki, sannan su sayar don su ci riba. Sukan biya bukatun rayuwa da wannan ribar da suka ci, daga baya su ƙara sawo wasu shanun don noman baɗi (Nuhu 2020)

 

3.4.5 Sauran Sana’o’in Maguzawa

Baya ga waɗannan sana’o’i huɗu da aka ambata, akan sami ‘yan ƙananan sana’o’in da Maguzawa ke yi lokaci-lokaci. Wasu ana yin su koyaushe, sai dai ba su da wani tasiri a tattalin arzikinsu. Irin waɗannan sana’o’i sun haɗa da wanzanci, gini, jima rini da sauransu. Akan sami mutanen da suke gudanar da su a tsakanin Maguzawa saboda bukatarsu. Amma ba lallai ne a sami mai gudanar da su a kowace al’umma ko ƙauye ko unguwa ba. Sana’ar da aka fi ba muhimmanci daga cikin irin waɗannan sana’o’i ita ce wanzanci. Maguzawa sukan bukaci wanzami wurin yin aski da gyaran fuska da yin tsagar gado da cire hakin wuya, da kaciya, da yin ƙaho da kuma adon da akan yi wa jikin ‘yan mata (Jarfa). Kamar maƙera, su ma wanzamai a wasu gidajen ba a biyan aikin da suka yi sai an girbe amfanin gona a cire musu nasu.

 

4.0 Kayan Faɗan Maguzawa

Kowace al’umma ta duniya takan yi tanadi na musamman don kare kanta daga abokan gaba. Irin wannan tanadi yakan shafi kayan faɗa waɗanda akan ajiye a gidaje ko a wani wuri na musamman don kau da ɓacin rana. Irin waɗannan kayan faɗa sukan kasance waɗanda suka yi tasiri a wannan muhallin ta fuskar sabo da sauƙin sarrafawa.

 

Ire-iren makaman Maguzawa sun haɗa da mashi da takobi da kwari da baka, da wuƙa da dai sauransu. Baya ga tanadin waɗannan makamai, sukan yi wata dabara ta sa musu dafi don su yi illa ko ɓarna kai tsaye ga wanda ko abin da aka taɓa da su. Akwai hanyoyi da yawa da Maguzawa ke bi wurin sa dafi ga makami. Wanda ya fi fice shi ne wanda ake dangantawa da tsafi da kuma sihirce-sihircen da suka gada.

 

 5.0 Hanyoyin Samar da Magungunan Maguzawa

 Tanadin magani abu ne da ya zama tilas a kowace al’umma ta duniya. Ko ba komai, makami ne na yaƙar babban maƙiyi, wato ciwo. Al’umma takan yi amfani da basirar da Allah ya huwace mata ne don samun magani. Su ma Maguzawa wannan basirar ba ta ɓace musu ba domin sun yi wa lamarin magani kyakkyawar tanadi. Hanyoyin samun magani a al’umar Maguzawa sun kasu kashi uku:

 

5.1 Itatuwa da Tsirrai

Maguzawa suna amfani da itatuwa da ganyayyakin da suke samu a gonakinsu da dazuzzukan da ke kewaye da su don maganin ciwo. Sukan yi amfani da hanyoyi da yawa wajen sarrafa waɗanan tsirrai don yin magani gwargwadon nau’in cutar ko dabarar sarrafa magani. Misali, wasu magungunan ganye ne ake dafawa a sha, wasu dafawa ake yi a yi wanka da ruwan. Wasu shanya ganye suke yi, ya bushe, a daka ya koma gari, a sha cikin kunu ko hura ko nono da dai sauransu. Wasu kuma sassaƙe ko ɓawon itace ake sarrafawa ta hanyoyi daban-dabam a sha, ko a shafa, ko a shaƙa, ko a turara da garwashi, da dai sauransu. A taƙaice dai amfani ake yi da tsirrai a sarrafa su ta yadda aka fahimci za su biya buƙatar magani.

 

5.2 Dabbobi

Maguzawa suna amfani da sassan dabbobin da suke tare da su ko ake samu a kewayen da suke wajen samar wa kansu magani. Wasu ciwarwartan akan danganta maganinsu ne da wata dabba ta hanyar amfani da namanta ko fatarta ko kashinta ko wasu sassa na kayan cikinta. Hanyoyin sarrafa maganin sun danganta da laƙani da kuma irin ciwo ko cutar da ake son warkarwa.

 

5.3 Tsafi

Rukuni na uku na magungunan Maguzawa shi ne wanda ya shafi sihiri ta hanyar tsafe-tsafen da suke yi. Bukatar magani wani ginshiƙi ne babba ga Bamaguje da ke samar da dangantaka tsakaninsa da abin da yake bauta wa. Maguzawa dai iskoki (aljannu) suke bauta wa. Su waɗannan iskoki ake neman biyan bukatarsu na magani ta hanyar shugaban tsafin. Galibi akan yi ‘yan yanke-yanke a zubar wa tsafin da jini don samun yardarsa ya biya buƙata na magani. A al’adar Maguzawa, sun fi alfahari da tsafi wurin biyan wannan buƙata. Haka kuma wasu sun danganta sauran nau’o’i ko hanyoyin samun magani na Maguzawa (da aka ambata a baya) ta tsafin da suke bauta wa. Wato tsafin ke ba da umurnin a yi amfani da wani tsiro ko wata dabba don samun waraka ko biyan buƙata.

 

6.0 Kammalawa

A wannan nazari, za a fahimci cewa, rayuwar mutanen da ake kira Maguzawa rayuwa ce da aka shimfiɗa cikin sauƙi kuma ta amfani da abin da suka waye da shi a muhallin nasu. Nazarin ya yi waiwaye ne a kan abubuwan da suke ɗauke da rayuwar Maguzawa. Waɗannan kuwa su ne abinci da sutura da muhalli da hanyoyin tattalin arziki da kayan faɗansu da kuma hanyoyin samar da magani. Daga abin da binciken ya gano, Bamaguje ba ya rena abin da ya mallaka. Haka kuma ba ya ɗaukar kayan aro ya zama nasa. Duk da kasancewar zamani riga ne, Maguzawa suna taka-tsantsan da faɗawa cikin haɗarin zamani. Wannan ne wataƙila ya sa ake yi musu wani kallo na daban wanda ya sa akasarin mutane suka kasa kusantar su ballantana a iya yin sharhin rayuwarsu kamar yadda ake yin na wasu ƙabilu. Haƙiƙa wannan nazari ya samar da wata makama ga masu sha’awar sanin yadda rayuwar Maguzawa take gudana.

 

7.0 Manazarta

 

Abdullahi, I. S. S. (2008). ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Abdullahi, I. S. S. (2008). “Bamaguje da Ɗan Akuya: Ƙauna ko Ƙiyayya?” Department of Nigerian Languages Seminar series, Sokoto: Usmanu Dafodiyo University 28th August.

 

Abdullahi, I. S. S. (2021). “Giya Madarar Arna: Nazarin Tu’ammalin Bamaguje da Giya” East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature Vol.4 Issue 4 ISSN- 2617-7250 (Online) ISSN 2617-443X (Print). Kenya: East African Scholars Publishers.

 

Abraham, R. C. (1962). Dictionary of Hausa Language. London: Hodder and Stoughton.

 

Adamu, M. T. (1997). Asalin Hausawa da Harshensu. Kano: Ɗan Sarkin Kura Publishers.

 

Akodu, A. (2001). Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Zaria: Gaskiya Corporation Limited.

 

Alhassan, H. da Sauransu (1982). Zaman Hausawa

 

Aliyu, A. Y. (1973). “Asalin Hausawa” a cikin littafin Bukin Makon Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

 

 Fletcher, D. C. (1929). “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment Report on ’Yanɗaka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833. Kaduna: National Archives and Monuments.

 

Greenberg, J. (1946). The Influence of Islam on a Sudanese Religion: Monographs of the American Ethnological Society. New York: J. J. Augustin Publisher.

 

Ibrahim, M. S. (1982). “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa). Kano: Jami’ar Bayero.

 

Kado, A. A. (1987). “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa) Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

 

Krusius, P. (1915). “Maguzawa” Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

 

Madauci I. da wasu (1968). Hausa Customs. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

 

Magaji, A. (2002). “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye- yanayensu a Ƙasar Katsina.” Kundin digiri na uku. Kano: Ja’mi’ar Bayero.

 

Malumfashi, A. A. (1987). “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study of Maguzawa Society in Malumfashi Area” Kano: Bayero University.

 

Nuhu, A. (2000). “Zamani Abokin Tafiya: Wasu Al’adun Maguzawan Ƙasar

Katsina a Ƙarni na 21” Kundin Digiri na Uku, Sakkwato: Jami’ar

Usmanu Danfodiyo.

 

 

 

Post a Comment

0 Comments