Wasu mutane biyu sun haɗu a tashar mota, sai ɗaya ya dinga ƙorafi a kan matsalar gida. Ƙarshe dai ɗayan ya kasa haƙuri, ya ce:
"Wai kai a tunaninka har wata matsala ce da kai?
To, saurari matsala ta ka ji,
A shekaru kaɗan da suka wuce na haɗu da wata bazawara muka yi aure. To da ma tana da ‘ya wadda ta isa aure. Jimawa kaɗan, baba na ya auri 'yar tata. Hakan yasa agola ta ta zama matar ubana, kuma uwa ta. Baba na kuma ya zama suruki na don ya auri 'yar matata.
Haka nan kuma matata ta zama surukar babana, tun da ya auri 'yarta.
Ana nan a haka, sai 'yar matata ta haihu a gidan babana. Yaron da aka haifa sai ya zama ƙanina tun da ɗan babana ne. Amma kuma ai ɗan 'yar matata ce - ka ga ke nan ƙanina ya zama jikana.
Wannan fa duk bai zama tashin hankali ba sai da mata ta ta haihu. To, yanzu yayar ɗana (matar baba na ke nan) ta zama kakar ɗana, tun da ɗan mijinta ne ya samu ƙaruwa.
Wannan ya sa babana ya zama surukin ɗana, tun da yayarsa babana ke aure.
Sai na zama surukin matar babana. Matata ta zama gwaggon ɗanta. Ɗana ya zama ɗan babana. Ni kuma na zama kakana.
Idan ba ku ruɗe ba ku yi comment a ƙasa.
Source: WhatsApp Group (Comedy Arena)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.