Kisan Gillar Hanifa

Fasihi Abdullahi Abubakar Lamido ne ya shirya wannan waƙa domin jajanta kisan gilla da aka yi wa Hanifa.

Hanifa

Da sunan Jalla Sarkinmu

Salati gun Habibinmu

Iyalai har sahabbanmu 

Ina baiti cikin hammu

Ba zan iya tsai da kwalla ba 


Idan kun lura yau hakkun 

Hakika mun shiga ukku

Muna tafiya cikin tasku 

Ku lura da duk makwabtanku

Ashe jiya ba kamar yau ba 


Muna karshe na zamani

Mutane babu addini 

A zuciya babu imani

Rashin kunya a yau launi 

Kamar ba a san da Allah ba 


A dauki mutum a sace shi 

A firgita duk iyayenshi

A je a ci mar mutuncinshi

A karbi kudi ga danginshi 

Ba za a ji tausayi nai ba 


Ku dubi Hanifa yarinya 

Iyaye sun mata tarbiyya 

Ta boko har Islamiya 

Suna fatar ta dau hanya

Ashe burin ba zai cika ba


Kwatsam burinsu ya yanke 

Da jin dadinsu an dauke 

Da koyarwa mutum ya fake 

Ashe mugun hali ya rike 

Da dai ba malami ne ba


Haba Abdulmalik Tanko 

Bugaggen mallamin boko 

Iyaye sunka baka riko

Ka  bata guba cikin koko

Ka daddatsa ta kamar dabba 


Saboda bakin rashin kunya 

La'ini mai bakar aniya

Ya je ya tsaya a kan hanya 

Ya dauki Hanifa yarinya 

Ashe zai je ya bata guba 


Ganin Uncle tana murna 

Zuma a gareta ka nuna 

Ashe tarko baki ka dana 

Zatonta karimci zai nuna 

Ashe bai shirya kirki ba 


Ka karta ka datsa gawanta 

Da kanka ka tona raminta 

Ka je ka ka bunne gawarta 

Ka karbi kudin iyayenta 

Da dai ba ka tausaya musu ba 


Ina ka baro tunaninka

Da imani da rahamarka 

Ka kama mutum da hannunka 

Ka karshi ka daddatse da wuka 

Ba za ka tuna da Allah ba


Abun haushin da matarka 

Ta aure har da 'ya'yanka 

Ka mance batun mutuncinka 

Ka dau hanya ta 'yan iska 

Da dai ba ka yo tunani ba 


Ka gan ka ya salihin bawa 

Ashe keta kaka shiryawa 

Kudin banza kake yunwa 

Kawai ka zabi tabewa 

Da dai baka zabi tsira ba 


Hukunci dole zai hau ka

Fa tabbas za ka sha duka 

Kisa ita ce makomarka

Saboda bakin hali naka 

Wallahi ba za mu yafe ba 


Sanan ka bata sunanka 

Da ma sunan iyalanka 

Da tozarci ma 'ya'yanka

Irinka halinka ba shakka 

Yana jawo tsiya babba 


Idan ba a tsire wannan ba

Idan ba a mai hukunci ba 

Idan ba a ba shi horo ba 

Kasar ga ba za mu huta ba 

Bala'i ba za shi kare ba 


A kan lamarinta nai kwalla 

Ina maimaita la haula

Irin wannan kisan gilla 

Yana janyo fushin Allah 

Mai yinsa ba zai yi karko ba


Abin ya bani mamaki

A zuci har ya min miki 

Ina tafiya ya min birki 

Gaba daya ya hanan aiki 

Ba zan iya manta wannan ba 


Cikin lamarin da daurin kai

Halin wannan akwai cin rai 

Mutane sun zamo birrai 

Gaba daya ba batun tausai 

Kamar ma ba Musulmi ba 


Ilahi na yi rokonka 

Ka kai rahama ga baiwarka

Hanifatu don buwayarka 

Iyaye nata ko dukka 

Hada su da dangana Rabba 


Ka sa nitsuwa a zucinsu

Ilahu ka kwaci hakkinsu 

Ka daukaka martabobinsu 

Maye musu wanga 'ya tasu 

Tsare su da mai halin dabba


A yau jama'a mu hankalta 

Mu tashi mazammu har mata 

Mu taimaki duk iyayenta 

Mu je mu tsaya wa hakkinta 

Mu kauce wa fushin Rabba 


Ina 'yan tutiyar 'yanci 

Ku taso babu lalaci

Ku bar zance na turanci

Ku kama fada da zalunci

Ku bar zance na kankamba 


Ta can ko na hangi wani lauya 

Ba Fir'aune maras kunya 

Ya na so zai yi jayayya 

Ya kare baki maras kunya 

Ya ce wai bai yi laifi ba 


Iyaye hattara tilas

Ku lura da masu yin cikas 

Barayi su da "kidnappers"

Gama a kasarmu ba tabbas 

Ba za mu aminci kowa ba 


Mutane sun ki bin Allah 

Kawai sai dai bidar "dollar"

Ta hanyar yin kisan gilla 

Abin ya kai ga La haula 

Ba zan iya fayyacewa ba 

 

A nan zan kare maqqala 

Amir Lamido Abdallah 

Ina roko wajen Jalla 

Ka yafe min dukan zalla

Ilahal Arshi na tuba 


19 Jumada Al-Akhirah 1443

Post a Comment

0 Comments