GAME DA GASAR RUBUTATTUN LABARAN HAUSA TA ARC. AHMED MUSA ƊANGIWA ZAGAYE NA BIYU, 2022
1. Gasa ta fara daga ranar 20 ga
watan Fabrairu, 2022 (20/02/2022), don haka masu sha'awar shiga za su tura
samfurin (tsakuren) labarinsu tun daga wannan rana har zuwa 20 ga Maris, 2022
(20/03/2022), in da za a rufe amsar samfurin. Wato kwanaki 30 kawai masu aika
samfurin labari suke da shi. A tura somin-taɓin
labari a fasalin PDF ko Word Document zuwa ga adireshin imel na
dangiwaliterary2020@gmail.com.
2. Za a tace samfuran labaran duk
da aka tura ta wancan imel a kan lokacin da aka ƙayyade, sai a fito da guda 30 daga
cikinsu, waɗanda suka
fi ƙayatarwa
da dacewa ta ƙa'idoji da dokokin wannan gasa. Labaran da suka sami nasara su
ne suka tsallake zagaye na farko kenan. Za a yi taciyar ne a tsakanin 20 ga
Maris, 2022 (20/03/2022) zuwa 4 ga Afirilu, 2022 (04/04/2022). Za a bayyana ma
duk wanda samfurin labarinsa ya ƙetare zuwa zagaye na biyu, sannan a buƙaci da
ya kawo ƙarashen
labarin wanda bai gaza a kalmomi 3000 ba, bai kuma wuce kalmomi 4000 ba.
3. Za a fara aikawa da cikakken
labarin ne tun daga 15 ga Afirilu, 2022 (15/04/2022) zuwa 15 ga Mayu 2022
(15/05/2022), in da za a dakatar da aika labaran. Kwanaki 30 kawai masu aika
cikakken labari suke da shi kafin rufe amsar labaran. Duk wanda labarinsa ya ƙetare
wannan tsakani to ba za a ɗauke
shi cikin wannan gasa ba.
4. Alƙalai za su yi aikin ba da
maki ga labarai 30 domin fito da sakamako na labarai 13 da suka fi yin zarra,
wanda za a bayyana su a ranar 5 ga Yuni, 2022 (05/06/2022). Hukuncin alƙalai
shi ne zai kawo ƙarshen amsar kowane irin ƙorafi daga masu shiga wannan gasa.
JIGOGIN LABARAN DA ZA A SHIGA
GASA DA SU.
1. Shaye-shaye da fataucin
miyagun ƙwayoyi
a tsakanin al'umma, musamman matasa.
2. Zaman banza da rashin samar wa
kai abun yi a tsakanin matasa.
Ƙarin bayani: Marubuci yana iya ɗaukar ɗaya daga cikin jigogin ya
gina labarinsa a kai, idan kuma zai iya haɗe
duka jigogin a labari guda, babu laifi a yi hakan.
WANE LABARI NE YA DACE A SHIGA
GASA DA SHI?
Kowane labarin Hausa wanda aka
gina shi a kan waɗancan
jigogi da ke baya to ya cancanta, amma dole ne a kiyaye da cewar:
-Ba a taɓa buga labarin a kowace irin kafa ta sada
zumunci ko jarida ko mujalla ko karantawa a kafafen yaɗa labarai ba.
-Ba a taɓa shiga wata gasa da shi ba kowace iri.
-Labari ya zama mallakin mai shi
ne, babu sofanen satar fusaha a cikinsa.
-Labari ya zama cikin
Daidaitaciyar Hausa tare da bin ƙa'idojin rubutunta.
WAƊANDA ZA SU SHIGA GASA.
1. Matasa daga shekaru 18 zuwa 30
ne kawai za su iya shiga wannan gasa. Don haka za a haɗo da kwafi ko hoto na takardar haihuwa ko wani
katin shaida mai ɗauke
da shekarar haihuwa a yayin aiko da samfurin labari.
2. Ba a buƙatar wata takardar karatu
ko ƙwarewa,
in dai mutum ya iya tsara labari da Hausa, to yana iya shiga a dama da shi.
3. Babu togaciyar jinsi; matasa
maza da mata kowa yana iya shiga.
4. Mutum ɗaya ko haɗaka
ta mutane biyu za su iya shiga da labari guda ɗaya,
amma kar a wuce haka.
MENE NE SAMFURIN KO TSAKUREN KO
SOMIN-TAƁIN
LABARI?
Abin da za a tura a matsayin
samfurin (tsakuren) labari daga kalmomi 500 ne zuwa 1000 na gundarin labarin da
za a shiga gasa da shi. Misali an tanadi labari mai kalmomi 3000 ko 4000, to
sai a tsakuro wani sashe na cikinsa, walau farko ko tsakiya ko kuma ƙarshe,
in da ya fi yi wa marubuci daɗi
dai, sai a tura. Idan an yi nasara shi ne za a buƙaci da a tura labarin baki ɗayansa a zagaye na biyu.
Haka ma ko da yanzu ne za a fara ƙirƙira labarin, wato babu shi a ajiye, to
iyakar kalmomi 500 zuwa 1000 kawai za a samar, sauran kuma sai a tanade su har
idan an yi nasarar zuwa zagaye na biyun sai a tura. Dole ne dai a ga tsakuren
labarin da aka aika a cikin labarin da za a aika cikakke.
Duk da haka idan akwai wani abu
da ba a gane ba, ko kuma ana neman ƙarin bayani game da wannan gasa, a nemi
kwamitin tuntuɓa ta
lambobin waya kamar haka:
08060767379
09033492760
07030319787
08109787949
08063548290
#Muhallisuturasecondedition
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.