Takardar Da Aka Gabatar Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, Ranar Alhamis, 30 Ga Satumba, 2021
AIWATARWA DA SADARWA A WAƘOƘIN
BAKA NA HAUSA
Na
SA’IDU
MUHAMMAD GUSAU
SASHEN
KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR
BAYERO, KANO-NIJERIYA
1.0
Gabatarwa
Yawancin waƙoƙin
baka na Hausa da ake yi sai an aiwatar da su domin su dace da saƙonnin da ake son isarwa a
cikin zubinsu[1].
Aiwatarwa da ake yi wa waƙar baka ta Hausa takan zamanto a zubin ƙwaƙwalwa da tunani na zuciya ne, sannan a
rera saƙonni
da ake son fitarwa, bisa rerawa ta zahiri. Tunani a ƙwaƙwalƙa da zuciya[2]
su suke ba makaɗi
dama ya ƙulla
batutuwa[3]
a sauwarce, ya tsara zirin tunaninsa a zuciya, kuma wani yanayi ya ba shi dama
ya furta shi a bayyane da ake kira sadawa
a ilimin waƙar
baka.
Sadarwa a waƙa ita ke bayyana furucin zuciya ko jumlolin baɗini a lokacin da aka rera waƙar baka a bainar jama’a. A al’ummar Hausawa ba a yin waƙar baka sai an sadar da ita.
Sadarwa ke nan ita take tabbatar da rerawar waƙar baka kuma ita take sa waƙar baka ta bayyana a zahiri
kowa da kowa ya iya sanin ta har kuma a dinga maimaita ta.
A wannan takarda an nufi aniyar yin magana ne a kan aiwatarwa
da kuma sadarwar waƙar baka ta Hausa. Za a duba aiwatarwa, sannan kuma a yi nazarin yadda ake
yin sadarwa ta waƙoƙin
baka na Hausa. sadarwa nan wajiba ce, idan ba a sadar da waƙar baka ba, to, ba a yi waƙar baka ba. Ashe kenan bayan
an yi tunani baɗini,
sannan, waƙar
baka za ta cika sai kuma a sadar da ita wato sai an rera ta, a kuma sadar da
ita ga jama’a, daɗa waƙar bakan nan ta gargajiya[4]
ce ko ta zamani[5].
2.0
Aiwatarwa[6]
A Ƙamusun Hausa-English na Awde Nicholas (1996) ya
nuna jumlar aiwatarwa tana nufin (1)
to go ahead with (2) to operate (3)to carry out; wato za a fassara waɗannan da (i) ci gaba da wani abu (ii)
sarrafa wani abu (iii) yin wani abu ko zartar da wani abu ko zartarwa (1996:3).
A littafin Hausa Metalange wato Ƙamus na keɓaɓɓun kalmomi (1990) an nuna kalmar aiwatarwa tana
nufin da ingilishi (1) Performance Class (2)
Grade word Class, akwai kuma Aiwatar
da harshe wadda aka fassara ta da Linguistic
Performance (1990, UPL Ibadan: 57; Edita Ɗalhatu Muhammad).
A fannin ilimin waƙar baka kuma, Gusau (2008) yana cewa: Aiwatarwa
hanya ce wadda ake bi a sarrafa waƙar baka, ko a yi ta (Gusau, 2008: 448 da Gusau, 2014, 5).
Kuma kalma ce wadda ake hankaltar da al’umma dangane da dabarun tafiyar da
rayuwa waɗanda za su ba da damar cim ma ganga mai
inganci (Funtua, A. I. da Gusau, S. M. 2011, 1).
2.1 Yin Waƙar Baka ko Sarrafa Waƙar Baka
A lokacin da makaɗi ya
zo yin waƙar
baka tun a ƙwaƙwalwarsa da tunaninsa yake
fara tsara ta. Wannan tsari shi ne na baɗini, wanda yake a rattaɓe a
zuciyarsa kuma a cikin jumlolinsa. To, tun daga wannan lokaci ne ya riga ya yi
waƙarsa
ta baka ta bin waɗannan
matakai:
-
Matakin Ƙullawa
-
Matakin Kiɗa
-
Matakin Rauji
-
Matakin Kalmomi
-
Gindin Waƙa
-
Layuka ko Saɗaru a Ɗiya
×
Nuna Farin Ciki
×
Nuna Baƙin Ciki
×
Faɗakarwa
×
Gargaɗi
×
Ilmantarwa
×
Nasihantarwa
×
Isharantarwa
×
Yabawa
×
Yin Zambo
×
Yin Habaici
×
Da Sauransu Kamar Kalmomin Azancin
Magana
2.1.1
Matakin Ƙullawa
Makaɗan baka sukan ƙulla waƙoƙinsu ta azanci da fasahar da
suke da su.
Ma’anar ƙulli ta ƙamus:
A ƙamus na Hausa-English (Awde, 1996: 102)
ya nuna Ƙulli shi ne (1) to knot (2)to plan (3) to conspire; wato (1)ya ƙulla (2) ya shirya ko ya yi
dabara (3) ya haɗa
kai. Shi kuma Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 285) cewa ya yi
ƙulla,
ita ce ɗaura ko ƙudura.
Ma’anar Ƙulli ko Ƙulla ko Ƙullawa ta isɗilahi wato ta fannin ilimin waƙar baka. Ita ce:
Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya faɗi yadda yake ƙulla waƙarsa a inda yake cewa:
Jagora: Ga makaɗi ya ƙulla waƙatai,
‘Y/Amshi: Sai a amsa mashi ba a ƙara mai,
Jagora: In naƙ ƙulla waƙa a ƙara man,
‘Y/Amshi: Mu haɗu duk
azanci gare mu,
: Shin a’a mutum guda za ya radde mu,
: Shirya kayan faɗa Maigida Tsahe,
: Ali ɗan Iro bai ɗauki
reni ba.
(Ɗanƙwairo, Waƙar ‘Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu II
(1960-1991)
Ƙullawa ta waƙoƙin makaɗan baka tana da matakai biyu. Akwai ƙullawa ta makaɗan ƙungiya,
sannan akwai ƙullawa
ta makaɗan kaɗaita. Ga su kamar haka:
i) Ƙullawar Makaɗan Ƙungiya
Waƙoƙin baka na Hausa waɗanda ake ƙullawa ta ƙungiya, waƙoƙi ne waɗanda ake tunaninsu ta tsakanin Jagora da kuma ‘yan amshinsa. Ita ƙungiya ita ce wadda ta ƙunshi Jagora da kuma yaransa
masu yi masa amshi na waƙar baka da kuma yin kiɗa.
Har wa yau, ƙungiya
ta ƙunshi
‘yan ma’abba ko sanƙirori ko masu kirarin baki. A wannan lokaci, za a haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin Jagora da ‘yan amshinsa, a
dinga tunanin yadda za a shirya waƙa, musamman ta kawo
jumloli da yadda za a tsara saɗaru ko layuka, sannan ana yi ana dakatawa
ko lumfasawa. Wannan shi ne ƙulla waƙa ta
makaɗan ƙungiya.
Su kuwa makaɗan kaɗaita, su ne waɗanda
Jagororinsu kawai za su dinga ƙulla kalmomi da jumloli, amma yaransu, za a sami waɗanda suke yin amshi wato +ciko kawai,
sai dai ba su yi musu kowane irin ƙari a waƙa. Akwai wasu jagororin da ba a ce musu ko ƙala, Jagora ne zai ƙulla waƙarsa kuma ya ƙare ta shi kaɗai. Irin wannan ƙulli jagora ne kawai zai yi tunanin waƙa a baɗininta idan ya gama ƙulla ta sai ya zo cikin
yaransa ya rera ko ya je wani wuri ya sadar da ita. A irin wannan waƙa, Jagora ne kawai ake jin
muryarsa yana rera waƙa, yana sadar da ita ga jama’a.
A bisa waɗannan matakai ne ake bi, ake ƙuƙƙulla, waƙoƙi na gargajiya ko waƙoƙi na zamani na baka da Hausawa suke yin
tunaninsu a baɗini, daga baya su rera su a yayin da
suke sadar da su.
2.1.2
Matakin Kiɗa
A Ƙamusun Hausa an nuna kiɗa yana nufin bugun ganga ko kalangu ko
abun bugawa ko bugun ƙwarya ko goge ko garaya ko taushi ko kotso da hannu ko da makaɗi ko da wani abu (CNHN, 2006: 243).
A ilimin fannin waƙar baka, kiɗa
yana nuni ne da wani amo ko sauti da ake samarwa ta gwama ko haɗa abubuwa biyu kamar dutsi + dutsi ko
tafi + tafi ko baki + ƙahon dabbobi ko ganga + gula (makaɗi) ko wani abu + wani abu ko sauransu. Kiɗa kuma yakan zama wani amo ne wanda yakan shiga jikin mai sauraro, ya sa
masa karsashi har ya dinga rausayawa, yana tattakawa ko jujjuyawa.
Gusau (2008: 54) yana ganin kiɗa shi ne wanzar da amo mai shiga jiki wanda kuma ake aiwatarwa ta haɗa abubuwa biyu ta matakin busawa ko
tafawa ko bugawa ko kaɗawa
ko gogawa ko girgizawa ko kuma wasun waɗannan.
Akwai kayayyakin kiɗa da
dama. Wasu na gargajiyar Hausawa ne, wasu kuma na baƙin wasu al’ummu ne waɗanda Hausawan suka aro, suna amfani da
su. A wajen Hausawa akwai kiɗa zallarsa kawai, ba tare da haɗawa da waƙa
ba, ko kirari ko kaɗa take.
Akwai kuma kiɗa ta amfani da kayan kiɗa wanda ake haɗawa da waƙa,
wanda kuma ake yi wa waƙoƙin
da makaɗan baka suke yi. Kiɗa a wajen Hausawa ya rarrabu zuwa:
A wajen aiwatarwa ta waƙar baka akan gwama ta da amon kiɗa wanda za su dinga tafiya a tare tsakanin muryar makaɗi da sautin gangar da makaɗin yake amfani da ita.
Bisa mahangar makaɗa,
akwai wasu hanyoyi da ake ɗora
kiɗa na waƙoƙinsu na baka domin su yi daidai da yadda
ake sadar da su. Waɗannan
hanyoyi sun haɗa da:
-
sadar da kiɗa daidai da nauyi na muryar makaɗi da kuma raujin da aka zaɓa wa matanin waƙa;
-
Dacewar amon kiɗa da gaɓoɓin murya bisa gurabunta na hawa da sauka da kuma faɗuwa;
-
Ƙarfafa madirar gaɓoɓi;
-
Wani bi a kaurara amon kiɗa;
-
Wani bi a sassauta amon kiɗa;
-
Wani bi a ja amon kiɗa;
-
Wani bi a matse ko a tauye
amon kiɗa;
-
Wani bi a ƙwairanta amon kiɗa;
Sannan kuma yanayin kiɗan
yana iya zama:
× Mai diri
× Mai ƙarfi
× Mai kauri
× Mai zaƙi
× Mai kumbura
× Mai kaurara
× da sauransu
2.1.3
Matakin Rauji
Ƙamus na Hausa a ɓangaren
Hausa-English (Awde, 1996: 131) ya bayyana kalmar rauji da clapping wato
yin tafi ko ban tafi (Awde, 1996, 131 & 210). A kuma littafin Ƙamus na Keɓaɓɓun kalmomi wato Hausa Metalanguage ya fassara Rauji da Ingilishi da Rhythems wato Kari
ko karin murya (Awde, 1996:361).
A fannin ilimin waƙar baka kuwa, rauji wani sauti
ko amo ne wanda yake tashi a sama ko ya sauka ko ya faɗi. Rauji yana iya zama murya ta wata halitta mai rai ko sautin wani abu
maras rai kamar ƙara ko doka ƙafafu a bisa ƙasa ko wani tsando ko sauti daga kukan tsuntsaye. Har wa yau kuma akwai rauji
mai ɗaɗi, mai zaƙi da
kuma rauji maras daɗi,
mai-ta-da-hankali, kamar kukan kanari (rauji mai zaƙi) da kuma kukan jaki (rauji maras zaƙi, mai ɗaukar hankali).
Wata ma’anar isɗilahi
kuma, rauji na iya zama masaukar murya a gaba.
A yayin da aka gwama rauji a waƙar baka ta Hausa ana ɗora shi bisa muryoyi na gaɓoɓi na kalmomi ne waɗanda akan sarƙa su a tayar da saɗara a ɗa na waƙa.
Rauji wanda aka zaɓa,
aka ɗora wa saɗara ko layi a ɗa na
farkon waƙa,
shi ne zai dinga daidaita rauji a dukkan layuka da ake ƙullawa a ɗiya na waƙar.
Nauyin rauji a waƙar baka ta Hausa gajere ne, shi
ya sa yake tafiya bisa gaɓoɓi na kalma gwargwadon hawansu da
saukarsu da faɗuwansu. Matakai waɗanda ake bi a wajen samar da rauji a waƙar baka ta Hausa sun haɗa da:
-
Rauji mai dogon zango
-
Rauji mai gajeren zango
-
Rauji mai matsakaicin zango
Sannan gaɓa ta rauji za ta iya zama mai nauyi
wadda za ta ƙunshi
[bww] ko [bwb], ko kuma ta zama mai sauƙi wadda za ta iya zama gaɓa mai [bw] kawai.
A wajen furta rauji na waƙar baka ana yi masa waɗannan
abubuwa kamar haka:
-
Kaurara gaɓa mai nauyi;
-
Jan gaɓa mai nauyi ko mai sauƙi;
-
Daidaita amsa-amon kari
(hawa ko sauka ko faɗuwa)
a ƙarshen
kowace saɗara ko layi.
Haka kuma ana yin rauji ne na waƙar baka daga karin murya (na
hawa da sauka da faɗuwa)
da kuma amon kiɗa
tun daga tunanin makaɗi a
zuciyarsa. Domin haka, ana samar wa waƙoƙin baka rauji ne ta waɗannan
hanyoyi:
×
Karin murya daga makaɗin waƙar;
×
Amon kiɗa daga kayan kiɗan da makaɗi
yake amfani da su, ta la’akari da madiransu na hawa da saukar amo ko kuma faɗuwarsa.
×
Daga nan sai a fitar mata da
raujinta;
×
Rauji zai samar wa waƙar baka wani amo wanda zai
fitar da ita kaɗai
daga sauran waƙoƙin baka na makaɗin.
2.1.4
Matakin Kalmomi
Kamar yadda aka nuna a baya, idan makaɗin baka ya tashi aiwatar da wata waƙa ta baka, yakan fara aiwatar da waƙar ne a cikin zuciyarsa da
kuma ƙwaƙwalwarsa tun kafin ya furta
waƙar a
waje. Haka kuma tunanin makaɗi na
kalmomi da yadda zai sarrafa su cikin azanci da hikima shi ne wani abu da zai biyo biyo baya a aiwatar da waƙar baka. Sannan kuma dukkan
makaɗi na ƙungiya da kuma makaɗi na ƙire duk suna yin aiwatarwa a wajen
daidaita waƙoƙinsu da tsawaita su. Matakin
kalmomi yakan bambanta dangane da kalmomi da makaɗi ya yi tunaninsu ko kuma ya zaɓo su wajen tsawaita waƙar da zai yi. Wasu daga cikin kalmomi da ake zaɓa a shirya waƙar baka sun haɗa
da:
2.1.4.1
Kalmomin Shirya Gindin Waƙa
Gindin waƙa
furuci ne na wasu kalmomi masu ma’ana masu nauyin saƙo, masu hikima da balaga da azanci waɗanda ake shiryawa don a gabatar da waƙar baka. Ta Gindin waƙa ne ake rarrabe ɗa da ɗa a waƙar
baka. Waƙoƙin baka sun kasu kashi biyu.
Akwai waɗanda ake yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Abdu Karen Gusau. Sannan kuma
akwai waƙoƙin da ba a yi wa Gindin Waƙa kamar waƙoƙin Alhaji Babangida Kakadawa. Ga Misali
na Gindin Waƙa:
G/Waƙa: A
lula ɗan haya,
: Mai gyaran kekuna.
(Abdu Karen Gusau; Waƙar Alhaji Alula Ɗanhayar Kekuna, Fagge, Kano)
Har wa yau kuma, Gindin waƙa yakan bayyana abin da waƙa take nufi tun kafin a shiga cikinta. Gindin waƙa wani ginshiƙi ne ko babban matangali na ginin waƙar baka. Wani kuma harsashe ne
ko majingini na farko a waƙar baka, inda duk bai zauna ba, waƙa ba za ta ba da sha’awa ba, balantana
har ta yi wani armashi. Idan makaɗi ya
sami zaunuwar Gindin waƙa, to, zai sami haske ya buɗu a
gare shi, ya sami walwala ta zaɓo
kalmomi waɗanda suka dace ya saka a waƙa waɗanda za su ba shi damar samun sauran ɗiyan waƙar.
Makaɗin baka yakan yi tunani a zuciyarsa idan
kuma wanda suke a ƙungiya ne sukan haɗa ƙarfi da azama su samo kalmomi zaunannu
kuma mafi girkuwa a waƙar da suke shiryawa ta baka su samar da Gindinta. A wajen shirya Gindin waƙa makaɗa sukan yi amfani da waɗannan matakai:
-
Yawanci Gindin waƙa bai shige layuka biyu (2)
zuwa huɗu (4) ba ;
-
Yakan ƙunshi kalmomi masu nauyi da
ake sarrafa su cikin azanci da hikima;
-
Gindin waƙa yakan ƙunshi sunan mai waƙa ko laƙabinsa ko alkunyarsa ko wata
ƙarina
da ke nuna Mai waƙa;
-
Sannan ana wakiltar Gindin
waƙa da
harafin [Ɗ] na
ABCD;
-
Ana kuma wakiltar adadin saɗaru ko layuka a Gindin waƙa da alkalumma na [1,2,3,4]
kamar haka: [Ɗ1] ko [Ɗ2] ko [Ɗ3]
ko [Ɗ4] da sauransu;
-
Ga misalai:
i) Gindin Waƙa; (mai layuka huɗu (4)
Ɗ1: Ka bawai maza,
Ɗ2: Na Magajin Gari
Bubakar,
Ɗ3: Kai ad da yanzu,
Ɗ4: Allah ya ba ka Sarkin Kabi.
(Mamman Inyaga Argungu; Wakar S/Kabi
Muhammadu Mera. Wato kalmomin nuna farin
ciki).
ii) Gindin Waƙa; (mai layuka biyu (2)
Ɗ1: Tankwafau namijin zaki,
Ɗ2: Sa’idu bai taɓa tsoro ba.
(Idi Ɗangiwa Zuru: Waƙar Sarkin Sudan Sa’idu, Kwantagora. Wato
kalmomin nuna farin ciki)
-
Yawancin kalmomi masu nauyin
ma’ana da hikimar zance da makaɗa
suke tsarawa a Gindin waƙa sun ƙunshi
na nuna farin ciki ko na nuna baƙin ciki. Misalin Gindin waƙa na kalmomin nuna baƙin ciki:
G/Waƙa: Ɗ1: Gagarabadon namiji
tsayayyen ɗan kasuwa
(Shata: waƙar ‘Gagarabadau, Mp3)
-
Kuma wani Gindin waƙar yakan ƙunshi kalmomin yabawa ko na
zambo ko na habaici da na zugugutawa da makamantansu. Misali:
G/Waƙa: Ɗ1: Ya ci maza ya kwan
yana shirye,
Ɗ2: Gamda’aren Sarki Tudu Alu.
(Narambaɗa, Waƙar
Tudu Alu; Kalmomin zuga da kururantawa da yabawa).
Akwai kuma a wani G/Waƙa:
Ɗ1: Madogara na Malam,
Ɗ2: Iro Uban Bawa,
Ɗ3: Maigida Shinkahi.
(Narambaɗa, Waƙar
Magajin Garin Shinkahi, Ibrahim; Kalmomin zuga da yabawa).
-
Haka kuma wani Gindin waƙar yakan ɗauki kalmomin faɗakarwa ko gargaɗi ko
ilimtarwa ko isharantarwa ko nasihantarwa da sauransu. Misali:
. G/Waƙa: Ɗ1 “Yan Nijeriya sai Hausa
(Abdu Karen Gusau; waƙar Harshen Hausa-kalmomin kishin Hausa da na gargaɗi da na ilimantarwa. Gusau, 2015: 64-75).
.G/Waƙa: Ɗ1 Mu kama sana’a ‘yan Nigeriya,
Ɗ2 Zaman banza ba namu ne ba.
(Abdu Karen Gusau, Waƙar Gargaɗi kan riƙo da sana’a – kalmomin gargaɗi da na faɗakarwa da na isharantarwa, Gusau, 2015: 75-78).
.G/Waƙa: Ɗ1 Shegiyar ƙafa ke kika saba da gulando,
Ɗ2 Ki tallafe ni, ɗaukar ni ƙafa kar ki gaza ni.
(Abdu Karan Gusau, Waƙar Shegiyar ƙafa – Kalmomin faɗakarwa da na gargaɗi da na isharantyarwa. Gusau, 2015:
96-97).
2.1.5
Layuka ko Saɗaru a Ɗiya
Layuka jam’i ne na layi (tilo). A Ƙamusun Hausa (CNHN, 2016 206-304)
an faɗi ma’anarsa kamar haka: (i) Miƙaƙƙen zane (ii) miƙaƙƙiyar hanya ta cikin gari, ko jerin
rumfunan kasuwa ko wani abu (iii)majalisar alƙalai ko kotu ko ɗakin shari’a. Amma kuma a ƙamus (Hausa-English) na Awde (1996:106) ya bayyana Layi (p/layuka) da harshen Inglishi da Line. A kuma ɓangaren
ƙamus
ɗin na English-Hausa, Awde (1996: 295) ya
fassara line da noun=n=: (1) layi (2) Baiti (3) Telephone line wato
waya. Ta Fuskar Saɗaru (Jam’i); saɗara (tilo) kuwa – Ƙamusun Hausa (CNHN, 2006: 381) ya fassara
ta da layi cikakke na rubutu.
A cikin layuka ne ko saɗaru
waƙar baka
take shirya saƙonni tun a ƙwaƙwalwa, sannan ta rera su, ta
sadar da su ga al’umma; ta amfani da mataki na kalmomi waɗanda suka haɗa da nau’o’i daban-dabam. Kuma har gami da kalmomi na maganganun habaici
da isharantarwa da gargaɗi da
ilimantarwa da tunasarwa da faɗakarwa
da makamantansu da yawa.
A waƙoƙin baka na Hausa akan shirya
layuka ko saɗaru masu sauƙi a ƙagi ɗa na waƙar
baka wanda zai ƙunshi saƙo ɗaya kawai. Akwai kuma layuka ko saɗaru da ake shiryawa masu tsauri, waɗanda za su haɗu su
tayar da ɗa ɗaya na waƙar
baka. Shi ɗa ɗaya mai tsauri yakan ƙunshi saƙonni
da yawan gaske kamar guɗa huɗu (4) ko ma fiye da haka waɗanda ake wakiltarsu kamar haka:
Ɗa ɗaya mai tsauri:
A1:
A2:
B1:
B2:
B3:
C1:
C2:
C3:
C4:
Da sauransu.
Za a ba da misali na ɗan
waƙa
mai sauƙi
(Mai saƙo guda ɗaya kawai) kamar haka:
A1: Ni kam lafiya nit taho
salla,
A2: Lafiya ni ishe Sarki,
Ɗ1:
Amadun Bubakar gwarzon Yari,
Ɗ2:
Dodo na Alƙali.
(Narambaɗa, waƙar Sarkin Gobir Ahmadu Bawa (1935-1975).
Shi kuma ɗan waƙa ɗaya mai tsauri (mai Saƙonni da yawa fiye da ɗaya), ga wani misali kamar haka:
A1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
A2 Irin assabad Bubakar baba yay
yo,
A1.1 Na Magaji mai Martaba ɗan Mu’azu,
A2 Irin assabad Bubakar baba yay
yo,
B1 Tsarin gaskiya Bello kai Shehu
yac ce,
B2 Bari masu son duk su maishe ka
yaro,
B 1.1 Tsarin gaskiya Bello kai
Shehu yac ce,
B2 Bari masu son duk su maishe ka
yaro,
B3 Da kyauta da ilimi da neman
dalili,
B4 Da gode ma Allah da istingfari,
B5 Da su Bello ɗan Shehu yat tsarmo kowa,
B6 Ka kai kamar Bello ka gadi Moyi,
B7 Saura ka kai inda mai Hausa yak
kai,
B6.1 Ka kai ka mar Bello ka gadi Moyi,
B7 Saura ka kai inda mai Hausa ya
kai,
Ɗ1: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
Ɗ2: Sarki Kudu Macciɗo ci maraya.
(Sa’idu Faru, waƙar Muhammadu Macciɗo
lokacin yana a matsayin Sarkin Kudun Sakkwato, ya rasu a 1995 yana Sarkin
Musulmi).
A layi na ɗan
waƙa
ana wakiltar sa da alƙalumma na [1-0], da haruffa na ABCD ban da [Ɗ] kamar yadda aka gani a misalan da suka
gabata. Har wa yau kuma ana iya wakiltar ɗan waƙa ta
jan layuka kawai. Misali:
Ɗanwaƙa mai layuka biyu ko uku
Ɗa: 1 _______________________
2 _______________________
3 _______________________
Ɗ1 ______________________
Ɗ2 ______________________
Ko ɗa mai layuka biyu
Ɗa: 1 _______________________
2 _______________________
Ɗ1
______________________
Ɗ2
______________________
Saƙonni
a ɗa na waƙa, bisa yawanci ba su shige layuka guda
biyar (5). Misali: A1, B1, C1, D1, E1, wato saƙo na ɗaya (1) zuwa na biyar (5).
A layuka ne kuma ko saɗaru
ake tunani a zuciya a gina saƙo na farin ciki ko na baƙin ciki ko na faɗakarwa
ko na tunasarwa ko na gargaɗi ko
na ilimantarwa ko na isharantarwa ko na yabawa ko na zambo ko na habaici ko na
wani saƙo da
makaɗi yake son ya gaya wa al’ummarsa a harshen
waƙar
baka. Alalmisali:
Jarora: Yara farau-farau farar tabarma,
: Farin cikin mai baƙunta,
Y/Amshi: Gagarabadon namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
(Shata, Gagarabadau; Gusau, 2018:20)
Akwai
kuma
Jarora: Ga wani ya yi ilimi babu hankali,
: Ga dai ilimi babu nutsuwa,
: An kira shi Dabtan ya amsa,
: Da ganin ƙurji sai ya yaɓa wuƙa,
Y/Amshi: Na gode wa Amadun Gaya.
(Shata, Waƙar Amadun gaya; Gusau, 2018: 23)
A lokacin da makaɗa
suke yin tunanin baɗini
na wata waƙa da
za su shirya sukan bambarta a wajen yin wannan tunani da kuma samo kalmomi na
waƙa.
i) Wasu makaɗan sukan zauna a ƙarƙashin wata inuwa kamar ta wata bishiya,
su kwanta su lulluɓe
kansu, suna tunanin wata waƙa. Alalmisali, Alhaji Ibrahim Narambaɗa, idan yana tunanin waƙa har zana tunanin nasa yake yi a ƙasa, ya dinga shata wani zani ko zane-zane
kamar zai zana wani hoto na musamman. Zai dinga zanawa a ƙasa a cikin layuka, ya dinga
yin zane-zane, yana tsara saɗaru
na waƙa.
ii) Wasu kuma makaɗan
sukan dinga jefo wasu kalmomin suna sarƙawa suna kuma zubar da wasu, suna
warwarewa, har su haɗa
kalmomin da suke bukata na waƙar. Wasu makaɗan,
kamar Salihu Jankiɗi,har
tattaka ‘yan amshinsa yake yi, suna zazzaune, idan sun jefo wasu kalmomi da ba
su dace ba. Ta haka dole ɗan
amshi ya yi taka-tsantsan da abubuwan da yake ba da tasa gudummawa.
iii) Wasu makaɗan, musamman makaɗan ƙire (kaɗaita) sukan sami saulin yin tunani ne a yayin da ‘yan amshinsa suke
maimaita kiɗa, su kuma makaɗan sukan yi shuru, suna numfasawa. A lokacin da kuma sanƙirorinsu suke ba da tasu
gudunmawa, su kuwa makaɗan
(Jagororin) suna yin shuru, suna saurarensu. Da sauran halayen makaɗan kaɗaita. A duk lokacin da makaɗan
suka yi shuru suna tunani ne a kan abubuwan da za su ƙara ƙulla waƙoƙinsu.
3.0 Sadarwa a Waƙar baka
Bayan makaɗan
baka sun gama tunanin waƙar da za su yi, sai kuma su
zo, su sadar da ita ga al’umma. Ana sadar da waƙar baka ga Hausawa a ɗaiɗaikun gidajensu da wani wuri da suka shirya
wanda ake kira dandali wato wurin yin wasannin jama’a da a yayin farauta ko noma, musamman a lokacin gayyar
noma a fadojin sarakuna da a
lokacin bukukuwan al’umma da kuma a taruka na makarantu da sauransu.
A ma’ana ta lugga ko ta ƙamus, Ƙamusun Hausa (2006: 380) ya bayyana kalmar
sada tana nufin (i)gama (ii) isar da (iii)sulhunta. Shi kuma littafin
Ƙamus
na Keɓaɓɓun Kalmomi wato Hausa Metalange (Muhammad,
1990 UPL Ibadan:104) cewa ya yi kalmar Sadarwa
da Ingilishi tana nufin Communication.
Shi ma Awde (1996:135) yana ganin kalmar Sadarwa tana nuni ne Communications
da Ingilishi.
Sadarwa a ilimin waƙar baka tana yin nuni ne game da wasu dabaru waɗanda ake amfani da su wajen isar da waƙoƙin baka ga waɗanda ake yi wa su. Ana isar da waƙoƙin baka ta hanyar rera wa mutane a wasu wurare da lokuta da yanayi.
3.1 Lokaci da Yanayi
Bisa yawancin lokuta na sadar da waƙoƙin baka na Hausa, kamar yadda aka yi
bayani a baya, akan sadar da waƙar baka ne a lokaci na safiya ko na hantsi ko na rana ko na yammaci ko na
daddare da dai sauran lokuta. Haka kuma Hausawa sukan sadar da waƙoƙin baka a ko wane yanayi na damina ko na
kaka ko na rani ko na bazara ko na hunturu ko na ɗari. Alalmisali, waƙoƙin
noma an fi yin su a yanayi na damina
wato lokacin da ruwan sama yake sauka. Haka kuma waƙoƙin ɓullowar kaka akan yi su ne da zaran
damina ta shige ko tana gab da wucewa wato an cim ma amfanin gona ka’in da
na’in da dai sauransu.
3.2 Wuraren Sadawar Waƙar Baka
Makaɗan Hausa sukan sadar da waƙoƙin da suka yi bisa maƙasudai ne daban-daban
gwargwadon waɗanda aka yi domin su. Waɗannan wurare da ake yin sadawar sababbin
waƙoƙin baka sun haɗa da:
i) Gidajen al’umma na ɗaiɗaikun mutane kamar gidajen sarakuna da
gidajen malamai da gidajen attajirai da gidajen masu jarunta da sauran gidajen
masu sana’a da kuma sauran gidaje na ɗaiɗaikun al’umma.
ii) Wurare na bukukuwa, kamar bikin aure da bikin suna da bikin kalankuwa da
bukukuwan sarauta na al’adar Hausawa da bukukuwan masu sana’o’i da bukukuwan
nunin amfanin gona da bukukuwan murna da bukukuwan da akan shirya na musamman
da sauransu;
iii) Dandali na shirya wasannin yara, tun a musamman lokacin kiɗan kalangu na ‘yan mata da na asauwara
da kuma kiɗan duma da makamantansu.
iv) Wuraren farauta, a fagagen da ake farauta a cikin dazuzzuka akan yi wa
mafarauta sababbin waƙoƙi, kuma
ana sadar da su da waƙoƙin
ne a lokacin farautar a cikin dajin farauta, musamman a yayin da alalmisali,
farauta ta rincime, ana buga in buga. Waƙoƙin da Kassu Zurmi ya yi sababbi, na
farauta ya rera su ne kuma ya sadar da su kai tsaye a fagen farauta.
v)
Wurin noma, haka abin yake wurin manoma,
musamman a yayi na gayyar noma a wata gona, kamar a Gandun Sarki, ko a gonar
wasu Sarakai, ko a gonakin taimakon sauran talakawa. Nan ake sadar da sababbin
waƙoƙi ga manoma, musamman waɗanda suke da sarautun noma kamar Sarkin
Noma da Madakin Noma da Gojen Noma da Kayayen Noma da sauran jaruman noma da
makamantansu;
vi) Wurin wasanni; Wurin wasannin al’ada a ƙasar Hausa wuri ne da ake rera sababbin
waƙoƙi a kuma sadar da su ga waɗanda aka yi wa su da sauran jama’a masu
sauraro. Wurin wasannin al’ada sun haɗa da:
-
Wasan Asauwara wadda ake yi
a kowace ranar kasuwa ta gari. Ana yin wasan Asauwara a ranar cin kasuwa ta
wani gari da yammaci ne, gab da kamar la’asar sakaliya wato kasuwa za ta watse.
A wasan Asauwara ana yin waƙoƙi ne
tsakanin matasa-‘yan maza da ‘yan mata ko zabiyi da kuma zabaya. Kuma ana yin
wasan Baura da kiɗan Baura,
a wannan lokaci ma ana rera waƙoƙi
sababbi da zimmar sadar da su.
-
Wasan kokawa
-
Wasan dambe
-
Wasan Sharu: wanda ake yi a
lokacin da Hausawa suka shaƙu da Fulani
-
Da sauran wasanni.
Wurin wasannin al’adun
Hausawa, wuri ne ma wanda ake sadar da waƙoƙin baka na Hausa.
vii)
Wuraren Tarukan Makarantu:
A lokacin da Hausawa suka sadu da Turawa,
musamman a zamanin mulkin mallaka; Turawa suka ƙagi makarantu ga Hausawa tun daga
zamanin karatun manya har zuwa karatun yara, an kakkafa wa Hausawa makarantu na
boko daban-daban.
To a yanzu a waɗannan makarantu tun daga na boko da kuma na islamiyoyi da a masallatan
addinin Musulunci duka ana yin taruka mabambanta kamar:
-
Tarukan fitar ɗalibai.
-
Taruka na aikin makarantu,
kamar tarukan gama makaranta wato Conɓocation a Jami’a.
-
Taruka na maulidi, kamar
Maulidin Annabi (SAW) da na Shaihunai da na Mujahidai da na sauransu.
-
Tarukan ga-Fili-ga-mai-doki.
-
Taruka na Musamman.
-
Da sauransu.
viii)
Wurare na Musamman
Akwai kuma wasu wurare da ake shirya
taruka na musamman domin kawai a rera waƙoƙi sababbi, a sadar da su ga mutanen da
aka yi wa su da sauran jama’a na musamman. A ire-iren wurare da muhallai na
musamman waɗanda ake nema domin a sadar da waƙoƙi sababbi sukan ƙunshi;
-
Wuri wanda aka zagaye shi,
kuma aka yi masa shuke-skuke na ciyayi da wasu hakukuwa masu ƙayatarwa, musamman masu ƙara ganin ido ko warware
kwarkwatar ido;
-
Wuri da aka tanada a matsayi
na Gadina;
-
Wuri da aka tanada a matsayi
na utel-utel ko ɗakin
taro na musamman a manyan garuruwa da birane;
-
Wurin da aka keɓe domin shaƙatawa, ko na masaukan baƙi;
-
da sauransu da yawa.
4.0 Kammalawa
Wannan takarda ta yi nazari ne game da yadda ake aiwatarwa da kuma sadarwa
na waƙoƙin baka na Hausa. An yi
bayani ne dangane da wasu matakai na aiwatarwa da kuma wasu wurare waɗanda ake sadar da sababbin waƙoƙi ga mutanen da aka yi wa su, da sauran
jama’a masu sauraron rerawarsu. An kuma nuna ba za yi tunanin waƙar baka ta Hausa ba, ba a
sadar da ita ba. Wannan ne ya tabbatar da ba za a yi tunanin a samar da waƙar baka tun daga ƙwaƙwalwa har zuwa tsantsar zuciyar makaɗi ba, sai an furta ta, a sadawar da za a
yi mata.
Haka kuma an nuna, waƙar baka tunani ne wanda ake aiwatarwa a rera cikin karin murya da kiɗa wato rauji tsararre, a kuma sadar da
ita ga al’umma domin ta zaburar da su ta kuma hankaltar da mutane a kan dabarun
tafiyar da rayuwa da kuma abubuwan da za su ba da damar a cim ma masauki mai
inganci.
Wani abin lura da shi game da waƙar baka kuma, Hausawa sun fi la’akari da ma’ana da saƙonnin ɗiyanta fiye da amon kiɗa wanda ake gwama waƙar da shi. Hausawa sun ɗauki kiɗa a matsayi na mahaɗin
rauji ne, ba zai taɓa
zuwa a sama da muryoyin da makaɗa
suke furtawa ba. Makaɗan
baka sun fi son a dinga sassauta kiɗa ne bisa ga muryoyinsu. A ko da yaushe, furucin Jagora da na ‘yan
amshinsa su ne a gaba wato a sama, duk kuwa da kiɗan da wasu Hausawa suke yi a Sitidiyo wanda yake zama a sama da muryar
Jagora ko ta ‘yan amshinsa a CD ko a memory ko a sauransu.
Akwai bukatar kuma a lura, makaɗan Hausa su ne suke tsara waƙoƙinsu
da kansu. Kuma su makaɗan
Hausa mutane ne masu fahimta, masu magana da harshen Hausa da al’adunsa, masu
zalaƙa da
hazaƙa da
hikima da balagar zance da kuma azanci na tunanin waƙar baka da shirya ta da rera ta da kuma
sadar da ita ga sauran al’ummar Hausawa da kuma waɗanda suke ji da fahimtar harshen Hausa.
Yana kuma da kyau a san, Hausawan farko su ne suke fara nazarin waƙoƙinsu na makaɗan baka, sannan sarakunan ƙasa, da gidajen rediyo da talabijin da makarantun soro wato na zaure da
makarantun boko da su kansu makaɗan
baka da sauransu. Ta haka ne nazarin waƙar baka ya zama karɓaɓɓe ga al’ummar Hausawa kuma abin yi ga manazarta a makarantun boko da kuma
makarantun zaure wato na soro da ɗaliban
ilimi da sauran masu sha’awar nazarin waƙar baka.
Alhamdu lillahi, Allah shi ne masani wanda ya zagaye komai da saninsa.
Tsira da amincin Allah, su tabbata ga Annabi Muhammadu, sallallahu alaihi wa sallama.
Manazarta
Awde, N. (1996). Hausa-English and
English-Hausa Dictionary. New York, N10016: Hippocrene Books, Incoporation,
171 Madison Aɓenue.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar
Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Funtua, A. I. & Gusau, S. M. (2011). Waƙoƙin Baka na Hausa. Katsina: Department of
Hausa, Federal College of Education and Printed by Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. & Mustapha S., Ɗanmaigoro, A. & Sabe, B.A. (2018). AStudies in the Songs of Dr. Mamman Shata Katsina. Katsina:
Department of Nigerian Languages, Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina
(UMYUK).
Gusau, S. M. (1993 & 2003). Jagoran
Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2002). Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi. Kaduna, Nigeria: Baraka Press and Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu
da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙi na Hausa: Juzu’i na Ɗaya. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2013). Tatsuniya a
Rubuce. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2014).Waƙar Baka Bahausiya (The Hausa Oral Song). Kano: Bayero University, Kano, Inaugural Lecture
Series No14. Being Professorial Inaugural Lecture.
Gusau, S. M. (2015). Abdu Karen
Gusau. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S. M. (2016). Ƙamusun Kayan Kiɗan Hausa. Kano: Century Research and Publishing
Limited.
Gusau, S.M. (2013). Mizani Tsakanin Waƙoƙin Hausa na Baka da Rubutattu’ Takarda
Wadda ya Gabatar a cikin Studies in Hausa
Language, Literature and Culture: The First (1st) National
Conference. (Yalwa, L. D.; Gusau, S. M.; Birniwa, H. A.; Abdulƙadir, M. Y. & Chamo I.
Y. (Edt). Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya and Printed by Zaria: Ahmadu
Bello University Press Limited.
Muhammad D.(Ed) (1990) Hausa
Metalanguage: Ƙamus na Keɓaɓɓun Kalmomi. Ɓol. 1. Yaba, Lagos: Nigerian
Educational Research and Deɓelopment
Council, 3, Jibawu Street.Printed by Ibadan: University Press Limited.
[1] Ita aiwatarwa wata
hanya ce wadda ake bi ana yi ko ana ƙaga waƙar baka, kuma ana shirya
ta. Akwai makaɗa waɗanda suke tsayawa gida
ko wani wuri su shirya waƙar
baka, misali Alhaji Salihu Jankiɗi, Sarkin Taushin Sarkin
Musulmi Abubakar III (1938-1988) da Ibrahim Narambaɗa, makaɗin
Sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa I(1935-1975) da sauransu. Waɗannan
makaɗa
su ne ake kira Makaɗan Shiri wato makaɗa masu shirya waƙar baka a keɓe.
Sannan kuma akwai Makaɗan
Ƙire,
wato
makaɗa
masu yin waƙa
nan take, duk inda ta faɗi rataya. Duka makaɗan
shiri da makaɗan ƙire
suna bin tsari na aiwatar da waƙar
baka, dukansu sai sun tsara waƙar
baka a jumlace a ƙwaƙwarwarsu da kuma
tunaninsu a zuciya, sannan su rera ta a matsayin sadarwa. Za a kuma wakilci
yadda makaɗan shiri suke aiwatar da waƙar baka kamar haka: +Ƙungiya +Jagora +’Y/Amshi
+Ƙulli
+Ƙari
(da muƙarrabansa)
+Gindin Waƙa
+Kiɗa.
Ana kuma wakiltar aiwatarwar makɗan ƙire a dunƙule kamar haka: +Kaɗaita
+Jagora –‘Y/Amshi +Ƙulli
–Ƙari
(da wasu muƙarrabansa)
+/-Gindin Waƙa
+/-Kiɗa
(Gusau, 2008 :448-449).
[2] Wato tsara jumloli na
baɗini
a matsayi na deep Structure. Kuma
jumlolin na baɗini su ne sauwarce-sauwarce na
mutum ko sarƙe-sarƙen zuciya waɗanda
wani lokaci akan sami dama a feɗe su a zahiri.
[3] Maganganu na waƙa, masu hikima da azanci
da kuma balaga da ake sarƙawa
ta amfani da fasaha da zalaƙar
magana.
[4] Waƙar baka ta gargajiya ita
ce waƙar
da ake aiwatar da ita, sannan a rera da ka, a kuma ta haddace da ka, a ajiye ta
a cikin ka (haddacewa). Kamar waƙoƙin Mamman Shata Katsina.
[5] Waƙar zamani kuma ita ce
wadda ake aiwatar da ita, sannan a rera ta a sitidiyo, a ajiye ta a na’urar
CD-CD ko memory ko wata na’ura ta zamani. Wasu sukan haddace ta da ka, su dinga
maimaita ta da ka. Amma duk da haka ana naɗar ta a CD, kuma a ajiye
ta a wata na’ura ta zamani irin wadda ake naɗar waƙar baka da ita.
[6] Wato ita ce ake
fassarawa da ingilishi, deep structure.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.