Dandalin Tambayoyi da Amsoshi

An ƙirƙiri wannan shafi ne domin ɗalibai da masana da manazarta Hausa da ke makarantu daban-daban. Za ku iya amfani da wurin rubuta tsokaci (comment) da ke ƙasa domin duba tattaunawar da ta gaba ko tura sabon saƙo.

Manufar wannan kafa ita ce samar da haɗin kai da zamowa farfajiyar ƙaruwa da juna musamman ta hanyar turo tambayoyi, amsa tambayoyi, turo muhimman bayanai da suka shafi karatun Hausa da ilimummumukan zamani da zamantakewa, da makamantansu.

Za ku iya turo tambayoyi ko ku amsa tambayoyi da aka turo.

Mun gode.

Aji

Post a Comment

6 Comments

  1. Na ji daɗin ganin wannan zaure. Allah ya ƙara ɗaukaka harshen Hausa. Amin.

    ReplyDelete
  2. Tunani mai kyau.

    Allah ya albarkacin wannan dandali

    ReplyDelete
  3. Wannan dandali zai taimaka matuƙa wajen tattauna muhimman abubuwa da za su ciyar da harshen Hausa gaba. Allah Ya saka maka da alheri, amin.

    ReplyDelete
  4. Da kyau! Wai kare ya ga rawar kura.

    Madalla da wannan dandali mai albarka. Allah ya sa mu amfana.

    ReplyDelete
  5. Maasha Allah.
    Muna maraba da wannan dandali mai albarka wanda zai jagoranci wayar da kan ɗalibai da malamai da ma sauran masu nazari wajen warware zare da Abawa dangane da abin da ya shige wa al'umma duhu game da Harshenmu kuma abin Alfaharinmu don ganin ya ci gaba da ƙanshin ɗan goma. Allah Ya ƙaro basira kuma Ya yi mana jagora baki ɗaya. Amin.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.