Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.
Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (3)
NA
SHEHU HIRABRI
08143533314
BABI NA UKU
ZAMBO A CIKIN WASU WAƘOƘIN
ALHAJI MUSA ƊANBA’U GIDAN BUWAI
3.0 Shimfiɗa
Wannan babi zai yi bayani tare da kawo
misalai a kan asalin kalmar zambo da ma’anrta da ire-irenta da dalilin da ya sa
ake yin zambo da amfanin sa ga al’umma tare da yin sharhinsa a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.
3.1 Asalin Kalmar Zambo
An samu bambancin ra’ayi dangane da
asalin kalmar zambo. Masana da manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu
dangane da asalin kalmar. Abdullahi, (1995: 21) cewa ya yi: “Asalin zambo abu
ne mai wuya a ce ga lokacin da aka fara samun sa a cikin waƙa
kamar yadda ba a iya cewa ga rana ko lokacin da aka fara waƙa
gaba ɗayanta.
A nan ina ganin tun lokacin da ɗan Adam ya fara buɗe baki
da sunan yin waƙa ya ƙirƙira
dabarar yin zambo don yi da wani ko musguna masa a kaikaice. Da haka dai zambo
ya ci gaba da yawaita a cikin waƙar baka
ta Hasua har kawowa wannan lokaci da ya zama ruwan dare a cikin waƙoƙi.”
Yahaya da wasu (2006: 40) cewa suka
yi: “Asalin kalmar zambo, Bahaushiyar kalma ce, ba aro ta an ka yi ba.” Dalilin
da suka kafa shi ne, zambo daɗaɗɗen abu
ne a cikin tarihin adabin Bahaushe na gargajiya.
Wasu na ganin asalin kalmar zambo daga
harshen Larabci aka samo ta, wato “alzammu” mai ma’ana da Larabci zargi. Sannu
a hankali kalmar ta tashi daga zammu ta koma zambo (Yahaya da wasu, 2006: 40).
Bunza, (2009: 132) cewa ya yi: “kalmar
zambo ta fuskar furuci da rubutunsu da ma’anarsu ta fi kusa da kalmar zamba.”
3.2 Ma’anar Zambo
Masana malamai da manazarta da dama
sun bayyana ra’ayi dangane da ma’anar zambo kamar haka:
Gusau, (1979: 39) cewa ya yi: “Zambo kalma
ce wadda ake amfani da ita a matsayin kishiyar yabo, wato a siffanta wani mutum
da wasu siffofi munana waɗanda za su walaƙanta
shi da jawo masa rashin martaba a idon ‘yan Adam tare da kau da kai cewa wannan
mutum yana da waɗannan siffofi ko ba shi da su.”
Dangambo, (1984: 32) cewa ya yi:
“Zambo zagi ne na kai tsaye, cikin zambo ana siffanta mutum da halayensa da ɗabi’unsa
da danginsa da iyayensa da dai duk wani abu da ya shafe shi wanda zai taimaka a
gane da shi ake.”
Gusau, (1988:315) cewa ya yi: “Zambo
wasu kalmomi ne na muni da ci wa mutum mutunci da ake amfani da su kai tsaye ga
wanda ake buƙata. A wajen zambo ana iya fitowa fili a
faɗi wata
fitacciyar siffa ta mutum wanda nan take ake saurin gane wanda ake nufi.”
Modibbo, (1989: 32) cewa ya yi: “Zambo
dai shi ne faɗin
mugun abu ga mutum, kuma zambo kishiyar yabo ne. akan ɓaci
mutum da abin da yake na gaskiya, amma maras kyau ko kuma ƙage.”
Abdullahi, (1995: 21) cewa ya yi:
“Zambo magana ce da akan shirya a cikin waƙa domin
muzanta mutum. Mawaƙan Hausa na baka
da marubuta suna amfani da zambo a cikin waƙoƙinsu
don musgunawa abokan hamayyarsu ko abokan hamayyar waɗanda
suke yi wa waƙa, ta fitowa ƙuru-ƙuru
su muzanta su ta siffanta su da wasu abubuwan munana marasa kyau kamar rowa
rashin fara’a da dai sauransu.”
Shinkafi, (1998: 20) cewa ya yi:
“Zambo siffanta mutum da wasu siffofi munana domin a muzanta shi ga idon mutane
ko da ba ya da su. Zambo kishiyar yabo ne.”
Dumfawa, (2005:19) cewa ya yi: “Kalmar
zambo tana nufin aibanta wani mutum ko wani abu dangane da sifarsa ko aƙidarsa
ta yin amfani da wasu lafuzza na aibantawa ko muzantawa ko munanawa.”
Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero (2006:489) an bayyana cewa: “Zambo na nufin ƙaga
wa mutum magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata
masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. Maroƙa sun
fi yin haka a cikin waƙa.”
Bunza, (2009: 132) cewa ya yi: “Kalmar
zambo ta fuskar makusanciyar ma’ana tana da alaƙa da
habaici, ta fuskar furucinsu da rubutunsu da ma’anarsu tafi kusa da kalmar
“zamba”. Zambo ya fi habaici zafi domin ƙaga shi
ake yi a liƙa wa wanda ake yi wa. Daga cikin kayan
cikin zambo akwai:
i.
Wulaƙanta
wanda ake yi wa da wani abu na ƙasƙanci
ga irin matsayinsa.
ii.
Ƙara
gishiri ga halinsa, ko wani aibi da aka san shi da shi.
iii.
Ƙago
abin da bai ji ba bai gani ba, a ce ya yi, ko ya ce ko nasa ne.
iv.
Yi masa muguwar fata.”
Zaruk da wasu (2011) cewa suka yi: “Zambo ɗan uwan
habaici ne. sai dai shi zambo ya fi habaici tsanani. Galibi idan an yi wa mutum
zambo domin a tozarta shi a idanun jama’a idan za a yi wa mutum zambo akan ɗauki
wani hali nasa ko sifa a yi masa zambo da shi.”
Ɗanhausa,
(2012) cewa ya yi: “Zambo ana yin sa ne musamman dan faɗakar da
mutum ta hanyar ɓata shi, wato fallasa shi domin a nuna ana
sane da ire-iren miyagun ɗabi’u da ke tare da shi haɗe da ba
shi shawara amma ba kai tsaye ba, ta cikin hikima wato rara-gefe idan an
misalta shi da zambo.”
Yahya da wasu (2015: 17) cewa suka yi:
“An bayyana zambo a matsayin kalma wadda ake amfani da ita a matsayin kishiyar
yabo wato a siffanta wani mutum da wasu siffofi munana waɗanda za
su wulaƙanta shi da jawo masa rashin martaba a
idon ‘yan Adam tare da kau da kai cewa wannan mutum yana da waɗannan
siffofi ko ba shi da su.”
Yakasai (2012: 171) cewa ya yi: “Zambo
salo ne da ‘yan siyasa musamman mawaƙa suke
amfani da shi domin su muzanta wani ko wasu ƙungiyoyin
siyasa ta fuskar ambata tare da ƙirƙiro
wasu miyagun ɗabi’u
ko asali su danganta su ga wanda suke son su naƙƙasa
domin mutane su kauce wa jefa masa ƙuri’a
lokacin zaɓe.”
Idan aka yi la’akari da waɗanna
ma’anonin da suka gabata, a tawa fahimta ana iya cewa: Zambo suka ce da ake yi
kai tsaye ta hanyar kawo hoton mutum, ko wani abu cikin surarsa ko halayensa ko
kuma duk wani bayani wanda zai taimaka a fahimce da wanda ake kai tsaye domin a
ɓata
masa rai tare da walaƙanta
shi da kuma kadar masa da ƙima da
mutunci a idon jama’a.
3.3 Ire-Iren Zambo
An samu
bambancin ra’ayi dangane da ire-iren zambo. Barmo (2014: 15) da Modibbo
(1989:32) sun bayyana ire-iren zambo kamar haka:
1.
Zambon halitta
2.
Zambon asali
3.
Zambon sarauta
4.
Zambon hali
Shi
kuwa Tuluwa (2012: 75) ya kawo ire-iren zambo kamar haka:
1.
Zambon kama ko halitta
2.
Zambon asali
3.
Zambon matsayi
4.
Zambon hali
A nan
an samu bambanci tsakanin zambo sarauta da zambon matsayi.
1.3.1
Zambon kama ko Halitta: Zambo ne da mawaƙa
ke yi ta hanyar bayyana wata halitta da Allah ya yi wa mutum ko kuma su kalli
wani abu da ya yi kama da halittar ya kira mutum da sunan wannan abin ko ya
kwatanta su. Misali, a waƙar
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai inda yake cewa:
Jagora: Ga wani ɗan
takara da doro,
Abu dai zuƙui-zuƙui,
Ke kuma bushiya ki ɓoye doronki,
Ba ki bakin komai.
Yara: Wurin hwarauta banza ce.
Gindi: ‘Ya’yan Nijeriya,
Siyasa ta tashi,
Ku dawo mu yi ƙoƙari,
Mu koma PDP
1.3.2
Zambon Asali: Zambo ne da mawaƙa
ke yi wa mutum ta hanyar bayyana wani abu da ya shafi tushen asalin mutum ta
fuskar tozartawa ko muzantawa. Misali kamar zambon da Audu Stim ya yi wa wani
sharifi inda yake cewa:
Wane ba mu zagin
babanai,
Don darajar
kakansa,
Wurin uwa tai muka
komawa
Mu yi mai gora,
Mun san asalin
wance
Tasha tat tashi.
Gindi: Bafarawa
Gwamnan Sakkwato,
Mai adalci mu muna tare da kai,
Gwamna muna bayanka.
Wani
misali a cikin waƙar Ɗanba’u
inda yake cewa:
Jagora: Kowat taso
tare da manya,
Ka san yana da tarihi,
Don haka manya sunka gaya mini,
Yara: Danginsu Maguzawa ne.
Gindi: Ɗantakarar
zama gwamna,
Magatakarda wamakko,
Aliyu kar ka ɗau reni,
Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.
1.3.3
Zambon Matsayi: Zambo ne da ke da fuska
biyu. A fuska ta farko mawaƙa kan
yi amfani da matsayin da mutum ya samu musamman lokacin da aka yi jayayyar
sarauta ko mulki ko wani abu makamancinsu, sai su yi amfani da wannan matsayi
su wa abokan hamayya zambo. Misali a waƙar Ɗanba’u
ta ciyaman ɗin Gada
Tanimun Ɗangaladima inda yake cewa:
Jagora: Ƙara hanƙuri
kar ka ji komai,
Hanƙurinka shi na kai ka haka,
Hak ka yi ciyaman ƙasar
Gada
Ka kada biri sarkin ƙwalama,
Ci ƙungurguma a ci buzuzu,
Yara: Na ce biri a yi a hankali
Wata ran cikinka ya ɓaci.
A fuska ta biyu mawaƙan
sukan yi zambo domin ƙoƙarin
ɓata
wani matsayi da wani mutum yake da shi a idon jama’a domin muzanta shi ko a ɓata
masa rai. Misali a waƙar Ɗanba’u
ta Aliyu Magatakarda Wamakko inda yake cewa:
Jagora:
Aliyu kai ka gadi sarauta,
Ka yi naɗi daidai da sarauta,
Wanda duk bai gadi sarauta ba,
Yara ko ga naɗi sai mun gani.
Yara: Wane naɗi nai
ya cika girma,
Wanga uban huni sai ‘yan dako.
Gindi: Ƙi sake
bajini gwarzon maza,
Ali sarkin Yamman Sakkwato.
1.3.4
Zambon Hali: Zambo ne da mawaƙa
kan yi ta hanyar amfani da mugun halin mutum sai a yi masa zambo a kai nai.
Wani lokaci kuma sukan kwatanta halin mutun da na wata dabba mai irin halinsa
sai su yi zambo su ɗora a kansa. Misali, ana iya wa mutum
zambo ta hanyar rowa da sata da zina da kushili da ƙarya da
munafunci da zalunci da makamantansu. Haka kuma ana wa mutum zambo da halin
dabba kamar biri da jaki da kusu (ɓera) da muzuru da
bunsuru da kare da makamantansu. misali a waƙar Ɗanba’u
ta Matawallen Sakkwato Aminu Waziri yake wa abokin hamayya zambo da halin rowa
inda yake cewa:
Jagora: Ga wani na
neman Matawalle,
Kai ƙwanƙiro wa
za ya naɗa ka,
Kowa ya san bai alheri,
Yara: Bai iya kyauta ba a yaba mai,
Gindi: Ɗan
waziri ka ƙara shirawa
Aminu yau kai am matawalle.
Wani misali a cikin waƙar
Narambaɗa ta
mazan gabas tsayaye yana yi wa wani ɗan sarki zambo da
halin ƙarya da rowa, inda yake cewa:
Jagora: Ka ga ɗan
sarki da kurruwa da hwaɗi
Ga ya da ƙarya ga ya da
rowa,
Yara: Ko ka girmama shi ba ya sarki.
Gindi: Masu gari mazan gabas tsayayye
3.4 Dalilin Yin Zambo
Dalilai da dama ke sa a yi zambo, daga
cikinsu akwai:
i.
Duk lokaci da aka yi jayayya ta siyasa ko
sarauta ko neman aure ko nema wani muƙami ko
wani matsayi da makamantansu. Mawaƙa da waɗanda ba
mawaƙa ba kan yi zambo ga abokan hamayya.
ii.
Ana yin zambo domin a muzanta mutum ko
wulaƙanta shi ko cin zarafinsa.
iii.
Ana yin zambo domin a bayyana wani mugun
hali ko ɗabi’a
da mutum ke da.
iv.
Ana yin zambo domin a huce haushi musamman
in akwai wata adawa ko husuma a tsaknin wasu.
v.
Ana yin zambo domin tsoratarwa a kan wani
abu da wani ke son ya yi ga wani mutum ko wani al’amari kamar sarauta ko siyasa
ko wani abin da ya shafi zamantakewar al’ummar Hausawa.
vi.
Ana yin zambo don samar da nishaɗi da
raha a cikin zukatan al’umma.
vii.
Ana yin zambo don a ɓata wa
mutum rai.
3.5 Amfanin Zambo
Duk da yake zambo suka ce da ake yi
kai tsaye ta fuskar ɓatanci, amma kuma yana da amfani matuƙa.
Daga cikin amfanin zambo akwai:
1.
Zambo yana hana yin shishigi watau mutum
ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.
2.
Zambo wani ado ne da ke ƙawata
waƙa tare da ƙara
mata armashi, ba waƙa kawai ba har
sauran zantukan yau da kullum.
3.
Zambo na sa mutum ya san miyagun ɗabi’unsa
ko ƙazafi ko wani abin da jama’a ke zarginsa
da shi.
4.
Zambo na sa mutum ya daina wasu miyagun
halaye ko ɗabi’u
5.
Zambo na bayyana miyagun ɗabi’un
jama’a cikin hikima domin a ƙaurace
musu.
6.
Zambo kan taimaka wajen ƙara
soke abokan hamayya.
7.
Ƙwarewa
wajen gina zambo a cikin waƙoƙi
musamman na siyasa ko sarauta na ƙara wa
mawaƙi ɗaukaka
da farin jini ga jama’a.
8.
Ƙwarewa
wajen gina zambo a cikin waƙoƙi,
na sa mawaƙi ko maroƙi ya
samu alheri.
9.
Zambo wata taska ce ta adana adabin
al’ummar Hausawa.
10. Zambo
na samar da nishaɗi cikin raha da wartsakewar rayuwa.
3.6 Zambo A Cikin Wasu Waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai
A sama an kawo ma’anar zambo da
ire-irensa da dalilan da ke sa a yi shi tare da bayyana amfaninsa. A nan kuwa
za a kawo zambo a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u tare da yin sharhinsa a bisa
mizanin nazari.
Kamar yadda Yahya( 1997) ya bayyana
cewa: “Zambo wasu zantuka ne ake yi ta hanyar zaɓen wasu
kalmomi da za su ɓata ko musguna wa wanda ake wa. Akan
kwatanta kama ko ɗabi’a ko hali na mutum da wasu siffofi don
a wulaƙanta shi. Kenan zambo yakan bayyana wanda
ake wa shi a fili ba tare da wata wahala ba.
Za a ga irin waɗannan
bayanan da Yahya, (1997) ya bayyana a kan zambo a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u. Haka kuma Ɗanba’u
na amfani da hanyoyi biyu wajen gina zambo a cikin waƙoƙinsa.
Hanya ta farko Ɗanba’u
kan dubi abin da ke faruwa tsakanin wanda yake wa waƙa da
abokin hamayyarsa sai ya gina zambo. Hanya ta biyu Ɗanba’u
kan gina zambo ta hanyar bayyana wani abu da ke faruwa tsakaninsa (shi mai kiɗi) da
wani mutum sai ya gina zambo a cikin waƙa.
A waƙar
Alhaji Musa Ɗanba’u mai taken:
Ciyaman
bugun ciyamomi:
Bala ba
a jan ka ɗan
Musa.
Wadda
ya yi wa ciyaman ɗin Yabo Alhaji Bala Musa Yabo, inda yake
cewa
Jagora: Wani ya
sha karo da ɗan
Musa,
Ado na ji Bala ya kasai,
Can nig gane shi Dagawa,
Wawa ya ɗau buhuhuwan lalle
Yara: Ya ce za ya kasuwa muza.
Idan an lura, wannan ɗan waƙa
mawaƙin ya bayyana wata gwagwarmayar da aka yi
a lokacin zaɓen
ciyamomi inda Bala Musa ya samu nasarar lashe zaɓen, sai
ya yi amfani da galabar da ya samu sai ya wa abokin takararsa zambo da cewa ya
sha karo da ɗan
Musa. Kuma an kasai. A nan kowa zai fahimci da wanda ake wato abokin takararsa,
kuma don ya ƙara bayyana wanda yake wa zambo sai ya
kawo sunan garin Muza saboda abokin hamayyarsa ɗan
garin Binjin Muza ne. Haka kuma a wani ɗan yake
cewa:
Jagora: Kansiloli
daban-daban Audu,
Kansiloli daban-daban Ada,
Ga kowane yana ta ƙiba,
Ɗan tsuntsun tsorolo tsomodo,
Yara: Shi har yanzu bai yi gwaɓi ba.
A wannan ɗan waƙar
mawaƙin ya kawo siffar wani kansila wadda za ta
sa a fahimci wanda ake wa zambo. Saboda ya nuna shi wannan mutum siriri ne kuma
bai da ƙiba.
Duk dai
a cikin wannan waƙar ya ƙara
da cewa:
Jagora: Wani
ciyaman na duba,
Ƙazami ne ku mun san shi,
Taro munka je da shi Legas,
Kwana ukku bai yi wanka ba,
Yadda ya mammatso ni sai nic ce,
Yara: Tahi
dan nan kana yi man wari.
A wannan ɗan waƙa
ya yi wa wani ciyaman zambo ne a kan wata halayyarsa ta zama da dauɗa,
domin idan aka gan shi kamar ba ciyaman ba, ga shi da rowa kuma ko kansa bai
amfana ba.
Waƙar
Gwamnanmu Mun yi Mun Ƙare Ta Alhaji Aliyu
Magatakarda Wamakko
Amshi: Ɗantakarar
zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka ɗau reni,
Kuma kar ka ɗau wulaƙanci.
A cikin wannan waƙar
Ɗanba’u ya baje kolinsa ta hanyar gina
zambo a ɗiya da
dama, kamar haka:
Jagora: Tun sadda wane yai gwamna,
Martabar jaharmu ta hwaɗi,
Mai ilimi da da marar ilimi,
Dole ne a samu bambanci,
Ku Sakkwatawa albishirinku,
Ga ɗan
uwanku nan ɗanku,
Shi za ya takarar gwamna,
Ku daure ku ba shi goyon baya,
Yara: In Aliyu ya zamo gwamna,
Martabar jaharmu ta tashi.
A wannan ɗan waƙar
mawaƙin ya kawo bayanai kai tsaye waɗanda ke
sa a fahimci da wanda ake, kamar “gwamna da ilimi” a nan kowa zai fahimci
gwamnan da ake magana wato gwamnan da ke jayayya da ɗan
takarar da ake yi wa waƙa. Haka
kuma ya kawo maganar ilimi kasancewar gwamnan bai yi karatu mai zurfi ba daga
firamari sai takardar kammala karatun piɓotal. Shi kuma wanda ake
yi wa waƙa a ƙasar
Amurika ya yi karatunsa na digiri. A nan ya soki gwamna da cewa tun lokacin da
wannan gwamnan ya fara mulki martabar jiharsu ta faɗi
saboda ba ya da ilimin gudanar da mulki. Sannan ya yabi ɗan
takararsa da cewa idan suka zaɓe shi martabar jaharsu za ta dawo
saboda yana da ilimin gudanar da mulki.
Haka
kuma a cikin wani ɗan waƙar yake
cewa:
Jagora: Tsaya abin
ga na da mamaki,
Birni da ƙauye na duba,
Kuma manya da yara na duba,
Duk inda ka ishe ɗan abarba,
Yara:
Ya iya shirin munahucci.
Jagora: wannan
Yara: Ya iya shirin azuranci.
A wannan ɗan waƙar
mawaƙin ya yi amfani da alamar wata jam’iya mai
hoton abarba ya kira su da suna ‘yan abarba’ wanda kowa zai fahimci ‘yan
jam’iyar da yake nufi. Ya soke su ta hanyar mamaki da cewa ‘yan birni da ƙauye
manya da yaransu duk sun iya munafucci da azuzanci.
Duk a
cikin waƙar ya ƙara da
cewa:
Jagora: Ni Ɗanba’u
hamdullahi,
Na yi godiya wajen Allah,
Siyasar su wane ta watse,
Yau shekara takwas suna mulki,
Girman sarakuna sun kasai,
Ga ɗan talakka ya sha ƙwaya,
Wai za ya kori sarkinmu,
Kahin ya kori sarkinmu,
Allah ya biya buƙatunmu.
Yara: Sai ga sakamako ya yi,
Shi ya rigayi hisshe shi.
A wannan ɗan waƙar
mawaƙin ya yi zambo ga wasu ‘yan siyasa abokan
hamayyar wanda yake yi wa waƙa ta
hanyar ayyana wasu abubuwa da suka faru tsakaninsu bayan sun yi mulki shekara
takwas daga ƙarshe suka samu rabuwar jam’iya. Haka kuma
ya bayyana wasu raɗe-raɗin da
ake yi cikin gari na cewa shi jagoran mai mulki ya ce sai ya tuɓe
sarkin garin daga karagar mulki. Wannan bayani da ya kawo ƙarara
za a fahimci da waɗanda ake wa zambo.
Haka
kuma a wani ɗan waƙar
yake cewa:
Jagora: A yanke
mutum a yanke dabba,
Don tattalin baƙin
tsahi,
Don a hau kujerar mulki.
Yara: In lokacinka ya ƙare,
Tsahinka dun na banza ne.
Jagora: wawa
Yara: In lokacinka ya ƙare
Tsahinka duk na banza ne,
Jagora: Saga!
Yara:
In lokacinka ya ƙare,
Tsahinka dun na banza ne.
A wannan ɗan waƙar,
mawaƙin ya yi zambo ne a kan wani shugaba wanda
al’ummar garin ke zarginsa da yin tsafi domin ya samu mulki. Shi ne mawaƙin
ke cewa in lokacinka ya ƙare
tsafinsa duk na banza ne bai tasiri.
Haka kuma a cikin wani ɗan waƙa
ya ƙara da cewa:
Jagora:
An tsai da wane takarar gwamna,
Kare mai baƙin jini
da yawa,
Yara: Du inda ya bi ya hurce,
‘Yan yara na yi mai yihu
Jagora: Yihu kare
A nan Ɗanba’u
ya yi amfani da wasu abubuwa da suke faruwa ga wannan ɗan
takara cewa magoya bayan wannan jam’iyar sun camfa shi da cewa baƙin
jini gare shi ba su son sa a canza shi. shugabansu ya nuna sai shi, shi ne Ɗanba’u
ke kira kare mai baƙin jini da yawa
ma’ana a jam’iyarsa ma ba a son sa balantana ‘yan adawa sai ya siffanta shi da
kare kasancewar kare bai da farin jini ga yara, duk inda suka gan shi ƙaryarsa
ta ƙare, sai jifa. A nan kai tsaye za a iya
fahimtar da wanda ake yi wa zambo, wato abokin takarar wanda yake yi wa waƙa
kuma ya kira shi kare domin ya ƙara
wulaƙanta shi da rage ƙimarsa
a idon jama’a.
A wani ɗan waƙa
cewa ya yi:
Jagora: Ina ɗan
buga-buga wane?
Ya leƙa Gabas ya leƙa
Yamma,
Ya leƙa Gusun ya leƙa
Arewa,
Kullum wurin munahucci,
Ba Sakkwato noz ba da Sakkwato Sawuz,
Yara: Ko Isa mun hi ƙarhinka,
Jagora: Wawa,
Yara: Ko Isa mun hi ƙarhinka.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u na yi wa jagoran jam’iyar adawar
wanda yake yi wa waƙa zambo lokacin da
yake shige-shige domin ya koma jam’iyar da ke mulkin ƙasar
don su haɗe su
samu nasarar lashe zaɓe daga ƙarshe
dai bai samu nasara ba. Yana sukar su cewa ba su da kowa shi adda mutane. Shi
ne mawaƙin ke cewa ba Sakkwato Noz ba da Sakkwato
Sawuz, ko a garinsu Isa sun fi ƙarfinsa.
Waɗannan
bayanai da mawaƙin ya kawo tare da
ambata sunan garin wannan mutum ya bayyana wanda ake wa zambo kai tsaye.
A wani ɗan waƙar
yake cewa:
Jagora: Kowa taso
tare da manya,
Ka san yana da tarihi,
Don haka manya sun ka gaya mini,
Yara: Danginsu Maguzawa ne.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa jagoran jam’iyyar da ke
adawa da wanda yake yi wa waƙa zambo
ta hanyar raɗe-raɗin da
ke yawo cikin gari cewa asalinsu Maguzawa ne, wannan ya faru ne lokacin da ya
fito takarar gwamna domin a sa mutane su ƙyamace
shi. shi ne a nan Ɗanba’u yake sukar
sa da wannan kalmar ta Maguzanci. Har yake ƙara
tabatar da abin, da ƙara masa gishiri
cewa manya ne suka faɗa masa. A nan wannan kalmar ta
Maguzanci ta bayyana wanda yake yi wa zambo.
Haka kuma a wani ɗan waƙar
yake cewa:
Jagora: Ku ƙara
shiri in za ku shirawa,
Ku ja ɗama in
za ku shirawa,
An ce mahaukaci ya rantce,
Ya shedi ba ya kaffara,
Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,
In kunka yarda yai gwamna,
Yara: Irin ta dauri ta dawo,
Har yau muna cikin ƙangi.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa zambo a kan ɗabi’a shi ta rantsuwa musamman a wurin
kamfe. Sau da yawa idan ya je kamfen yakan yi rantsuwa a cikin jawabansa, kusan
kowane ɗan gari
ya san shi da wannan ɗabi’ar. Wata rana a garin Wamakko
wajen ƙaddamar da ɗan
takararsu, al’umma sun taru ga kafafen watsa labarai na jiha da na ƙasa
da na ƙasashen waje irin su BBC da ƁOA da
makamantansu ya yi rantsuwa cewa ko kansila abokan hamayya ba za su ci ba balle
gwamna. Shi ne Ɗanba’u ke yi masa
zambo ta hanyar ɗabi’arsa ta rantsuwa domin jama’a su
fahimci da wanda yake.
Haka kuma a cikin wani ɗan waƙar
ya ƙara da cewa:
Jagora: Mun san
masu takarar gwamna,
‘yan takara zama mun san su,
‘Yan shaye-shaye mun san su,
Mun bar wane ɗan wiwi ne,
Yara: Can niga ganai cikin lungu,
Ya laɓe ana yi mai moli.
A nan Ɗanba’u
yana yi wa wasu ‘yan takara zambo ta hanyar bayyana wata ɗabi’a
ta shaye-shaye da wani ɗan takara yake da ita. Wannan ɗabi’a
ce da kusan kowa ya san wannan ɗan takarar. Shi kuma ɗan
takarar guda wanda ya kira ɗan takarar zama shi kuma jam’iyarsa
ba ta da ƙarfi ko mazaɓarsa ba
ya iya ci balantana ya ci zaɓe.
Haka
kuma duk a cikin wannan waƙar ta
Gwamnanmu mun yi mun ƙare
yake cewa:
Jagora: Yanzu kowa
ka cin amana jama’a,
A kwan a tashi Ɗanba’u,
Sai ka ganai cikin tarko,
Tarkon da ba ya hishe shi,
Ji wanda a cikin jama’a tai,
Sai ga shi yanzu ya bar su,
Waɗanga
nan da ya samu,
Ya biɗo abara
don ya raba musu,
Yara: Sai ga abarba ta tsutsu.
Jagora: Da ya biɗo
abarba don ya raba musu,
Yara: Sai ga abarba ta tsutsa.
Jagora: Sakkwato
mun canza musu suna,
Ba ‘yan abarba as sunansu ba,
Yara: ‘Yan tukuwa ɗiyan ɗiɗi.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani jagoran siyasa zambo
da magoya bayansa ta hanyar sukar jagoran da ke cin amanar jama’a a cikin
jagorancinsa kuma duk mai cin amanar jama’a sai ya shiga cikin tarko kuma
tarkon da ba ya fita. Shi ne Ɗanba’u
a cikin zambo yake nuna amanar da ya ci ta jama’arsa ma’ana yana cikin jam’iyar
da aka zaɓe shi
shekara takwas yana mulki cikinta amma yau ga shi ya fita ya ɗauko wata
jam’iya mai alamar abarba. A nan kai tsaye za a fahimci da wanda yake. Haka
kuma ya kira ‘yan jam’iyya mai alamar abarba da suna ‘yan tukuwa ɗiyan ɗiɗi. Ɗiɗi sunan
wata mahaukaciya ne.
A waƙar
Dr. Samaila Sambawa mai taken:
Amshi: Yaro ya ja maka a karya,
Ɗan
takarar gwamnan Kebi,
Dr Sama’ila Sambawa.
A cikin wannan waƙar
Danba’u ya yi amfani da zambo a ɗiyan waƙoƙi
da dama kamar haka:
Jagora:
Jahar Kebbi ba wargi ce ba,
Kuna da ɗinbin
al’umma,
Ku zaɓi mutum
cincimtace,
Irin Sama’ila Sambawa,
Don kar ku yarda da jemage,
Ko yaushe kai nai soke yake,
Yara: Ba za ya yarda da kowa ba.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya. Ya
yi amfani da salon jan ra’ayi ta hanyar yabon al’ummar Kebbi sannan ya tallata ɗan
takararsa, kuma ya soke abokin hamayyar Sambawa inda ya kira shi jemage. Jemage
wani ƙazamin tusntsu ne da ke kashi a baki kuma
duk inda yake wurin bai shaƙuwa
kuma jemage bai da farin jini ga mutane. Ya kuma siffanta shi da wata mugunyar ɗabi’a
ta soke kai, Bahaushe na da tunanin duk mai yawan soke kai mugu ne kuma mugu
bai cika yarda da mutane ba. A nan kusan kowa ya san da wanda ake wato shi ne
abokin takarar Sambawa.
A wani ɗan waƙar
kuma cewa ya yi:
Jagora: A Jahar
Kebbi kowa ya waye,
Ba su koma zaɓenka ɓarawo
Ya kwashe kuɗin talakawanai,
Ya je ƙasar waje ya ɓoye,
Yara: Har na ji mutane suna hwaɗin
Olle raga muna nerori.
A nan zambon ƙarara
yake domin abokin takarar Sambawa an zaɓe shi a
karo na farko a matsayin gwamna yanzu kuma a karo na biyu ne za su kara da
Sambawa. Shi ne Ɗanba’u ke cewa
al’ummar Kebbi sun waye, ma’ana sun gane ba su koma zaɓensa.
Sun fahimci ɓarawo
ne ya kwashe kuɗinsu ya je ƙasar
waje ya ɓoye.
Wai a kan tsananin yawan kuɗin da ya sata har ya ji mutane suna
faɗin olle
raga muna nerori. Olle a harshen Yarbanci na nufin ɓarawo.
A daidai wannan lokacin ana raɗe-raɗin cewa
an kama gwamnonin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da kuɗaɗe a ƙasar
waje. Shi ne Ɗanba’u ya yi amfani da wannan raɗe-raɗin ya
gina zambo.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
Ɗanba’u cewa ya yi:
Jagora: Mulkinka
wane mulkin banza ne,
Mulkinka ba ya da tasiri,
Tun randa wane ya zam gwabna,
A jahar Kebbi kowa na kuka,
Talakawa sun damu da kai,
Na ji suna roƙon Allah
Yara: Yada munka ga hwarkon mulkinka,
Ya Allah gwada muna ƙarshe
nai.
A wannan ɗan waƙar
ba a buƙatar wani dogon bayani domin an fito da
hoton wanda ake wa zambo ƙarara
ma’ana an ambaci muƙaminsa wato gwamna kuma kowa ya san shi ne abokin
hamayyar Sambawa.
Duk a
cikin wannan waƙar yake cewa:
Jagora: Wani ya ga
alamun ya hwaɗi,
Can nis same shi Ɗanwarai
Ya ɗauko
shatar babban mota,
An shaƙe mai ita da albasa,
Yara: Ya ce a kai mai a Ibadan,
Can za a kai ta a saisam mai.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya gina zambo ne ta hanyar yi wa
abokin hamayya burga da kuma ɗebe tababa da nuna Sambawa zai sami
nasara domin shi kansa abokin hamayya ya ga alamun faɗuwa shi
ya sa ya raba hannu biyu domin ko ya faɗi zai
ci gaba da sana’ar albasa tai. A nan kamar yadda ƙamusun
Hausa na Jam’ar Bayero (2006) ya bayyana cewa: “Zambo na nufin ƙagawa
mutum magana wadda za ta muzanta shi ko ɓata
masa suna.” Irin wannan ne Ɗanba’u
ya yi ta hanyar ƙaga wa abokin hamayyar
Sambawa wanda ke riƙe da kujerar
gwamna cewa an gane shi Ɗanwarai,
Ɗanwarai wani gari ne kusa da Alieru wai ya
ɗauko
shatar babbar mota an shaƙe ta da
albasa ya ce a kai mai Ibadan a sayar mai.
A wani ɗan waƙar
kuma yake cewa:
Jagora: APP kun ɓata shirinku,
Kun kada girman sarakuna,
Ga wanda ya gadi sarauta,
Sai ɗai ku ƙwace
rawaninai,
Yara: Ku ɗauka ku
ba maginin laka.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani wanda ya ci zaɓen
gwamna a ƙarƙashin
jam’iyar APP zambo ta hanyar kama sunan jam’iya ƙarara
da sukar su a kan sun kada girman sarakuna ta hanyar tuɓe wani
baban sarki a jahar Kebbi wanda ya gadi sarautar. Haka kuma ya soke sabon
sarkin da aka naɗa ta hanyar kiransa ‘magini’ kuma ko
maginin na laka. A nan abu ne a bayyane, inda gwamnatin jahar Kebbi ta tuɓe
babban sarki na jahar suka naɗa wani. Shi ne Ɗanba’u
ya yi amfani da shi ya gina zambonsa.
Waƙar
Yusuf Musa Illela Mai Taken:
Riƙa
bari wargi,
Karo da kai ba ya
da daɗi,
Isuhu Musa
Ciyaman,
Kai
ne suka sauna.
Wannan waƙar ita
ma ba a bar ta a baya ba domin Ɗanba’u
ya yi amfani da zambo a ciki inda yake cewa:
Jagora: Koma ganin
bushiya a birnin Illela,
Ƙila ko ta tahiyatta,
Yara: Tana nan Illela,
Don ko jiya mun ganat,
Ga ‘yan yara ga hannu.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa abokin takarar Yusuf Musa
zambo ta hanyar fito da wata siffa ta ƙirar
jikinsa domin ya bayyana wanda yake yi wa zambo ƙarara
cewa yana da doro. Sai ya siffanta shi da bushiya domin kowa ya fahimci da
wanda yake. Sannan shi kuma ya ƙara baƙanta
masa rai.
Haka
kuma ya ƙara de cewa:
Jagora:
Duk baƙo ya shigo Illela,
Sai ka ji ya ce,
Garinga maye nika shakku,
Baƙin angulu,
Ka yi hurhura ka gama aski,
Yara: Kai ka shafa muna lahiya,
A bar ce muna mayu.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u na yi wa wani mutum zambo a kan
wani zargi da ake ma zuri’arsu da shi wato “maita”. Shi ne Ɗanba’u
ya yi amfani da wannan zargin da ake yi musu ya yi masa zambo.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Adamu
Bakane,
Ka yi dangali bana ka huta,
Adamu Bakane,
Mai gida baban Shehu da Inuwa,
Yi zamannka ka huta,
Ƙattan
banzan ga masu kuri Illela,
Yara: Ƙyale su
da ‘yan yara su ka ruga musu kashi.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa manya-manyan masu kuɗin
Illela zambo kasancewar sun taru a jam’iya ɗaya shi
kuma Adamu Bakane ɗai ne sai yaronsa guda kuma Allah ya ba su
nasarar lashe zaɓe shi ne Ɗanba’u
ya haɗe su
duk ya kira su da ƙattan banza domin
duk taronsu da dukiyarsu sun kasa cin zaɓen ƙaramar
hukuma.
A wani ɗan waƙar
yake cewa:
Jagora: Wanda
Allah ya ba,
A bi shi shi ad daidai,
Waɗanda ba
su buƙatak ka,
Ga su nan sun muzanta,
Yara: Tun da ba su da komai
Ƙasa ga kuma ba su da kowa.
A nan ya yi wa ‘yan adawar ciyaman
zambo cewa sun muzanta ba su da komai. Kuma ba su da kowa dan haka tun da Allah
ya zaɓe shi
to abi shi shi ad daidai.
A wani ɗan waƙar
ya ƙara da cewa:
Jagora: Ar!
Ga wani ya yi takarab bayis,
Ta ruhe da shi ya hwasa kuka,
Yanzu swata yaka nema,
Bakin dutse ka kai ka iske,
Yara: Tun da ɗan
asali ba ya kasuwanci da ƙazami.
A wanna ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa ɗan
takarar mataimakin ciyaman wanda ya faɗi zaɓe zambo
ta hanyar muƙamin da ya nema wato bayis bai samu nasara
ba. waɗannan
kalmomi na takara da bayis ƙarara
sun bayyana wanda ake wa zambo,. Haka kuma ya ƙara
sukar sa da wasu kalmomi masu zafi kamar swata da ƙazami.
Haka
kuma a cikin wani ɗan waƙar yake
cewa:
Jagora:
Buhun lalle yai kama da buhu bai yi buhu ba,
Shi buhun lalle
yai kama da buhu ba yada nauyi,
Da ina tsoron wane, yanzu na bar tsoron shi.
Yara: Tun da bakin garkassu munka watce musu
kaya.
A nan Ɗanba’u
ya yi wa wani babban mutum ɗan siyasa na garin Illela zambo ta
hanyar kiransa buhun lalle. Saboda shi buhun lalle ana kiran sa buhu matsawar
dai an cika shi kamar yadda ake cika buhun hatsi ko na shinkafa. Amma ba
matsayinsu ɗaya ba,
kuma nauyinsu da darajarsu ba ɗaya ba. Haka kuma Ɗanba’u
ya ƙara fito da zambo a fili cewa: “A da ina
tsoron wane” ma’ana akan kuɗinsa da sauran abin da ya mallaka
dun wanda zai yi jayayya da shi zai ji tsoro. Ya ƙara da
cewa: “Yanzu na bar tsoron shi tun da bakin garkarsu munka watce musu kaya.”
Ma’ana a bakin garkarsu aka kashe shi zaɓe. A
nan a taƙaice ya yi wa wannan ɗan
siyasa zambo ne a kan gashi da girma da dukiya amma ba su amfane shi ba. duk
zamansa babban jagora ya kasa cin rumfar gidansu.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
duk a cikin wannan waƙar yake
cewa:
Jagora: Bambaɗawan
lokal,
Su wane sanƙira,
Ka da ka hwaɗa Ɗanba’u,
Yara: Wanga lokaci ba ka da ƙarhi,
Jagora:
Da kai nike kai wane,
Raƙumi ɗan
atololo
bana ina za ka da kaya?
Yara: Za ya je ɓantala
gindi,
Inda mata suke banza.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi amfani da matsayin wannan
mutum ma’ana muƙaminsa na PRO ya
fassara shi da bambaɗawa lokal da kuma kalmar sanƙira
domin ya baƙanta masa rai tare da bayyana shi ta
hanyar da kowa zai fahimci da wanda ake. Haka kuma ya ƙara yi
masa zambo ta hanyar siffarsa kamar tsawonsa, da idanunsa da wuyansa za a gansu
kamar na raƙumi. Shi ne ya kira shi raƙumi.
Haka kuma ya yi amfani da wata ɗabi’arsa ta neman mata ya danganta
shi da ɓantalagindi.
A yanayin tunanin Bahaushe idan ya ce ɓantalangindi to
yana nufin wurin da matan banza suka keɓanta
suna holewa.
Waƙar
Sarkin Yamman Sakkwato Mai Taken: Alhaji
Aliyu Magatakardan Wamakko
Ƙi sake
bajini gwarzon maza,
Ali sarkin Yamman
Sakkwato.
A wannan waƙar
Alhaji Musa Ɗanba’u ya gina turken zambo a ɗiyan waƙa
a wurare daban-daban kamar haka:
Jagora:
Aliyu kai ka gadi sarauta,
Ka yi naɗi daidai da sarauta,
Wanda duk bai gadi sarauta ba,
Yara ko ga naɗi sai mun ganai,
Yara: Wane naɗi nai
ya cika girma,
Wanga uban huni sai ‘yan dako.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani basarake abokin
hamayyar sarkin Yamma a gefen siyasa wanda aka naɗa su
lokaci ɗaya
zambo a kan gadon sarauta, kasancewar shi sarkin yamma ɗan
gidan sarauta ne. ya gadi sarautar kuma an naɗa shi.
shi kuma wanda yake yi wa zambo ba inda ya gadi sarauta kuma sarautar da aka yi
masa ba a taɓa yin
ta a Sakkwato ba shi aka fara yi wa ita. Shi ne yake yin zambo cewa wanda duk
bai gadi sarauta ba yara ko ga naɗi nai za a gane bai gadi sarauta
ba, saboda haka naɗinsa ya cika girma kamar gammo. A nan za a
fahimci wanda ake yi wa zambo kasancewar bai gadi sarauta ba kuma ba a taɓa yin
sarautar ba sai gare shi.
A wani ɗan waƙar
yace:
Jagora: I taƙamarka
Alu daidai kake,
Taƙama sai dai ɗan
sarki,
Jan biri in dai ya yi taƙama,
Yara: Tabbata hwadaman nan ya gani,
Yana nuhwa ya kare geron wani.
A wannan ɗan waƙar
ma ya yi zambo ne a kan gadon sarauta cewa Alu ya gadi sarauta shi kuma bai
gada ba. kamar dai yadda aka yi bayani a ɗan waƙar
da ya gabata. Sai dai a wannan ɗan waƙar ya ƙara
kawo siffar wanda yake yi wa zambo ta yadda za a ƙara
fahimtar sa, ta hanyar launin jikinsa tare da danganta shi da biri don ƙara
baƙanta masa rai.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Ran Juma’a
na kwan mamaki,
An yi sarautu Sakkwato bunni,
Mai kurin shi ad da mutance,
An yi naɗi kowa ya watce,
Mai jama’a ya kwashi abinai,
Sai nib biya garkar wani sarki,
Ni ishe ‘yan banga sun taru,
Yara: Da haka ‘yan sholi ɗai ɗan nig
gani.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani basarake da aka naɗa su
tare da Alu zambo ta hanyar wani abin da ya faru a ranar da aka naɗa
sarautar bayan kammala naɗi. Da ma akwai jayayyar siyasa
tsakaninsu duk da kasancewarsu jam’iyarsu ɗaya
amma shi wanda ake wa zambo koyaushe yana bugun gaban cewa ya fi Alu mutane
sannan kuma shi a tare da gwamna shi kuma Alu ya samu saɓani da
gwamna ga shi mataimakin gwamna amma komai ba a yi da shi ta hanyar gudanar da
mulki. Wannan rashin kulawar da ake wa Alu shi ya ja ra’ayin al’ummar garin
suke ƙaunar sa saboda tausai, ranar naɗi bayan
watsewa sai jama’a suka yi gidan Alu. Shi ne domin ya ƙara
bayyanar da wanda yake, saboda ‘yan banga ke gadin gidansa, haka kuma a sashen
gidansa akwai dabar ‘yan shaye-shaye babba kasancewar hukuma ba ta zuwa wurin
kamun ‘yan shaye-shaye.
A waƙar
jam’iyar P.D.P. mai taken
Ya ‘yan Nijieriya,
Siyasa ta tashi,
Ku dawo mu yi ƙoƙari
Mu koma PDP
Ita ma
wannan waƙar ba a baro ta a baya ba wajen gina
turken zambo kamar inda yake cewa:
Jagora: Babu mai
cin bashi,
Cikin siyasar PDP
In kana son ka shigo
Cikin siyasar PDP,
Ka biya bashin banki,
Ka je mu je tare da kai,
Kar tafiya ta yi nisa,
Yara: Ka je ka goga mai laɓo.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani babban jigon siyasa
na fatin da ke adawa da PDP, mai kuɗi ne kuma ɗan
kasuwa ne wanda ake raɗe-raɗi a
cikin gari cewa ba kuɗinsa ne yake kasuwanci da su ba,
banki ne ya ba shi bashi. Shi ne Ɗanba’u
yake yi masa zambo da wannan kalma ta bashi domin kowa ya fahimci wanda yake wa
zambo.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Ko cikin
mata,
Wance ‘yar jidalin mata ce,
Kullun habshi takai,
Kamar karyar zango,
Yara: An yi an ƙare,
Ke baƙin jidali ya hwarma.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wata mata ‘yar siyasa
zambo a kan halayyarta ta faɗa da mutane musamman a fagen siyasa
har ma ‘yan siyasa na amfani da ita wajen cin zarafin abokan adawa.
Haka kuma a cikin wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Wanda duk
ke kwakwa,
Ba mutumen kirki ne ba,
Yara: Da ɗan ƙwaya,
Sai ɗan dara,
Sai ko ɗan
daga.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa ‘yan wata jam’iya mai
alamar icen kwakwa zambo ta hanyar kiran su ‘yan kwakwa, tare da zagin su da
rashin kirki da miyagun ɗabi’u na shaye-shaye da caca.
A wani ɗan waƙar
kuma yake cewa.
Jagora: Ashe wane
barazanarka,
Aikin banza ce,
Ba ya da kowa,
Garinsu koran,
Shi ɗai ne,
Yara: Mun ji labarin ko gidansu,
An ce ya sai da.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani mai goyon bayan
jam’iyar da ke adawa da PDP zambo ta hanyar nuna cewa barazanar da yake yi
aikin banza ce saboda bai da kowa ma’ana ba ya da mata ba ya da ɗa, kuma
bai da mutum ɗaya da
yake a ƙarƙashinsa,
ƙuri’arsa kaɗai ya
mallaka. Sai ya ƙara bayyana shi ta
hanyar da kowa zai fahimci shi da cewa har gidansu an ce ya sai da kuma gaskiya
ne dai-dai lokacin ya sai da gidansu.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
yana cewa:
Jagora: Ga wani ɗan
takara da doro,
Abu dai zuƙui-zuƙui,
Ke kuma bushiya ki ɓoye doronki,
Yara: Ba ki bakin komai,
Wurin hwarauta banza ce,
Jagora: Na ga
baki bakin komai,
Yara: Wurin hwarauta banza ce.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
takara zambo ta hanyar wata halitta da Allah ya yi masa ta doro sai ya siffanta
shi da bushiya kasancewar ta a dunƙule da
doro da cewa a wurin hwarauta banza ce don yara ka kama ta don ba ta iya gudu
kamar zomo ko kurege kuma ba ta iya tashi sama kamar tsuntsaye saboda haka shi
ma kayar da shi zaɓe ba wani abu ne mai wuya ba.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Bana duna
baƙin kare,
Dubara ta ƙare,
Kai kare ɗauke ƙafarka,
Na ga gungu ‘yan yara,
Yara: Kar su ɓata ma
tsari.
Jagora: In kai
kare ɗauke ƙafarka,
Na ga gungu ‘yan yara,
Yara: Kar su
ɓatama
tsari.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa zambo a kan wata halitta da Allah ya yi masa ta launin jikinsa wato baƙi
ya kuma danganta shi da kare don ya wulaƙanta
shi. Duna na nufin mutum mai baƙi da
yawa. Wannan kalma ta duna ita ta bayyana wanda yake wa zambo.
A waƙar
Aliyu Magatakarda Wammako mai taken:
Ƙara
shirawa,
Aliyu zaɓaɓɓen
gwamna,
Mai ban tsoro magatakarda
Wamakko,
Sarkin Yamman
Sakkwato bai san wargi ba.
A wannan waƙar Ɗanba’u
ya gina zambo a ɗiyan waƙa da
dama kamar inda yake cewa:
Jagora: Mugun
madambaci kake Ali,
Baba da ka tattako, ka bugi bakin dogo,
Ya tahi ba ban kwana,
Yara: Bar maganar guntu,
Shi hadda ciki nai ya hude.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wasu abokan hamayyar Alu
da suka sha kaye a zaɓen 2007 zambo ta hanyar faɗuwa zaɓe, tare
da bayyana ƙirar halittarsu ta yadda kai tsaye za a
fahimci su. Inda ya kira babban jigon da dogo shi kuma wanda jigon ya tsaisuwa
takara, ya kira shi guntu. Masu waɗannan siffofin a
Sakkwato ba ɓace
suke ba, domin da an ce dogo kusan kowa ya san da wanda ake.
A wani ɗan waƙa
kuma yake cewa.
Jagora: Waɗansu
maza, sun yi rantsuwa kuma sun ƙara,
Sun ce maka ɗan Barade ba ka zama gwamna,
Allah ya yarda yau Alu ka zama gwamna,
Bamaguje kai kuma ya za ka yi zancen kononka,
Yara: Du hatcin Sakkwato kaf ba su cire mai
kahwara
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani babban jigo na siyasa a jam’iyar da ke adawa da Alu a kan wata ɗabi’arsa
ta rantsuwa musamman awajen yaƙin
neman zaɓe inda
yake rantsuwa cewa ba gwamna ba ko kansila jam’iyarsu Alu ba ta ci. Mai wannan ɗabi’ar
a Sakkwato kowa ya san shi, haka kuma ya ƙara
kiran sa da kalmar Bamaguje wadda da yawan masu adawa da shi sukan jefi shi da
ita. Dalilin da ya sa ake kiransa Bamaguje shi ne Bagobiri ne saboda irin rigimar da Usmanu Bini Fodiyo ya yi da
Gobirawa a kan Musulunci.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Wane
Sakkwatawa sun ɗaukai mutumen kirki,
Dab baya ya yi lalata,
Ya tafka abin kumya.
Yara: Dan nan daraja tai ta hwaɗi,
Jagora: Mun gane shi mutumci madara ne,
Da ya zube a ƙasa,
Yara: Ban san wani mai kwasa tai ba.
A wannan ɗan waƙar,
makaɗin ya
yi wa wani ɗan
siyasa zambo wanda Sakkwatawa suka karɓe shi hannu
biyu-biyu suka goya masa baya ya ci zaɓe har sau biyu,
daga baya sai ya juya masu baya a kan wata ‘yar matsala har dattijawan garin
suka roƙe shi wata alfarma domin a samu zaman
lafiya a garin ya yi amfani da ƙarfin
mulki ya ƙi. Daga nan su kuma suka juya masa baya
wannan matsala ta yi sanidiyar faɗuwa zaɓe daga
baya ya yi biɗa shiri
abin ya ci tura. Shi ne Ɗanba’u
ke yi masa zambo da cewa Sakkwatawa sun ɗauke shi
mutumin kirki daga baya ya yi lalata, daraja tai ta faɗi don
haka shi mutumci madara ne idan ya zuɓe bai kwasuwa.
A wani ɗan waƙa
kuma yake cewa:
Jagora: Ji wane ɗan hwaɗin rai
wai
bai biɗar
sanata,
Shugaban ƙasa yaka so,
Bana ya yi ɓakan-ɓakatantam,
Bai yi president ba,
Kuma nan ga jiha tai ya hwaɗi,
Ba zama Sakkwato,
Yara: Sai dai ya tsaya Kwatano,
Ko kuma ya wuce birnin Ghana.
A wannan ɗan waƙar
zambo a fili yake ba ya buƙatar
dogon sharhi. Amma a taƙaice ga
al’adar siyasa Nijeriya, idan gwamna ya yi mulki a zangon na biyu ya ƙare,
zai nemi kujerar sanata, shi wannan gwamna ya ƙi neman
kujerar sanata sai ya nemi kujerar shugaban ƙasa bai
samu nasara ba kuma ɗan takararsa na gwamna bai samu nasara ba.
shi ne Ɗanba’u ke yin zambo da kiran sa ɗan faɗin rai
wai bai biɗar
sanata shugaban ƙasa yake so daga ƙarshe
ya ƙara bayyana wanda yake wa zambo ta hanyar
ambatar sunann garinsu da cewa ba zama Sakkwato, ambatar Sakkwato. Ya bayyana
kai tsaye wanda ake nufi.
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Mai
jamai’as siyasa,
Bana ya hwaɗi ina magana,
Ɗan Sakandare ya kasai,
Ya shiga sabbatu,
Yara: Bana ko magana tai ya noce.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa zambo ta hanyar waƙar da
wani makaɗi ya yi
masa inda yake kiran sa mai jami’ar siyasa ƙasar ga
kowa iya ta sai ya ambaci sunan wannan wanda yake wa waƙa, ya
ce shi ya koya masa. Wannan kalamin da makaɗin ya
yi na mai jama’ar siyasa sai ya zama sara a wannan lokaci. Shi ne Ɗanba’u
ke mai da martani ta hanyar zambo cewa mai jama’ar siyasa ya faɗi ina
magana? Ɗan sakandare ya kasai. Mai jama’ar siyasa
a Sakkwato sananne ne.
A waƙar
Tanimu Ɗangaladiman Ƙyaɗawa mai
taken:
Dogo kana da
shirin yaƙi,
Tanimu
na Alhaji Yakubu.
A wannan waƙar
Alhaji Musa Ɗanba’u ya fito da zambo a cikin ɗiyan waƙar
wurare da dama kamar haka:
Jagora: Ranar zaɓen Gada
Ɗanba’u,
Ban gani ba labari naj ji,
Waɗansu
maza sun ji azaba,
Wani ya bar hula da agogo,
Wani kau ya mance gilashi nai
Wasu kau sun ɗauko ƙahwahunsu,
Yara: Can sun ka mance kubuttansu.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi amfani da wasu abubuwan da
suka faru a ranar da aka yi zaɓen ciyaman a Gada. An yi
gwagwarmaya sosai kuma an samu tashin hankali bayan kammala zaɓe.
Tanimun ya samu nasara sai aka fara yi wa ‘yan adawa kuwa daga ƙarshe
aka biyo manyan ‘yan adawa da gudu to a nan fa wasu suka yadda hula, wasu
agogo, wasu gilashi wasu a guje ba takalma. Shi ne Ɗanba’u
ke yin zambo cewa ranar zaɓen Gada wasu maza sun ji azaba.
Wani ya bar hula da agogo wani ya mance gilashi nai wasu ko sun hawo ƙafafunsu
can sun ka mance kubuttansu. Kubuttai na nufin rufaffen takalmi na roba. A nan
a Gada kowa ya san waɗanda wannan abin ya faru a kansu.
A wani ɗan waƙa
kuma yana cewa:
Jagora: Ƙara
hanƙuri kar ka ji komai,
Hanƙurinka shi nak kai ka haka,
Hak ka yi ciyaman ƙasar
Gada,
Kak kada biri sarkin ƙwalama,
Ci ƙurgurguma a ci buzuzu,
Nac ce biri a yi a
hankali,
Yara: Wata ran cikinka yana ɓaci.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa abokin takarar Tanimun
zambo a kan nasarar da aka samu a kansa. Shi ne yake cewa ka kada biri sarkin
kwalama. A nan ya kira shi biri ne domin a wulaƙanta
shi tare da muzanta shi a idon duniya. A nan kowa ya san wanda ake wa zambo
wato wanda Tanimu ya kasuwa zaɓe.
Haka
kuma a wasu ɗiyan waƙa
yake cewa:
Jagora: Nai roƙo
Ɗanba’u wajenka Tanimun na ƙara,
Dauda ƙiri nike kallo ka ba shi wuri nai ya dace,
Na so a hidda ɗan gwadda mai ja,
Yara: Mun gane bai muna alheri.
Jagora: A in kun
yi mitin kuma kun ƙare,
Don Allah kira Dauda Ƙiri,
Ka san aikin nai dattijo,
A ba shi babban aikinai,
Tunda wurinai ya saba,
A hid da wanga hwarin doki,
Yara: Don na ga bai muna alheri.
A waɗannan ɗiyan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani mai riƙe
da muƙami lokal gwammen a Gada zambo ta hanyar
siffar jikinsa mai launin ja ko fari inda ya kira shi da jar gwadda da kuma
farin doki. Sannan ya bayyana halayarsa ta rowa tare da kawo wasu bayanai ta
hanyar kawo sunan Dauda Ƙiri
domin ya ƙara fito da abin fili kasancewar Dauda Ƙiri
aka cire aka sa shi tare da yi wa Dauda Ƙiri roƙo
cewa a maisam mai muƙaminsa a fid da
wancan farin doki tun da bai masu alheri.
A waƙar
Ciyaman ɗin
Shagari, Alhaji Muhammadu Galadima Horo mai taken:
Dogo kana halin
kyauta,
Alhaji Ɗan’ige
ɗan
dattijo,
Mamman
ciyaman Shagari,
A wannan waƙar ma Ɗanba’u
ya yi zambo a cikin wasu ɗiyan waƙa kamar
haka:
Jagora: Na san
karo da kai,
Ba ya da daɗi,
Kai ji wane ya sha kaye,
Don na gane shi can malisa,
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi,
Jagora: wawa
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi,
Jagora: saga
Yara: Ya tara leda yana ƙullin magi.
Jagora: Ka gama da
tsohon kolo,
Wane ya bar gidanai,
Yara: An ce yanzu kulun,
Yana loja kwance.
A waɗannan ɗiyan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa abokin takarar Ɗan’ige
zambo da cewa ya sha kaye, kuma an gama da shi ya kira shi tsohon kolo, sannan
ya soke shi da wurin zamansa, wato loja sannan ya kira shi wawa da saga. A nan
kalamun shan kaye da kuma zama loja sun bayyana wanda ake wa zambo. Domin an
san wanda ya sha kaye kuma kowa ya san ya daina zama garinsu garin da ya koma
akwai wata loja nan ne wurin zama nai kullum.
A wasu ɗiyan waƙa
suke cewa:
Yaro: Wani ciyaman
na nan mai rowa,
Da du, ya gane ni ya sha toka,
Wani mai idanun ‘yabin,
Yara: Kuma ya yi kan
‘yan jarirai.
Jagora: Ina mai idanun
mussoshi,
Yara: Kuma ya yi kan ‘yan jarirai.
A
wani ɗa yake
cewa:
Jagora: Wani ciyaman ne,
Sarkin rowa,
Sai son a zo a yi mai waƙa,
To ba ni yin aikin banza,
Yara: Na daina yin waƙa
kyauta.
Jagora: Wawa,
Yara: Na daina yin waƙa
kyauta.
Jagora: Saga!
Yara: Na daina yin waƙa
kyauta.
A waɗannan ɗiyan waƙa
Ɗanba’u da yaransa sun yi wa wani ciyaman
zambo ta hanyar halinsa na rowa tare da bayyana siffofinsa ta yadda kowa zai
iya fahimtar da wanda ake kamar inda yake cewa mai idanun ‘yabin kuma ya yi kan
‘yan jarirai. A wani layin waƙa Ɗanba’u
ya bayyana ‘yabin a karin harshen Sakkwatanci da cewa mussa (ma’ana kyanwa) ke
nan shi wannan yana da irin idon kyanwa, kuma yana da ƙaramin
kai kamar na jarirai. A nan sun yi amfani da nau’o’in zambo iri biyu na hali da
kuma na halitta.
A waƙar
ciyaman ɗin
Gwadabawa Alhaji Musa Lumu mai taken:
Gwaron giwa kullun
yana halin yabo,
Alhaji LumunMusa
ciyaman zarumi.
Ita ma wannan waƙar
ba a bar ta a baya ba domin akwai zambo a cikinta kamar inda yake cewa:
Jagora: Ƙasar
Gwadabawa,
Mu mun yi babban arziki,
Don mun ije kunkuru mai idanu tsatstsaye.
Yara: Kai bari ɗan
tulluƙi ba a yi komai da kai.
A
wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Wane an
kashe shi sai ya tcira man tcegumi
Mai babban gaba mi gami na ni da kai?
Yara: Ka isko ni gida ka ce za ka tungatci da ni.
A waɗannan ɗiyan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa ɗan
takara da Musa Lumu ya kasuwa zambo ta hanyar halitta da Allah ya yi masa inda
ya siffanta halittarsa da kunkuru tare da bayyana yadda idanunsa suke da kuma
yanayin ƙirar jikinsa wato ɗan
tulluƙi kuma mai babban gaba tare da ambatar an
ije shi da an kashe shi, tare da bayyana wani saɓani da
ya faru tsakaninsu inda yake cewa ka isko ni gida ka ce za ka tungatsi da ni.
Bayan kammala ɗan waƙar
sai Ɗanba’u ya ce: “Ba ka faɗa da
Musa Lumu shi da yak kashe ka sai Ɗanba’u
da am macce.”
Haka
kuma a wani ɗan waƙa
suke cewa:
Yaro: Haji Ɗanba’u
akwai tambaya ta ni da kai,
Yaran Musa akwai tambayata ni da ku,
Maroƙan Musa
akwai tambayata ni da ku,
Shin don Allah ina mai hwaɗin sai
ya bugan?
Wani ɗan kutuɓi baƙi mai idanun raguna,
To na zage ka,
Yara/jagora:
Komai kakai man sai ka yi,
Jagora: Wane yau
na zage ka,
Yara: Komai kakai man sai ka yi.
A wannan ɗan waƙar
sun yi wa wani mutum wanda saɓanin siyasa ya haɗa su
zambo ta hanyar bayyana abin da ya faru tsakaninsu tare da kawo hoton sifarsa
wato kutuɓi baƙi
mai idanun raguna ta yadda kowa zai fahimce shi, sannan daga ƙarshe
kai tsaye suka ce sun zage shi komai zai yi ya yi.
A waƙar
Sardaunan Hamma’ali Malami Maigandi mai taken:
Sardaunan
Hamma’ali zaki
Malami
Maigandi bi da arna,
A
wannan waƙar ita ma Ɗanba’u
ya yi zambo a cikinta kamar inda yake cewa:
Jagora: Hamma’ali
na tafi yawo,
Ga wani nai muna kurin banza,
Ya ce shi aka wa Sardauna,
Sai nac ce kauce da nesa,
Yara: Kusun kusumi ba ya kyau da sarki.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum wanda ya yi
neman sarautar Sardaunan Hamma’ali bai samu ba. zambo ta hanyar halittarsa wato
siffar jikinsa inda ya kira shi da kusun kusumi ba ya kyau da sarki. Da ya kai ƙarshen
ɗan waƙar
sai ya ce ana sarki babu kyau babu kyawun kama?
A wani ɗan waƙar
yana cewa:
Jagora: Cikin ‘yan
sarki na Hamma’ali,
Akwai wani sata yakai da rana
Shi wannan ya zame muzuru,
Yara: ‘Yan
kaji bai bari su girma.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
sarkin Hamma’ali wanda a masarautar shi ne kawai bai goyon bayan Sardauna. Shi
ne Ɗanba’u ke yi masa zambo ta hanyar ƙirƙiro
sata ya laƙa masa domin a wulaƙanta
shi a ci zarafinsa tare da baƙanta
masa rai da siffanta shi da muzuru. Duk ɗan sarkin
da ke jiran sarauta aka kira shi ɓarawo ai an nakasa shi. A nan kusan
‘yan Hamma’ali duk sun san ɗan sarkin da ake nufi.
A waƙar
Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko mai taken:
Maganin wargi ɗan
Garba,
Aliyu Sabon
gwamnan Sakkwato,
Ba
a kai ma reni ko kusa.
Wannan
waƙar ita ma akwai zambo a cikinta. A cikin
wasu ɗiyan waƙa
kamar haka:
Jagora: Su wane
sun ci amana Allah,
Yanzu amana ta kama su,
Sun yi gidaje gadan-gadan,
Gahwa gidaje daidai jin daɗi,
Yara: Ba a da dama zaunawa ciki.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wasu manyan ‘yan siyasa da
suka faɗi zaɓe a
jahar Sakkwato, suka kasa zama garin zambo ta hanyar bayyana manya-manyan
gidaje da suka yi amma ba su iya zama garin saboda baƙin ciki
da kuma tsoron kada a yi musu wani abu. Waɗannan
‘yan siyasa a jahar Sakkwato sanannu ne.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Wane giyam
mulki ta ɗibai,
Hay ya je Gada ya sha wallah,
Ya ce ko hullatai ya aje ƙasag
ga,
Sai tai gwamna Sakkwato.
Yara: Mai bundigar iskan ga talo-talo,
Bana ya hau dokin rantsuwa.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani mai mulki zambo ta
hanyar wata halayyarsa, ta rantsuwa da kuma wani jawabi da ya yi a garin Gada
wurin kamfe inda yake cewa duk wanda ya tsaisuwa takara gwamna sai ya ci zaɓe. Shi
ne yake danganta maganarsa da bindigar iska wato maganar banza kuma ya kira shi
talo-talo kuma ya hau dokin rantsuwa.
3.7 Naɗewa
A wannan babi an yi bayani a kan zambo
tun daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-iren zambo daga ra’ayoyin masana da
manazarta daban-daban, tare da kawo dalilan da ke sa a yi shi. haka kuma an
bayyana muhimmancin ko amfanin da ake samu ta hanyarsa. Daga ƙarshe
an kawo sharhin zambo a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ta hanyar fitowa da
abubuwan da masana da manazarta suka bayyana a matsayin zambo. Haka kuma an
nazarci wasu waƙoƙinsa
da ke ɗauke da
zambo aka kawo misalai a wurare daban-daban.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.