Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.
Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (4)
NA
SHEHU HIRABRI
08143533314
BABI NA HUƊU
HABAICI A CIKIN WASU WAƘOƘIN
ALHAJI MUSA ƊANBA’U GIDAN BUWAI
4.0 Shimfiɗa
A cikin
wannan babi za a yi bayani tare da kawo misalai tun daga asalin kalmar habaici
da ma’anarta da ire-irenta da dalilin da ya sa ake yin habaici da amfaninsa
tare da yin sharhinsa a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.
4.1 Asalin Kalmar Habaici
Ra’ayin masana ya haɗu a kan
cewa, asalin kalmar habaici, Bahaushiyar kalma ce wadda za a iya danganta ta da
maganganun hikima da azanci da gwaninta da naƙaltar
harshe da Hasuawa suka gada tun iyaye da kakanni. Saboda haka ba ta da alaƙa
da kowane harshe sai Hausa. Haka kuma ba a iya cewa ga lokaci da aka fara
amfani da ita. Hausawa sun taso suna shirya habaicinsu da kansu a cikin waƙoƙi
da maganganunsu na yau da kullum. Habaici ya ƙara
samun gata ta hanyar makaɗa da mawaƙa da
manazarta.
4.2 Ma’anar Habaici
Malamai masana da manazarta da dama
sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar habaici. Ga wasu daga cikinsu:
Ɗangambo,
(1984: 42) cewa ya yi: “Habaici magana ce mai ɓoyayyiyar
manufa, ba kasafai akan gane da wanda ake ba.”
Garba, (1998: 18) cewa ya yi: “Habaici
magana ce mai ɗaci da
Bahaushe ke faɗa a
sakaye domin ya sanya dabi’ar gyara kayanka a wanda ba ya zama sauke mu raba.”
Zaruk da wasu (2005: 47-48) cewa suka
yi: “Idan aka ce habaici ko gugar zana duk ana nufin abu ɗaya ne.
Habaici shi ne yi da mutum a kaikaice. Habaici ya fi yawa inda kishi yake ko ƙyashi.
Galibi mutane suna ɗauka cewa habaici salon mata ne, dalili
kuwa shi ne a tsakanin mata kishi da gasa da ganin ƙyashi
suka fi yawa. Duk da haka za a iya cewa habaici ana samun sa a mata ana kuma
samun sa a maza. Wasu maza idan suna gaba ko ta sana’a ko ta wani abu na cigaba
sukan yi wa juna habaici.
Dunfawa, (2005: 20) cewa ya yi:
‘Habaici na nufin faɗa wa wani ko wasu aibin wani abu da suka
yi, ko suke yi a fakaice ba tare da ambaton suna ko siffanta wanda ake yi wa ba
wato ta yadda za ta sa a gane shi.”
Ƙamusun
Hausa, (2006: 187) cewa ya yi: “Habaici na nufin suka mutum a fakaice ta hanyar
magana.”
Yahaya,
da wasu (2006: 42) cewa suka yi: “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a
fakaice don muzanta mutum. Shi ma zance ne na hikima da ake amfani da shi a yi
da mutum a kaikaice. A wajen yin habaici ba a kan fito fili a bayyana wanda ake
nufi ƙuru-ƙuru ba,
sai dai akan yi amfani da wasu kalmomin sakaya kamar wanga ko wagga ko su wane
da makamantansu.”
Ɗanhausa,
(2012: 13) cewa ya yi: “Habaici magana ce da ake yi cikin hikima da nufin gaya
wa wani saƙo amma ba kai tsaye ba, a fakaice wato a ɓoyayyar
manufa. Akan yi magana da nufin wani abu da ake yi domin shi, amma shi habaici
idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai yake gane wanda aka yi habaicin
domin shi ba.”
Yahya, da wasu (2015: 75) cewa suka
yi: “Habaici yana nufin magana ce mai ɗaci da Bahaushe ke
faɗa wa ɗan
uwansu a sakaye domin ya sanya shi ya gyara wani mummunan halinsa ko kuma domin
faɗakarwa
ga ‘yan uwa kowa ya shiga taitayinsa ko kuma kawai don ba da haushi.”
Yahya da wasu (2016: 218) cewa suka
yi: “Habaici wani nau’i ne na zancen hikima da ake amfani da shi a yi da mutum
a fakaice don ɓata wa
wani mutum rai ko yi masa ƙaimi da
kuzari ko yi masa faɗakarwa, ba tare da bayyana mutumin da ake
nufi ƙuru-ƙuru ba,
amma shi wanda ake nufi wani lokaci zai gane, sai dai sauran jama’a da wuya su
fahimta idan ba wanda ya san abin da ake ciki ba.”
Ta la’akari da ma’anonin da malamai
masana da manazarta suka bayar, a tawa fahimta ana iya cewa: Habaici suka ce da
ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban
sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai
ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya
san abin da ke faruwa.
4.3 Ire-iren Habaici
A Hausa akwai ire-iren habaici kamar
haka:
1.
Habaicin hannunka-mai-sanda
2.
Habaicin gugar zana
3.
Habaicin zagi a kasuwa
4.
Habaici mai karin magana
4.3.1 Habaicin Hannunka-mai-sanda
Habaici ne da ake yi domin jawo
hankalin wani mutum ko nuni kan wani abu da ake so ya lura da shi ko ya gyara
ko kuma don a sa mutum ya kama kansa. Misali, a waƙar Ɗanba’u
ta D.P.N. inda yake cewa:
Jagora: Ina
horon wane,
Kullum ya kauce ya ƙiya,
Wane ka bar neman shiga,
In ‘yan taron daba,
Yara: siyasar ‘yan gurguzu,
Ai siyasar ƙeta ce.
A
wani ɗan waƙar
kuma cewa ya yi:
Jagora: Ina jin
tsoron mutum,
Mai buƙatar gardama,
Ban so haka nan ba,
Wallahi Allah ya sani,
Ina kallon wane ya kama daji
Yara: Wane dawo ga hanya,
Inda kowa ka murna ya hi kyau.
Gindi: D.P.N. ta
yi daidai,
Da ‘yan Nijeirya,
Alheri yanzu kowa,
Buƙatatai
yake.
4.3.2 Habaicin Gugar Zana
Habaici ne da ya shafi gugar zana.
Akan yi shi ne a kaikaice ba tare da fitowa ƙuru-ƙuru
ba, ta hanyar faɗin wasu daga cikin ɗabi’un
ko halayen mutum ko kuma a yi masa ƙage.
Misali a waƙar Alhaji Musa Ɗanba’u
ta D.P.N. inda yake cewa:
Jagora: Mu ba
duba mukai ba,
Kuma ba tsafi mukai ba,
Roƙon Allah mukai,
D.P.N. dai ta hau,
Yara: Mazanmu da matanmu,
Kowa ya zauna lahiya.
A
nazarin waƙa, duk inda aka sami irin wannan magana
akwai wanda ko waɗanda suke yin abin. Kenan ma’ana masu duba
da tsafi. ‘Yan jam’iyar da ke adawa da D.P.N.
A wani ɗan waƙa
suke cewa:
Yaro: Mi ar ranak kilinge,
Ga harka duniya,
Ko ga shi cikin gida,
Yara: Kyalla
shurewa takai,
Jagora:
Yanzu ko ga shi cikin gida,
Yara: Kyalla shurewa takai.
Gindi: D.P.N. ta
yi daidai,
Da ‘yan Najeriya,
Alheri yanzu kowa,
Buƙatatai
yake.
4.3.3 Habaicin Zagi a Kasuwa
Habaici ne wanda ake yi ta hanyar jefa
magana kai tsaye ba tare da nuna wanda ake da shi ba, sai dai kowa zai rasa da wanda
ake nufi. Amma a mafi yawan lokuta mai yin habaicin ya san da wanda yake. Shi
ne Bahaushe ke cewa: “Kowa ya yi zagi a kasuwa, ya san da wanda yake.” Misali a
cikin waƙar Ɗanba’u
ta PDP akwai inda yake cewa:
Jagora: “Yan
siysa,
Ku yi hakƙuri,
Da Musa Ɗanba’u,
Kun san ku nawa ne,
Sannan ni naku ne,
Ko da kun ƙi ni,
Mai kama ta kuka so,
In kuka ƙi ni da
ɗa,
Yara: Kun ganan da jika da goya.
Gindin Waƙa:
Ya ‘yan Nijeriya,
Siyasa ta tashi,
Ku dawo mu yi ƙoƙari,
Mu koma P.D.P.
4.3.4 Habaici Mai Karin Magana
Habaici ne wanda ake yi cikin sigar
karin magana. Ma’ana ana amfani da karin magana wajen bayyana manufar da ake
son a bayyana. Misali:
Cin ɗanƙo
har da su kaza.
Wani
misali a cikin waƙar Ɗanba’u
inda yake cewa:
Jagora: Na gaya ma
mutane,
Ɗauke dahi sai giwa,
Maza tahi kauce zomo,
Yara: Ba ka iya wa kai nan?
Gindin Waƙar:
Ƙara shirawa,
Aliyu zaɓaɓɓen gwamna,
Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,
Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.
A wata
waƙa kuma yake cewa:
Jagora:
Wane bai da kirki sam-sam-sam,
Ya gama da dum masu biya tai,
Yanzu babu mai kuɗi sai shi,
Na ce Allah na gode ma,
Yara: Da na san bari ba shegiya ba ce.
Gindin waƙa:
P.D.P. hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarfi da
martaba.
4.4 Dalilin Yin Habaici
Akwai dalilai da dama da ke sa a yi
habaici daga ciki akwai:
1.
Bayyana hasada
2.
Huce haushi
3.
Rowa
4.
Tsokanar faɗa
5.
Gargaɗi da
hannunka-mai-sanda
6.
Ramuwar gayya
7.
Kishi ko rashin jituwa (Yahaya da wasu
2006: 43).
4.5 Amfanin Habaici
Duk da kasancewar habaici suka ce da
ake yi a kaikaice ta hanyar cin zarafi amma kuma, yana da amfani matuƙa.
Daga cikin amfaninsa akwai:
1.
Habaici wata taska ce ta adana adabin
Bahaushe.
2.
Habaici wani ado ne na harshe da ke ƙawata
waƙa tare da ƙara
mata armashi, da kuma zantukan yau da kullum.
3.
Habaici na faɗakar da
mutum ta hanyar sanin miyagun ɗabi’u ko ƙazafi
ko wani abin da jama’a ke zargin sa da shi.
4.
Habaici na sa mutum ya daina wasu miyagun ɗabi’u
ko halaye.
5.
Habaici kan taimaka wajen ƙara
soke abokin hamayya.
6.
Habaici na samar da nishaɗi da
raha a cikin zukatan jama’a.
7.
Ƙwarewa
wajen gina habaici a cikin waƙoƙi
musamman na sarauta ko siyasa na ƙara wa
makaɗi ɗaukaka
da farin jini ga jama’a.
8.
Habaici na hana yin shisshigi watau mutum
ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.
9.
Ƙwarewa
wajen gina habaici na sa makaɗi ko maroƙi ya
samu alheri.
10. Amfani
da habaici a cikin waƙoƙi
da zantuka na yau da kullum a cikin harshe yana ƙara bunƙasa
harshe.
4.6 Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai
A sama an kawo ma’anar habaici da
ire-irensa da dalilan da ke sa a yi shi tare da bayyana amfaninsa. A nan kuma
za a yi sharhin habaici a cikin wasu waƙoƙin
Alahaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.
Kamar yadda Yahya da wasu (2016: 218)
ke cewa: “Habaici wani nau’i ne na zancen hikima da ake amfani da shi a yi da
mutum a fakaice don ɓata wa wani mutum rai ko yi masa faɗakarwa
ba tare da bayyana mutumin da ake nufi ba, wani lokaci zai gane sai dai sauran
jama’a da wuya su fahimta, in ba wanda ya san abin da ake ciki ba.”
Za a ga irin waɗannan
bayanan da Yahya da wasu (2016: 218) suka yi a cikin littafinsu mai suna Alun Nan Dai kan habaici a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.
A waƙar
jam’iyar P.D.P. mai taken:
Ya ‘yan Nijeriya,
Siyasa ta tashi,
Ku dawo mu yi ƙoƙari,
Mu
koma P.D.P.
A cikin wannan waƙar
Ɗanba’u ya yi habaici a wurare da dama a
cikin ɗiyan waƙa
kamar haka:
Jagora: Na yi
mamaki wane,
Don siyasa ta ƙare,
Shi muddin yag ganan,
Ya canza man huska,
Ga siyasa ta dawo,
Ga mu mu ko mun dawo,
An ce a haɗe,
Ba mu buƙata Ɗanba’u,
Kowa ya tsaya wurinsa,
A buga a gani,
Yara: A gane wa zai rinjaye.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa habaici ta hanyar wani abin da ya faru tsakaninsu, bayan wucewar siyasa
da cewa, duk lokacin da ya gan shi ya canza mai fuska, yanzu kuma siyasa ta
dawo, ya kira su ya ce a haɗe, shi ne yake ba shi amsa cewa
kowa ya tsaya wurinsa a buga a gani a gane wa zai yi rinjaye. A nan ya kira shi
da wane ba wanda zai haƙiƙance
cewa ga wanda yake nufi, amma shi wanda ake wa ya sani, da kuma wanda ya san
abin da ke tsakaninsu.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: ‘Yan
siyasa,
Ku yi hanƙuri,
Musa Ɗanba’u,
Kun san ku nawa ne,
Sannan ni naku ne,
Ko da kun ƙi ni mai kamata
kuka so,
In kuka ƙi ni da
ɗa,
Yara: Kun ganan da jika na goye.
Bayan kammala ɗan waƙar
sai Ɗanba’u ya ce: “Abin daga Allah ne.”
A wannan
ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici
waɗanda ke
jin haushinsa cewa su yi haƙuri da
shi domin ko da sun ƙi shi mai kama tai
suka so, in suka ƙi shi da ɗa, sun
gan shi da jika ya goya. Ma’ana da su so shi da kar su so shi ba abin da za su
iya yi masa. Haka kuma duk abin da za su ba shi ya sami fiye da haka, don haka
babu yadda za su yi da shi.
A wani ɗan waƙa
yeke cewa:
Jagora: Raƙumi
na tafiya,
Ɗauke da
kayanai,
Ya isko kunama yat taka,
Naj ji ya buga ihu,
Ƙasa
akwai shaggu,
‘Yar abig ga ‘yar tcito,
Ga shi yanzu ta halban,
Yara:
Har na gaza ɗaukar
kayan nan.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa habaici ta hanyar kwatance. Inda ya kwatanta wani babban ɗan
siyasa da raƙumi, da wani ƙaramin ɗan
siyasa a matsayin kunama. Inda yake nuna wani babban ɗan
siyasa ya faɗa wa
wani ƙaramin ɗan
siyasa, ƙaramin ya samu gagarumar nasara a kan
babban ɗan
siyasan. Shi ne yake cewa raƙumi na
tafiya ɗauke da
kayanai, ya isko kunama ya taka, sai nij ji ya buga ihu ya ce ƙasa
akwai shaggu, ‘yar abig ga ‘yar tcito ga shi yanzu ta halban har na gaza ɗaukar
kayan nan. A nan za a ga abin a dunƙule
yake ba kowa zai iya fahimtar wanda ake nufi ba.
Haka
kuma a cikin wata waƙar P.D.P. mai
taken:
P.D.P. hasken
Nijeriya,
Fati
mai ƙarfi da martaba.
A
wannan waƙar Ɗanba’u
ya yi habaici a ɗiyan waƙa
daban-daban kamar haka:
Jagora: Kai ji wane
yai tahiyar kura,
Yana gaba ya koma baya,
Inda yan nuhwa ba a karɓai ba,
Ya dawo bai ishe kowa ba.
Yay yi shiru yar riƙe
baki,
Nac ce duk mai koraj jama’a,
Yara:
Sai ya biɗi mai
ba shi shawara.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani ɗan
siyasa habaici ta hanyar kiran sa da wane yai tahiyar kura yana gaba ya koma
baya inda ya nufa ba a ɗaukai ba ya dawo bai ishe kowa ba.
Ma’ana yana cikin jam’iyatai, ya fita ya koma wata jam’iya. Jam’iyar da ya koma
ba su karɓe shi
ba, ya dawo jam’iyyarsa ta farko suka ƙi karɓar sa.
Wai sai ya yi shiru ya riƙe baki
yana mamaki, sai yake cewa: “Kowa ke korar jama’a, sai ya biɗi mai
ba shi shawara.” Ma’ana duk mai wulaƙanta
jama’a sai ya neme su, domin da yana da abokan shawara da haka ba ta faru ba.
Nan canza jam’iyya zuwa wata jam’iya ga ‘yan siyasa abu ne wanda ya zama ruwan
dare. Don haka zai yi wuya a gane wanda ake nufi kai tsaye, sai waɗanda
suka san abin tun farko.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Mai ƙarƙarin
hawan icen kwakwa,
Idan ka hwaɗo ka ƙalle,
Kai cikin dubu nika tona ka,
Yara:
Baƙar magana wadda kai muna.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani ɗan
siyasa habaici da cewa mai ƙarƙarin hawan iccen kwakwa, ma’ana mai son shiga
jam’iya mai alamar kwakwa. Idan ka hwaɗo ka ƙalle.
Ma’ana idan ya shiga jam’iyar, aka yi zaɓe suka
faɗi. Kai
cikin dubu nika tona ka, ma’ana cikin taron jama’a za su tona mai asiri. Baƙar
magana wadda kai muna. A nan ke nan akwai wata shawara da suka ba shi ya ƙi
ji har ya yi musu baƙar magna. Shi ne
yake yin ƙarin bayani domin wanda suka yi haka ya
san da shi ake amma wani ba zai fahimci da wanda ake ba.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Ku ji
kyanwa mai saurin tafiya,
Ƙarƙarin
takai dai ta ci kifi,
Dur radda ƙaya tal
laƙe miki,
Yau kowa bai tagaza miki,
Sai dai ki mace ‘yar damƙon
uwa,
Yara:
Don mun kula ɓarnarki
tai yawa.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani ɗan
siyasa habaici a kaikaice ta hanyar ɓoye sunansa ya
kira shi da kyanwa mai saurin tafiya, ƙarƙarin
takai ta ci kifi. Ma’ana wani ɗan siyasa ne ke ƙoƙarin
shiga wata jam’iya ko kuma tsayawa takara a wata jam’iya. Duk rad da ƙaya
ta laƙe miki yau kowa bai tagaza miki, ma’ana
dur randa aka yi zaɓe ya faɗi ko
suka faɗi ƙarya
tai ƙare domin kowa bai taimaka masa sai dai ya
mace, domin rashin kunyarsa ya yi yawa. A nan sai dai hasashe kawai ga mai
saurare amma ba za a iya cewa ga wanda ake nufi ba. Don haka habaici ya amsa
kirarinsa cewa habaici masu faɗa kowa amsa da shi ake.
A waƙar
Tanimu Ɗangaladiman Kyaɗawa mai
taken:
Dogo kana da
shirin Yaƙi,
Tanimun
na Alhaji Yakubu.
A
wannan waƙar Ɗanba’u
ya yi habaici a ɗiyan waƙa
daban-daban kamar haka:
Jagora: Ni
munahukin Gada na san shi,
Don baƙin
jininai ya yi yawa,
Ɗazu ya
wuce mu muna hira,
Sai nij ji yara suna ihu,
Wada nij ji ana karɗa-karɗa,
Nac ce gudun ga na aura ne,
Yara: Shi bai yawo
a cikin Gada,
Kuma bai shiri da maƙwabtansa.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum habaici ta
hanyar gugar zana inda ya fito da wasu ‘yan halayensa a kaikaice ta yadda ba a
iya gane wanda ake nufi kai tsaye, sai ya danganta shi da yadda mutane ke gudun
munafuki da yadda kare ke samun barazana ga yara, idan sun haɗu. Don
haka shi munafuki za a ga ba a cika yarda da shi ba, kuma mutane ba su
ra’ayinsa.
A wani ɗan waƙa
suna cewa:
Yaro: Kowa da abin
da yake sauna,
Kowa da abin da yake tsoro,
Kusu kyanwa yaka jin tsoro,
Jagora/Yara: In ga
kura a cikin gari,
Aura ba za ya hitowa ba.
Jagora: A in ga
kura a cikin gari,
Aura ba za ya hitowa.
A wannan ɗan waƙa
sun yi wa wani ɗan siyasa habaici ta hanyar nasara da
gogansu ke samu ga wanda yake wa habaici cewa kowa da abin da yake tsoro kusu (ɓera)
kyanwa yaka tsoro. Aura (kare) kura yaka tsoro. Shi kuma wanda ake wa habaici,
Tanimun yake tsoro. A nan za a ga abin a ɓoye
yake ga mai sauraro ko karatu sai in an bayyana.
A waƙar
Matawallen Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ma ya yi habaici a cikin ta kamar
haka:
Jagora: Ko a
siyasa in ta tashi,
Mai jama’a shi ne aka zaɓe,
Kai wane kar ka fito a gane ka,
Baƙin
jininka kare ya ɓaci,
Yara: Ko da ka je
ka buga fosta,
Ko a gida wani ba ya laƙa
ta.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa wanda ke son ya yi takara habaici cewa ko a siyasa in ta tashi mai
jama’a shi ne aka zaɓe, kai wane kar ka fito a gane ka.
Ma’ana ko ya fito ba a zaɓen sa domin ba ya da jama’a saboda
baƙin jinin da yake da shi, kamar yadda kare
ke da baƙin jini ga yara. Don haka ya ji yana
maganar zai buga fosta to ko ya je ya buga fosta ko a gida mutane ba su laƙa
ta. A nan ya kira shi da wane kuma masu son su fito takara suna da yawa
don haka zai yi wuya a gane wanda ake nufi.
A wani ɗan waƙar
makaɗin ya ƙara
da cewa:
Jagora: Abin da
duk kura ka buƙata,
Ba haka sarkin fawa ka so ba,
Kura kwaɗanki
har ya ɓaci,
Ita dai kullum ta ci nama,
Yara: Dur randa ta
shiga ba daidai ba,
Sai ta sha kashi ga mutane.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani habaici a kaikaice ta
hanyar amfani da sunan sarkin fawa da kura da cewa abin da duk kura ka buƙata
ba haka sarkin fawa ka so ba. A nan za a iya cewa maigida ne da yaronsa.
Maigida shi ne sarkin fawa, yaron shi ne kura. Shi sarkin fawa duk lokacin da da
ya yi yanka yana son ya sayar ya sami riba, ita kuma kura biɗa takai
ta mamaye sarkin fawa. Ma’ana shi maigidan yana hasashen hanyar da za a bi a
sami nasara, shi kuma yaron zagon ƙasa
yake wa maigidan saboda kwaɗayin samun abin duniya har yake son
ya zalunci maigidan. Du randa ta shiga ba daidai ba sai ya sha kashi ga mutane.
Ma’ana duk randa ya kuskura maigidan ya gane sai ya ci kwakwarsa ɗanya.
A waƙar
Attahiru Bafarawa mai taken:
Kada ka ji tsoron
maza,
Riƙa
zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa
Attahiru.
A
wannan waƙar akwai habaici a ciki inda yake cewa:
Jagora: Ga ɗammanin
Haji Ɗanba’u,
Idan an je a wurin buki,
Idan masu kuɗi sun
haɗu,
To da sun je kyauta sukai,
Wani mai kuɗi ya
barkace,
Yara:
Rabon guraye yakai.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum mai kuɗi
habaici ta hanyar gugar zana da wani halin rowa da cewa ga ɗammanin
Haji Ɗanba’u idan an je wurin buki, idan masu kuɗi sun
haɗu da
sun zo kyauta sukai, wani mai kuɗi ya barkace rabon guraye yakai.
Ma’ana rowa gare shi bai iya kyauta amma gaba yake wurin rabon abinci. A nan
wanda ake wa habaicin ya san da shi ake. Haka kuma duk wanda ya je wurin bikin
ya ga lokacin da mai kuɗin ke rabon abinci zai fahimci da
wanda ake. A nan ma’anar da Yahya da wasu (2016: 218) cikin Alun Nan Dai suka bayyana a sama ta fito
fili.
A wani ɗan waƙa
ya ce:
Jagora: Bafarawa
Attahiru,
Ga mota za ya ban,
Katan keke ya hana.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum wanda ya hana a
ba shi kyautar mota habaici da cewa Bafarawa ga mota za ya ban kata keke ya
hana. A nan wanda ya hana Bafarawa ya ba shi mota ya san da shi ake kuma
Bafarawa ya san da wanda ake domin ya san abin da ya faru, amma kuma wanda bai
san abin da ke faruwa ba, ba zai gane ba.
A waƙar
jam’iyar D.P.N. mai taken:
D.P.N. ta yi
daidai da,
‘Yan Nijeriya,
Alheri yanzu kowa,
Buƙatatai
yake.
A wannan waƙa Ɗanba’u
ya baje kolinsa wajen habaici a cikin ɗiyan waƙa
da dama kamar haka:
Jagora: Mu ba duba
mukai ba,
Kuma ba tsahi mukai ba,
Roƙon
Allah muke,
D.P.N.
dai ta hau,
Yara: Mazanmu da
matanmu,
Kowa ya zauna tahiya.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici.
Irin wannan habaici da ya zo a cikin wannan ɗan waƙa
shi ake kira habaicin zagi a kasuwa. A nazarin waƙa duk
inda aka samu irin wannan magana akwai wanda ko waɗanda
suke yi abin ke nan ma’ana masu duba da tsafi. Su roƙon
Allah sukai, su kuma ‘yan wata jam’iya su ke duba da tsafi amma dai ba su ce
musu suna yi ba, shi ya sa ake wa habaici kirari da maso faɗa kowa
tamkar da shi ake.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Ni mamaki
nake,
Mai duba shi da boka siyasa guda akai,
Mai duba ya buga yace su za su ci,
Boka ya yi tsahi da ‘yan kaji bakwai,
Kuma Allah yai hani tona sirinai aji,
Yara:
To du a gama ta sai sun yi kunya duniya.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wasu ‘yan siyasa habaici a
kaikaice ta hanyar gugar zana inda ya ɗan ƙyafato
wasu ɓoyayyun
halayensu waɗanda ba
su fito fili jama’a suka sani ba, na duba da tsafi, domin Ɗanba’u
da kansa a cikin layi na biyar a cikin wanann ɗan waƙar
cewa ya yi: “Kuma Allah yai hani tona sirinai a ji.” Sai yara suka cika da
cewa: “To du a gama ta sai sun yi kunya duniya.” Ma’ana ba kowa ya san suna
tsafi ba amma duk a gama ta sai asirinsu ya tonu.
A wasu ɗiyan waƙa
ya ƙara da cewa:
Jagora: Ina horon
wane,
Kullun ya kauce ya ƙiya,
Wane ka bar neman shiga,
Inda ‘yan taron daba,
Yara: Siyasar ‘yan
gurguzu,
Ai siyasar ƙeta ce.
Jagora: Ina jin
tsoron mutum,
Mai buƙatar
gardama,
Ban so haka nan ba,
Wallahi Allah ya sani,
Ina kallo wane ya kama daji,
Yara: Wane dawo ga
hanya,
Inda kowa ka murna ya hi kyau.
Jagora: Mutane ku
yi hankali,
Da sarkin ɓanna
kare,
Yana iya canye awakinku,
In ta zaburo,
Yara: Ya ko runtce
ido,
Ya dawo ya ce ba shi ba ne.
A irin wannan habaici da ya zo a cikin
ɗiyan waƙar
da suka gabata a sama shi ake kira habaicin hannunka-mai-sanda. Habaicin
hannunka-mai-sanda habaici ne da ake yi domin jawo hankalin wani ko nuni a kan
wani abin da ake so ya lura da shi ko ya gyara ko kuma don a sa mutum ya kama
kansa. Za a ga ɗiyan waƙar uku
da suka gabata dun hannunka-mai-sanda ne ake yi.
A ɗan waƙa
na farko yana yi wa wani mutum habaici ta hanyar yi masa hannunka-mai-sanda
inda ya ambaci kalmar horo kai tsaye cewa ina horon wane kullun ya kauce ya ƙiya. Ma’ana yana hana shi shiga abin da bai da
amfani ya ƙi, ya ƙara da
cewa wane ka bar neman shiga inda ‘yan taron daba, siysar ‘yan gurguzu
ai siyasar ƙeta ce. A nan ɗan waƙar
ya fito da gargaɗi fili ba sai an yi dogon bayani ba.
A ɗan waƙa
na biyu shi ma yana jawo hankalin wanda ake wa habaici ta hanyar bayyana damuwa
game da wanda ake faɗa wa gaskiya amma yana gardama. To ga shi
an nuna masa hanyar gaskiya ya kauce mata, ya kama hanyar ƙarya.
Duk da cewa ya kama hanyar da ba ta ƙwarai
ba. ma’ana ya shiga jam’iyyar da ba D.P.N. ba, saboda soyayya da yake masa ya ƙara
kiran sa da cewa wane dawo ga hanya inda kowa ka murna ya fi kyau.
Ma’ana jam’iyar D.P.N.
Shi ma ɗan waƙa
na uku gargɗi ne
yake yi ta hanyar habaicin hannunka-mai-sanda da cewa mutane su yi hankali da
sarkin ɓarna
kare. A nan yana kira ne ga mutane kaikaice su yi hankali da wani mutum wanda
ya kira kare domin bai da amana, ana iya ba shi hakkensu ya cinye.
A waɗannan ɗiyan waƙar
da suka gabata, za a ga abin a dunƙule ba
za a iya cewa ga wanda ake nufi ba.
A wani ɗan waƙa
ya ce:
Jagora: Baƙin
kwaɗayin
wane,
Ya kai shi ɗaukar
arkane,
Yara: Ga jirgin
Makka,
Ya taka motar Ɗandume.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani habaici ta hanyar gugar zana ya kawo wani halinsa na kwaɗayi,
sai ya kira shi da wane ta yadda ba za a iya gane wanda ake nufi ba kai tsaye.
A wani ɗan waƙa
ya ƙara da cewa:
Jagora: Na san
kissa kare,
Ɗauke ƙahwa
da ya yi,
Ba ciyo ne takai ba,
Yara: Tsoro yaka
yi,
A korai da manyan dutsuna.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum habaici a
kaikaice ta hanyar kwatance inda ya kwatanta abin da kare ta hanyar kissa da
cewa, na san kissa kare ɗauke ƙafar da
ya yi ba ciyo ne takai ba. ma’ana wani mutum ne ya bar zuwa wajen da suke zama.
Shi ne ɗauke ƙafar
da ya yi. Me ya sa ya bar zuwa wurin, sai ya ce: “Saboda bai da lafiya.” Shi ne
yake cewa ba ciyo ne takai ba, ma’ana ƙarya
yakai lafiyarsa lau. Dalilin da ya sa ya bar zuwa wurin shi ne yake cewa:
“Tsoro yaka yi a korai da manyan dutsuna.” Ma’ana kada a yi masa wulaƙanci.
A nan za a ga abin a dunƙule ba
za a iya bayyana wanda ake nufi ba.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: In tafiya
tai tsawo,
Kai amali ka tsarsuwa,
Jaki sarkin kuɗa,
Yara: Duk yada ka
so ya kai,
Inda zango bai zuwa.
A wannan ɗan waƙa
Ɗanba’u ya yi wa wani habaici ta hanyar
kasawa a kan neman wata buƙata sai
ya kwatanta abin da raƙumi da
jaki da nuna cewa idan tafiya ta yi tsawo sai amali. Ma’ana raƙumi
yana iya tafiya daga ƙasa
zuwa wata ƙasa amma jaki bai iyawa. Shi ne Ɗanba’u
ke kwatanta tafiya wasu ‘yan siyasa da nuna gwarzonsa shi ne amale. Shi ke iya
wa tafiyar shi kuma wancan abokin adawa shi ne jaki duk yadda ake so yakai wani
wurin ba zai iya ba.
A wani ɗan waƙa
kuma yake cewa:
Jagora: Ni na san
ungulu,
Kolo rage taƙama,
Taƙamar
banza shi kai,
Yara: Yana iya
tahiya,
Da ya iske mushe yai ta ci.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa habaici ta hanyar ɓoye sunansa ya kira shi da ungulu
(kolo) kuma ya ɗan zoji wata ɗabi’arsa
ta taƙama da cewa taƙamar
banza ce tunda yana tafiya ya iske mushe ya sauka ya yi ta ci. Ma’anar mushe
shi ne cin haƙin mutum ba da son ransa ba, don haka taƙamarsa
ta banza ce tunda azzalumi ne.
A wani ɗan waƙa
suke cewa:
Yaro: Mi ar ranar
kilinge,
Ga harkad duniya,
Ko ga shi cikin gida,
Yara: Kyalla
shurewa takai,
Jagora: Yanzu ko
ga shi cikin gida,
Yara:
Kyalla shurewa takai.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa habaici a kaikaice ta hanyar ɓoye sunansa ya yi
amfani da wani suna na daban wato kilinge da cewa mi ye ranar kilinge. Kilinge
na nufin wuƙa wadda ta sallace ma’ana marar kaifi
wadda ba ta iya yankan komai. Kyalla kuma na nufin babbar akuya lafiyayya. A
nan abin da yake nufi shi ne, miye ranar wannan mutumin da ya ɓoye
sunansa a cikin jam’iyyar siyasa tunda bai iya amfana mata komai.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Ni na san,
Maitatsine,
Wuyal lamari garai,
Don Allah dai mutane,
Ku bar yarda da shi,
Yara: Ko an yi
shiri da shi,
Watce tsarin nan yakai.
A wannan ɗan waƙar,
Ɗanba’u ya yi wa wani ɗan
siyasa habaici ta hanyar yi wa jama’a hannunka-mai-sanda game da shi, cewa su
bar yarda da shi domin ko an ƙulla
harka da shi ɓata
tsarin yake.
A waƙar
Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko mai taken:
Ɗantakarar
zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka ɗau
reni,
Kuma
kar ka ɗau wulaƙanci.
A wannan waƙar Ɗanba’u
ya yi habaici a cikin wasu ɗiyan waƙa,
kamar inda yake cewa:
Jagora: Ni na
tabbata kana da basira,
Na sani kana da tunani,
To amma fa ka ƙara
kulawa,
Angulu munahukin Allah ne,
Yara: In ka ganai
wurin yaƙi,
Shi ba da gaske ya zo ba.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani habaici ta hanyar yi wa ɗan takara
hannunka-mai-sanda cewa ya san yana da basira kuma ya san yana da tunani, to
amma fa ya ƙara kulawa, sai ya ɓoye suna,
sai ya kira shi da angulu munafukin Allah ne in ka ganai wurin yaƙi
shi ba da gaske ya zo ba. ma’ana duk yadda yake nuna goyon bayansa kada ya
amince masa. Ba da gaske yake ba.
A wani ɗan waƙa
kuma cewa ya yi:
Jagora: Ga
magatakarda ga Muntari,
To amma fa ku ƙara
kulawa,
In dai abin rabo ya samu,
A danƙa ma
masu imani,
Yara: Don kada a
bai wa kuraye shiya,
In sun haɗe shi
an huta.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wasu habaici ta hanyar
hannunka-mai-sanda ga ɗan takarar gwamna da mataimakinsa
da cewa su ƙara kulawa in dai abin rabo ya samu a damƙa
ma masu imani, ke nan waɗanda aka saba ba abin rabon suna
zalunci, a canza su idan kuma aka ci gaba da ba su ba za su yi adalci ba canye
shi za su yi. A nan za a ga an yi suka a kaikaice ta yadda ba za a iya gane da
wa ake ba.
A waƙar
Dr. Aliyu Magatakarda mai taken:
Maganin wargi ɗan
Garba,
Aliyu sabon gwamna
Sakwkato,
Ba
a kai ma reni ko kusa.
A wannan waƙar Ɗanba’u
ya yi habaici a cikin wasu ɗiyan waƙa kamar
haka:
Jagora: Ka ga mutum-mutumi
da kamar mutum,
Da ka ganai ka ga tsumma ne kurum,
Bai hana komai bai tare komai,
Ka yi shi don ya tsare ma gona,
Yara:
Bai hana tsuntsu ɓata ma ita.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani mutum habaici da cewa ka ga mutum mutumi da kamar mutum.
Mutum-mutumi na nufin karare ko itace da aka haɗawa, a
sa masa riga da hula a cikin gona matsayin mai tsaro musannan ga yara da
tsuntsaye. Ma’ana ga mutum cikakke da ka gan shi ka ga kamilin mutum wanda ke
iya yin abin kirki, amma bai iya komai ba, tsumma ne kawai, ma’ana girman ne
kawai, bai da wani amfani ga jama’a, da shi da mutum-mutumi duk ɗaya. To
in ka aje shi ne domin ya tsare ma gona, bai hana tsuntsu ɓata ma
ita ma’ana idan an aje shi domin ya magance wata matsala, to aikin banza aka yi
domin ba zai iya ba, kunya kawai za a ji. A nan za a ga abin a dunƙule
ba za a iya gane wanda ake nufi ba.
A wani ɗan waƙa
ya ƙara da cewa:
Jagora: Allah
waddan gurun kolo,
Da ɗai bai
saba kashin kunya ba,
Shi bai saba kashin kunya ba,
Ba ka sani sai ka je gaisai,
In ya yi ma kyauta ka duba,
Ka dubi girmanai ka ga kyauta,
Yara:
Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
yi wa wani babban mutum habaici ta hanyar raina kyautar da yake yi, da cewa
idan ya yi ma kyauta ka dubi kyautar ka dubi girmansa ka dubi kyautar abin
akwai kunya. A nan Ɗanba’u ya danganta
girmansa da gurun kolo. Kasancewar gurun kolo bai da amfani domin ba a
ra’ayinsa. Shi ma girmansa bai da amfani domin bai iya kyautata ma jama’a. Sai
dai ya yi abin a kaikaice ta yadda ba za a iya gane wanda ake nufi ba.
A waƙar
Alhaji Aliyu Magatakardan Wamakko mai taken:
Ƙara
shirawa
Aliyu zaɓaɓɓen
gwamna,
Mai ban tsoro
Magatakardan Wamakko,
Sarkin Yamman
Sakkwato bai san wargi ba.
A wannan
waƙar Ɗanba’u
ya gina habaici a ɗiyan waƙa
daban-daban kamar haka:
Jagora: Mun sani
Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,
Don kak ka bi shawarar buhun kowa,
Mai so a ƙi wa kowa komai,
Yara: Ɗan
Barade Alu,
Kai ta wa mutane adalci.
A wannan ɗan waƙar
makaɗin ya
jefi tsuntsu biyu da dutsi ɗaya ya yi wa wani mutum na tare da
gwamna habaici kuma, ya yi wa gwamna hannunka-mai-sanda da cewa Allah shi ka ba
da mulki kuma ya ba shi, kada ya bi shawara buhun kowa mai son a ƙi
wa kowa komai, ɗan Barade Alu kai ta wa mutane adalci. A
nan yana ƙara ba gawamna shawara cewa kada ya bi
shawara wani mutum da yake tare da shi mai rowa wanda ba ya son a yi alheri.
A wani ɗan waƙa
kuma yake cewa:
Jagora: In ka ji ƙi
gudu Ɗanba’u,
Sa gudu ne ab bai zo ba,
Ranaz zaɓenka ɗan
Barade na wamakko,
Waɗansu
maza hay Yamai suna ɓoyo,
Yara:
Kahin a yi zaɓe sun tcere.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wasu mutane habaici ta
hanyar tserewar da suka yi ranar zaɓe ganin cewa ba su
da nasara, kafin a gama zaɓe a ƙidaya (ƙirga)
sai suka tsere suka tafi Yamai a ƙasar
Nijar. Shi ne yake sukar su cewa duk wanda ya ce ba ya gudu to wanda ke sa gudu
ne bai zo ba, da mai sa gudu ya zo ma’ana ruwan ƙuri’ar
da suka ga ana yi wa Alu, sai ga shi sun tsere da kafafunsu sun bar ƙasa
sukutum saboda kunya da gudun wulaƙanci. A
nan waɗanda
ake wa habaici sun san da su ake, kuma duk wanda ya san lokacin da suka tsere
sun san da wanda ake amma wanda duk saurare kawai yake bai san abin da ke
faruwa ba, bai iya gane wanda ake wa habaicin.
A wasu ɗiyan waƙar
kuma ga abin da yake cewa:
Jagora: Na gaya ma
mutane ɗauke
dahi sai giwa,
Yara: Maza tahi
kauce zomo ba ka iyawa wa kai nan?
Yaro: Da ma hanƙurin
kwaram sai goga,
Wuyau ta sai ƙarfe,
Jure fari sai tofa,
Baba ruwa da kada ba a zuwa wanka,
Sai dai a tsaya kallo.
Jagora/yara: Wani
ya shiga zai wanka,
Da ya shiga bai kai wajje ba.
A waɗannan ɗiyan waƙar
suna jifar tsuntsu biyu da dutsi ɗaya suna gwarzanta gogansu suna
sukar abokin hamayyarsa kaikaice a kan kasawar da ya yi. Ɗauke
dafi sai giwa, gogansu ne giwa. Maza tafi kauce zomo, abokin hamayya ne zomo,
ba ka iya wa wa kai nan?
A ɗa na
biyu inda aka ce da ma hanƙurin
kwaram sai goga, gwarzonsa ke nan, jure fari sai tofa, ruwa da kada sai kallo
wani ya shiga zai wanka da ya shiga bai kai wajje ba. A nan duk habaici ne
kaikaice ake wa abokin hamayya na kasawar da ya yi.
A waƙar
Sardaunan Hamma’ali mai taken:
Sardaunan
Hamma’ali zaki,
Malami
Maigandi bi da arna.
A
wannan waƙar ma makaɗin ya
yi habaici a cikin ta inda yake cewa:
Jagora: Na sauka
kware don in ga ciyaman,
Na tahi ofis sai nig gaisai,
Sai ya ce a ba ni kuɗɗin mai,
Da ya ce a ba ni kuɗin mai,
Ni yi jira ba a miƙa
min ba,
Ni mamaki ya kama ni,
Ga rijiya ta ba da ruwanta,
Yara:
Sai guga ta hana a ɗebo.
Sai jagora ya ce: “Ke guga ‘yar baƙin
ciki,” a nan dai ya ba da bayanin abin da ya faru da kansa a ƙarshe
sai ya yi suka kaikaice rijiya ta ba da ruwanta sai guga ta hana a ɗebo.
Ma’ana ciyaman shi ne shugaba kuma shi ke da iko a kan komai na ƙaramar
hukumar, ya ce a ba shi kuɗin mai amma wanda an ka ce ya ba
shi ya hana. A nan ciyaman shi ne rijiya. Wanda aka ce ya ba shi kuɗi shi
ne guga.
A waƙar
Dr. Sama’ila Sambawa mai taken:
Yaro ya ja maka a ƙarya,
Ɗan
takarar Gwamnan Kebbi,
Dr.
Sama’ila Sambawa.
A cikin wannan waƙar
Ɗanba’u ya yi habaici a cikin wasu ɗiyan waƙar
kamar haka:
Jagora: Du ya da
aura ya kai ƙarhi,
Ba ya shiga ɗakin
kura,
Idan ba da bindiga ya zo ba,
Ko da da bindiga ya zo ma,
Kare ba ya i mata wa ash shi.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani habaici da cewa duk
yadda aura (kare) ya kai ƙarfi ba
ya shiga ramin kura. Ma’ana duk yadda wanda ake wa habaici yake ganin yana da ƙarfi,
to ya sani bai yi ƙarfin sambawa ba
in ba da bindga ya zo ba, ma’ana sai ya yi gagarumin shiri, kuma ko da ya yi
gagaruma shiri, ba ya iya wa da shi. Ma’ana wanda ake wa habaici duk yadda yake
ganin yana da jama’a to bai iyawa da Sambawa.
A wani ɗan waƙa
yake cewa:
Jagora: Wani ya ci
tuwonsa na shinkahwa,
Ya ɗauki
Pure water ya sha,
Sai ya gano bawan Allah,
Mai cin tuwon dussa kullum,
Ya ce ya hana masa dussatai,
Ku al’umma na tambaiku,
Shin wannan shi ne adalici?
Yara: Wannan ya yi
babban zalunci,
Ko ba a ce masa komai ba.
A wannan ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wani mutum habaici
kaikaice cewa wani ya ci tuwonsa na shinkafa ya ɗauki
pure water ya sha, ma’ana yana bisa babban aikinsa sai ya gano bawan Allah mai
cin tuwon dussa kullum. Ma’ana shi wanda ke bisa ƙaramin
aikin da ko cefane ba ya yi masa ya ce ya hana masa dussatai. Ma’ana ya kore
shi daga aiki. Ku al’umma na tambai ku shin wannan shi ne adalci? Sai ya ba da
amsa da kansa cewa wannan ya yi babban zalunci koba a ce masa komai ba. A nan
za a ga abin a dunƙule yake. A taƙaice
ambatar wani ke nuna habaici a cikin ɗan waƙar
domin ba a fayyace ba.
A waƙar
ciyaman ɗin
Gwadabawa Alhaji Musa Lumu mai taken:
Gwabron giwa
kullun yana halin yabo,
Alhaji Lumu Musa
ciyaman zarumi.
A
wannan waƙar Ɗanba’u
ya yi habaici inda yake cewa:
Jagora: Baƙar
akuya wance ke ad da ƙallallen
ƙaho,
Ban layya da ke kuma ba mu yin suna da
ke,
Yara: Mu ba mu
sayen ki bari masu yin tsahi su sai.
A wannan
ɗan waƙar
Ɗanba’u ya yi wa wata mace habaici ta
hanyar ɓoye
sunanta da cewa: “Baƙar akuya wance ke
ad da ƙallalen ƙaho ban
layya da ke kuma ba mu yin suna da ke mu ba sayen ki bari masu yin tsafi su
saye ma’ana ba su buƙatar ta a
jam’iyyarsu, domin halayyarta da ɗabi’unta kamar yadda ba a buƙatar
a yi layya da dabba mai ƙallalen
ƙaho kuma ba a yin suna da ita. Don haka
duk mai halayya irin tata ba a buƙatar ta
a siyasa. A nan yana da wuya a fahimci wadda yake nufi. Rashin gane waddea ake
nufi ya tabbatar da habaicin da ake bayani a kai.
4.7 Naɗewa
Wannan babi an yi bayanin habaici tun
daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-irenta, daga ra’ayoyin masana da
manazarta daban-daban tare da kawo dalilan da ke sa a yi habaici. Haka kuma an
bayyana muhimmanci/amfani da ake samu ta hanyoyinsa. A ƙarshe
an kawo sharhin habaici a cikin wasu waƙoƙin
Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ta hanyar fitowa da
abubuwan da masana suka bayyana a matsayin habaici. Haka kuma an yi nazarin
wasu waƙoƙinsa da
ke ɗauke da
habaici aka kawo misalai a wurare daban-daban.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.